Sunday, October 14, 2012

HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI


Gabatarwa: Dasunan Allah Mai yawan rahama maiyawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a wannan karon za mu karkata akalar mu zuwa wani bangare da ya ke hararomu a 'yan kwanakin nan, wannanan bangaran kuwa shi ne na SALLAR IDI! Domin mu ga yadda musulunci ya tsara mana komai abinda ya rage kawai a garemu shi ne bi, komai angama, Allah tabbatar da duga-dugammu akan tafarkin Ma'aikin Allah.
Mecece Sallar Idi: ''Ita sallar idi sallace da ake gabatar da ita a wani lokaci kebantacce, awata siffa kebantacciya, sau biyu a shekara''. Kafin mu kai ga fashin bakin wannan ta'arifi na sallar idi, bari mu gabatar da tabbatuwarta tukunna.
Tabbatuwar Sallar Idi: Sallolin idi guda biyu da musulunci yake da su (Karamar Sallah da Babbar Sallah) kowacce ta tabbata a shara'a, ba wai bikine haka kwai na gargajiyaba.
Tabbatuwar Karamar Sallah: itace sallar da ake gabatarwa a ranar 1 ga Shawwal, don godiya ga Allah akan baiwar da ya yi mana na kammala azumin watan Ramadan, wannan sallar ta tabbata a Suratul-A'alah aya ta:14-15, Allah madaukakin sarki yana cewa: ''Tabbas duk wanda ya bayar da zakka (Fidda-kai) ya rabauta. Kuma ya anbaci sunan UbangijinSa sannan kuma ya yi sallah''. Sai malamai sukace 'Zakka da aka anbata a ayar farko itace zakkar fidda-kai, Sallah kuma da aka anbata a aya ta biyu itace, karamar sallah domin itace ake fitar da zakkar Fidda-kai kafin a ta fi, sannan kuma ga zikirin da aka an'anbata shine wanda ake yi lokacin tafiya sallar idin'.
Tabbatuwar Babbar Sallah: Ita kuma sallah ce da ake gabatar da ita a ranar 10 ga watan Zul-Hajji. Ita ma babbar Sallah ta tabbata a Suratul-Kauthar a aya ta: 2. a inda Allah madaukakin sarki yake cewa ''Ka yi Sallah domin Ubangijinka, kuma ka soke (abin hadayarka)'', malamai sukace 'Babbar Sallah ce domin an hada Sallah da Yanka' a ayar kamar wacce ta gabata an'hada Zakka da Sallah. Wannan tabbatuwar  wadannan sallolike nan ta ayoyin alkur'ani, hakanamma sun tabbata ta ayyukan Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, Bukhari da Muslim da Abu-Daud da Nasa'i duk sun ruwaito daga Jabir-Allah Ya kara masa yarda yace ''Na harci Sallar idi tare da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- sai ya fara gabatar da sallah kafin Huduba ba tare da an yi kiran sallaba ko an tada Ikama''. Haka shima Bara'u dan Azib –Allah Ya kara masa yarda yace ''Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya yi mana huduba a ranar babbar sallah, bayan ya idar da sallah sai yace ''Duk wanda ya yi wannan sallar tamu, kuma ya yi yanka irin namu to yankanshi ya yi daidai, wandako ya yanka kafin ayi sallah to wannan bashi (da ladan) yanka''. Wannan hadisin malaman Hadisi bakwaine suka ruwaito shi.
Hukuncin Sallar Idi: Hukuncin sallar idi shine, Sunnace mai karfin gaske, domin Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya aikata ta kuma ya lizimceta, hakanan kuma ya fitar da mata da kanan yara zuwa halartar wannan sallah. Saboda haka bai kamata mutum ya yi sakaci da itaba har ya rasa samun wannan sallah wanda saboda ita nema aka bada hutu a kasa baki daya, ka rufe shagonka na kasuwanci ka dakatar da ayyukanka.
Lokacin Sallar Idi: Kamar yadda bayani ya gabata a ta'arifi cewa sallace da ake gabatarwa a lokaci kebantacce to wannan lokacin kuwa shine ''Daga lokacin da rana ta fito ta daga kamar tsawon sandar mashi harzuwa lokacin da rana zata karkata daga tsakiyar sama''. Amma malamai sukace 'An fi so a babbar sallah a yi ta da wurwuri domin mutane su samu su koma gida domin su yanka layyarsu a daidai lokacin walaha, sannan kuma su ci abinci domin basu ci ba suka fito sallah. Amma akaramar sallah an fi so a dan jinkirta sallar domin mutane su samu su gama fitar da Zakkar su ta fidda-kai, su kuma ci abinci domin iti an fi so a ci kafin a fito sallah'.
Ladubban Sallar Idi: Akwai wadansu ladubba da yakamata a ladabtu da su, wadannan ladubba suna da yawa daga ciki akwai:
1.       Yin wanka da sanya turare da kuma sanya tufafi masu kyau sababbine ko nada.
2.       Hakanan yana daga cikin labudda a ci abinci kafin a fita sallar idi a karamar sallah, da kuma jinkirta cin abinci a babbar sallah har sai an yi sallah, da kuma cin wani abu na hantar dabbar layyah ga wanda ya yi. Ankarbo daga Buraidah –Allah Ya yarda da shi- yace; ''Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya kasance baya fita zuwa masallcin idi a karamar sallah har sai ya ci abinci, kuma ya kasance baya cin abinci a babbar sallah har sai ya dawo daga masallacin idi, sai ya ci wani abu na dabbar layyarsa''.wannan Hadisi Tirmizine ya ruwaito.
3.        Kana yana daga cikin ladubba yin kabarbari, kuma lafazinta shine: Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha Illallahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil Hamd.
4.       Yin gaisuwar sallah wato kacewa dan'uwanka musulmi ''Allah Ya karba mana ya karba muku''.
Siffar Sallar Idi: Kamar yadda ya gabata a farkon bayani cewa sallace da ake gabatar da ita a wata siffa kebantatta, wannan siffa kuwa itace; wannan sallah ana yin ta ne Raka'a biyu, kuma ana bayyana karatun, ba tare da angabatar da kiran sallah ba, ko tada ikama, sannan kuma ba'a gabatar da nafila kafin sallar ko bayan sallar. A raka'ar farko bayan kabbarar harama anayin kabarbari shida kafin fara karatu (wato kabarbari bakwai kenana). A Raka'a ta biyu bayan kabbarar tasowa sai a yi kabarbari biyar, kafin fara karatu (wato kabarbari shida kenan), wadannan kabarbari liman da mamu duk suna yinsu sai dai mamu baya karatun sallah saboda karatun liman, sannan sai ayi sallar kamar sauran salloli, bayan liman ya yi Tahiya ya yi sallama sai ya gabatar da Huduba, sannan yana da matukar muhimmanci a tsaya a saurari hudubar, wadannanfa sune ayyukan ranar, amma wacce gaggawa mutane suke yi suke barin sauraron Hudubar?.
