Sunday, December 22, 2013

015- SALLAH GINSHIKIN ADDINI


Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya, bayan haka; A yanzu kuma za mu fara kawowa masu karatu bayanai ne da suka shafi hukunce hukunce Sallah bayan da muka kawo bayanai da suka shafi tsarki.
   Ita dai Sallah itace tafi komai girma a musulunci akan dukkan wanda yake musulmi, kenan ta fi hajji da azumi da zakka…' hakika anshar'anta sallah a mafi kyawun tsarin ibada, kuma ita wannan sallah ta kunshi nau'ukan ibada masu tarin yawa, kama daga Zikiri da karatun Alkur'ani da tsayuwa gaban Ubangiji da ruku'I da sujjada da addu'a da tasbihi da kabbara, babu wata shari'a ta wani manzo daga daga cikin manzannin Allah da babu sallah a ciki.
   Tabbas Allah madaukakin sarki ya faralantata ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi a daran mi'iraji a sama, sabanin sauran hukunce-hukunce, kenan wannan yana nuni ga girman da wannan sallah take da shi da kuma irin matsayin da take da shi a wurin Allah.
  Hakika bayanai na ayoyi da ingantattun hadisai sun tabbatar da falalar sallah da kuma wajibcinta akan kowa, wajibcin sallah wannan sanannene a musulunci, mai littafin Iziyyah yana cewa:
 '' Dukkan wanda ya yi musun cewa sallah ba wajibiba ce ko wani abu na wajibabbunta ko wani abu na rukunan musulunci guda biyar to wannan kafirine wanda ya yi ridda, za'a nemi ya tuba tsawan kwanaki uku, idan ya tuba shikenan idan ko bai tuba ba sai a kasheshi. Wanda kuma ya yadda wajibice (ita sallar) amma ya ki ya yi za'a saurara masa har zuwa abinda zai saura na lokacinta na laruri gwargwadon raka'a cikakkiya, idan har hakan ya faru bai yi sallar ba sai a kasheshi da takobi a matsayin haddi''.
   Wannan zai kara fayyace maka yadda malamai suka yi bayanin sallah da kuma yadda suka san matsayinta a musulunci.
Mecece Sallah: A gundarin vakin larabci idan akace sallah ana nufin: Addu'a. Amma shar'ance idan akace sallah ana nufin:
'' Ibadace data kunshi maganganu da ayyuka kebantattu, ana budeta ne da Kabbara a kuma rufeta da Sallama''.
  Hakika an faralanta wadannan salloli guda biyarne a kowanne yini da dare bayan shigar lokacin ko wacce a kan kowanne musulmi wanda hukunce-hukuncen shara'a suka hau kansa.
  Allah madaukakin sarki yana cewa: '' Lalle ita sallah ta kasance akan ko wanne mumini wajibice wacce aka yiwa lokaci''. Suratun Nisa'I, aya ta: 103. ma'ana farillace alokutan da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya bayyana da maganganunsa da kuma ayyukansa. Ayoyi masu tarin yawa a cikin Alkur'ani mai garima sunyi bayanin sallah da matsayinta, duk wanda lokacin sallah ya yi alhalin yana da hankalinsa kuma ya balaga to wannan sallah ta wajaba akanshi sai dai kawai da mai al'adace ko mai jinin biki wadannan bata hau kansuba kuma ba zasu rama ba.
  Ya hau kan dukkan wanda yake kula da karamin yaro day a umarceshi da yin sallah idan ya kai shekara bakwai dudda bata wajaba akansaba, sai dai domin ya san muhimmancinta ya kuma saba da ita, kuma za'a rubuta masa shi yaron da kuma mai kula da shin lada. Yana zama wajibi ga dukkan wanda ke kula da yaro ya dakki yaron idan ya yi wasa da sallar a lokacin da ya kai shekaru goma, domin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:
'' Ku umarci 'ya'yanku da sallah tun suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dakke su akanta idan sun kai shekaru goma, kuma ku raba musu wurin kwanciya''. Abu Daud: 494, Tirmizi: 407.
   Bai halatta mutum ya jinkirta sallah daga barin lokacinta, mai littafin Akhdari yake cewa: Duk wanda ya jinkirta sallah har lokacinta ya fita to yana da zunubi mai girmangaske sai dai idan mantuwace ko bacci.
   Bai halatta mutum ya jinkirta sallah sai dai kawai wanda yake son ya hadata da wacce ta biyota idan sun kasance wadanda ake hadawanne kuma ya kasance cikin wanda aka halatta musu hadawar kamar yadda bayanai zasu zo. Amma jinkirta salloli rana akaisu dare ko sallolin dare a kaisu rana ko sallar asuba sai rana ta fito du wannan bai halattaba ta ko wanne irin hali ko saboda janaba ko najasa duk bai halattaba, mutumdai zai sallacetane alokacinta gwargwadon halinsa, amma ka ga wani a masallaci dab da rana za ta fadi yana sallah wacce yake yi to? balle ace ana biki ko aikin gona ko aikin ofis, wata da aka kaita dakin miji ta fito tana alwala zata yi sallah sai ake mamaki wai amarya zata yi sallah ba'a kammala bikiba, Tsarki ya tabbata ga Allah, wani kuma ma'aikacine baya sallar azahar da la'asar a wurin aiki sai bayan ya kammala ya koma gida sai ya hadasu duka, Allah ya tsaremu.
   Wasu kuma da jahilci ya yi musu katutu idan basu da lafiya suna kwance a gida ko a asibiti to ba'a maganar sallah wai ai ba zai iya sakkowa daga gadon asibiba ko ba zai iya canza tufafin dake jikinsaba saboda najasa ko ba wata kasa da zai yi taimama da ita ko bai sami wanda zai kawo mishiba sai ya jinkirta sallah yana ganin sai ya sami sauki sannan ya rama wani sai ya tara sallolin kwanaki hamsin ko goma gwargwadon rashin lafiyar wannan abune mai hatsarin gaske, wani kuma sabo da antsareshi a bayan kanta yana ganin ai tufafinsa akwai najasa watakilama ya yi mafarki yana da janaba, sannan shi kuma bai yi tambayaba, abinda yake wajibi ya yi sallah a gwargwadon yadda ya sami kansa awannan lokacin kuma sallarshi ta yi, ba zai sake ba. To ya mantane ai a sallar zai roki Allah ya fitar da shi daga cikin halin day a sami kansa.
  Da yawa malamai suna cewa dukkan wanda ya bar sallah don bai dauketa komaiba da kasala da yawa malamai sukace ya bar musulunci, saboda Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:
''Abindake tsakanin mutum da kafirci shine barin Sallah'' Muslim:82.
'Yan-uwa mu tashi tsaye mu kara kula da sallah mu sani babu rabo na aljanna ga dukkan wanda ya bar sallah, ba'a jinkirta sallah saboda hayaniyar biki ko aiki ko hadahadar kasuwa, sallah wajibice mu zaburar da kawunammu da na iyalammu baki daya, Allah ya karba mana ya sa mu dace, amin.
Kammalawa: Daga wadannan takaitattun bayanai ya bayyana a fili cewa sallah ba wata al'ada bace da aka gada iyaye da kakanniba da za'a yi a lokacin da aka dama, wannan ibadace da Allah yake sakankawa akanta, Allah ya yi mana jagora.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com   

014- HUKUNCIN JININ ISTIHALA ( JININ CIWO)


Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna daukene da abinda ya shafi jinin istihala wato jinin ciwo, saboda baya amsa jinin al'ada  wato jinin haila haka kuma ba amsa sunan jinin biki wato jinin haihuwa kenan, wato kenen shi wannan jinin ba jinin al'ada bane ba kuma jinin haihuwa bane saboda haka baya dauke da hukunce-hukuncensu, baya hana sallah da azumi da saduwa kamar yadda wadancan suke hanawa.
Matashiya: Domin yin kandagarki yana da matukar kyau da tsari mace ta lura da abubuwa kamar haka:
(1) Launin Jininta: Ta yi kokari ta gane launin jininta na al'ada wanne kala yake zuwa mata 'Baki ne ko Ja'.
(2) Lokacin Zuwa: Shin al'adarta tana zuwa mata ne a farkon wata ko tsakiyarsa ko karshe.
(3) Kwanakinsa: Kuma ta kiyaye kwanaki nawa yake zuwa mata a duk lokacin da take al'ada.
(4) Shinshina: Wato yanayinsa yana da karnine ko wari.
   Dukkanin wadannan abubuwa ana bukatar ta gane su kuma ta fahimcesu tun lokaci da take lafiya, -Allah ya sawwake – domin idan jini ya ci gaba da zuwa saboda ciwo da wadannancan bayanai za'a yi aiki domin a gano mata kwanakin jininta na al'ada da kuma kwanakin da suke na rashin lafiya.
Jinin Istihala: Shine ballewar jini ba'a lokacinsaba, ta wata jijiya da ake kira 'Azil'.
   Al'amari mai jinin Istihala al'amarine mai rikitarwa domin yadda jinin al'ada yake kama da jinin istihala, to idan jinin ya kasance yana zuba a koda yaushe ko mafi yawancin lokaci to a irin wannan lokaci me zata yi la'akari da shi a matsayin al'ada me kuma zata yi la'akari da shi a matsayin jinin istihala ta yadda ba zatabar azumi da sallah ba saboda shi? Domin mai jinin istihala ana mata hukunci mata masu tsarkine, kada a manta ya kandauki mace tsawan shekaru ko watanni ba al'amarine da za'a yi wasa da shi ba. La'akari da wannan bayani lalle mace mai jinin istihala tanada yanayi guda uku:
Yanayi Na Farko: Ya kasance dama tanada lissafin tsarin al'adarta kafin wannan ciwo na zubar jini ya sameta, kamar ace dama ta kasance kafin jinin istihala tana al'adane tsawan kwanaki biyar ko takwas missali a farkon wata ko a tsakiya kuma ta san adadin lokacin, to wannan zata zauna ne a matsayin mai al'ada gwargwadon yadda ta saba, sai ta bar sallah da azumi domin a wannan lokacin ana mata hukuncin mace mai jinin al'ada, idan al'adar ta dauke (Kwanakin da ta kaddarasu cewa sune na al'adar) sai ta yi wanka ta kuma yi sallah, sai ya zama  jinin da ya ci gaba da zuwa jinin istihalane ba jinin al'adaba, kamar yadda Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yace ma Ummu Habiba '' Ki zauna gwargwadon da al'adarki take zuwa, sannan sai ki yi wanka ki kuma yi sallah'', Muslim 334, hakanan kuma Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya fadawa Fatima diyar Abu Hubaish cewa : ''Ai wannan wata jijiyace, ba al'ada bace idan lokacin al'adarki ya iso sai ki bar sallah'' Bukhari 228, Muslim 333.  
Yanayi Na Biyu: Idan ya zama bata da wani yanayi sananne saidai jinin nata ana banbanceshi yana dauke da siffar jinin al'ada, kamar ya kasance baki ko mai kauri ko ya kasance yana da wata shinshina amma sauran baya kama da siffar jinin al'ada, kamar ya kasance jaa amma bashi da shisshina kuma bashi da kauri, to a irin wannan yanayi za ta yi la'akari da jinin da yake dauke da siffar jinin al'ada a matsayin jinin al'ada sai ta bar sallah da azumi…' sai kuma ta yi la'akari da wanda ba shiba jinin ciwone bana al'adaba, sannan sai ta yi wanka idan wannan jinin da yake dauke da siffar jinin al'adar ya dauke, daga nan kuma sai ayi mata hukuncin mace mai tsarki, kenan sai ta ci gaba da sallah da azumi…' ko dako jinni na zuba, kamar yadda Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya fadawa Fatima diyar Abi Hubaish:
'' Idan ya kasance jinin al'ada, shifa jinine baki akasanshi, to sai ki dakatar da sallah, idan kuma dayanne sai ki yi alwala ki yi sallah''. Abu Daud 286, Nasa'I,220, Ibnu Hibban 1348.
Yanayi Na Uku: Idan ya kasance bata da wani abu da take gane jinin al'ada da shi, kuma babu wata siffa da take banbance jinin al'ada da wanda ba na al'adaba, to anan zata yi la'akarine da mafi yawan kwanakin al'ada a kowanne wata wato kwanaki shida ko bakwai, domin wadannan kwanakin sune mafi yawan kwanakin da mata suke al'ada, wannan ko saboda hadisin Hamnatu diyar Jahash Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi:
'' Abin sani kawai wannan (Jinin ciwon) wani zungurine daga shaidan, saboda haka sai ki yi al'adarki kwana shida ko kwanaki bakwai, sannan sai ki yi wanka, idan kika tsarkaka sai ki yi sallah kwanaki ashirin da hudu ko ashirin da uku, kuma ki yi azumi ki yi sallah, yin haka ya isarmiki, haka za ki dinga yi kamar yadda mata suke al'ada''. Tirmizi: 128, Abu Daud: 287, Ibnu Majah: 627.
   Atakaice: Idan aka yi la'akari da bayan da suka gabata za mu fahimci cewa; mai yanayi tabbatacce zata yi anfani da wannan yanayin ne, wacce take abinda take banbance al'ada da jinin da ba na al'adaba za ta yi anfanine da wannan, amma wacce bata da wata alama to za ta yi al'ada kwanaki shida ko bakwai.
   Abinda kan mai jinin istihala (jiwo): Dudda cewa a hukumce mace mai jinin istihala wato jinin ciwo macece mai tsarki dudda cewa jinni na tare da ita alokaci, saboda haka za ta yi lura da abubuwa kamar haka:
1. Ya zama wajibi ta yi wankan daukewar jinin al'ada bayan wucewar kwanakin da aka yi la'akari da su a matsayin jinin al'ada.
2. Za ta wanke gabanta domin gusar da abinda ya fita alokacin kowacce sallah.
3. Za ta sanya auduga ko makamancinta a gabanta domin hana shi diga kasa, wato zata yi kunzugu kenan.
4. Za ta dinga yin al'awala a kowacce sallah, kenan ba zata yi salloli biyu da al'awala dayaba, saidai idan ramuwace, Allah kadai shine masani.
  Kammalawa: Daga wadannan bayanan da suka gabata ya bayyana a fili yadda musulunci ya kula sosai kan abinda ya shafi hukunce-hukunce jinin dake samun mata, kama daga jinin al'ada jinin biki har zuwa wannan jinni na istihala wato jinin ciwo, kuma wannan yana nuna muhimmancin al'ummar muslmi su tashi tsaye domin sanin wannan al'amari musammanma mata, kuma daga nana za mu dasa aya akan abinda ya shafi tsarki za kuma mu shiga abinda ya sahafi Sallah da izinin Allah.      
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Friday, November 8, 2013

