Cin Dukiyar Maraya: A yanzu za mu yi
bayani akan abu na biyar cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar
da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu shine Cin Dukiyar Maraya.
Maraya: shine wanda
mahaifinshi ya rasu kafin ya balaga ya yi hankali. Ma'aikin Allah ya ja kunnen
al'umma sosai da sosai akan kulawa da hakkin maraya da tausaya masa, da
fadi-tashi akan al'amuransa kuma ya bayyana falalar hakan awurare dadama. To
amma abin takaici sai awayi-gari dan abinda uba ya mutu ya barwa 'ya'yansa sai
wani/wasu subi takan wannan abinda aka bari kafin dan lokaci ane meshi a rasa.
Allah madaukakin sarki yana cewa dangane da masu cin dukiyoyin marayu da
zalunci: ''Lalle dukkanin wadanda suke cin dukiyoyin marayu da zalunci,
abin sani kawai suna cin wutane a cikinsu, kuma da sannu za'a kona su a wuta
wacce ake rurata'' Suratun Nisa'I, aya ta:10.
Akwai hanyoyi da dama da mutane suke bi
wurin cinye wannan dukiya ta maraya, wasu idan suna hurda da mutum sai ya zama
akwai wasu kudadensa ko filayansa komadai wasu kadarori da yasan ba wanda ya
sani sai shi, sai kawai ya yi shiru akansu ya ki fito da su in kuma ya ga suna
da yawa ko za'a gane sai ya dan tsakuro wasu daga ciki sauran kuma ya yi shiru
akansu, ana samun masu irin wannan mummunan hali cikin matan mamacin ko
'ya'yanshi ko abokanshi ko abokan cinikayyarsa d.s, wannan haramunne ko tantama
babu kuma duk wanda ya yi irin wannan hali sai ya amayar da abinda ya ci a
ranar alkima alokacin da hakan ba zai yi anfaniba.
A wasu wuraren kuwa hukumomin yankinne
–masu unguwanni da dagatai Hakimai (wadanda ake kira masu kasa) suke wadaka da
abinda akabarwa magada said an abinda aka sammusu, gonakine ko fadamu ko
madaime aka bari.
A wani lokacin kuma shi malamin da kakira
domin ya raba gado shine wanda zai kamfaci wani kaso mai tsoka yace wannan na
masu rabone, ko kuma a zaga ta baya ahada baki dashi don ya karawa wani, waifa
wanda zai yi fada akan wannan mummunan hali shine kuma zai zama ja-gaba, Allah
ya sawwake.
Awani jikon kuma 'ya'ya mata da matan
mamacin sune za'ayi rabon gado amma kwatata-kwata basusan me aka rababa, ko dai
'yan-uwan mamacin su yi watsi da su ko kuma 'ya'ya maza su yi watsi da
'yan-uwansu 'ya'ya mata, ko kuma duk ba wannan ba wacce tafi 'ya'ya sai tai
zamanta akan dukiyar kaji don rashin jin tsoron Allah wai ana cewa ba'a raba
gado da mara 'ya'ya, sauda yawa wata irin kazantar da ake yi awurin rabon gado
kare ba zai ci ba.
Awani karon kuma shi wanda akaba dukiyar
marayun ya kula da ita bayan an gama rabo shine zai hauta da casa
kafin-kiftawa-da bisimillah ya hallaka dukiyar bakidayanta.
Bai halatta a dankawa yara kanana
dukirasu ta gadoba sai bayan sun cika sharudda guda biyu:
(1) Balaga: Dole kai da akaba
dukiyar mamaci ka ci gaba da riketa kana jujjuyata ba zaka danka masaba sai ya
balaga, ita kuma alamar mutum ya balaga alamace kamar haka:
(a) Mafarki: Alokacin day a
yaro ko yarinya ta yi ko ya yi mafarkin ya sadu da mace ko macen an sadu da ita
kuma mani ya fita, to daga wannan lokacin hukunce-hkuncen shara'a sun haukanshi
ko kanta mala'iku za su dinga rubuta musu ayyukan da kowa ya yi mekyau ko mara
kyau sun yi aure ko ba su yi aureba domin babu wanda yace sai mutum ya yi aure
sannan za'a bude masa fayil a wurin Allah. Ko kuma maniyyin ya fita a farke ba
wai sai abacciba kadai.
(b) Bayyanar Gashin
Mara: Hakanan idan gashin mara mai kaush-kaushi ya bayyana a gaban 'Ya mace
ko Da namiji.
(C) Jinin Al'ada: Hakanan daga
lokacin da mace ta ga jinin al'ada to daga wannan lokaci ta balaga
hukunce-hukuncen Allah sun hau kanta, anan nake cewa dolene iyaye su tashi
tsaye wurin kula da 'ya'yansu.
(d) Cika shekara
15:
Alokacin da Dan amiji ya cika shekara 15 ko 17 ko 18, kamar yadda malamai suka
karawa juna sani to lalle ya balaga.
Wadannan alamun balaga ko wacce daya
cingashin kanta take yi, ba lalle bane cewa sai sun bayyana duka, alokacin da
daya ta bayyana shekenan, kuma ya zama dole iyaye da masu ruko su kula sosai da
sosai, domin sai kaga yaro ko yarinya sun sha azumi amma kwatakwata ba maganr
ramawa wai andauka sai anyi aure sannan mutum zai dinga cika ibadarsa.
(2) Sharadi Na Biyu
Wayau: Koda yaron da kake kulawa da dukiya
ya balaga to bai halatta ka bashi dukiyarba sai ka jarraba hankalinsa da
dabararsa da wayonsa, idan ya natsu sai ka danka masa, idan kuwa bai natsuba to
bai halatta ka bashiba.