Wanda bai samu sallar idi ba ya samu ya yi sallah Raka'a hudu kamar nafilfili, idan kuma ya ga dama ya yi ta a siffar sallar idi.
Idan kazo ka sami liman yana Tahiya sai ka zauna tare da shi, idan ya yi sallama sai ka mike ka kawo raka'oinka biyu a siffar su da ta gabata.
Wadansu Mas'aloli: A yanzu za'a kawo wadansu halaye da mutum yakan samu kanshi a ciki idan ya zo ya samu tuni anfara sallah.
1.      Idan mutum ya zo ya sami liman ya kammala kabarbari ya fara karatu ya zai yi?. Amsa: Anan zaka yi wadannan kabarbarin, kasancewar ba abune mejan lokaci ba, sannan sai ka raurari karatun liman.
2.       Idan ka zo ka sami liman ya fara kabarbari amma bai gamaba, to anan zaka yi sauran kabarbarin da suka ragewa liman tare da shi, sannan sai ka kawo wadanda suka wuceka, koda liman ya fara karatu, kenan anan ba zaka yi wadanda suka wucekaba a lokacin kabarbarin liman.
3.      Idan kazo ka sami liman yana Ruku'u sai ka yi kabbarar harama kadai ka bishi, ba sai ka kawo sauran kabarbarinba.
Tambihi: Ya kamata mu san girman wadannan salloli da matsayinsu a addini, tunda har yakai Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa a fita sallar har da mata da kananan yara, har mata marasa tsarki idan sun je sai su yi nesa da wurin sallah idan anzo huduba suma sai su anfana. Kada mu sha'afa akan wannan sallarne aka bada hutu duka kasa, aka rufe shaguna kada mutum ya shagala a wannan lokaci da abinda zai hana mishi samun wannan sallah. Sannan kuma a kula da yara da irin suturar da za su sa, domin idan ka ga wadansu yaran ba kace 'ya'yan musulmi bane, wannan baidace ba kuma baikamata, wasu kuma rawa kamar mazari, Allah Ya sawwaka, amin.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata ya bayyana a garemu cewar sallar idi ba wata gargajiya bace ibadace da Allah ya shar'anta ta ta harshen fiyayyan halitta Annabi Muhammad –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, itako ibada anayinta akan yadda aka tsarata ne, Allah ya karbi ibadarmu ya sa ayi sallah lamilafiya ya tsaremu ya tsare mana imaninnu, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
 e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu
www.youtube.com/Aliyu Muhammad Sadisu

Wednesday, October 3, 2012

Aikin Hajji A Wannan Shekarar 1433 (2012) Ina Mafita??


Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga ma'aikin Allah. Bayan haka lalle wannan masifa da ta aukawa kasarnan a wannan gagarumin aiki wanda yake rukunine daga cikin rukunan addinin musulunci abin a tsaya ai nazarinta ne domin aga ta ina ta fito kuma ya za'a tunkareta ta yadda ba zata sake aukuwaba, domin ace mutum ya isa kasa mai tsarki lamilafiya amma kuma a dawo da shi kai wannan ba karamin tashin hankali bane Ya Allah muna rokonka da kada musake ganin maimaituwar wannan al'amari. Kamar yadda na fada lalle ya kamata mu tsaya mu yi wa wannan lamari karatun ta-natsu, mabudin wannan karatu itace ayar dake cikin Suratus Shura aya ta 30. ''Kuma duk abinda ya sameku na kowacce irin masifa to fa saboda abinda kuka gabatarne, kuma (Allah) Yana ga abubuwa masu tarin yawa''.
          Lalle la'akari da wannan ayar yana dakyau mu tsaya muga me aka gabatar da ya haifar da wannan al'amari don asan matakin da za'a dauka don hana aukuwar irinshi nan gaba. Ni a ganina wadannan al'amurra sune kamar haka:
1. Mahrami: Shine mutumin da yake haramunne ya auri matar da yake tare da ita (kamar uba mahramine na 'yarshi, ko kaka ko siriki) shi yasa sai ace mahrami ko miji, Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa: Bai halatta ga dukkan matar da tai imani da Allah da ranar lahira da ta yi tafiya kwana guda ba tare da maharraminta ba'' Hadisai da suka zo daga ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- a kan haka suna da matukar yawa da fayyace al'amurra a fili da suke nuna irin gatan da musulunci ya yi mace lura da cewa ita mai raunice baibukar taimakoce a koda yaushe  kuma ko wanne iri. An ruwaito cewa wani daga cikin Sahabban ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- an sanyashi cikin wadanda za su tafi yaki sai yace medakinshi zata tafi aikin hajji sai ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace acire sunansa ya tafi ya je ya yi aikin hajji tare da maidakinshi. Kuma wannan al'amarii sannannene cewa alokacin da mace take tare da mahraminta ko mijinta zata dada kamewa doruwa akan wacce take da ita, in kuma ba kamammiya bace to zata kame da izinin Allah, kuma zata zama tana da abokin hira a wannan tafiyar, hikimomi da zaka iya zakulowa cikin muhimmacin mahrami a tare da mace a Halin tafiya ba karamin al'amari bane, duk wanda ya taba yin aikin Hajji zai tabbatar da muhimmancin mahrami tare da mace, ba Mijin-Biza ba domin akwai halin da ake shiga na sai ka rike mata hannu ko jiki, wanda yake haka ba zai yiwuba idan ba maharramaka bace. Malamai sun karawa juna sani kan abinda ya shafi aikin Hajji shin idan aka sami tawaga amintacciya  mace zata iya tafiya a cikinsu ko dab a mahraminta? Sai wannan tawaga ta zama kamar mataimaka a gareta? Malamai da yawa sun tafi akan haka,
          Maganar mahrami maganace da ta taso a aikin Hajjin wannan shekarar ta 1433 Hijira ko 2012 miladiyya, a inda akan hakanne hukumar kasar Saudiya ta dawo da mahajjata mata masu tarin yawa daga kasar, na farko da maganar mahrami tabbatacciiyace a shara'a domin ta fitone daga bakin Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ba Magana bace da hukumar kasar Saudiya ta kirkiri bam domin na ji Nura Das Ahirarsa da jaridar Leadership Hausa bugu na 313, a shafi na 25 yana cewa Ba kowanne mahajjaci bane ke bin akidar Wahabiyaci, Su a mazahabinsu na Ja'afariyyah wanda aka fi sani Shi'a mace idan ta amincewa kanta ko waliyyanta sun amince mata zata iya tafiya ko inane, wannan Magana tasu ta nuna abinda acewa su Shi'a ba abinda ya hada su da karantarwar ma'aikin Allah, in banda ina maganar bin tafarkin ma'aikin Allah ina kuma maganar wahabiyanci?. Maganar maharami manace data mamaye kafafan yada rabaru a kasarnan kuma maganace da take bukatar a tsaya a yi mata karatun-ta-tsau domin sanin hikimomi da tausayawa da musulunci ya yiwa 'ya mace, kafafan yada labaru sun cancanci yabo yadda suka tunubi malumma akan wannan al'amari wato suka maida al'amarin zuwa ga masu shi. To amma hanzari-ba-gudu-ba maganar da kafofin yada labarai suke yi na cewa anya maganar mahramce kadai tasa wannan al'amari ya faru koko akwai lauje cikin nadi domin mata 'yan Nijeriya kawai aka dawo da su banda 'yan wadansu kasashen? Wannan maganar ya kamata a yi la'akari da ita, wannan ya kaimu abu na biiyu wato.
2. Gurbacewar Tarbiya: A gaskiya Najeriya tana da matukar kima da daraja a idanun kasar Saudiya, amma a gaskiya halayyar da 'yan Najeriya suke nunawa a wadannan wurare masu tsarki musamman ma a birnin Makkah birni mafi tsarki da daraja gaskiya a kwai bantakaici, mata nawane suka tsallake mazajensu su kai zaman dirshan a birnin makkah, me ya kaita? me take yi? Asalin Magana a musulunci mace bata ciyar da kanta kwata-kwata, idan ta yi aure mijinta ya ciyar da ita idan batai aure ba mahaifinta ko waliyyinta ya ciyar da ita. Duk mutumin da ya tabayin aikin hajji zai ga irin halayya da sutura ta rashin mutunci da wasu matan -wasu cikin mahajjata- suke nunawa a ranar sallah matsattsun kaya wasanni marasa kyau tun kafin a gama zaman mina, ballantana a gidan da alhazai suka sauka ka ga yadda ake da 'yan-tuwo-tuwodin abin zai baka mamaki kamar ba a kasa mai tsarki ake ba, idan akai maganar dogon-gida ko Sara-Mansur abirni Makkah da sauran unguwanni kamar su Jabal abin ba'a cewa komai. Ni inagani ya kamata ofishi Najeriya ya shirya wata bita da karantar da 'yan Najeriya da tarbiyantar da su a biranan Makkah da Jiddah da kuma Madina, kuma ya tashi tsaye yaga 'yan Najeriya suna zaune akasar a bisa doka, anan ba ina cewa duka 'yan Najeriya haka suke ba a'a kwata-kwata, akwai tsayayyu, amma mu sani idan fitina ta zo ba tana takaituwa bane ga wadanda suka janyota kamar yadda muka gani a wannan shekarar, zaka iya samun macan da bata ganin jirgin sama a kasaba sai wannan karon amma gashi bala'in wasu ya janyo mata, Allah Madaukakin sarki yana cewa:
          ''Kuma ku ji tsoron fitina wacce ba ta samun danda suka yi zalunci daga cikinku kadai, kuma ku sani lalle ne Allah Mai tsanani ukuba ne'' Sutul-Anfalm aya ta 25.
Mai karatu idan kana jin abinda 'yan Najeriya suke aikata a kasa mai tsarki musamman mata abin zai dauure maka kai matuka da gaske, yanzu idan aka ce maka dukkan matan da suka je Umarar nan data wuce sun dawo nan Najeriya? Me zakace ko kuma ka tambaya.
          Sannan suma hukumar alhazai ta Najeriya ya kamata ta tashi haikan wurin sanyawa maniyyata tsoron Allah da kula da dokokin Sa, a samu malamai masu tsoron Allah wadanda ba himmarsu a biya musu kujeraba, wadannan dakakkun malamai sukasance na dindin-din ko kaso mai yawa daga cikin su sannan abasu damar gudanar da aikin nasu.
3. Mace mai Juna-biyu: Lallekan akwai maganar wahala ga mace mai juna-biyu a aikin hajji mutum ma yana shi kadai ya yacika, amma irin matakin da hukuma ta dauka na haramtawa mace mai juna-biyu aikin hajji wai koda kuwa na wata dayane gaskiya ya kamata a sake duba wannan Magana idan andubeta ta bangaren kiwon lafiya a dubeta ta bangaren addini, babu wani dalili aduk abinda malamai sukai ijima'i aka kafa dalili da shi da ya nuna cewa mace mai juna-biyu bata da damar zuwa aikin hajji, ni ina jin tsoro kada irin wannan hani da aka yiwa wadannan matan yasa aka wannan dayyar matsalar, kada mu sha'afa maganar addini ake yi asalima shi aikin hajjin ginshikine daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar, saboda haka kada ka kuskura ka hana wani wannan aiki ba tare da kanada kakkarfan dalili da zaka gabatarwa Allah ba a ranar kiyama, a shekarar da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- Ya yi aikin Hajji wanda shine kuma akekira da hajjin bankwana, adaidai lokacin da Ma'aikin Allah ya isa Zul-Hulaifah inda nan ne mikatin mutanan madina yana zuwa wurin medakin Sayyidina Abubakar ta sauka (tahaihu), kaga kenan ta fito ne ma da tsohon ciki, awannan tafiya da ake akasa ko a doki ko a rakumi, wanda ba za'a hada hakan da jirgin-sama ba ko na ruwa ko mota ba. Wannan matsananciyar dokar data zamar da mata da yawa Hajji Haram ya kamata a sake dubata, wadda ta sanadiyyar ta ake ruwaito mata da yawa suna zubar da cikinsu, irin wannan mataki na anfani da na'urori masu gani harhanji masu ganin-kwakwaf na cewar indai har anbankado cewar tana da ciki to Hajji Haram ya kamata a sake dubawa.