Lum'atu Li'itiqaad (Aliyu M.Sadisu 02)

http://www.youtube.com/v/qkstRJwTayY?autohide=1&version=3&autohide=1&autoplay=1&attribution_tag=7PUFKeugZ8iwupLCX3Nvyg&showinfo=1&feature=share

Monday, November 4, 2013

Lum'atu Li'itiqaad (01)

http://www.youtube.com/v/7ijHOTkvurg?autohide=1&version=3&autohide=1&showinfo=1&autoplay=1&attribution_tag=yXIuAJkv1ltyAjNMUR5Nrw&feature=share

Tuesday, October 29, 2013

013- HUKUNCIN JININ HAIHUWA ( JININ BIKI)


Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna daukene da abinda ya shafi jerin hukunce hukuncen jinin biki wanda ake kira jinin haihua wanda yake da izinin Allah bayanshi za mu kawo a wannan karon bayan da abayanan da suka gabata muka kawo bayanai akan jinin al'ada.
Menene Jinni Biki: Jinine da yake fitowa daga mahaiffa ta sanadiyyar haihuwa. Kenan shi jinin biki jinine da yake da alaka da haihuwa, idan mace taga jini kwana daya ko biyu kafin haihuwa to shima malamai suna lissafashi cikin jinin haihuwa.
Mafiyawan Kwanakinsa: Mafi yawan kwanakin da macan data haihu zata ga jinin haihuwa malamai sun karawa juna sani, wadansu sukace kwanaki ar'bainne (40), wadansu kuma sukace kwanaki sittinne (60) kamar yadda mai Akhdari ya bayyana. Sabanin na al'ada shi kwanaki goma sha-biyarne.
  Idan mace ta haihu sai jinin bai dauke ba to zata jira kwanaki arba'in, ko sittin,  idan ya dauke a kwanakin  shikenan sai ta yi wankan tsarki na daukewar jinin haihuwa ta ci gaba da sallah da kuma sauran ayyuka na ibada, idan kuma bai daukeba to sai a nemi magani ya zama jinin ciwo sai ta yi wankan tsarki ta ci gaba da ibada, idan kuma jinin ya dauke kafin kwanakin kamar ya dauke ranar da aka yi haihuwar to annan ma zata yi wankana ta ci gaba da sallah, laifine maigirman gaske mace jinin haihuwarta ya dauke amma taki yin sallah wai sai ta yi arba'in wannan ba tsari bane na addinin musulunci, domin tsarin musulunci dazarar jinin yananan kafin kwanaki arba'in to dazarar ba za'a yi sallah ba, amma dazarar jini ya dauke ko kafin sunane to dazarar za'a ci gaba da sallah, sai a kiyaye.
  Imam Tirmizi yake cewa: Malamai sun yi ijima'i tun daga Sahabbai da Tabi'ai da wadanda suka zo bayansu (Sun yi ijima'i) akan cewa lalle mace mai haihuwa zata bar salla tsawon kwanaki arba'in sai dai idan ta ga tsarki kafin hakan (kafin kwanaki arba'in din) sai ta yi wanka ta kuma yi sallah.
   Idan mace ta yi bari sai ya zamana halittar mutum ta bayyana a barin kamar ace ga tsarin halittar ba wai gudan jini bane ya zamana kuma akwai jini day a zuba to anan tana da hukuncin jinin biki jinin haihuwa, gwar gwadon kwanakin da asune ahalittar take bayyana a ciki sune watanni ukune galibi ammadai mafi karanci sune kwanaki tamanin (80).
  Idan ta yi barin gudan jini ko gudan tsoka ta yadda halittar mutum bata bayyanaba to ba'a la'akari da wannan jinin da ya zubo, saboda haka ba zatabar sallah ba kuma ba zatabar azumiba saboda jinin domin bata da hukuncin jinin biki.
  Idan jinin haihuwa ya dauke kafin wadancan kwanakin da aka yi bayaninsu to zata yi wankane ta kuma yi sallah ko da jinin ya daukene a ranar da aka yi haihuwar, to idan jinin ya dauke kafin wadancan kwanakin sai kuma ya dawo to sai mu tsaya mu gani idan tsakani daukewar da dawowar ya kai kwanaki goma sha-biyar zuwa abinda ya yi sama to wanda ya dawodin jinin al'adane bana biki bane, amma idan tazarar batakai kwanaki goma shabiyarba to jinin da ya dawo cikon jinin haihuwane.
Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai Jinin Bikiba: Mu sani dukkan abuwan da jinin al'ada yake hanawa ayiwa mai al'ada to jinin haihuwama yana hanawa a yi wa mai biki, haka namma abinda jinin al'ada yake hanawa mai al'adar ta yi to jinin haihuwama yana hanawa ta yi, kamar: Saki, saduwa, taba Alkur'ani, zama a masallaci dadai sauransu kamar yadda bayani ya gabata a jinin al'ada.
   Haka namma kamar yadda ya halatta mai al'ada ta yi kunzugu megidanta ya shasshafata ya taba ko ina a jikinta in banda daga cikibiya zuwa gwiwa to haka namma ya halatta ga mai jinin haihuwa.
Kammalawa: Daga wadannan takaitattun bayanai da suka gabata ya bayyana a fili cewa al'amarin jinin haihuwa ba abune da za'a yi wasa akansaba, watakila hankali ya tafi kan bukukuwa suna maijego kuma bata sallah kuma ga shi jinni ya dauke, kuma mun fahimci munin tsohuwar al'adar nan na cewa maijego sai ta yi arba'in kafin ta fara sallah ashe al'amari da bashi da alaka da addinin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
    

Friday, October 25, 2013

012- HUKUNCIN JININ AL'ADA ( JININ HAILA)


Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna daukene da abinda ya shafi jerin hukunce hukuncen jinin al'ada wanda ake kira jinin haila wanda yake da izinin Allah bayanshi za mu kawo hukunce hukuncen jinin biki (wato jinin haihuwa.
Muhimmanci: yana da matukar muhimmanci sanin hukunce hukunce jinin al'ada, muhimancin bawai ya tsaya ga mata bane kadai a'a harda maza, domin abubuwa da yawa na ibada da na zamantakewa suna da alaka da jinin al'ada, misali mai jinin al'ada bata sallah ko azumi ko dawafi, wannan bangaran ibada kenan amma ta bangaren zamantakewa mai jinin al'ada ba'a sakinta ba kuma a saduwa da ita, sannan ga yadda Allah ya sanya idda da jinin al'ada, ta yadda idan aka saki mace sai ta ga tsarki uku (al'ada uku) kafin akace ta kammala idda sannan ai maganar sabon aure, to idan tana al'ada bayan kowadanne watanni shida kenan sai bayan shekara daya da rabi za'a fara maganar aure, shi yasa muka ce sanin hukunce hukuncen wannan jinni ba wai ya rataya ga mata bane kadai har da maza.
Menene Jinin Al'ada: Jinin al'ada jinine da yake fita da karan kansa daka gaban macan da a al'dance zata iya daukar ciki ba tare da ya wuce kwanaki goma sha-biyarba.
   Wannan shi ake nufii da jinin al'ada, da akace 'jinine da yake fita da kansa' kenan idan ya zamana ba da kansa ya fitaba kamar ace cinnaka ya cije ta a gaba ko kunama sai jinni ya balle mata to wannan bai zama jinin al'adaba.
   Da akace 'Ta gaba' kenan idan ya fita ta dubura ko ta hanci wannan bai zama jinin al'adaba. Da akace 'Wacce a al'adance zata iya daukar ciki' kenan idan ya fita daga wacce a al'adance ba zata iya daukar cikiba sabo da yarinta ko girma to wannan shima bai zama jinin al'adaba.
  Amma da aka ce 'Ba tare da ya wuce kwanaki goma sha-biyarba' kenan idan ya wuce kwanaki sha-biyar to bai zama kuma jinin al'adaba.
  Wadannan nau'uka da akace basu zama jinin al'adaba kenan hukuncin jinin al'ada bai hau kansuba za su yi sallah domin jinin ciwone sai a nemi magani, Allah ya sawwake.
Mafi Karancinsa: Malamai sun karawa juna sani kan mafi karancin jinin al'ada, mafi karancinsa shine 'dugo guda' kenan idan ya duga sannan ya dauke, shikenan ta yi al'ada kuma ta dauke.
Mafi Yawansa: Mafi yawan kwanakin jinin al'ada shine kwanaki goma sha-biyar kenan idan ya wuce haka to bai zama jinin al'adaba muddin ba ciki take da shiba.  
Mata Dangane Da Al'ada: anan mu sani mata suna da halaye biyar musamman idan muka yi la'akari da shekarunsu domin auna jinin da ya zo na al'adane ko bana al'ada bane, kamar haka:
1. Kasa da shekara tara: Idan jinni ya zowa yarinyar da take kasa da shekara tara to malamai sun tabbatar da wannan ba jinin al'ada bane, jinin ciwone sai a nemi magani.
2. Tara Zuwa Sama: Idan zamana jinin ya zo ne ga wacce ta cika she kara tara zuwa zamanta budurwa, to a irin wannan lokaci sai a tambayi kwararrun mata da likita domin a fayyace jinin na al'adane ko na ciwo. Kada mu sha'afa yanayin abinci da kuma yanayin zafi da sanyi da hutu da wahala suna tasiri.
3. Budurci Zuwa Sheka 50: Idan jinni ya zo daga lokacin da ta zama mudurwa zuwa shekaru hamsin (50) kai tsaye malamai sun tabbatar da cewa wannan jinin na al'adane.
4. Daga 50 - 69: Idan jini ya zowa mace a tsakanin wadannan shekaru wato daga shekara hamsin zuwa sittin da tara (50-69) to malamai sukace za'a tambayi kwararrun mata da likitoci domin sanin wannan jinin na ciwone ko na al'ada.
5. Daga 70: Idan jini ya zo bayan mace ta cika shekara saba'in (70) zuwa sama to malamai sukace wannan kai tsaye ba jinin al'ada bane.     
   Ashe tantance shekarun haihuwa ba karamin abu bane domin tuni musulunci ya gina hukunce hukunce akansu, kuma ana ginine akan tsarin kalandar musulunci, wadannan bayanai na karkasuwar mata har zuwa gida buyar kamar yadda ya gabata haka malam Adawi ya kawo a cikin littafinsa 'Hashiyatul Adawi', Allah ya ji kansa da gafara.
  Ina dada jadda cewa yanayin abin ci da da abin sha da sanyi ko yanayin zafi suna tasiri matuka, dukkan abinda ba'a mahimtaba dangane da yana yin zuwan jinni ko daukewarsa yarinyace ko babba to kamata ya yi ayi tambaya cikin gaggawa lura da yadda muka yi bayan da cewa yanada alaka da hukunce hukunce, kina yin jinkiri sai salloli su kubuce miki, kuma wannan yana nuna cewa mace da aka saka zata iya kammala idda akasa da watanni uku.
  Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin ya zama shine zuwansa na farko sannan ya tabbata cewa jinin al'adane to ta sani ta balaga, dukkanin hukunce-hukuncen musulunci sun hau kanta, idan ta yi salatin Annabi za'a rubuta bata lada idan kuma ta bari samari suna jagwalgwalata ita za'a rubutawa zunubi, ba wanda yace wai sai ta yi aure sannan za'a fara yi mata rubutu, kenan har azumi sai ta ranka wanda ta sha.
   Tabbatuwar Jinin Al'ada: Shifa abinda ya shafi jinin al'ada al'amari da Allah madaukain sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai girma, Allah yana cewa:
   ''Kuma suna tambayarka dangane da al'ada, Kace: Shidinnan cutane, ku ninci (saduwa da) mata a lokacin al'ada, kada ku kusance su har sai sun yi tsarki (Jinin ya dauke) idan suka tsarkaka (suka yi wanka) to ku je musu ta inda Allah ya umarceku, Lalle Allah yana son masu yawan tuba kuma yana son masu tsarkaka''. Bakara, ayata: 222.   
   Haka kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace; (Wannan) Wani abune da Allah ya dorawa mata 'ya'yan Adam''. Ashe ba shaci-fadin da ake cewa bane ai sanadiyyar da yasa mata suke al'ada shine wannan ganyan bishiyar da Nana Hawwa'u ta ci a gidan aljanna, amma Annabi Adam mala'ikane ya rike masa makoshi (makogaro) sai ya amayar da abin shi yasa maza basa yi. Wannan labarin bashi da kanshin gaskiya domin ayoyin Alkur'ani sun tabbatar da  Annabi Adam ya ci itaciyar.

   Shifa jinin al'ada kada amanta jinine da yake fitowa daga can cikin mahaifa a lokuta sanannu, Allah madaukakin Sarki ya haliccishi domin ya zama abin ci ga yaro a lokacin da yake cikin mahaifiyarsa domin inda zai yi tarayya da mahaifiiyar ta shi a abincin da take ci to da karfinta ya ragu sosai, sa Allah ya sanya shi ya zama abinci ga reshi, shi yasa dakyar kaga mace tanada juna biyu (ciki) kuma tana al'ada. Idan kuma ta haihu sai Allah ya zamar da shi nono jaririn yana sha amatsayin abin ci, shi yasa kadan ake samun matan da suke shayarwa kuma suna al'ada. Idan ya zamana mace bata da juna biyu (ciki) kuma bata shayarwa sai ya kasance ba inda zaii je to shine sai ya taru a mahaifarta, shine mafi yawancin lokuta yake fita a kowanne wata cikin kwanuka shida ko bakwai, ya kan karu ko ya ragu akan hakan –kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah- gwargadon yadda Allah ya tsara halittarsa.  
Karkasuwar Mata: Mawallafin littafin Akhadari ya kasa mata zuwa kashi uku dangane da jinin al'ada, kashi na farko; itace wacce ta fara, kashi na biyu kuma; wacce ta saba, sannan sai kashi na uku; mai juna-biyu (wato mai ciki), ga bayanansu kamar haka;
1. Wacce Ta Fara: Ita wacce ta fara al'ada ya zama yinta na yanzu shi ne ganin al'adarta na farko a rayuwarta, to abinda dake kanta zata zuba idone ta ga kwanaki nawa zauka kafin ya yanke, ta yadda ba zai wuce kwanaki sha-biyarba, idan ko ya wuce sha-biyar to abinda ya doru akan kwanaki sha-biyar bai zama al'adaba, kenan mafi yawan kwanakin da zata saurara sune kwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewa kafin hakan, abin nufi in ya wuce to ya zama (Isthala) cuta sai a nemi magani, anan nake cewa iyaye su kara sa ido akan 'ya'yayansu mata su dungu tuntubarsu suna fahimtar da su tun kafin lokacin ya yi domin kada lokaci ya yi yarinya ta ga jini ta fashe da kuka, ko makamantan haka, wata babbar macece amma bata san menene jinin al'adaba ita dai kawai tace tana ganin jini a wani lokaci bayan wasu kwanaki kuma sai ta daina ganinshi.   
2. Wacce Ta Saba: Abinda ake nufi da wacce ta saba itace wacce ta gabatar da al'ada sau uku a adadin kwanaki guda, misali wacce ta yi al'adar farko a kwanaki biyar, da ta sake yi sai ya yi mata kwanaki biyar da ta yi na uku shima kwanaki biyar, to wannan sai muce sunanta wacce ta saba domin ta saba akan kwanaki sanannu. Amma idan ta yi al'adar karo na farko kwanaki uku karo na biyu kuma kwanaki biyar karo na uku kwanaki shida to ba za'a kira wannan wacce ta saba ba, domin ba ta da tsayayyun kwanaki.
   Ita wacce ta saba wato wacce take da sanannun kwanakin al'ada to wadannan kwanakin sune kwanakin al'adarta, idan kwanakin suka cika al'adar kuma ta dauke sai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar da ibada, amma idan kwanakin suka cika al'adar kuma bata daukeba sai ta kara kwanaki uku, haka zata dinga kara kwanaki uku har kwanaki shabiyar su cika, misali idan al'adarta kwanaki biyarne sai kuma jinin bai daukeba a kwanaki biyar din sai ta kara kwanaki uku na sauraron daukewar sun zama takwas kenan, idan ya dauke shikenan sai wanka, idan kuma bai dauke ba sai ta kara uku akan wadancan takwasdin sun zama sha-daya idan bai daukeba sai ta kara uku sun zama sha-hudu idan bai daukeba sai ta kara kwana daaya, ya zama goma sha-biyar kenan, sai ta yi wankan kammala al'ada ko ya dauke ko bai daukeba domin kwanakin al'ada makurarsu shine kwana goma sha-biyar kuma sun cika, abinda ya ci gaba da zuwa ba sunan shi jinin al'ada sunanshi jinin cuta (Istihala) sai a nemi magani.
   Adukkan wadancan kare-karen kwanaki da aka yi inda ace bayan ta kara kwana uku na saurare sai ya dauke a kwana na daya cinkin hukun shikenen sai ta yi wankan tsarki.
   Mu sani kamar yadda bayani ya gabata shi jinin al'ada bai wuce kwanaki goma sha-biyar ga wacce ta fara da wacce ta saba.
3. Mai Juna-biyu (Mai ciki): Galibin mata masu juna biyu basa al'ada, sabo da haka da zarar mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga al'ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita .
  Idan al'ada ta zowa mace mai junabiyu to ida cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin al'ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan kuma cikin ya kai watanni shida to al'adar zata iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da biyar, kada a sha'afa wurin tuntubar likita idan ana da juna biyu kuma aka ga jini.
  Tanbihi Na Daya: Idan mace jini yana mata wasa wato ya zo yau gobe sai kuma ya dauke bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abinda zata yi anan shine, ta tsaya ta yi karatun ta natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo sune kwanakin al'ada sai kuma ta ware kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki domin da hakane zata cika kwanakinta na al'ada, misali kwanaki tara; sai ya zo a rana ta farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da ta tara. To anan sai muce ta yi al'adar kwana biyar a cikin kwanaki goma, wannan matar ita ake kira (Al-Mulaffiqa) alarabcin mata masu al'ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da dawowarsa to na biyun zai zama sabon jinine kenan, ba na dane ya dawaoba.
   Alamar Daukewar Jinin Al'ada: idan jinin al'ada ya dauke akwai alama da shara'a ta sanya domin ya zama shine manuniya akan cewar al'adarki ta dauke, wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, sune kamar haka:
1. Bushewar Gaba: Abinda ake nufi anan shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gabanta ta fito da shi busasshe ba wani jini a tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata al'adarta ta dauke.
2. Farar Kumfa: wannan wani ruwane fari mai laushi da yake zuwa karshan al'ada, idan mace ta ga irin haka a karshan al'adarta to ta sani ta kammala.
   Wadannan alamomi su suke nuna daukewar al'adar mace, idan mace bata taba ganin al'adaba sai a wannan karon sai ta fara ganin bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki ba sai ta jira farar kumfaba, amma idan wacce ta saba ganice sai ta ga bushewar gaba to malamai sukace zata zata dan saurara kadan domin jirar faran kumfa, amma jinkirin ba zai kai ga fitar zababban lokacin sallah ba.
  A dunkuledai kowanne daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu alokaci gudaba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai ta yi wankan tsarki domin ta ci gaba da ibada, domin idan bata yi wankaba ko da jinin ya dauke mijinta ba zai sadu da itaba ba kuma zata yi sallaba, da dai sauransu.
   Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga-diddiga bayan daukewar jinin al'ada to kada ta damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jinine, amma idan a karshen jinine to wannan ba komai, Ummu Atiyyah medakin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) tace: ((Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi-fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani abune)). Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa'i, Hadisi Na: 368, Ibnu Majah Hadisi Na: 647, Darimi Hadisi Na: 865.
  Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar asuba, amma ba'ace tat shi cikin dareba domin ta duba.
   Idan mai al'ada ko mai biki (jinin haihuwa) ta ga tsarki kafin rana ta fadi to sallar azahar da la'asar sun hau kanta, hakanan kuma idan ta ga tsarki kafin hudowar alfiji to tabbas za ta yi sallar magariba da lisha.
Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai-al'adaba:
  Anan za'a lissafa abubuwan da basu halatta mai al'ada ta yi su ba ko ayi mata ba, wadannan abubuwane guda goma:
1. Sallah: Bai halatta mai al'ada ta yi sallaba farilla ko nafila, idan kuma tayi ta yi ba'akarba ba sannan kuma ta yi laifi, sannan bayan ta kammala al'adar ba zata rama sallolinba.
 2. Saki: Baya halatta matar da take al'ada a saketa, wannan ya sabawa karantarwar musulunci, saboda haka koda yana son ya saketa to ya bari sai ta kammala al'ada kafin ya sadu da ita sai ya saketa, amma idan ya saketa tana jinin al'adar to sakin ya yi amma za'a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin bai kai ukuba.
3. Dawafi: Bai halatta mai al'ada ta yi dawafin Ka'abah, amma zata yi sauran dukkan abinda maniyyaci yake yi, kamar tsaiwar Arafah da kwanan mina dana muzdalifa da jifa da Labbaika, da daidai sauransu.
 4. Zama A Masallaci: mai al'adah ba zata zauna a cikin masallaciba, domin sauraron karatu ko karantarwa ko taro da dai sauransu.
 5. Azumi: Bai halatta mai al'ada ta yi azumi na farilla ko na nafila, idan ta yi kuma bai yiba, saboda haka zata lissafa azumin da ta sha bayan watan ya wuce sai ta ramasu. Ba'a ajiye azumi domin tsammanin gobe al'ada zata zo, amma dazaran ta zo to dazaran ba azumi, dazaran bata zoba to dazaran akwai azumi, ko da kin ji tafiyar jinin ajiki amma bai fitoba to biki fara al'adaba, sai ya fitane za'a fara lissafi.
 6. Taba Alkur'ani: mai al'ada bata taba kasantuwarsa littafi mai tsarki sannan kuma ita bata da tsarki, amma wannan bay a hana idan ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa wuri.
 7. Karatun Alkur'ani: mai al'ada bata karanta Alkur'ani, duddacewa wadansu malamai suna ganin ya halatta ta karantashi da ka domin kada ta manta sabanin dauka.
 8. Saduwa: Bai halattaba saduwa da mace tana al'ada, idan ta ki yadda da mijinta  ya sadu da ita domin tana al'ada ba za'ace ta sabawa Allahba asalima ta yi biyayyane ga reshi, bai halatta a sadu da mace tana al'adaba har sai al'adar ta dauke kuma ta yi wankan tsarki, kenan koda al'adar ta dauke amma batayi wankaba to bai halatta a sadu da itaba. Ya halatta miji ya taba duk inda yake so a jikin matarsa alokacin da take al'ada bayan ta yi kunzugu inbanda daga cikbiyarta zugwiwarta wannan kan bai halattaba har sai jinin ya dauke kuma tayi wanka, hakanan itama ya halatta ta taba ko ina a jikinsa duk da tana al'ada.       
9. Tabbatar Da Rashin Tsarki: Al'ada tana tabbatar da wacce take da ita bata da tsarki.
10. Wajabta Wanka: Al'ada tana wajabta wanka, wato dukkan matar da ta yi al'ada kuma al'adar ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta. Shi kuma bayani akan abinda ya shafi wankan tsarki tuni ya gabata, da fatan Allah ya yi mana jagora ya karba mana ayyukammu.
Kammalawa: Daga wadannan bayanan da suka gabata ya bayyana a fili cewa lalle jinin al'ada bakaramin hukunce-hukunce yake da shi ba, kuma lalle idan aka kallaci yadda ake sakaci tsakanin maza da mata akan abinda ya shafi wannan al'amari to lalle abin yanada ban tsoro. Anan gaba abinda zai biyo baya shine hukuncin jinin biki wato jinin haihuwa.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Thursday, October 3, 2013

011- TAIMAMA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA


Matashiya: Hakika Allah mai girma da daukaka ya shar'anta tsarkaka daga hadasin da yake karami ko babba kafin gabatar da sallah, wannan tsarkaka kuma bata yiwa sai da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, gabatar da wannan tsarki da kuma rowan da aka ambata shine abinda yake wajibi muddin akwai dama, sai dai akan sami wasu lokuta da ake rasa rowan kwatakwata ko kuma ga ruwan amma idan aka yi alwala da shi ko wanka za'a rasa wanda za'a sha, koma yin anfani da rowan zai haifar da wasu cututtuka da dai sauran wasu dalilai shar'antattu da zasu hana amfani da ruwan to akan haka aka shar'anta Taimama domin sawwakewa al'umma, da kuma dauke dukkan wata damuwa akan hakan.
Mecece Taimama?: Taimama itace; Shafar fuska da hannaye a wuri mai tsarki ta yana yi kebantacce.
  Kenan ba kowacce shafar fuska da hannu ne yake zama taimama ba, sannan kuma ba a kowanne wuri ake yi ba, sannan ba yadda aka ga dama ake yi ba.
Tabbatuwar Taimama: Taimama ta tabbata daga haske na Alkur'ani da kuma Hadisan ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allan su tabbata a gareshi- kana da ijima'in malamai.
Tabbatuwarta A Kur'ani: Allah ya yi bayanini shar'antuwar taimama a cikin Alkur'ani mai girma a Suratun Nisa'I, aya ta 43, da kuma Suratul Ma'idah aya ta: 6. amma ayanzu zamu kawo bayani akan ayar suratul ma'idah, wato aya ta shida kenan, Allah madaukakin sarki yana cewa:
   ''Ya ku dukkanin wadanda su ka yi imani! Idan kun tashi za ku yi sallah to ku wanke fuskokinku da kuma hannayanku zuwa gwiwar hannu, ku kuma shafi kawunanku  kuma ku (wanke) kafafuwanku zuwa idon sawu, idan kun kasance masu janaba to ku tsarkaka (ku yi wanka), idan kuma kun kasance marasa lafiya ko kuna kan tafiya ko kuma daya daga cikinku ya yi bayan gida, ko kuma kun taba mata (janaba) baku sami ruwa ba to sai ku yi taimama a wuri mai tsarki sai ku sahfi fuskokinku da kuma hannayanku daga wurin, Allah baya nufin ya sanya mukun kunci ko kaka, saidai yanason ya tsarkake ku kuma domin ya cika ni'imarsa a gareku domin ku gode masa. (Ma'idah, aya ta:6).
  Wannan ayar babbar ayace, ta kunshi hukunce-hukuncen Alwala da abinda yake karyata, da kuma janaba da yadda ake wankan tsarki, da kuma taimama da abinda ke sawa ayi taimamar da kuma yadda ake yenta, sannan da manufar da tasa Allah ya shar'anta taimamar, Allah muna gode maka, akan wannan ni'ima.
Tabbatuwar Taimama A Hadisi: Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- yace: ''An bani abubuwa biyar da ba'a ba wani ba kafin ni; An taimakamin da tsoro (ma'ana sanya tsoronsa a zukatan makiya) na tafira tsawan wata guda, kuma an sanya min kasa ta zama wurin sallah da kuma tsarki, duk inda wani mutum daga cikin al'ummata sallah ta riskeshi to ya yi sallar shi'' a wata riwayar ''To anan inda yake masallacinsa yake da kuma abin tsarkinsa''. Bukhari, Hadisi na: 335, Muslim Hadisi na: 521.
  Wannan hadisin ba karamin hadisi bane, domin ya yi bayanin gatan da Allah ya yi wa wannan al'ummar gatan da bai yiwa wata al'ummaba, a ciki ya ambaci cewa an sanya masa kasa ta zama wurin sallah, al'ummomi da suka gabata basa sallah a ko ina sai a inda aka kebe musu, amma mu ko atsakar da ji ne sai ka tsaya ka kallaci alkibla ka yi sallar ka, kuma yace an sanya masa kasa ta zama wurin tsarki, za ka yi tsarki da ita kamar yadda bayanai suka gabata a baya akan istijmari, sannan kuma zaka yi taimama da ita kamar yadda ake kawo bayani a yanzu haka.
  Taimama matsayine na musamman da wannan al'umma ta kebantu da ita, Allah bai sanya taimama ga wata al'ummaba kafin wannan al'ummar domin yalwatawa ga wannan al'ummar.
Ijima'i: Malamai duk sun yi ijima'i akan tabbatuwar taimama.
  Ita taimama tana tsayawane matsayin ruwa a shar'ance lokacin da rowan ya faskara, dukkan abinda kasan ba'a yi said a ruwa to ana yi da taimama, kamar sallah, dawafi, karatun Alkur'ani da dai sauransu.
  Taimama Tana Tsayawa Matsayin A Lokuta Kamar: Kenan anan za'a lissafo abubuwan da suke sawa a yi taimama, domin kada kabar sallah ta wuce maka kace ai baka sami ruwa bane wannan ba zai sa ka sami sassauci ba domin sabo da hakan aka shar'anta taimama, wadannan wurare sune kamar haka:
1. Rashin Ruwa: Kasan cewa suna cikin tafiya ko suna zaune a gida sai suka rasa ruwa sun nema iya yadda za su iya basu sami ruwan ba, to anan tunda sun nema basu samu ba ba za su bari lokaci ya wuce ba su ce sai sun je gida sai su gabatar da taimama su yi sallar su, ko da a cikin su akwai masu janaba, ko matan da al'adar su ta dauke. Kuma da zarar sun gabatar da wannan taimama to sun sauke wajibinsu ko da an sami ruwa ba za su sakeba. Wato shi addinin musulunci gwargwadon yadda ka gane shi a yadda yake gwargwadon yadda yake da sauki a gareka.
2. Ruwan Ba Zai Isaba: Idan kuma a tare da ku akwai ruwan amma kuna da matukar mukata domin shi zaku sha da shi zaku yi girki ko shi za ku ba dabbobi ko shi kuke sawa a injin mota ta yadda idan ku ka yi alwala da shi ba zai ishe ku wadancan bukatuba, asalima za'a iya tagayyara, ko kuma ga ruwancan kuna hangowa to amma miyagun namun dajine a wurin ko kuma matattarar barayine wurin to anan fa hukunciku duka shine wadanda basu da ruwa, saboda haka wadanda suke dashi kadan domin bukatunsu sai su sha su yi taimama.  
3. Cuta: Idan ga ruwan, amma ka ji tsoron cuta a jikinka ko kuma ciwon zai sami jinkirin warkewa, sai ka yi taimama.
4. Rashin Motsi: Idan ya zamana yana fama da rashin lafiya amma zai iya alwala sai dai ba zai iya motsawaba domin ya debo ruwan alwalar kuma bai sami wanda zai debo mai ruwanba ko babu wanda zai yi mishi alwalar kai tsaye sai ya yi taimama.
5. Sanyi: Idan yana matukar jin tsoron sanyi idan ya yi anfani da ruwa, kuma ga shi yana son yin alwala ko wankan tsarki ga shi bai sami abinda zai dumama ruwanba to kai tsaye sai ya yi taimama.
    
