Matashiya: Bayanda bayanai
suka gabata akan abubuwan da suke wajabta wanka, ayanzu za mu kawo bayani akan
yadda ake gabatar da waken da izinin Allah.
Da farko dai mu sani shi wannan wanka
amanace daga cikin tarin amanar dake tsakanin bawa da mahaliccinsa, saboda haka
ya zama wajibi ka kiyaye wannan amanar, kuma ka himmatu da sanin hukunce
hukuncen wannan wanka, domin ka gabatar da shi a yadda musulunci ya tsara,
abinda ya rikice maka sai ka yi tambaya, kada kace wai kunya zata hanaka, jin
kunya a irin wadannan al'amurra abune da musulunci bai yarda da shiba, kuma
wani nau'ne na tsoro da shaidan yake tsoratar da mutane da shi, kuma ya sanyawa
mutum kasalar da ba zai iya gudanar da cikakken addiniba. Al'amarin
hukunce-hukuncen tsarki al'amarine mai girman gaske, sakaci a cikin wannan
lamari yana da matukar hadari, domin kada ka manta hukunce-hukunce sallah ya
ratayune fa da tsarki wacce kuma sallar nan itace ginshikin addini.
Farillan Wanka: Ka/Ki sani shi
wankan tsarki yana da farillai da kuma sunnoni dama mustahabbai, amfanin
saninsu shine domin duk abinda yake farillane sai baka yi shi to wankan bai
yiba, amma idan sunnah ka bari wankan ya yi saidai ka rage lada. Su farillan
guda biyarne;
(1) Niyya: Abinda ake nufi
shine ka kudurce a zuciyarka/ki yanzu hakannan wankan janaba zaka yi ko zaki
yi, ko kuma na daukewar al'ada ko biki…', wannan itace niyya, ba wadansu
abubuwa ake karantawaba, niyya kuma tana da matukar muhimmanci, ai kaga shi
yasa ta zo a farko.
(2) Game Jiki Da
Ruwa: Ana so ka tabbatar ko ina a jikinka ya sami ruwa, kada ka manta da
dukkan mahadar gaba.
(3) Cuccudawa: Ka tabbata ka
cuccuda ka gurza ko ina da gwargwadon hali, kada ka manta da kasan hammata da
dukkan matse-matsi…'.
(4) Tsefe Gashi: Ka tabbata ruwa ya
shiga ko ina a cikin gashin kanka ko kanki, Ma'aikin Allah –Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi- yana cewa: ''Karkashi ko wanne gashi akwai
janaba, ku wanke gashi, ku kuma tsaftace jiki''. Abudaud, 248, Tirmizi:
106, Ibnu Maja: 597.
(5) Yi Lokaci Guda: Wannan shi ake
nufi 'Muwalat' ma'ana idan ka fara to kada wani abu ya katseka
sai ka kammala.
Wadannan sune farillai ka tabbata sun cika a
duk lokacin da kake wanka, kada ka manta shi wankan tsarki anayin shine da ruwa
mai tsarki mai tsarkakewa ken an banda mai sabulu. Ka samu idan kana da janaba
kuma kanason ka yi wankan tsarki da kuma wankan zuwa wurin aiki ko kasuwa da
sauransu, sai ka fara gabatar da wankan tsarki tukunna, idan ka gama sai ka sa
sabulu ka ci gaba da wankanka.
Siiffar Wankan
Janaba: Da farko za ka yi niyya a zuciyarka (kamar yadda bayani ya gabata).
Sannan ka ce: Bismillah, sai ka wanke hannayanka biyu sau uku, sai kuma
ka wanke gabanta (al'aura), hannun dama na zuba ruwa na hagu yana wankewa,
sannan sai ka goge hannun naka a bango, sai ka gabatar da cikakkiyar alwala,
sannan sai ka kamfaci ruwa ka zuba a kanka domin ka kosar da gashin kanka zaka
yi hakanne sau uku. Sannan sai ka dibi ruwa ka kwarara a jikinka kana cuccudawa
domin rowan ya kai ko ina, Shikenan ka gama.
