Wednesday, April 25, 2012

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(ASIRI) 2/7#

ASIRI: A yanzu za mu yi bayani akan abu na biyu cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Yace suna halakarwa, wannan abukuwa shi ne SIHIRI (ASIRI). Asiri shi ne abu na biyu da Ma'aiki Allah ya lissafa cikin abubuwa bakwai masu halakarwa bayan shirka da Allah. Sihiri/Asiri yana daga cikin abinda yake raba bawa da Allah cikin kankanin lokaci, mutum ya dauke dogaron shi da Allah ya sanya shi ga siddabaru ko wani mai siddabaru, wanda hakan zai iya kai mutum ya rasa addinnisa bakidaya. Idan mai karatu yana beye da tarihin musulunci ya san yadda Annabi Musa Alaihissalam ya yi fama da masihirtan zamaninsa mabiya Fir'auna, wadanda Fir'aunan ya gayyato daga ko'ina domin su kalubalanci Annabi Musa. Wannan ya nuna lalle Matsafa sunci karansu ba babbaka a zamanin Fir'auna, amma cikin taimakon Allah alokacin da suka ga Mu'ujizar Annabi Musa suka yi imani da shi sai suka watsar da dukkan kayan tsafe-tsafensu, ba irin barazanar da Fir'auna bai yi musu ba amma suka ce "Ka yi duk abinda zaka yi'' wannan ya nuna mana tarihin matsafa dadadde ne, kuma a haryanzun nan suna nan. Abinda ake so daga dukkan wanda yake musulmi shi ne ya sani Allah ya haramta tsafi/sihiri/asiri/tsubbu/bokanci/duba da dukkanin jinsin wadannan al'amurra, harma ga shi Ma'aikin Allah ya sanya shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa, Lalle Ma'aikin Allah ya isar da Manzanci. Lokaci ba zai bari mukawo dukkanin halayan matsafa ba amma daga ciki asani 'Tintiran Makaryata ne' domin missalan da suke nuna haka, al'ummar da suka zo kafin wannan al'ummar ta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Allah ya bamu bayanin su a cikin littansa mai tsarki Alkur'ani, inda a Suratul-Bakara a aya ta 101 -102 yake bamu labarin wadansu inda yake cewa " Kuma alokacin da wani Manzo (Maigirma) ya zo musu daga wurin Allah mai gasgata dukkan abinda yake tare dasu, (Alokacin da wannan manzon ya zo musu) sai wasu daga cikin wadanda aka baiwa littafi sukai watsi da littafin Allah can bayan su kamar kace basu sani ba. Suka bi abinda shaidanu suke karanta musu akan mulkin (Annabi) Sulaimana, Kuma (Annabi) Sulaimana bai kafirci ba, saidai shaidanune suka kafirce, (domin) suna koyawa mutane Asiri…'' wannan yanuna mana cewa dukkan irin labarinda ake bayarwa na cewa Annabi Sulaiman ya mulki mutane ne da aljanu ta hanyar Asiri karyane tsantsa, wadda wadancan shaidanu suka dinga rura wutarta har yakai aka kirki wadansu hatimai ake sayarwa/bayarwa ga dukkan masu mulki ko masu san mulki wai Hatimin Annabi Sulaiman! Aji tsoron Allah asani za'a tsaya a gaban Allah ranar kiyama, ko kuma hatimin Annabi Yusufu –Alaihissalam- wai maganin farin jinni. Anan koda ace wani abu ya faru sai wani boka yace aje wuri kaza a tona za'aga abukaza da kaza, kuma aka tona din aka gani a sani fa karya ne, domin zai iya tsarawa ya aiki aljanin da suke aiki tare yaje ya aikata hakan sannan yace maka/ki wanene/wance suka aikata maka/ki.. Abin mamaki da ban takaici shine kaga mutum ya yi karatu digiri na daya koma har ya kai ga digirin-digirgir amma kaga wani mutum ne yake juya shi, wanda watakila mutumin ka ganshi ba arabi ba boko, ko wani alhaji bai da dama ya sayi wani abu sai ya gayawa wai malaminsa, har abin ya shiga cikin jikin mutane idan Allah ya yi maka budi na Karin girma ko abin hannu ko ilimi da dai sauran su, sai kaji ana cewa tofa sai ka tashi tsaye, ko kuma mace ce megidanta zai kara aure, wata kila wanda yake wannan maganar wakiline (agent) na wani boka da suke hada-hada tare, Allah Ya tsare al'ummar musumli daga sharrukansu, amin. Saudayawa abinda yasa ake cewa ka tashi tsaye wai saboda magabta da mahassada, anan nake cewa addinin musulunci baibarmu haka kara zubeba, ya tsara mana hanyoyin da ake bi don kaucema sharrin masharranta. Hanyoyin Neman Tsari: Idan aka kallaci hanyoyin za'a rabasu gida biyu. Hanya Ta Farko: Adunkule wannan hanya ita ce lizimtar