   Wadannan bayanan suna nuna mana cewa rashin lafiya bata dauke sallah, domin koda ba zai iya alwalaba saboda tsoron sanyi ko jinkirin warkewa ko dai daya daga cikin abubuwan da aka ambata to sai ya yi taimama, abin takaici shine sai ka ga dazarar mutum bashi da lafiya to abu na farko da zai ajiye shine sallah, inda zaka je gai dashi kace ya yi sallah kuwa sai ka ga ana kallonka ana nuna maka halin da yake ciki kamar kai baka da tausayi, inda kuma zaka dan shafa masa dari ko dari biyu sai ya miko hannu, Allah Ya sawwake.
   Hakanan inda mutum za'a tsare shi, ba zai bada hanzarin ai lokacin da suke a tsare ba'a barinsu su yi alwala to ba sai ya yi taimamaba.
   Idan mutum yana da ciwo a gabban alwalarsa kuma ba zai cutuba idan ya shafa hannunsa akan bandejin ko karan dorin to sai ya yi alwalar idan ya zo wurin sai ya shafa kawai ba sai ya wankeba.
  Idan galibin jiki ya zama ba lafiya kamar ya zama ba inda ya raje sai hannu ko kafa to anan kai tsaye sai ya wuce zuwa taimama. Shi bayani akan abinda ya shafi wanke wasu gabobi sannan ayi shafa akan wasu gabobi sabo matsanancin rashin lafiya day a shafi gabban alwala ko taimama darasine mai zaman kansa, a littafin Iziyyah shine fasali na gwoma sha-daya, malamin ya ware fasalinne domin bayanin cututtuka da zasu sami gabban alwala, kuma ya kawo fasalinne bayan ya kammala bayani akan taimama a fasali na goma, Allah ya saka masa da alkhairi.
   Ya halatta ka yi taimama a duk inda yake doron kasa kamar inda yake; rairayi ko jangargari ko dutse ko kamfa ko kasar gishiri ko ta kanwa ko inda yake dusar-kankarace.
Siffar Taimama: Yadda ake gabatar da taimama shine; zaka wara yatsun hannayanka biyu ne sai ka buga a kasa, sannan sai ya shafi fuskassa da cikin tafikan hannunsa, sai kuma ya shafi hannayansa zuwa wuyan hannu (Ku'i), zai yi ko kari ya tabbata ya game ko'ina na fuskarsa a lokacin da yake shafar kar ya manta da karkashin gemu da kuma hannayansa, idan yana da zobe sai ya cire domin shafar ta game ko ina, idan lokacin da ya shafo kasar kwai yayi ko kura sai ya karkade, ba'ace dole sai mutum ya sa kasa a fuskarsa ba.
   Idan kuma ya ga dama sai ya yi shafar sau biyu to tafarko sai ya shafi fuska da ita ta biyun kuma ya shafi hannuwa zuwa gwiwar hannu.      
  Za'a ko yi yadda ake taimamane da sauran ibadu a gaban malamai, karantawa anan kadai ba zata wadatarba, su kuma malamai su ji tsoron Allah su koyawa al'umma wadannan ayyuka a'aikace, sawa'un makarantun islamiyyune ko malaman da suke koyar da darussan addinin musulunci a cikin jami'o'i ko a kwalejojin ilimi, ko kuma malamai da suke karantarwa a cikin masallatai, kada ka taba jin dan ka karantar da baki kowa ya gane, a'a sai ka yi a aikace, kada ka manta sai da ma'aikin Allah ya koyawa sahabbansa wadannan ayyuka a aikace, ka ko san idan saurin ganewane sun fika sun fi daliban da kake koyarwa.
 Abundake Bata Taimama; Taimama tana baci da duk abinda yake bata alwala babbane ko karami, kamar tusa fitsari…. Fitar maniyyi, jinin al'ada, sannan kuma idan uzurin da ya sa aka yi taimama ya gushe to taimama ta gushe.
  Wanda ya rasa ruwa kuma ya rasa kasar da zai yi taimama akanta, ko kuma ya kai wani halin dab a zai iya taba ruwaba ko kasa to shi wannan zai yi sallar ne a yadda ya sami kansa, ba tare da alwala ko taimama ba, domin Allah bai dorawa rai sai abinda zata iya.
  Duk wanda ya yi taimama domin ya yi sallar farillah to ya halatta ya yi nafila da wannan taimamar. Idan mutum ya yi taimama ya yi sallah da ita sai kuma lokacin wata sallar ya yi kuma gashi ba abinda ya karya mishi taimama to sai ya sake wata taimamar kafin ya yi sallar, domin abin nufi anan sai ya sake neman ruwa idan bai samu ba to sai ya yi taimama.
   Idan mutum ana binshi wadansu salloli da ya manta da su to ya samu ya sallacesu da taimama guda.
Kammalawa: wannan kadan kenan daga cikin abubuwan da suka shafi taimama da fatan sun wadatar, kuma za'a koma ga malamai.    
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com