Shawarwari/Mafita: Ni ina ganin bin wadannan shawarwari zai zama wata mafita ga rashin sake maimaituwar irin wannan al'amari, da muke rokon Allah Ya kiyayemu daga maimaituwar wannan alamari:
1.     Tsayawa da tabbatar da mahrami shar'antacce muddin akwai yadda za'a same shi  ba abinda ake cewa mijin-biza ba.
2.     Gabatar da cikakkiyar bita akan mece ''Rifka Ma'amuna'' sannan suwaye, a kuma gabatar musu da bita ta sanin makamar aikin ''Rifka Ma'amuna''.
3.     Tashi tsaye domin a wayar da kan mutane dangane da matsayin mahrami a shara'a, da kuma bayanin gatan da musulunci ya yiwa mata akan sanya musu mahrami da ya yi.
4.     Kimsawa maniyyata tsoron Allah madaukakin sarki, da kuma falalar da maibin Allah yake da ita da kuma narkon sabawa Allah, a gida Najeriya ko a kasa mai tsarki.
5.     Kimsawa maniyyata bin tafarkin Ma'aikin Allah da kuma cewar rabauta duniya da lahira ta tattarune akan tsantsanta biyayya ga reshi.
6.     Karfa halartar maniyyata  wuraran bita.
7.     Samar da wata manhaja ta baidaya kakkarfa akan abinda ya sha fi bita.
8.     Kara samarwa malamai masu tsoron Allah gurabu a harkar hajji, da kuma basu karfin fada aji.
9.     Kara sa ido da dokar da ta dace ga duk wanda ya yi fitsara a duk wurin da ya shafi Hajji tun daga wuraren bita har kamala aikin hajji.
10. Sanya ido ga dukkanin jahar da ta bari wani alhajinta ya ki dawowa.
11. Karamin ofishin jakadancin Najeriya dake birinin Jiddah ya samara da wata ganawa da 'yan Najeriya dake Makkah, Jiddah da Madina domin karantar da su da kuma kara nuna musu tsarkin wurin da suke zaune.
12. Daukar matakin ladabtarwa ga duk dan Najeriyar da ya karya ittifakiyar da aka yi da kasar Saudiyyah.
13. Sake duba maganar mace me juna-biyu, domin kada mu manta tun kafin Saudiya su nemi su zamar da wasu mata Hajji Haram tuni Najeriya ta zamar da wasu.

          Allah madaukakin sarki ya tsaremu ya tsare mana imanimmu, ya kawo mana karshen wannan kiki-kaka da ake yi da alheri, Allah ya kai alhazammu mata da maza kasa mai tsarki lafiya ya kuma dawo mana da su lafiya. Ya Allah katsare mana kasarmu ka zaunar da mu lafiya da dukkanin kasashen musulmi bakiya, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
 e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu
www.youtube.com/Aliyu Muhammad Sadisu

KURAKURAI A KIRAN SALLAH


بِسْمِ اَللهِ اَلرَّحْمَنِ اَلرَّحِيمِ
Gabatarwa:
Dasunan Allah maiyawan rahama maiyawan jinkai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyan halittar Allah, manzan tsira Annabi Muhammad da Iyalan Sa da Sahabban Sa baki daya da wadanda suka bi bayansu da kyautatawa izuwa ranar sakamako, amin.
Bayan haka, hakika wannan bita da 'yan uwa suka shirya a Shirin Hasken-Musulunci anan Minna, fadar Jahar Neja ayau (Alhamis: 4, ga Ramadan 1432 daidai da 4, Agusta 2011) lallai tana da matukar muhimmanci musamman a irin wannan lokaci, wanda yake a fili take irin gudun mawar da ladanai suke bayarwa a cikin al'umma baki daya.
          Wannan matashiya da zamu tattauna a kanta maitaken "Kura-Kuran da ake samu a kiran sallah'' muna fatan ta zama wani abune da za mu yiwa juna gyara, don gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba, kuma muna so a wannan haduwa ya zana an magance wadannan kura-kurai duddacewa ba su ke nanba, amma har idan muka gane cewa akwai kurakuran kuma muka dauki hanyoyin gyara to zamu sami taimakon Allah akai, Allah ya yi mana jagora amin.
          A cikin wadannan kurakurai akwai wadanda su ke da alaka da maikiran sallah, akwai kuma wadanda suke da alaka da ma'anonin kiran sallah ta yadda idan ma'anar ta canza sai ta maida shi ba kuma kiran sallah ba. Sannan akwai wadanda suke da alaka da al'umma baki daya, lalle wanan yana nuna mana cewa matsayin ladaini a cikin al'umma ba karamin matsayi bane, muna rokon Allah da sunayan kyawawa da siffofin sa madaukaka ya yima jagora amin.
          A yanzu za'a dan lissafa wasu daga ciki, ayi kuma dan karin haske sannan abada shawarwari.
Akwai wadansu abubuwa da zasu shiga cikin kura kuran da ake samu a kiran sallah, kamar:
1. Rashin Kiran Sallah A Farkon Lokacinta: Kamar yadda malamai suka zayyana bayana a littafai cewar kiran sallah shi ne: Sanar da mutane shigar lokacin sallah. Kuma kamar aka sani kowacce sallah tanada lokacinta kuma gashi malam ya kara mana bayi ya kuma fito mana da lokatan fili, wanda rashin kiran sallah a farkon lokacin ta ya haifar da angama kiran sallah sai a tada ikama, wanda anasone tsakanin kiran sallah da tada ikama a sami tazara ta yadda mara alwala zai yi alwala, wanda sai ya yi tsarki ya je ya yi tsarki, anan kenan zamu gane yana daga cikin manyan ayyukan ladan da lokacin sallah ya yi ya kita domin ya sanar da al'umma shigar lokacinta.
          Babbancin kiran sallah da ikama shine: Kiran sallah sanar da mutane shigar lokacin sallah (Ladani kuma shi ya kamata ya fi kowa tantance lokutan sallah), ita kuma ikama: sanar da wadanda ke cikin masallaci anfara sallah.
2. Rashin Tantance Lokaci: Ladani ya sani shi ne mutum na farko da yafi kowa sanin canjin lokaci da yadda yake karuwa da kuma yadda yake raguwa, kuma idan zai yi anfani da agogo kada ya dogara da agogo daya, ya zamana yana dasu uku ko hudu, rashin wannan wadansu ladanan suke kiran sallah tsakaddare ko dab da magariba idan hadari ya rufe rana.
          Ladanifa ya sani sallolin mutane da azuminsu suna ratayene  a wuyanshi, miliyoyin mutane basa shanruwa ko su dakatar da sahur sai ladan ya kira sallah.
3. Rashin Tsayawa A Koyi Kiran Sallah: wannan yana daga cikin manyan matsalolin da ake samu, ta yadda inda za'a kowa ya fadi malamin da ya koya masa kiran sallah to da anyi zuffa. Hakan ya haifar da kowa yake yin yadda ya ga dama, wasuma ka ji da yarukansu suke yi ba da larabciba.
4. Rashin Tantacce Ladanai A Masallaci: wannan yasa kowa ya zama ladani, wanda yake wannan kuwa kuskure ne, wannan baihana a sami ladanai a masallaci gudaba, su zama biyu ko uku ko dai gwargwadon abida ya sawwaka amma tsayyayu, wannan zai sa asan cewa ladani wane yana kiran sallar asubahine kafin alfijiri ya keto amma ladani wane sai bayan alfijiri, kamar yadda ya kasance tsakanin Bilal da Ibnu ummi maktum Allah ya kara musu yarda.
5. Rashin Sanin Ma'anonin Kiran Sallah: wannan ya haifar da abubuwa masu yawa, da basa cikin addini, misali: Ladani ya kammala kiran sallah sai yace 'Ayi alwala, a jaddada' inda yasan ma'anar
حَيَّ عَلَى اَلصَّلاَةِ، حَيَّ عَلَى اَلْفَلاَحِ
Hayya alas Swalah, Hayya alal Falah da bai fadi waccar maganarba.
6. Rashin Kula Da Ladubban Sallah: wannan ya sa sai kaka ladani yana kiran sallah amma sai kaga kamar yana wani abu da bashi da alaka da addini, wani lokacin sai ya yi kamar ya juyawa alkibla baya.
7. Kura kurai a lafuzza: ana samun kurakurai masu tarin yawa a lafuzzan kiran sallah. Wadannan kurakurai sun kashi kashi biyu.
(a) Kuskure mai canza ma'ana: irin wadannan kura-kurai suna fitar da shi daga kiran sallah kwatakwata ya zama wani abu daban, misali:
اَللهُ أَكْبَرُ – أَكْبَارُ
(b) Kuskure na bata lafuzza: wanda yake fitar da shi daga duniyar larabci, misali:
أشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رسولُ اللهِ
Shawarwari:
A takaitaccen wanna jawabi da kuma wadannan abubuwa dana gani ina bada shwara kamar haka:
1. Bayar da mintina bayan kiran sallah kafin tayar da sallah, wannan ko zai tabbatane idan ankira kowacce sallah a farkon lokacin. Misali Azahar minti 20 la'asar minti 15 magariba minti 10 lisha minti 15 asuba minti 20.
2. Ladani ya zama yana da agogo kamar uku banda na wayarshi, kuma ba zaije kiran sallah ba sai ya duba su duka.
3. Aiki da dukkan abubuwan da aka gabatar a wannan bita.
4. Gyara inda duk mutum ya ji yana da kuskure.
5. Isar da wadannan bayanai ga wadanda basu zo wannan bita ba.
6. Ladanai su samara da wata haduwa da zasu dinga yi lokaci lokaci domin tuntubar juna koda ko za'a fara a matakin unguwa unguwa ne.
7. Ci gaba da shirya irin wannan bitar lokaci bayan lokaci
8. Koyon kiran sallah baki da baki daga wurin malamai masana.
          Allah ya gafartamana ya kuma ya fe mana, Allah ya karbi ayyukammu amin summa amin.
وصلى الله وسلم على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
 e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu
www.youtube.com/Aliyu Muhammad Sadisu

Friday, September 28, 2012

HUKUNCE-HUKUNCEN LAYYAH


Gabatarwa: Dasunan Allah Mai yawan rahama maiyawai jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a wannan karon za mu karkata akalar mu zuwa wani bangare da ya ke hararomu a 'yan kwanakin nan, wannanan bangaran kuwa shi ne na LAYYAH! Domin mu ga yadda musulunci ya tsara mana komai abinda ya rage kawai a garemu shi ne bi, komai angama, Allah tabbatar da duga-dugammu akan tafarkin Ma'aikin Allah.
Mecece Layyah?: "Layyah, ita ce dukkan abinda ake neman kusanci ga Allah ta sanadiyyar yankashi ko soke shi, a kwanukan yanka na abinda ya shafi dabbobin gida"( wato: Rago da tinkiya, akuya da taure, sa da saniya, rakumi da rakuma). Wannan shi ake nufi da layya, wanda anan kawai mai karatu yasan wanne yanka ne na layyah? Wannene kuma na aci nama kawai. Yanzu inda za mu bi wannan ta'arifin a hankali zamu ga cewa, da aka ce ""Layyah, ita ce dukkan abinda ake neman kusanci ga Allah ta sanadiyyar yankashi ko soke shi," wannan yana nuna cewa idan ba'a nufaci Allah da yankanba to abinda aka yanka zai amsa sunan Layyah kamar cewa 'Sabo da yara' da makamantan irin wadannan maganganu day a kamata a kauce musu. Amma da akace ' a kwanukan yanka' wannan ya nuna idan akai kafin wadannan kwanuka ko bayansu abin yankan bai zama Layyaba. Da aka ce 'na abinda ya shafi dabbobin gida' wadannane kawai dabbobin da ake layya da wadanda aka ammata a sama cikin baka biyu.
Tabbatuwar Layyah Ashara'a: Layyya ta tabbata da fadin Allah Mai girma da daukaka a Suratul-Kauthar aya ta 2. "To kai sallah don Ubangijinka, kuma ka soke abin Layyarka" wato ya yi Sallar idi, sannan kuma iyi sanka, adaya daga cikin maganganun malaman Tafsiri. Sannan kuma Layyah ta tabbata da aikin Ma'aikin tsira da a mincing Allah su tabbata agashi domin ya yanka Layyarshi da hannun mai alfarma ya yanka ruguna biyu masu kaho, kamar yadda Anas ya ruwaito, kuma malamai sunyi Ijma'I akan haka.
Hukuncin Layyah: Sunna ce maikarfi ga wanda ya sami iko mace ko namiji, ba wajibi bace saidai idan mutum ne ya dorawa kansa, kamar ya yi alwashi cewa In ya samu wannan aikin ko in ya ci jarabawannan ko in medakin shi ta sauka lafiya sai ya yi layya, to da zarar abinda ya anbata ya auku layya ta zama wajibi akanshi.
Falalar Yin Layyah: Nana Aishah Allah ya kara mata yarda ta ruwaito cewa lallai Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce " Dan'adam bai taba yin wani aiki aranar Babbar Sallah ba da yafi soyiwa a gurin Allah  kamar zubar da jinni ba. Lalle tabbas zata zo (tabbar layya) ranar kiyama da kahonta, da gashinta, kuma lallai jinin tabbas yana aukuwa ga Allah a wani wuri tun kafi ya diga a kasa, ku yi ta da dadin rai." Tirmizi ya ruwato shi hadisi na 1493.
Mace Na Layyah?: Anan mu sani duk abibda  shari'ar musulunci ta zo da shi ba banbanci mace da na miji sai abinda dalili ya banbance, saboda haka ya halatta mace ta yi layya kuma mijinta ya yi idan yana da hali hakanan 'ya'yanta, mu sani layyah ba biki bace ibadace da ake baiwa mutum lada idan ya yi kamar yadda akace ya yi kuma ya yi shi domin Allah, anan yana dakyau maza su sani iyalansu ba gasa suke da su ba, ibadace da Allah Ya shar'anta ta akan maza da mata.
Ya Halatta Aci Bashi?: E, ya hallata ga mutumin da yake da tabbas na kudi ya ci bashi domin ya sayi dabbar da zai layya da ita, mu lura munce wanda yak e da tabbas, kamar ma'aikacin da yake jiran albashi, ko dankasun da ya sayo kaya ga shi jibge ba'a yana jiran masu saya.
Dabbobin Da Ba'a Layya Da Su: Anan yana da kyau wanda zai yi layyah ya sa ido sosai ya tabbatar da cewa dabbar da zai yanka bata sami kanta cikin wadannan dabbobin da ba'a layya dasu ba, domin mu sani shi Allah ba'a masa karbi kar ka rasa -tsarki ya tabbata a gareshi. Hadisi daga Barra'u dan Azib Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce "Ba'ayin layyah da gurguwa wacce gurguntakatta ta a fili take, hakanan da Mai ido daya wacce hakan a fili yake (ina ga makauniya baki daya?), hakanan da mara lafiya wacce rashin lafiyar tat a a fili yake, hakanan da kyamusassa wacce take bata da mai. Hakanan Aliyu bn Abi Talib Allah ya kara masa yarda, ya ce ' Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- ya umar ce mu da musa ido sosai akan idanu da kunnuwa, kuma kada muyi layya da mai yankakken kunne ta fuskar tsawo ko fadi na kunnen' Timizi ya ruwaito 1498, duk wannan idan ya bayyana kamar daya bisa uku, dukkanin wadannan bayanai suna nuna mana itafa layya ibada ce yadda ake so zaka yi, ba yadda kai kake so ba, balle ace kwai bage-bagen dabba.
Siffar Ragon Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata aga reshi. Wannan yana dakyau amatsayinka na wanda yake koyi da Ma'aikin Allah kasan Shi da me ya yi layyah? Anas ibnu Malik, yake cewa ''Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya yi layya da raguna biyu, farare masu ratsi baki-baki, masu kaho, ya yankasu da hannunshi, ya anbaci Allah ya yi kabbar''  Bukhari 5565, Muslim 1966, Tirmizi1494. wannan hadisi ba karamin sakwnni yake dauke da su ba, kamar yadda bayanai za su zo nan gaba. Zamu fahimci abinda ya fi shi ne duk mai layyah ya yanka layyar shi da hannun shi, kuma karatun yankan 'Bismillahi Wallahu Akbar. Ya Allah ka karbamin ni da iyalan gidana (in ya sanya iyalan na shi cikin layyar)
Ya Halatta A Hada Kudi Ayi Layyah? Tabbas wanna ba karamar tambaya bace so ake musulmi ya zama da zaran wani abu ya same shi ya san yadda zai warware al'amurra akan karantarwar Annabinshi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Bai halatta sama da mutum guda su taru akan rago ko tinkiya ko taure ko akuya ba, amma ya halatta mutane biyu zuwa bakwai su hada kudi akan sa, ko saniya, ko rakumi, ko rakuma, domin su yi layyah.
Kwanakin Layyah: Abinda aka fi so shine mutum ya yanka layyarsa a ranar sallah bayan ansakko sallah kenan, amma idan hakan bai samuba ya halatta ya yanka washegari wato ranar shadaya idan hakan bai yiwuba ya samu ya yanka wanwashegari wato ranar shibiyu duk wadannanan layyarsu ta yi ba kuma ramuwa suka yi ba.
Yadda Ake Da Naman Layyah: bayan anyanka dabbar kai da ka yi  zaka diba a ciki ka ci kuma zaka bayar da wani kason kyauta wani kuma kabayar sadaka, wato zaka kasa shi gida uku kenana, ya halatta kabayar da shi danye kamar yadda ya hallata kabayar da shi soyayye ko gasasshe, anan idan an tashi rabon bawai lalle zakaba wanda ya baka bane, babban makasudin layyah bayan neman kusanci da Allah shine  al'ummar musulmi su tashi su kasha kwalamar dake cikin wadannan kwanaki da wanda ya yi da wanda bai yiba, kenan ba maganar ka jin-jina nauyin wanda aka kawo maka domin kaima ka maida irinshi.
Kammalawa: Awannan dan-takaitaccan bayani da ya gabata munsan mecece layyah da matsayinta a musulunci, kuma munsan cewa layyah ibasace ba biki bace, sannan maza na yi kuma mata na yi, sannan ba'ace sai mai mata ba ko sai mai miji, kuma munfahimci cewa layyah wata hanyace ta takaita talauci da kwadayi a cikin al'umma, sannan munsan kadan daga cikin hukunce-hukuncenta, Allah nuna mana lokacin ya kuma karbi ibadarmu amin summa amin, ayi sallah lafiya Allah Ya maimaitana cikin koshin lafiya da imani. Naku:
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
 e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu

Thursday, September 27, 2012

ZIYARA A BIRNIN MADINA


بسم الله الرحمن الرحيم
الحمد لله رب العالمين، والصلاة والسلام على نبينا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين
Gabatarwa: Dasunan Allah mai yawam rahama mai yawan jinkai, dukkan godiya ta tabbata a gareshi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabimmu Annabi Muhammad, da iyalanshi da sahabbanshi baki daya.
          Bayan haka hakika wannan gidauniya ta Annuriyyah ta nema daga gare ni da in kasance cikin wadanda za su gabatarwa da Alhazai bita cikin jerin gwanon abubuwan da yake da alaka da su inda aka fara wannar bita tun ranar lahadin da ta gabata, matashiyar da zan gabatar da jawabi akai itace: Ziyara A Garin Madina. Wanda nake rokon Allah da dukkanin sunayansa mafiya tsarki da siffofinsa mafiya kamala da ya yi mini jagora, ya kuma albarkaci wannan zama namu da wannar gidauniya ya karba mana ayyukammu, amin.
          Wannan jawabi zai tattaru ne akan:
-         Gabatarwa
-         Shinfida
-         Falalar Birnin Madina
-         Ladubban Zama A Birnin Madina
-         Falalar Sallah A Masallacin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi)
-         Abubuwan Yi A Birnin Madina
-         Ibadu
-         Wuraren Ziyara Da Takaitaccen Tarihinsu.
Shinfida. Lalle madina wacce take birnine na Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) inda kuma take masaukar wahayi inda Ma'ika jibrilu amintaccen Allah ya dinga sassauka ga Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), birnin da yake shi ne matattarar imani, mahadar dukkanin wadanda suka yi hijira da wadanda suka tarbesu, hedikwatar musulunci ta farko wanda yake anan ne aka kafa tutar jihadi, daga nan ne kuma aka fita domin a fitar da mutane daga duhu zuwa ga haske, daga nan dinne duniya ta dau haske baki daya, nan ne kuma Allah Madaukakin sarki Ya zabawa Manzan Shi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya zama wurin hijirarshi, a wannan birni kuma ya rayu, kuma a nan ya koma ga Mahaliccin shi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), anan kuma kabarinshi yake wanda yake babu wani mutum da zai iya tabbatar da inda kabarin wani Abbabi yake inbanda kabarin shi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi). Allah Ya kaimu wannan birni na Ma'aikin shi lafiya, amin.
          A yanzu haka za mu bi wadancan gabobin da suka gabata daya-bayan-daya Allah Ya yi mana jagora, amin.
Falalar Birnin Madina: Hakika wannan birni yana da dunbun daraja da falala wanda yake Allah kadai ya san iyakarsu, ayanzu haka ga kadan daga cikin abinda ya tabbata daga Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) na falalar wannan birni:
(1) Allah madaukakin sarki ya sanya shi Harami amintacce kamar yadda ya sanya birinin Makkah harami amintacce, Allah madaukakin sarki yana cewa dangane da birnin Makkah:
Ma'ana: ''Kuma sukace: Har in mukabi gaskiyar dake tare da kai za'a fitar da mu daga kasarmu. Sai Allah yace: Yanzu shin bamu tabbatar musu da wani Harami (na musamman) wanda yake amintacce ba, ana shigo da dukkan nau'ukan 'ya'yan itatuwa wanda yake arzikine daka garemu?, sai dai mafi yawansu ba su sani ba''. (Suratul-Kasas, aya ta:57) Allah madaukakin sarki ya fadi haka a wurare da dama dan gane da Makkah.
    Kuma Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yana cewa dangane da Madina
(( إِنَّ إِبْرَاهِيمَ حَرَّمَ مَكَّةَ، وَإِنِّي حَرَّمْتُ اَلْمَدِينَةَ)) رَوَاهُ مُسْلِم
Ma'ana: Lalle (Annabi) Ibrahim ya haramtar da Makkah, Kuma lalle ni na ramtar da Madina)).
Wannan Hadisi Muslim ne ya ruwaito shi.
(2) Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya kira wannan birni da suna ''Taibah'' wato daddadan abu, wato kenan birnine mai dadi, mai albarka.
(3) Imani yana tattarewa ya koma wannan birni mai albarka, Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yana cewa :
مُتَّفَقٌ عَلَيْهِ ((   ((إِنَّ اَلإيـمَانَ لَيَأْرَزُ إِلَى اَلْمَدِينَةِ كَمَا تَأْرَزُ اَلْحَيَّةُ إِلَى حُجْرِهَا
Ma'ana: "Lalle Imani yana tattara zuwa madina kamar yadda macijiya take tattara a raminta".
Bukhari da Muslim suka ruwaito.
(4) Birnine da yake haxiye sauran birane. Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya siffanta ta da cewa garine da yake cinye garuruwa, kamar yadda yake cewa ''An umarceni –da yin hijira zuwa-wani gari da yake cinye garuruwa, suna kiranshi da: Yasriba-wato-Madina'' Bukhari da Muslim suka ruwaito.
             Yasriba shine sunan Madina kafin isar Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) da ya isa sai ya canza sunan garin, Allah madaukakin sarki yana cewa –A lokacin da yake fada mana maganar munafuqai aranar Gwalalo.  Ma'ana: Kuma a lokacin da wata tawaga daga cikinsu (su munamukai sukace) Ya ku mutanan Yasriba baku da matsaya ku koma….)
(5) Birnine da Allah ya zabeshi ya zama wurin hijirar manzonshi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi).
(6) Yadda ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya nuna darajarta da girman sabawa Allah a cikinta, Ma'aikin Allah yana cewa:
((اَلْمَدِينَةُ حَرَمٌ مَا بَيْنَ عَيْرٍ إِلَى ثَوْرٍ، مَنْ أَحْدَثَ فِيهَا حَدَثًا أَوْ آوَى مُحْدِثًا فَعَلَيْهِ لَعْنَةُ اَللهِ وَالْمَلاَئِكَةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ))                                   رَوَاهُ اَلْبُخَارِيُّ وَمُسْلِم.
Ma'ana: Madina Haramce daga (Dutsan) Air zuwa (Dutsan) Saur, duk wanda ya aikata barna a cikinta ko ya baiwa mabarnaci mafaka Tsinuwar Allah ta tabbata a kanshi da Mala'iku da mutane baki daya''                    Bukhari da Muslim.
(7) Addu'ar Albarka. Yana daga cikin falalar wannan birni addu'ar albarka da ya samu daga ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), ma'aikin Allah yana cewa:
اَللَّهُمَّ بَارِكْ لَنَا فِي ثَمَرِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مَدِينَتِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي صَاعِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مُدِّنَا)) مسلم
Ma'ana ''Ya Allah ka sanya mana albarka a 'ya'yan itatuwammu, ka sanya mana albarka a Madinarmu, ka sanya mana albarka a Sa'immu, ka sanya mana albarka a mudummu''  
                                                                    Muslinme ya ruwaito.
(8) Annoba da Julal basa shiga madina. Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yana cewa:
''Mala'ikune akan ganuwowin madina Annoba bata shigarta haka namma Jujal''  Bukhari da Muslim.
