Kada ka manta sallah itace shisshike na biyu daga cikin shikashikan
musulunci guda biyar, itace kuma ginshikin addinin musulunci duk wanda ya
tsaida ita to ya tsayar da addini, haka kuma duk wanda yabar sallah to yabar
addini. Ita kuma sallah bata zama sallah sai idan an yi alwala, an tsarkaka
daga dukkanin najasa an gusar da hadasi da kuma kabasi, wato dukkanin najasar
da ta fito daga jiki ita ake kira Hadasi, kamar mutum ya yi: fitsari,
bayangida, maziyyi…'' shikuma kabasi shine dukkanin najasar da ta shafi
jikinka, ko tufafinka, ko kuma wurin sallah. Gusar da wadannan abubuwa na
hadasi da kuma kabasi da aiwatar da alwala, basa tabbata sai da ruwa mai tsarki
kuma mai tsarkakewa, wato kenan rowan sai ya cika sharudda biyu, na farko ya
zama mai tsarki, na biyu kuma ya zama zai iya tsarkake wani.
Allah madaukakin sarki yana cewa ''Kuma mun saukar da ruwa daga
sama wanda za'a yi tsarki da shi'' Suratl Furkan, aya ta:48.
Wannan ayar tana kunshe da hukunce hukunce da dama, daga ciki akwa:
Allah ya sanya ruwa shine abinda za'ayi tsarki da shi, ba'ayi da yawu/miyau,
abunmamaki sai mutum ya gama fitsa sai lakato yawunsa ya goga abansa, lalle
wannan ya yi nesa da makaranta. Abu na biyu kuma shine ruwan sama ruwane da
za'a yi tsarki da shi kai tsaye, abu na uku dukkan ruwan da yake a cikakkiyar
siffarsa ta ruwa babu abinda ya canza shi to za'a yi tsarki da shi.
Abubuwan Da Suke
Canza Ruwa. Abubuwan da suke canza ruwa har ya zama wannan ba za'a yi
ibada da shi ba (kamar alwala, tsarki..) abubuwane guda uku, da zarar ruwa ya
canza da daya daga cikinsu to wannan rowan ba za'a yi ibada dashiba, wadannan
abubuwa sune:
(1) Launi: Kazarar kalar ruwa
ta canza ba yadda aka san ruwaba, ko dai ya yi canza ya yi ja, ko baki, ko
kore…' to wannan rowan ba za'a yi ibada dashiba.
(2) Dandano: Idan dandanon ruwa
ya canza to wannan ruwan ba za'a yi ibada dashi ba.
(3) Shinshina: Hakana duk abinda
ya jirta kanshin ruwa zuwa wani abu daban to wannan ruwan ba za'a yi ibada da
shi ba.
Idan ruwa ya canza da yada daga cikin wadancan
abubuwa uku kenan wadannan abubuwa sun jirkita shi ta yadda ba zai iya amsa
sunan ruwaba, domin ya zama Sobo (Zobo) ko kunu ko ruwannan datti, to wannan
ruwan ba za'a yi ibada da shiba. Amma idan daya daga cikinsu ya fada cikin ruwa
amma bai canza ruwanba ta dayan wadancan fuskoki uku to babu abinda ya sami ruwan
za'a yi aiki da shi, kuma za'a ibada da shi. Wannan zai nuna kuskren da ake yi
na idan ansa hannu a ruwa ko mutum ya tara fanfo sai kasa hannu ko kasa kwano
ko buta sai ace za'a malalar da ruwan wai bashi da tsarki, ko wata dabba da ake
ci (wacce ba ta cin najasa) ta sha, ko kuma dabba ta fada rijiya ko ma mutum
sai ace wai za'a kwashe ruwan rijiyar azubar (ko guga kaza) wannan duk bai halattaba a musulunci, duk
abinda ka ga ya cikin ruwa kuma ka cire shi ka ga babu abinda ya canza rowan
kwatakwata cikin wadancan abubuwa uku ka yi shiru da bakinka aci gaba da aiki
da ruwa.
Nau'ukan Abinda
Ruwa Yake Canzawa Da Su: Canzawar ruwa da muke Magana akanshi yana da kyau
musan abinda ruwa yake da canzawa da shi lura da hukunce-hukuncen kowanne,
kamar haka:
- Da Makwancinsa: Idan ruwa ya canza
kala ko dandano ko shinshina, saboda inda yake, kamar Jarkasa, Farar kasa,
Kanwa, Kainuwa, Gansakuka… duk wadannan idan ruwa ya canza ya yi fari saboda
wurin farar kasace ko ya yi Jaa saboda wurin jarkasace ko dandanonshi ya yi
gafi saboda wurin kanwace ko tekuce ko wuraran da ake hakar mai, duk wannan
canza wad a ruwa ya yi babu abinda ya shafeka zaka yi ibadarka da shi
salin-alin alattacciyar ibada.
Kenan waccar Magana da aka yi sai idan ruwan ya canza da wani abu na
daban da ba makwancinsaba ta yadda zai iya yuwuwa a rabasu amma a inda yake
makwancinsane babu yadda za'a yi ka rabasu.
- Abu Mai Tsarki: Idan wani abu mai
tsarki kamar gishiri ko yaji ko miya ko sabulu ya zuba cikin ruwa amma
kwatakwata bai canza ruwanba to wannan ruwan za'a yi ibada dashi kamar yadda
bayanai suka gabata, amma idan sun canza ruwane to wannan rowan ba za'a yi
ibada da shi ba, amma za'a yi ayyukan gida da shi, kamar girki wanki kunun-zaki
d.s.
- Najasa: Idan najasa ta
jirkita ruwa ta daya daga cikin abubuwannan uku, to bai halatta a yi anfani da
wannan rowan kwatakwata ba za'a yi ibada da shi ba, kuma ba za'a yi wasu ayyuka
nadaban da shiba kenan kwararar da shi kawai za'a yi.
Lalle wannan ya nuna mana muhimmacin ruwa da kuma yadda addinin
musulunci ruwa shine abinda ba yi za su ibada da shi bai sa musu feturba ko gas
domin rahamar Allah ga bayinsa sai ya sanya musu ruwa kuma ya sanya shi ya zama
sinadarin rayuwa. Saidai kawai idan mutum bai sami ruwaba a lokacinda zai yi
tsarki sai ya yi Istijmari, ko zai yi alwala kuma gashi babu ruwa sai ya yi
taimama, kamar yadda bayanansu zasu zo nan gaba.
Kammalawa: Daga wadannan
bayanai da suka gabata zai nuna baka yadda addinin musulunci ya baima ruwa
kulawa ya kuma sawwake shi, kuma wannan yana nuna mana yadda ya zama wajibi mu
tashi musan hukunce-hukuncen ruwa domin idan mutum bai sani ba sai ya debi ruwan
wanki ko kuma ruwan da ya gama wanka da shi bayan ya zama sabulu ya ce zai yi
tsarki da shi, domin wasu sun dauka ruwan alwala shi ake bashi wannan
hukunce-hukunce amma shi tsarki mutum zai iya yi da ko wanne, alhali abin ba
haka bane, Allah ya sawwake amin. Allah Shi ne masani.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com