Wadannan sharudda guda biyu sune aya ta: 6 cikin Suratun Nisa'I ta yi
bayani, Allah madaukakin sarki yana cewa:
''Kuma ku jarraba marayu har idan suka isa aure to idan kun
tabbatar da wayonsu sai ku ba su dukiyoyinsu, kada ku ci ita (dukiyar) da barna
da gaggawa kafin su girma (komai yak are), duk wanda yake mawadacine to ya
kame, wandako fakirine (marashine) to ya ci gwargwadon wahalarsa, idan zaku
danka musu (dukiyar) to ku kafa musu sahaida, lalle Allah Ya isa mai lissafi
akan komai''.
Wannan babbar ayace akan abinda ya shafi kulawa da dukiyar maraya a
tsari mai cike da adalci da tausawa da baima kowa hakkinsa. Da farkodai ayar ta
yi nuni da adinga jarraba su marayun har idan aka ga sun cika wadancan sharudda
biyu sai aba su dukiyarsu, sannan ayar ta ja kunnen masu kula da dukiyar da
kada su tasata a gaba da ci ham-ham kafin yara su girma babu komai, sai ayar ta
bayya hakkin mai kula da dukiyar idan shi mai kula da dukiyar maraya dama
mawadacine yana da harkokinshi to ya ci gaba da kulawa da amma ya kame daga cin
wani abu na dukiyar, idan ko talaka kulawa da dukiyar marayan ta shagaltar da
shi daga nashi fadi-ta-shin, to ya dauki gwargwadon wahalarsa, ma'ana inda wani
kadauka aiki yake kulama da dukiyarka nawa zaka bashi, to abinda kasan zaka
bashi haka zaka dauka.
Sannan ayar ta nuna mana cewa
idan lokacin dankawa maraya dukiyarsa ya yi kada ku kunshe kanku a daki a'a ku
kafa shaidu, to kenamma a lokacin da zaka karbi dukiyar maraya ka tabbatar ansa
shaidu kuma a rubuta adadin abinda ka rike, kada ka yarda ace ai ba sai
anrubutaba ba danka bane, sauda yawa mutum ba zai raka kaba yace dare ya yi ma,
wasu su za su zugo maryun bayan sun girma ace babanku yabar muku abukaza da abu
kaza a nemi a hada ka fada da 'ya'yan kaninka ko yayanka, Allah Ya sawwake,
sannan wurin shaidun ba lalle bane ace sai dattijai a hada da matasa wada suke
da wayau Allah ne dai kadai yasan gawar fari.
Sai Allah Ya rufe ayar da ya isa ya zama mai lissafi, wannan yana nuna
mana cewa a tsaya ayi lissafi mai kyau lokacin karba da kuma lokacin bayarwa,
zaka lissafa duk abinda kake kashewa marayan dake hannunka kamar kudin
makaranta, kudin koyon sana'a, domin zaka tsayane ka kula da tarbiyyarsa
lokacin muzurai ayi mishi muzurai, lokacin fada ayi mishi fada in ya yi abin
duka adoke shi amma ba duka mai tsananiba, domin sai an rintse ido akeshan
magani musamman a rirn wannan lokaci ta tarbiyya ta sukurkuce. Kasa shi
makarantar Islamiyyah data book da koyon sana'a, sai kaga ya girma ya zama
natsattsen mutum kamili, ga kuma irin wannan dinbin lada da kasamu, domin duk
wadannan al'amurra da kake wa wannan maraya kana da lada na musamman awurin
Allah.
Ayoyin Alkur'ani mai girma sun zo da bayanin kada ku yi kusa da dukiyar
maraya said a abinda yake shine mafi kyau, saboda yadda ayoyi suke Magana akan
dukiyar maraya saida yakai wasu sun nemi su ware dukiyarsu data maraya ba tare
da sun hadaba koda ko jinsinsu guda kamar dabbobi kayan gona kudi d.s, a Suratul
Bakara aya ta: 220, Allah madaukakin sarki yana cewa:
''Kuma suna tambayarka dankane da marayu, kace: Kyautata
musu shine daidai, har idan kuka hada (dukiyarku da ta su ai 'yan-uwankune (ba
komai), Allah Yasan mabarnaci kuma ya san mai gyara''.
Kuma ya kamata al'umma su tsaya su yi karatun-ta natsu akan marayu bai
gagara mutum shima ya mutu ya bar na shi yaran kanana ai shima ba zai so abinda ya bar musu wani ya
yi wadaka da shiba.
Saboda haka lissafa cin dukiyar maraya ba-gaira-ba sabab da Ma'aikin
Allah ya lissafa shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa ba karamin tashin
hankali bane
Kammalawa: Awannan takaitaccan bayani day a gabata
lalle munsan irin hakkin da maraya yake da shi, da kuma wajibcin tsayawa
tsayin-daka akan akula da dukiyar maraya, sannan da bayanin minzalin da maraya
zai kai sannan a danka masa dukiyarsa, sannan da bayanin cewa wannan aiki ba
karamin matsayi yake da shi a wurin Allah ba, wannan kuma zai dada fayyace mana
yadda musulunci a kullum yake kulawa da masu rauni, sannan ga shi yadda bayani
ya gabata wadanda suka fi shan wahala sune mata da kananan yara, kuma ga yadda
Allah Ya yi bayani akan dukkan mai cin dukiyar maraya da zalinci to wuta yake
cima cikinsa, Allah Ya tsaremu kuma dukkan wadanda suke kula da marayun dake
hannunsu ya Allah ka taimaka musu wurin sauke wannan nauyi, kuma Ya Allah ladan
da kake baiwa wadanda suke kulawa da marayu ya Allah ka tabbatar mana mu da su
baki daya, Amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda.
Minna,
jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

No comments:
Post a Comment