Tuesday, September 24, 2013

010- YADDA AKE WANKAN TSARKI


Matashiya: Bayanda bayanai suka gabata akan abubuwan da suke wajabta wanka, ayanzu za mu kawo bayani akan yadda ake gabatar da waken da izinin Allah.
   Da farko dai mu sani shi wannan wanka amanace daga cikin tarin amanar dake tsakanin bawa da mahaliccinsa, saboda haka ya zama wajibi ka kiyaye wannan amanar, kuma ka himmatu da sanin hukunce hukuncen wannan wanka, domin ka gabatar da shi a yadda musulunci ya tsara, abinda ya rikice maka sai ka yi tambaya, kada kace wai kunya zata hanaka, jin kunya a irin wadannan al'amurra abune da musulunci bai yarda da shiba, kuma wani nau'ne na tsoro da shaidan yake tsoratar da mutane da shi, kuma ya sanyawa mutum kasalar da ba zai iya gudanar da cikakken addiniba. Al'amarin hukunce-hukuncen tsarki al'amarine mai girman gaske, sakaci a cikin wannan lamari yana da matukar hadari, domin kada ka manta hukunce-hukunce sallah ya ratayune fa da tsarki wacce kuma sallar nan itace ginshikin addini.
Farillan Wanka: Ka/Ki sani shi wankan tsarki yana da farillai da kuma sunnoni dama mustahabbai, amfanin saninsu shine domin duk abinda yake farillane sai baka yi shi to wankan bai yiba, amma idan sunnah ka bari wankan ya yi saidai ka rage lada. Su farillan guda biyarne;
(1) Niyya: Abinda ake nufi shine ka kudurce a zuciyarka/ki yanzu hakannan wankan janaba zaka yi ko zaki yi, ko kuma na daukewar al'ada ko biki…', wannan itace niyya, ba wadansu abubuwa ake karantawaba, niyya kuma tana da matukar muhimmanci, ai kaga shi yasa ta zo a farko.
(2) Game Jiki Da Ruwa: Ana so ka tabbatar ko ina a jikinka ya sami ruwa, kada ka manta da dukkan mahadar gaba.
(3) Cuccudawa: Ka tabbata ka cuccuda ka gurza ko ina da gwargwadon hali, kada ka manta da kasan hammata da dukkan matse-matsi…'.
(4) Tsefe Gashi: Ka tabbata ruwa ya shiga ko ina a cikin gashin kanka ko kanki, Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa: ''Karkashi ko wanne gashi akwai janaba, ku wanke gashi, ku kuma tsaftace jiki''. Abudaud, 248, Tirmizi: 106, Ibnu Maja: 597.
(5) Yi Lokaci Guda: Wannan shi ake nufi 'Muwalat' ma'ana idan ka fara to kada wani abu ya katseka sai ka kammala.
   Wadannan sune farillai ka tabbata sun cika a duk lokacin da kake wanka, kada ka manta shi wankan tsarki anayin shine da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa ken an banda mai sabulu. Ka samu idan kana da janaba kuma kanason ka yi wankan tsarki da kuma wankan zuwa wurin aiki ko kasuwa da sauransu, sai ka fara gabatar da wankan tsarki tukunna, idan ka gama sai ka sa sabulu ka ci gaba da wankanka.
Siiffar Wankan Janaba: Da farko za ka yi niyya a zuciyarka (kamar yadda bayani ya gabata). Sannan ka ce: Bismillah, sai ka wanke hannayanka biyu sau uku, sai kuma ka wanke gabanta (al'aura), hannun dama na zuba ruwa na hagu yana wankewa, sannan sai ka goge hannun naka a bango, sai ka gabatar da cikakkiyar alwala, sannan sai ka kamfaci ruwa ka zuba a kanka domin ka kosar da gashin kanka zaka yi hakanne sau uku. Sannan sai ka dibi ruwa ka kwarara a jikinka kana cuccudawa domin rowan ya kai ko ina, Shikenan ka gama.
   Kana da dama ka wuce zuwa sallah kai tsaye batare da ka yi alwalaba, sai dai idan wani abu cikin abubuwan da suke karya alwala ya faru. Kada ka manta koda kana cikin wanka alwalarka ta karye wankanka nanan ba abinda ya sameshi, sai idan kana so ka yi sallah to sai ka yi alwala.
   Banbanci Janaba Da Al'ada: Anan ana so ki gane wankan janaba da wankan daukewar jinin al'ada ko biki duk iri dayane, inda suka banbanta kadanne. Wuri na farko: Niyya, domin da ita ake banbace ibada da ibada kamar wannan da muke Magana kai. A wankan janaba mace ba sai ta kwance kitson ta ba domin hakan zai zama akwai wahalarwa sai ya wajaba ta tabbata ruwa ya shiga asalin tushan gashin kai, amma a wankan daukewar al'ada ko na biki ya halatta ta kwance kitson dake kanata, amma ba wajibi bane, a dai tabbata ruwa ya shiga ko ina wannan kuma ya shafi maza kamar yadda ya shafi mata, akwai maza masu yawan gemu da suma to dolene a tabbata ruwa ya kai ga asalin tushan gashi, a cuccuda ko ina da ina, idan mutum yana sanye da zobe ya tabbata ruwa ya shiga karkashin zoben, akyautata wanka a kuma karanta ruwa. Allah ya sa mu dace.
   Idan mace al'adarta ta dauke kuma ga wankan janaba akanta, to wanka guda za ta yi sai ta gwama niyyar kamar yadda wadansu malamai suka fada, domin wankan janaba dana al'ada duka wajibine kuma komai nasu dayane…'.
   Idan mutum yana da janaba kuma ga wankan juma'a, to anan ya samu ya shgar da wankan juma'a cikin na janaba, ba wai ya shigar da na janaba cikin na juma'aba, domin na janaba wajine, amma na juma'a ba wajibibane a mafi yawan maganganun malamai.
   Idan ka yi wankan janaba sai kuma ka manta baka yi alwalaba wankanka ya yi, kuma ka samu ka yi sallah ko da baka yi alwalaba muddin ba wani abun da ke karya alwala da ya faru, domin alwalar ta shiga wanka duk inda zaka wanke a alwala ka wanke shi a wanka, kuma kamar yadda alwala take wajibi kafin sallah haka wanka yake wajibi ga mai janaba.
   Amma idan mutum ya yi wankan juma'a to sai ya yi alwala kafin sallah.
  Ya hallata miji da mata su yi wankan janaba tare, kamar yadda aka ruwaito daga daya daga matan ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana yi.
   Ka samu ka jinkirta wanka amma sai ka yi alwala domin alwalar na rage kaifin janaba, kuma tana kara kuzari idan za'a sake saduwa.
  Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata ya bayyana a fili yadda addinin musulunci ya kula da tsarkaka da kuma lafiya, domin janaba bakaramin al'amari bace, saboda haka aka shar'anta wanka, kuma aka kawo siffar wankan daki-daki domin ka fahimci a musulunci ba'a yin abu da ka, fatammu shine Allah ya karba mana kurakurai kuma ya gafarta mana, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
    

16 comments: