RIBA/KUDIN-RUWA: A yanzu za mu yi
bayani akan abu na hudu cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar
da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu kuwa itace Riba/Kudin-Ruwa/Bashi da
ruwa.
Mecece Riba?:
Ashar'ance Riba
Itace: Kari akan wadansu abubuwa kebantattu.
Tsoratarwa A Kan
Mu'amala Da Riba:
Ayoyi masu tarin
yawa sunyi bayanin narkon azabar da Allah madaukakin sarki ya tanadar mai
mu'amala da riba, hakanan Ma'aikin Allah Ya yi bayanin haka harma gashi ya
lissafa riba cikin abubuwan da suka halakar da maita'amuli da riba, Allah Ya
tsaremu amin.
Allah madaukain
sarki yana cewa ''Duk wadanda suke cin riba bazasu taba tashi ba (daga
kabarinsu) saidai kamar wanda aljan ya shafeshi, abinda ya sa haka saboda su
(masu mu'amala da riba) sunce ai abinsani kawai kasuwanci kamar ribane, kuma
Allah Ya halasta kasuwanci kuma Ya haramta riba, to duk wanda wa'azi ya zo masa
daga wurin Ubangijinsa sai ya hanu (daga ta'amuli da riba) to yana da abinda ya
wuce, kuma (sauran) al'amarinsa yana wurin Allah, amma duk wadanda suka ci gaba
(da mu'amala da riba) to wadannan sune 'yanwuta kuma wadanda zasu dawwama acikinta*
Allah Yana kwashe albarka (daga dukiyar da ake) mu'amalar riba da ita, kuma
(Allah) Yana rainon sadaka, kuma (Shi) Allah bayason dukkan maiyawan kafirci
kuma mai laifi''. Bakara, aya ta:275-276.
Lalle wadannan
ayoyi guda sun yi bayanin yadda Allah ya kyamaci riba Ya haramtata kuma Ya yaye
shubuhar wadanda suke ganin kasuwanci da riba duk abu dayane, Allah Ya nuna
mana cewa Shi Ya halatta kasuwanci kuma Ya haramta riba, kuma Ya bayyana
yalwatur rahmarsa cewa duk wanda wa'azi yazo gareshi ya ji cewa ta'amuli da
riba Allah Ya haramta shi kuma ya hanu ya yarda da haramcin ya tuba to abinda
ya yi da ya wuce, amma sauran al'amarin sa yana wurin maliccinsa.
Hakanan bayan
wadannan ayoyin biyu Allah madaukakin sarki Ya ce ''Ya ku wadanda suka yi
imani ku ji tsoron Allah kubar abinda ya saura na riba har in kun kasance ku
muminaine. * Har idan baku aikata (Tuba ba) to ana shelanta muku yaki da Allah
da Manzanshi, idan kuka tuba kuna da asalin dukiyarku, kada kuyi zalinci ba
kuma za'a taba zaluntar ku ba.'' Bakara, aya ta:278-279.
A iya sanina Masu
mu'amala da riba da masu kiyayya da salihan bayi sukadai Allah ya shelantawa
yaki, lalle wannan kadai ya ishi bala'I ga masu ta'amuli da riba.
Hakanan kuma
Ma'aikin Allah Ya tsoratar akan ma'amala da riba, Jabir dan Abdullah ya ruwaito
Hadisi daga Ma'aikin Allah ya ce: Ma'aikin Allah Ya tsinewa wanda ya bada riba
da wanda akaba, da wanda ya rubuta (sakatare) da wadanda suka tsaya amatsayin
shaidu' Ma'aikin Allah Yace ''Duk daya suke'' Muslim ya ruwaito hadisi
na 1597, da Ibnu Hajar a Bulughul Marama Hadisi na 801. Hakika
wannan tsinuwa da Ma'aikin Allah Ya yi wa masu ta'amali da riba lalle yana muna
mana bala'in da ke cikin riba, mutum na farko da aka tsinewa shine wanda ya
bayar ko waye talaka ko mai kuli, shugaba ko wanda ake shugabanta. Mutum na
biyu shine 'Wanda akaba' ko waye kuwa. Mutum na uku 'Wanda ya zama mai rubutu a
tsakanin maikarba da mai bayarwa' mutum na karshe da tsinuwar Ma'aikin Allah ta
hada dashi a wannan Hadisin 'Sune wadanda suke shaida' sanna Ma'aikin Allah Ya
ce duka daya suke. Allah ya tsaremu baki daya.
Ita riba tana cikin
abubuwan da dukka shari'un da suka gaba ta sun haramtar da ita, asalima shi
ta'amuli da riba daya ne daga cikin siffofin yahudawa da Allah Ya tsine musu
tsinuwar kuma ta har abada.
Kadan Daga Cikin
Abinda Yasa Aka Haramta Riba.
Tabbas akwai cindukiyar mutane ba tare da hakki shar'antattacceba, akwai
kuma cutar da talakawa da mabukata ta yadda ake nunnunka musu bashi musammamma
idan sun kasa biya, sannan akwai kuma rashin tausayi, sannan al'amarine da yake
toshe hanyar bada kyakkyawan taimako, yake bude hanyar mummunan taimako wanda
ke dankwafar da marashi ko-da-ko Bankine koma kasa, abune kuma da yake gurgunta
kasuwanci da masana'antu, sanna kuma al'amarine da yake zama sanadiyyar
salwantar dukiya kuma gashi yadda musulunci ya baiwa dukiya kima da daraja,
wannan yasa duk abinda zai kawowa dukiya cikas musulunci ya kawar da shi kamar
sata, sane, fashi, daukar dukiya a bada ita ga wanda baida kimiyyar kula da ita
d.s, to wannan yana daga cikin abinda yasa aka haramta Riba, idan ba'a manta ba
ashekara ta 2009 da duniya ta samu kanta cikin matsin tattalin arziki ai
nan-da-nan manyan bankuma a turai suka bayyana cewa sun kudin ruwa da suke
karba da kashi kaza (a yanzu na manta) ashe suma sunsan cewa riba tana cikin
abinda ke karya tattalin arziki cikin gaggawa.
Kada maikarau ya sha'afa cin Riba yana daya daga cikin siffofin Yahudawa
da Allah Madaukakin sarki ya tsine musu a kanta, Allah madaukakin sarki Yana
cewa: ''Kuma saboda tsananin zalincin Yahudawa muka haramta musu abubu
masu dadi, da kuma yadda suke kange (mutane) masu yawa daga hanyar daidai, da
kuma yadda suke karbar kudin Ruwa kuma tuni an hanasu, da kuma yadda suke cin
dukiyar mutane da barna''. Suratun Nisa'i, aya ta 161.
Riba itace kari akan wadansu abubuwa kebantattu,kamar yadda bayani ya
gabata, ashe wannan yana nuna mana cewa ba komai bane riba ke shiga cikinshi.
To yanzu wadanne abubuwane wadannan?. Ankarbo daga Ubata dan Samit –Allah Ya
kara masa yarda- Hadisine Marfu'I yace ''Zinare da Zinare, Azufra da
Azurfa, Iburo da Iburo, Shinkafa da Shinkafa, Dabino da Dabino, Gishiri da
Gishiri, (ayi su) daidai-wa-daida, Hannu-da-Hannu''. Bukhari Hadisi na 2176
da Muslim 1584 (kuma wannan lafazin riwayar Musline). Ayanzu wannan
Hadisi ya zayyano mana abubuwa guda shida ya kuma bayyana mana yadda za'a yi
mu'amala da su, yadda za'a yi mu'amala da su sharuddabe guda biyu alokacin da
bubuwan suka zama jinsi guda, abu na farko ya zama daidai wa-dai-da, abu na
biyu ya zama hannu-da-hannu, idan aka saba haka to an ci Riba kamar yadda
wadansu hadisan suka nuna.
Mudauki misalan abubuwa biyu cikin wadancan abubuwa shida da aka anbata
a Hadisi, misalin abu na farko shine 'Zinare' idan kana da zinare nima ina da
zinare ina son inbaka nawa in karbi naka (misanye) sai aka auna nauyinsu ya
zama daidai to anan sai inkarbi naka ka karbi nawa (hannun-kuturu-da-na-makaho)
ba zan kara maka komaiba, ba zaka karamin komai ba, in an yi kari to wannan
Karin ya zama riba, ko da an gyara na wani ba'a gyara na wani ba, balle na ki
dankunnen zinarine nawa kuma awarwarone duk ba wani kari, kenan idan kai da
kake sayarwa na kawo maka nawa kilo ashirin na awarwaro sai kaban kilo ashirin
na sarka, shikenan taro ya tashi ba maganar in kara maka dari biyar ko dubu, in
an yi kari to an ci riba.
Misalin abu na biyu kuwa shine mudauki shinkafa, Shinkafa bakidayanta
jinsi gudace ta gida da ta waje, kenan yanzu idan na baka shinfa 'yar gwamnati
kwano goma kai kuma kana da ta gida to kaima kwano goma zaka bani hannu-da-hannu,
idan aka yi kari to an ci riba, ashe yanzu idan aka baka shinkafar gwamnati
kwano goma aka ce ka bada ta gida kwano goma da rabi to wannan abinda aka kara
ya zama riba komai kankantar shi hakanan komai girmanshi, Allah Ya sawwake,
lalle wannan yana nuna mana mu kusanci malamai kenan, hakanan idan aka bayar da
ta gwamnati yanzu kwano goma sai aka ce kazo bayan karfe kaza ka karbi ta gida
kwano goman shima ya zama riba tunda an sami jinkiri, domin hadisin ya nuna ayi
daidai-wa-daida, kuma hannu da hannu, kamar yadda bayani zaizo, da izinin
Allah.
