Sunday, March 24, 2013

001- IBADA DA HUKUNCI


Gabatarwa: Dasunan Allah Mai Rahama, mai jinkai, tsira da amincin Allah ya tabbata ga Ma'aikin Allah Annabi Muhammad. Awannan lokacin da izinin Allah mai kowa mai komai muna fatan kawo wadansu bayanaine na daban bayan kammala waccan doguwar salsala da take dauke da wadansu abubuwa bakwai masu halakarwa. Wannan bayanai kuwa matashiyarsu itace: Ibada Da Hukunci. Fatammu shine kawo bayanai filla-filla kan abinda ya shafi hukunce-hukncen nau'ukan ibada kamar tsarki da rowan da ake tsarki da shi, da kuma bayanai akan abinda yake najasa da alwala da abinda ke bata alwalar ta taimama da wankan tsarki da abinda ke sa wankan, da huknce hukuncen sallah, kamar sharuddan sallah lokutanta kiran sallah, salloli na farilla nafilfili, tada ikama, kabaliyya da ba'adiyyah, hukunce-hukunce masallaci, sallar kasaru. Hakanan muna fatan kawo bayan kan Azumi da Hajji d.s…gwargwadon abinda Allah Ya hore, da fatan zamu tsaya musan Ibadar da Allah ya dora mana kuma musan hukunce hukuncen wannan ibadar, Allah Ya yi mana jagora, amin summa amin, asha karatu lafiya.
Ibada: Ma'anar ibada itace ''Gamamman sunane da ya tara dukkanin abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi, na zantuttukane ko na ayyuka na filine  koko na zuciyane''.
Kenan ibada tana shiga ayyukan gabbai kamar: Alwala, zakka Hajji, kamar yadda maganama ke shiga cikin ibada kamar: Karatun Kur'ani, Salati ga Ma'aikin Allah, na bayyane kamar tsarki dana boye kamar niyya.
Hukunci: idan akace hukunci shine hukunce-hukuncen da shara'a ta na cewa abu kaza: Wajibine, ko Haramunne, ko kuma Mustahabbine ko Makaruhine, ko kumama Halasne.  Wadannan abubuwa biyar su ake kira da Ahkamus Shar'iyyah At-Takleefiyyah. Kuma ga bayanansu da Shara'a ta yi:
(1) Wajibi: Shine abinda ana bada lada ga duk wanda ya aikata shi akan an'umarceshi, kuma ana azabtar da duk wanda ya barshi. Kamar salloli na farilla da tsarki da Azumin Ramadan…'
(2) Haramun: Shine abinda idan mutum ya aikata shi za ayi masa ukuba, idan kuma ya barshi yana da lada. Kamar: Sata, Zina, Luwadi, Shangiya.
(3) Musthabbi: Shine idan mutum ya aikata za'a bashi lada, amma idan bai aikataba babu komai akansa. Kenan aikata shi ya fi. Kamar daga hunnuwa a lokacin kabbarar harama, kamar karatun mamu alokacin da liman yake karatunsa aboye.
(4) Makaruhi: Shine abinda idan an barshi akwai lada, idan kuma an aikata babu ukuba, kenan barinshi ya fi. Kamar susa ana sallah da dan waige kadan. 
(5) Halas: Shine abinda idan an aikata babu lada akan aikatshin da aka yi, hakanan idan an barshi babu lada akan barin na shi da aka yi, kenan sai an kallaci niyyar da tasa aka yi ko aka bari akan haka za'a sami lada ko zunubi. Kamar bacci, idan mutum ya yi bacci da wuri domin ya tashi cikin dare ya yi nafilfili da addu'oi to wannan yana da lada, hakanan idan ya yi bacci domin yaba jikinsa hakkinsa, tunda yazo a hadisi jikinkama yana da hakki, to duk wadannan akwai lada. Idan kuma mutum ya yi bacci alokacin da yasan indai ya yi bacci a wannan lokacin took zai iya rasa sallah to ba'ayarda ya yi bacci a wannan lokacinba, shi yasa aka hana bacci tsakanin Magariba da Lisha.
   Wadannan sune hukunce hukunce da sune ake hukunci, kuma tananne ake kaiwa inda za'a yi hukunci akan ibadar mutum ta yi ko bata yi ba, kenan dole mu tashi tsaye musan yadda za mu yi ibadarmu yadda Mahaliccimmu ya umarcemu mu yi ta harshen Annabinsa Annabi Muhammad -Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, ka da mu yi sakaci mu da iyalammu da kannemmu da yayyammu… Allah ya yi mana jagora amin.
  Lalle tsayawa akan a fahimci wannan addini na musulunci yana cikin mafiya kyawun ayyukan da Allah ke so, kuma alamace ta Allah na son mutum da alheri, kamar Yadda Ma'aikin Allah -Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yake cewa ((Duk wanda Allah yake nufinshi da alheri sai ya fahimtar da addi)). Bukhari ya ruwaitoshi a hadisi na:71, Muslim kuma: 1027.
Allah madaukakin sarki yana cewa: ''Shine wanda Ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin da yake na gaskiya'' Suratut- Tauba: 33. Shiriyar Itace ilimi mai anfani, Addini na kwarai kuwa shine: Ayyuka masu kyau.
  Babu wata tantama tabbas yakama kafin mutum ya himmatu wurin aikata kowanne irin aiki yasan hanyar day a kamata yabi domin aikin na shi ya zama ya yi shi daidai, ta yadda zai yi ya sauke aikin da aka dora masa wanda zai zama sanadiyyar tseratar da shi daga wuta da kuma shigarshi aljanna.
Akan Haka Mutane Sun Kasu Kashi Uku:
(1) Wadanda suka hada ilimi mai anfani da kuma aiki na kwarai. Wadannan sun rabauta duniniya da lahira, don Allay ya yarda da su.
(2) Wadanda suka san ilimi mai anfani amma basu yi aiki da shiba, wadannan sune wadanda Allah ya yi fushi da su.
(3) Wadanda suke aiki tukuru amma ba tare da ilimiba, wadannan sune batattu.
Kammalawa: Daga takaitaccan wannan jawabi ya bayyana agaremu ashe ibada ta ka su kashi-kashi, akwai ta kabbai, akwai ta zuciya akwai kuma ta zahiri, kuma ita ibada hanyace da mutum zai sami yarda Mahaliccinshi domin yanayin abinda Mahaliccin ya yarda dashi, amma duk wannan zai same su ne idan mutum ya bi karantarwar farin jakada Ma'aikin Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, kin yin aiki da karantarwa yanasa Allah ya yi fushi da mutum, kamar kuma yin aiki ba akan karantarwarba yana sa mutum ya kasance cikin batattu. Allah Ya tsaremu.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna, Jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

2 comments: