Shinfida: Mu sani ya
'yan-uwa masu albarka, wannan addini na musulunci addinine da yake cikakken
addini ta kowanne bangare, bai takaitu ga alwala da sallaba kadai, ya shafi
kowanne bangare na rayuwa, kamar tsafta kiwon lafiya zamantakewa, kasuwanci
taimakon juna, tsare-tsaren gudanarwa dadai sauransu.
A yanzu zamu kawo bayanaine da suka shafi
tsarki, dame-dame ake yiwa tsarki? Me rashin tsarkin yake jawowa? Ya ladubban
yin tsarkin suke? Ya ake shiga makewayi? Dadai sauran wadansu batutuwa da suke
da alaka da wannan maudu'i, da fatan Allah ya yi mana jagora ya kuma fahimtar
da mu.
Abubuwan Da Akewa
Tsarki: ana yin tsarki ne daga dukkan abinda ya fito ta daya daga mafitar guda
biyu ko ma ta duka inbanda hutu (tusa). Kenan ana yiwa fitsari, bayangida
maniyyi maziyyi jinin al'ada….tsarki, kawai dai idan mutum yana da alwala sai
ya yi tusa to alwalar kawai zai sake ba sai ya dauki butu ya yi tsarki ba.
Hukuncin Tsarki: Tsarki wajibine,
saboda haka dukkan wanda dayan wadancan abubuwa da makamantansu suka same shi
to dole ya tabbata ya gabatar da ya yi tsarki.
Abinda Ake Tsarki
Da Shi: Abinda ake tsarki da ashar'ance shine ruwa mai tsarki mai tsarkakewa,
wannan shi ake kira Istinja'u. Saidai idan mutum bai sami ruwanba sai ya
yi da duwatsu a kalla guda uku, idan ya ga na ukun ya fito a bushe ba wata
laima shikenen, idan kuma akwai laima to sai ya kara su kai biyar wuturi ake
bukata (3,5,7,9…) wannan kuma ana yinshi a fitsari ko bayan gida, sannan idan
ka sami ruwa ba sai ka sake ba, wannan hukunci shi ake kira Istijmari,
ka samu ka hada duka a lokaci guda, misali idan ka yi bayan gida sai kasa
tsinke ko takarda mara rubutu sai ka share sannan sai ka biyo shi da ruwa.
Kenan ba'a tsarki da yawu (miyau).
Kada asha'afa, idan aka yi la'akari da
abinda ya fita da kuma abinda ya fantsamo maka, za'a raba tsarki zuwa gida
biyu:
(1) Tsarkin Hadasi: Shine tsarkin
abinda ya fita daga dayan mafita guda biyu, kamar fitsari, maziyyi…'.
(2) Tsarkin Kabasi: Shine tsarkake
abinda ya taba jiki ko tufafi ko kuma wuri, kuma ko wannensu baya yiwuwa said a
ruwa mai tsarki mai tsarkakewa.
Amma idan aka yi la'akari da girma ko rashin
girma za'a kasa tsarki zuwa gida biyu shima:
(1) Babba wanda ake kira
Hadasul Akbar: Ankira shi babbane domin ba'a tsarkaka daga gareshi sai an
yi wanka, kamar fitar maniyyi, ko saduwa, ko daukewar jinin al'ada ko na biki.
(2) Karami wanda ake kira Hadasul
Asghar: wanda yake tsarki ko alwala ta wadatar, kamar fitsari ko maziyyi.
Yadda ake yi: Da
farko mutum ya wanke hannunsa na hagu kafin ya sa a wurin da zai wanke, domin
hannun sa ya koshi da ruwa, sannan sai ya wanke wurin fitsari. Daga nan kuma
sai ya fara wanke wurin bayan gida musamman idan ya kaatse, ana bukatar mutum
ya wanke al'aurar sa baki dayanta musamman idan maziyyi ne ya fita.
Ladubban Zagawa
(Fitsari Ko Bayangida): Akwai tsari na ladubba da musulunci yake da su a
lokacin da mutum ya ke niyyar kewayawa, wannan zai nuna maka cewa musulunci ya
karade komai:
(1) Anbaton Allah: Ana bukatar kafin
ka shiga ka ambaci Allah domin ba'a anbaton Allah a makewayi, kuma ka nemi
Allah ya tsareka da sharrin aljanu, domin irin wadannan wurare matattarace ta
su, yace:
بِسْمِ
اَللهِ، اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ اَلْخُبُثِ وَالْخَبَائِثِ
Ma'ana: Da
sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina neman tsarinka (Ka tsareni) daga aljanu maza
da kuma aljanu mata.
Idan kuma zaka fito
sai kace:
غُفْرَانَكَ،
اَلْحَمْدُ للهِ اَلَّذِي أَذْهَبَ عَنِّي اَلأَذَى وَعَافَانِي
Ma'ana: (Ina
neman) gafarar Ka, Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya rabani
da wannan kazantar kuma ya bani lafiya.
Ka
sani ba'a shiga bayi da dukkan wani da yake dauke da sunan Allah, kamar zobe, ko carbi…'. Hakanan kuma
ba'a katse bayangida da dukkan wani abu da yake da sunan Allah.
(2) Fara Gabatar Da
Kafar Hagu Lokacin Shiga, kafar dama kuma lokacin fita.
(3) Ayi A Tsugunne: kada mutum ya yi
fitsari ko bayan gida a tsaye, sai dai idan wurin kangone ko yana tsoron
fitarin ya fallatso masa, sannan ba wanda zai ganshi ya samu ya yi a tsaye.
(4) Tabbatuwa A
Cikin Sutura: ana bukatar kada mutum ya yaye al'aurar sa tun yana tsaye,
sai ya tsugunna ya yi dab da kasa sai ya daga suturarsa, domin ba'a yarda wani
ya ga al'aurar wani ba in ba miji da mataba, amma halin ko unkula da wasu suke
nunawa na bayyanar da al'aurarsu ga kowa muddin jinsi gudane wannan baidaceba,
sai ka ji wana yace 'Ai duka mazane, abinda kake da shi ina dashi', wannan ba
koyarwar musulunci bace, haka namma mata, wannan zai kaika ka ga maza sun tube
suna wanka lokaci guda a dakin wanka guda, haka namma mata, wai sun dauka
abinda yake haram shine namiji ya ga al'aurar mace ko mace ta ga al'aurar
namiji, kai wani lokaci kana tafiya a cikin mota sai kai arba da wani gabjejen
kato yana wanka a rafi, wani kuma a gefan titi ya kafe mashin ko ya je kayan
tallansa, duk wadannan bakewawan halaye bane, mutum musulmi ya nisance su.
(5) Yafi Bada Karfi
A Kafarsa Ta Hagu: Kenan abinda akafi so shine mutum ya fi bayar da karfinsa a
kan kafarsa ta hagu.
(6) Ya Bude
Tsakanin Cinyoyinsa: kenan kada ya matse, ballantana ya sa matsattsiyar tufa
wacce idan yana fitsari na gaban ne kawai zai fita, sannan idan ya mayar cikin
wando sauran ya gangaro, Allah ya sawwake.
(7) Ya Nisanci Inda
Ruwa Yake: musulunci bai yadda mutun ya yi fitsari ko bayan gida a inda ruwa
yakeba ko kusa dashi, dan wannan zai haifar da cututtuka.
(8) Ya Rufe Kansa: Ana son wanda yake
bayangida ya rufe kansa a daidai lokacin da yake yi, domin koda wani ya yi
kuskuren ganinsa to shi bai ganshiba, abin zai zo da sauki, amma ba zaka ji
dadiba kana bayan gida ka hada ido da wani, wanda zai iya zama dalibinka ne ko
suruki ko da..,'.
(8) Kada Ayi Magana: anhana mutum yana
bayan gida yana Magana, sai dai idan akwai dalili mai kwari, kamar ka ga makaho
ya nufi rijiya ko karamin yaro…'.
(9) Kada A Tari
Iska: an hana idan mutum zai yi bayan gida a dawa (daji) an hana ya tari
iska, domin zai bsowa jama'a warin bayan gidansa, kenan sai ya yi nesa, ya kuma
duba ina iska take kadawa.
(10) Kaucewa Rami: Ba'a yarda idan za
ka yi fitsari ko bayangida ka yi aramiba saidai idan kai ka haka, domin bakasan
mekecikin ramin ba, takan yiwu akwai mugun abu.
(11) Kaucewa Wuraran
Tsinuwa: Wadannan wurare sune wuraran da mutane suke yawan tsinema dukkan wanda
ya yi musu bayangida a wurin, wadannan wurare sune:
(a) Inda mutane suke
zama su huta, jikin bangone ko karkashin bishi komadai inane.
(b) Kan hanya: Akwai
rashin mutunci mutum ya zo kan hanya ya gicciya bayangida, wannan dabi'a
musulunci bai yarda da ita ba.
( c ) Mashayarruwa:
Hakanan baya cikin karantarwar musulunci mutum ya zo inda al'umma suke diban
ruwa rafine ko wani gulbi ko gindin fanfo komadai inane ya aikata wannan
ta'asa. Wadannan wurare uku musulunci ya hana a aikata wannan danyan aiki a
wurin, domin mutum yana jawa kansa tsinuwa, Allah ya tsaremu.
(12) Nesa Da Jama'a: ana bukatar
dukkan wanda zai yi bayan gida ya yi nesa da jama'a ta yadda ba za su ganshiba
kuma ba za su ji nishin shiba, ba zai yi kyauba ace kana bayan gida mutane suna
ganinka ko suna jin nshinka, ko da a bayan bishiya ko ganyan kargo sai ka boye,
amma sau da yawa mutane suna tafiya a mota da motar ta tsaya sai ka ga kowa ya
tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a barshiba.
(13) Kada Ya
Fuskanci Alkibla: wato inda mutum yake kallo lokacin sallah, kuma kada ya
juya mata baya, wannan idan a dajine, amma idan a gidane to da sauki.
Abubuwan Da Rashin
Tsarki Yake Hanawa: kamar yadda bayani ya gabata cewar tsarki wajibine, to mu
sani idan mutum bashi da tsarki bai halatta a gareshi wadannan abubuwanba:
(1) Sallah: Bai halatta ga
wanda bashi da tsarki ba ya yi sallah nafila ko farillah.
(2) Dawafi: Kewayan Ka'aba kenan a birnin makkah,
saboda haka idan mutum yana dawafi sai ya yi tusa to dawafisa ya warware sai ya
sake alwala domin ita tusa ba'a yi mata tsarki.
(3) Sujjadar
Tilawa: Wato sujjadar da mutum zai yi ida yana karatun Alkur'ani mai girma sai
ya kai wadansu gurare, domin ba shi da tsarki, dudda malamai sun kawa juna sani
akai.
(4) Kabli Ko Ba'adi: Bai halatta ga
wanda bashi da tsarki ba ya yi kabli ko ba'adiba har sai ya yi tsarki, idan
akce kabli ana nufin sujjadar da mutum zai yi kafin ya yi sallama, amma idan
ake ba'adi to wacce zai yi bayan sallama. Idan jiya ba'adi ta kamaka sai kuma
ka manta baka yi to ya halatta ka yi ta a yanzu idan kana da tsarki.
(5) Daukar
Alkur'ani Mai Tsarki: idan mutum bashi da tsarki to sai yi tsarki kafin ya taba
wannan littafi mai tsarki.
Kammalawa: ina fatan wadannan
takaitattun bayanai sun warkar da abinda ake bukata, kuma sun nuna lallai
addinin musulunci gamamman addinine da ya shafi komai ya kuma yi bayani akan
komai, domin idan yakai bayan gida sai an nunawa mutum yadda ya kamata ya yi to
ashe wannan ba karamin gata musulunci ya yi mana, muna godiya ga Allah.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna, Jahar
Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.co
jaza kumullah bi khairin
ReplyDeleteallah ya kara muku daukaka ya kuma kare ku da mu daga dukkan sharri duniya da lahira,amin
ReplyDeleteAllah yasakawa mlm da alkairi
ReplyDeleteAllah ya saka da Alkhairi
ReplyDeleteAllah ya bada lada
ReplyDeleteHakika bayanin malam
ReplyDeleteYa gamsar.
Allah ya saka da alheri
نعم يا فضيلة الشيخ
ReplyDeleteEnter your comment...Masha Allah yasaka da alheri ameen
ReplyDeleteJazakallah Khair. Allah Ya Kara Ilimi
ReplyDelete