Mu koma kan wancan Hadisin da ya lissafafa abubuwa shida, sai malamai
magabata sukece 'Haramcin riba bai takaitu a kan wadannacan abubuwa shida kadai
ba, a'a, sudai wadancan shida sune asali duk abinda ke da alaka da daya daga
cikinsu sai yakarbi hukuncinshi. Sai malaman sukace abinda yasa Zinariya da
Azurfa (wato biyun farko a Hadisin) suka zama abinda riba ta ke shiga shine don
suna kudi, saboda haka duk abinda yake kudine Nairace ko Riyal ko Dala, ko
Saifa koma nenene indai kune to shima hukuncin Zinariya da Azurfa ya hau kan
shi, wannan zai nuna maka gamewa ta musulunci da kuma Mu'ujizar Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ta yadda ya yi jawabin da ya
shafi Riyal da Dala da Naira wanda yake alokacin da yake wannan jawabi babu
wadannan kudade, Allah Ya kara masa daukaka, amin.
Canjin-kudi: Canjin-kudi nau'ine
na kasuwanci da Allah ya halattashi, akan hakane har ake da 'yan-canji da
shugaban canji. Sai dai mu sani kudin da ake canzawa sun kasu kashi biyu, akwai
wadanda suke jinsi guda, kamar Naira da Naira ko Riyal da Riyal ko Dala da Dala
d.s, to dukkan kudadan da suke a junansu jinsi guda suke ya zama wajibi wurin
yin canji asan an cika sharudda guda biyu:
(a) Hannnu-da-hannu: idan aka sami
jinkiri to anci riba, misali idan na zo ka canzamin N500, to bai halatta
ka karba kace indawo anjima in karbi canjinba.
(b) Daidaiwadaida: kenan bai halatta
in baka N500ba, kai kuma ka bani N490 ko don sabbine ko dai
wadansu al'amura.
Sai kuma kudaden da jinsinsu ba guda ba ne,
kamar Naira da Dala ko Saifa da Riya, anan ya halatta asami fifiko inbaka Dala 100
ka bani N150,000. amma dole ya zama hannu da hannu, bai halatta a sami
jinkiriba.
Abinci: Musanyar abinci da abinci hasne
kuma nau'ine na halastaccan kasuwanci, saidai shima ya kamata asan abinda suke
jinsi guda da kuma wanda suke ba jinsi gudaba. Kamar shinkafa baki dayanta
jinsi gudane, kenan lokacin musanye dole asamu sharudda biyu hannu da hannu
kuma daidai wadaida, kamar yadda bayani ya gabata, hakanamma gero da gero bai
halatta inbaka gero na bara kwano goma kai kuma ka bani na bana kwano tara ko
shadayaba.
Lalle wannan yana nuna mana yadda kofofin
afkawa riba suke da yawa domin sau da yawa wani yana bada bashin kudi akan idan
za'a dawo mishi da su sai anyi kari, wanda yake da yawan Bankuna da daidaikun
jama'a akan haka suka ginu. Wannan nau'uka na riba bayanansu ba zai wadatarba a
dan wannan rubutu, sai dai a kusanci malamai sannan kuma alizimci karatu akan
kasuwanci, domin hatsarin da yake cikin Riba da fushin Allah akan dukkan mai
ta'amuli da ita hard a wanda ya rubuta da wanda ya tsaya shaida duk tsinuwar
Allah ta hau kansu kamar yadda bayani ya gabata, Allah muna rokonka ka ciyarmu
abinda yake halal kuma ka sa mu cika da imani, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda.
Minna,
jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Allah ya saka da alkhairi Ya kuma bamu damar aiki da abinda muka karanta Ya tsarkake mana niyyarmu Ya kuma bamu cikakken lada daga gareSa albarkacin rahama da tausayinSa Subhanah.
ReplyDeleteAmeen thumma ameen
DeleteAllah ya saka da alheri Malam.Ina da tambaya,tambaya ta shine kamar yanzu da ake sayan dollar ko wani nauin kudi online fa,kaga shi ba hannu da hannu bane.to ya wannan kasuwancin yake?
ReplyDeleteAllah yasaka da Alhairi, ina neman karin bayani dan gane da naira,dala,riyad da sauran su, yadda riba ke shiga cikin su, don kasancewar su duka jinsi guda ne a asalin su, domin ina fahintar anyi kiyasin su ne da zinariya ko azurfa a wajen hukunci, domin da zinariyar saudi da na amurka da na nigeria duka sun hadu a asali, kira ko ta sarrufi a kansu bai baya iya dauke riba a kansu, to me yasa kira ko tasarrufi a naira da dala da riyad yarabasu bayaga cewa duk jinsi guda ne? na gode, ina maka fatan Allah yakara basira, kuma yasaka da alhairin sa amin
ReplyDelete