Kana
da dama ka wuce zuwa sallah kai tsaye batare da ka yi alwalaba, sai dai idan
wani abu cikin abubuwan da suke karya alwala ya faru. Kada ka manta koda kana
cikin wanka alwalarka ta karye wankanka nanan ba abinda ya sameshi, sai idan
kana so ka yi sallah to sai ka yi alwala.
Banbanci Janaba Da Al'ada: Anan ana
so ki gane wankan janaba da wankan daukewar jinin al'ada ko biki duk iri
dayane, inda suka banbanta kadanne. Wuri na farko: Niyya, domin da ita ake
banbace ibada da ibada kamar wannan da muke Magana kai. A wankan janaba mace ba
sai ta kwance kitson ta ba domin hakan zai zama akwai wahalarwa sai ya wajaba
ta tabbata ruwa ya shiga asalin tushan gashin kai, amma a wankan daukewar
al'ada ko na biki ya halatta ta kwance kitson dake kanata, amma ba wajibi bane,
a dai tabbata ruwa ya shiga ko ina wannan kuma ya shafi maza kamar yadda ya
shafi mata, akwai maza masu yawan gemu da suma to dolene a tabbata ruwa ya kai
ga asalin tushan gashi, a cuccuda ko ina da ina, idan mutum yana sanye da zobe
ya tabbata ruwa ya shiga karkashin zoben, akyautata wanka a kuma karanta ruwa.
Allah ya sa mu dace.
Idan mace al'adarta ta dauke kuma ga wankan
janaba akanta, to wanka guda za ta yi sai ta gwama niyyar kamar yadda wadansu
malamai suka fada, domin wankan janaba dana al'ada duka wajibine kuma komai
nasu dayane…'.
Idan mutum yana da janaba kuma ga wankan
juma'a, to anan ya samu ya shgar da wankan juma'a cikin na janaba, ba wai ya
shigar da na janaba cikin na juma'aba, domin na janaba wajine, amma na juma'a
ba wajibibane a mafi yawan maganganun malamai.
Idan ka yi wankan janaba sai kuma ka manta
baka yi alwalaba wankanka ya yi, kuma ka samu ka yi sallah ko da baka yi
alwalaba muddin ba wani abun da ke karya alwala da ya faru, domin alwalar ta
shiga wanka duk inda zaka wanke a alwala ka wanke shi a wanka, kuma kamar yadda
alwala take wajibi kafin sallah haka wanka yake wajibi ga mai janaba.
Amma idan mutum ya yi wankan juma'a to sai
ya yi alwala kafin sallah.
Ya hallata miji da mata su yi wankan janaba
tare, kamar yadda aka ruwaito daga daya daga matan ma'aikin Allah –Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi- yana yi.
Ka samu ka jinkirta wanka amma sai ka yi
alwala domin alwalar na rage kaifin janaba, kuma tana kara kuzari idan za'a
sake saduwa.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da
suka gabata ya bayyana a fili yadda addinin musulunci ya kula da tsarkaka da
kuma lafiya, domin janaba bakaramin al'amari bace, saboda haka aka shar'anta
wanka, kuma aka kawo siffar wankan daki-daki domin ka fahimci a musulunci ba'a
yin abu da ka, fatammu shine Allah ya karba mana kurakurai kuma ya gafarta
mana, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Allah ya saka da Alkhairi MAlam
ReplyDeleteAmin.
Deleteya allah ya biya ku
ReplyDeleteAmin malam Alhassne.
ReplyDeleteALLAH ya saka da Alhairi
ReplyDeleteAssalam.shin acikin wankan janaba dolane sai hañnum mutun ya cuccuda ko ina?
ReplyDeleteALLAH YASAKA
ReplyDeleteAllah ya saka da alherinsa Malam, Malam hanunka zai cuccuda ko inane ko idan ya zuba ruwa ta ko Ina ya bukatar
ReplyDeleteya yabiyaka malam mungode sosai da sosai
ReplyDeleteMun gode Mallam
ReplyDeleteMasha allah
ReplyDeleteAllah yasaka da alkairi
ReplyDeleteMasha Allah
ReplyDeleteMashaa'allah
ReplyDeleteMasha Allah,Allah ya qara basira malan
ReplyDeleteMasha Allah..
ReplyDeleteAllah ya saka da Alkhairi malam..