dukkanin abubuwan da Allah Malicci Ya yi umarni da ayi daidai gwargwado, kamar tsayar da Sallah akan lokacin a cikin kyakkyawan tsarki, da yawan nafifilin da Shara'a ta zayyana da yawan karatun Al'kur'ani mai girma ya zamana akullum kana da abinda zaka karanta ba wai sai watan Ramadan ba, da Is'tighfari da kula da zikiran bayan Salloli, da addu'o'in shiga bandaki, domin bandaki yana daga cikin wuraren da suke matattara aljanu, mafi kyawun littafi na zikiri da aka rubuta anan kurkusa shine Hisnul Muslim zaka/ki same shi awuraren masu saida littafai na bakin titi ko na cikin shaguna, an fassarashi zuwa Hausa da Ingilishi. Hanya Ta Biyu: Kayyadaddiyar addu'a: kamar Ayatul Kursiyyi Ma'aikin Allah Yace duk wanda ya karanta ta alokacin da zai kwanta Allah zai sanya mishi/mata mai kula da shi/ita har gari yaw aye. Hakanan Amanar Rasulu (Ayoyi biyun Karshen Suratul Bakara) alokacin da mutum zai kwanta bacci, addu'a ta uku itace: zaka/ki buda hannayanka/ki biyu sai ka/ki karanta Kulhuwa sai ka/ki tofa a hannuwannaka/ki sannan sai ka/ki karan ta Falaki, ita ma ka/ki tofa, sannan sai ka/ki karanta Nasi ita ma ka/ki tofa, sannan sai ka/ki shafo jikinka/ki daga sama (kai) zuwa inda ka tsaya, sannan sai ka maimaita Kulhuwa da Falak da Nas, kana tofawa a hannayan naka/ki sannan ka/ki shafa a jiki, sannan sai ka/ki sake maimaitawa, sau uku kenan. Dukkan wadannan addu'o'in ana matukar bukatarsu zaka/ki samesu cikin wannan littafin na Hisnul Muslim. Allah ya karemu daga dukkan sharrin masharranta, amin. Wadannan wadansu hirzine da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin su tabbata a gareshi – ya karantar da wannan al'umma tashi, domin matsafa ba irin hanyar da baza su bi ba domin suga sun cutar da al'umma. Nau'ukan Sihiri: Sihiri yana da nau'uka iri daban daban da akebi, kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi – ya haramta hakan: Canfi: yana cikin irin abinda al'umma ta dade tana ta'amuli da shi a matsayin wata hanya ta samun alhairi ko akasin haka, akan canfa tsuntsu ko kukansa ko mutum ko makaho ko gurgu, Ma'aikin Allah –Tsira da amincin su tabbata a gareshi – yace 'Bai daga cikimmu duk wanda ya yi canfi, ko aka camfa shi'. Zaburar Da Tsuntsaye: shima wannan wani camfi ne da ake yi da tsuntsaye, mutum idan zai yi tafiya zai fita da duku-duku zuwa inda bishiyar da tsuntsaye suke taruwa ya raka ihu ta yadda zai tarwatsasu inda suka nufa to nanan sa'a take, wannanfa tun zamanin jahiliyyah, Allah Ya tsaremu, domin wannan yana bayyanar da haukan mutum a fili. Zane a kasa: shima wannan nau'ine na Sihiri a yi zane akasa domin gano wani alheri ko sharri, wato duba. Dabo/Rufa ido: suma waddannnan manyane anau'ukan Sihiri. Annamimanci: Shima wani nau'ine na sihiri dubi yadda dauke-dauken maganganu suke canza hakikanin al'amurra ya mai da maigaskiya makaryaci ko ya maida makaryaci maigaskiya. Ahadisin AbuHurairata Ma'aikin Allah –Tsira da amincin su tabbata a gareshi – Yace '' Duk wanda ya je wajan dan-duba ko boka, ya kuma gasgatashi dangane da abinda ya fada masa, tofa tabbas ya kafircewa duk abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad –Tsira da amincin su tabbata a gareshi –)) lalle wannan ya isa halaka, domin akan haka Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya lissafa shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa. Kammalawa: Lalle wannan takaitaccan bayani ya nuna yadda Asiri yake halakar da wanda ya yi da wanda aka yiwa, da kuma yadda yake nuna mu'amala da boka ko danduba yana cikin abinda yake warwarewa mutum imaninsa da Allah, domin duk wanda ya yi imani da Allah da Kaddara ba zai aikata wannan danyan aikinba. Allah ya tsaremu, amin. 
Aliyu Muhammad Sadisu, Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda. 
Minna, jahar Neja Nijeriya. 
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965, 
ko kuma a aliyusadis@gmail.com 
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a : htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com