Sunday, March 24, 2013

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Yiwa Mace Mumina Kazafi)7/7#


Yiwa Mace Mumina Kazafi: A yanzu za mu yi bayani akan abu na bakwai kuma na karshe cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu shine Yiwa Mace Mumina Kazafi.
Kazafi Shine: Jifan mutum da aikata alfasha ta zina, ko kore juna biyu ko ma Da ba tare da ya bayar cikakkun shaiduba.
       Alokacin da mutum ya jefa kanshi cikin irin wadannan halayya ta kazafi to lalle ya jefa kansa cikin halayyar da take halakarwa, domin yin kazafi ba karamin bala'ibane, alokacin da mutum ai wance mazinaciyace ko ya yi lalata da ita, ko wannan ciknnanata bana mijintabane ko danta/'yarta ai bana mijinta bane to lalle ya tsokano tsuliyar dodo dole ya kawo cikakkun shaidu na mutane hudu maza musulmai da zasu bada shaida akan hakan, idan kuma mai kawo shaiduba ko ya kawo basu cikaba to kowanne mutum gada cikinsu bulala tamanin (80) za'a yi masa, kamar yadda bayanai zasu zo nan gaba kadan.
       Wannan shiri da musulunci yake dashi bakaramin shiri bane domin kare mutunci, masu iya Magana na cewa mutunci madarane in ya zube bai kwasuwa, addinin musulunci yana daga cikin manyan manufofinsa kare mutunci, wannan yasa musulunci ya dauki irin wannan mataki musammamma 'ya mace, domin alokacin da aka bata mata suna to gaba daya anbata mata rayuwarta, shi yasa ayoyin da suka yi Magana akan kazafi sun anbaci macece basu anbaci namijiba wannanko ba wai dan hukuncin ya sha daban bane a'a hukuncin iri dayane ga duk wanda ya yi mace ko namiji kazafi, kuma bai iya kawo cikakkakun shaiduba, idan ko ya kawo shaidu da duk abinda Shara'a ke bukata suka cika to baza'a kira wannan da sunan kazafiba.
       Yiwa mace mumina kazafi bai halattaba kuma yana cikin abubuwan da suke halakarwa, saboda haka dadin fira ko kiyayya kada ta dauki mutum ya yiwa wata/wani kazafi ko yasa a yi.
Ayoyin Da Suka Yi Magana Akan Kazafi: Idan ka tsaya ka kalli ayoyin zaka gansu kashi ukune kuma duk suna cikin Suratun Nur.
Kashi Na Farko: Ayata: 4-5, Allah Madaukakin sarki yana cewa: ''Wadanda suke jifan mata masu kamunkai (da zina) sannan kuma basu kawo shaidu huduba to ku yi musu bulala tamanin (80), kuma kada ku sake karbar shaidarsu har abada, kuma waddan sune fasiakai. Saidai kawai wadanda suka tuba bayan haka kuma suka kyautata to lalle Allah mai yawan gafarane kuma mai yawan jinkai.''
    Anan Allah madaukakin sarki ya bayyana hukuncin duk mutumin da ya yiwa mace/namiji kazafi kuma bai iya kawo shaidu huduba sai Allah ya bayyana hukuncin da za'a yi masa. Abu na farko bulala tamanin (80), abu na biyu ba za'a sake karbar shaidarsaba har'abada, abu na uku kuma wannan mutumin fasikine. Sai idan ya tuba, to ananne malamai suke maganar shin inya tuba za'a ci gaba da karbar shaidarsa kuma shikenan shi ba fasiki bane? Amma ko ya tuba sai an yi mishi bulala tamanin.
Kashi Na Biyu: Ayoyin da suka yi bayanin maigidan da ya yiwa matarshi kazafi kuma bai iya kawo shaiduba to shi tsinuwa za su yi da matar ta shi, Allah Yana cewa:
''Wadanda kuma suke jifan matansu (da zina) kuma ya kasance basu da shaidu saidai karankansu, to shaidar dayansu (itace) Rantsuwa hudu da Allah lalle shi yana cikin masu gaskiya * (Rantsuwa) ta biyar tsinuwar Allah ta haukanshi in ya kasance cikin makaryata. * Kuma abinda zai hana ayi mata azaba (haddi) shine ta yi Rantsuwa hudu da Allah cewar lalle shi (mijin) yana cikin makaryata *. (Rantsuwa) ta biyar lalle fushin Allah ya tabbata akanta in (mijin nata) ya kasance cikin masu gaskiya'' Surartun Nur, ayata: 6-8.
Anan Allah madaukakin sarki ya yi bayanin idan miji ya yiwa matarshi kazafi kuma bai iya kawo shaidu huduba to 'Li'ani'' za su yi. Amma duk wanda ba miji bane to kodai ya kawo sahaidu mutane hudu maza musulmai ko kuma ayi mishi bulala tamanin, ba maganar shi wanda aka yiwa kazafi wai ya rantse idan ba haka bane, ko kuma shi da ya yi kazafin cewa ya rantse duk babu kodai shaidu ko bulala tamanin.
Kashi Na Uku: Ayoyin da suka yi Magana akan kazafin da aka yiwa mata muminai masu kamunkai natsattsu kammalallu to wadannan masu yiwa irin wadannan matan kazafi tsine musu aka yi duniya da lahira. Allah madaukakin sarki yana cewa:
 ''Lalle dukkanini wadanda ke jifan mata masu kamun kai gafalallu (daga aikata dukkanin alfasha) wadanda suke muminai to an tsine musu a duniya da kuma lahira, kuma suna da azaba maigirma* Aranar da harsunannu za su bada shaida akansu da hannayansu da kuma kafafuwansu ta sanadiyyar abinda suka kasance suna aikatawa* Awannan ranarce Allah zai cika musu sakamakonsu na gaskiya, kuma zasu sani lalle Allah shi wanda yake mai gaskiya kuma mai bayyanar da abubuwa''. Suratun Nur, ayata: 23-25.
Wannan ya nuna mana shi karankanshi kazafin ya kasu kashi-kashi, kashi na farko shine yiwa gama garin mutane wadanda suke suna da kyawawan halaye da kuma wanda ba'a rasaba, su aka anbaci hukunci yi musu kazafi a kashin farko, sai kuma wanda ya kasance tsakanin miji da mata. Sai wannan kashi na uku, wanda mutum zai ga mace/namiji mai kamun kai mai addini natsattse mumini kawai ya antayo ashar ya watsa mata/mashi ya dinga fadan wasu maganganu wanda da za'a tara mishi arzikin duniya domin ya kawo shaida akan haka ba zai iyaba. Domin wani ya dauka irin halin da yake dashi to kowa haka yake, to kaga bayan ya kasa kawo wadannan shaidu za'a yi masa hukuncin kazafi anan duniya sanna kuma ya jira ranar alkiyama, domin Allah baya bari a taba bayinsa na kwarai, Ya Allah ka samu daga cikinsu, ka karemu da sharrin masharranta ka tsaremu ka tsaremana imanimmu, amin.
Kammalawa: Daga takaitattun bayananan ya bayyana agaremu yadda musulunci ya dauki mutunci da daraja da kima ya karewa kowa mutuncinsa musamman 'ya mace, domin idan ba hakaba sai kowa ya fadi abinda ya ga dama ko asashi ya fada yana ganin bai huce aci tararshiba, amma idan yasan zai sha bulalane to dole ya naba'a yasan me zai fada, sai yazama yak are mutuncinsa dana zuriyarsa kamar yadda yak are mutuncin wani dana ziriyarsa.
Annanne kuma muka zo karshen wannan silsila wacce take dauke da sharhin wannan hadisi da Abu Hurairata ya ruwaito daga wurin Ma'aikin Allah na wadannan abubuwa bakwai masu halakarwa, lalle ma'aikin Allah ya isar da manzanci kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, hakika ta'amuli da wadannan abubuwa tabbas yana halakarwa kuma wannan kowa ya gani ya tabbatar wannan zai kara imanine bisa imani. Akaro na gaba zamu kawo bayanne kuma wadanda zasu haskaka mana rayuwarmu da addininmu, Allah ya kaimu wannan lokacin ya hadamu da imani, aimn.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna, Jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

No comments:

Post a Comment