      Wannan kadan kenan dangane da birnin madina banda abinda ya gabata tun a shinfida, sabo da lokaci.
Ladubban Zama A Madina: Lalle duk wanda Allah ya kaddari cewa yana cikin wadanda za su zauna kwana ko awanni a cikin wannan birni mai albarka to lalle ya sani cewa wannan ba karamar falala bace da Allah ya yi masa, sabo da haka sai ya godewa Allah akan wannan falalar, ya kuma kula da ladubban zama a wannan birni mai daraja kamar haka:
(1) Ka so wannan gari sabo da falalar da yake da ita, da son da ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yake masa.
     Anas Ibnu Malik (Allah Ya Kara mishi yarda) yana cewa ''Lalle ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya kasance idan ya dawo daga tafiya sai ya hango gine-ginen madina sai ya gyara abin zamansa, in kuma yana kan dabbane sai ya motsa ta, Saboda son da yake mata (wato madina).
(2) Ka kwadaitu da tsayuwa a kan al'amarin Allah, ka zama mai lizimtar biyayyah ga Allah da manzan Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), kana mai tsananin kaucewa sabon Allah da bidi'oi domin wadannan al'murra yinsu a harami ba karamin zunubi bane.
(3) Lizimtar Sallah a cikin masallacin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) kamar yadda bayani zai zo.
(4) Ka zama kyakkyawan abin koyi, domin fa kana inda daga nanne hasken ya haskaka duniya baki daya.
(5) Ka tuna fa kana inda nanne masaukar wahayi, kuma inda Allah ya zabawa manzanshi ya zame masa wurin hijira, kana inda yake nanne matattarar imani, kana inda nance makarantar da sahabban ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) su kai karatu kada kai wani aiki da ya sabawa na makarantarsu da malaminsu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi).
(6) Kada kaga tsuntuwa ka dauka sai dai idan zakai cigiya.
Falalar Sallah A Masallacin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi).
      Hakika sallah a wannan masallaci da wannan Annabi ya gina tana da matukar falala wacce bai kamata wanda ya sami kanshi a inda wannan masallaci yake ba ya yi sakaci, hadisai tabbatattu sun yi bayanin matsayin wannan masallaci da matsayin sallah a cikin shi. Na farko dai wannan masallaci yana cikin masallatai uku da ake nikar gari domin ziyartar su, kamar yadda Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yake cewa a hadisin Bukhari da Muslim.
((لاَ تُشَدُّ اَلرِّحَالُ إِلاَّ إِلَى ثَلاَثَةِ مَسَاجِدَ: اَلْمَسْجِدِ اَلْحَرَامِ، وَمَسْجِدِي هَذَا، وَالْمَسْجِدِ اَلأَقْصَى)) متفق عليه
Ma'ana: ''Ba'a nikar gari (don ziyara) sai masallatai uku; Masallaci mai alfarma (dake makka), da kuma wannan masallacin nawa, (dake birnin madina) da kuma masallacin can nesa (wandake Kudus).   Bukhari da Muslim.
    Abinda Ya Shafi Falalar Sallah a wannan masallacin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yana cewa;
((صَلاَةٌ فِي مَسْجِدِي هَذَا أَفْضَلُ مِنْ أَلْفِ صَلاَةٍ فِيمَا سِوَاهُ إِلاَّ اَلْمَسْجِدَ اَلْحَرَامَ)) متفق عليه
''Yin Sallah a cikin masallacin nan nawa ya fi salloli dubu a (masallacin) da ba shi ba in banda masallacin harami (Makka)'' Bukhari da Muslim.
 Lalle wannan ba karamar garabasa bace da rahamar Allah ga bayinsa, kuma yana da kyau mu fahimci abubuwa kamar haka:
a.     Wannan ninkin ladan da abinda yafi dubu ba wai ya takaitu da farilla bane banda nafila, ko ko nafila banda farilla, a'a ya shafi duka, raka'a biyu ta farilla acikinsa ta fi raka'oi dubu na farilla a inda ba shiba in banda haramin makkah, raka'a biyu ta nafila sun fi raka'o'i dubu na nafila a inda ba nan ba.
b.    Wannan ladan bawai ya takaitu a iya inda masallacin yake a lokacin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) kawai bane ya shafi har fadadashin da aka yi ne.
c.     Sai dai duk wanda yabi sallah a wajan masallaci yana da ladan jam'i amma baida wancan ladan da aka anbata domin a waje ya yi sallah ba a ciki ba. Anan nake cewa irin sakacin da ake na a zauna a waje aita fira ko aje a sayo kaya niki-niki jami'ai su hana a shiga masallaci da shi mutum ya yi sallah a waje bakaramar asara bace.
d.    A cikin masallacin akwai wani wuri wato Raudha, Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) a hadisin Bukhari da Muslim ya siffanta wurin da cewa Dausayine daga cikin dausayin aljanna. Kebance wannan wuri da irin wannan siffa lalle ya nuna falalarsa doruwa akan sauran wuraren.
Abubuwan Yi A Birnin Madina: Lalle ilalla a yanzu kasan takaitaccan bayani dangane da birnin madaina falalar birnin da ladubban zama a birnin. To yanzu idan Allah ya sa ka isa wannan birni menene abinyi kada ka manta tafiyarka ba tafiyar bude ido bace. Saboda haka babban abinda ya kaika shine ziyarar wannan masallaci da wannan Annabi cikamakin Annabawa farin jakada ya gina da hannayanshi masu albarka, sabo dahaka kada hankalinka ya dauku daga barin salloli da karatun alkur'ani da zikiri a cikin wannan masallaci, domin duk ibadar da ka gudanar a cikin wannan masallaci ladanta ya nin-ninka wacce aka yi a wajan wannan masallaci inbanda masallaci Ka'abah.
     Sannan yanzu bari a kawo abinda ake yi a birnin madina:
Ibadu. Idan akace ibadu to jam'ine na ibada ita kuma ibada  ''Gamamman sunane da ya tara dukkan abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi na ayyuka ko na Magana na zahiri ko na baxini''
          Yanzu munsan mecece ibada, kuma lura da ta'arifin ta lalle munsan tanada nau'i daban-daban, kadan daga ciki sune:
(1) Ikhlasi: Yi domin Allah,  kada ka kuskura ka yi wani aiki a wannan birni mai tarin albarka wanda yake badon Allah ba ko Allah bai saka ba, lalle mutum zai yi asara, ba'a lissafawa Allah ayyuka ko ayi mishi gori wadannan suna lalata ayyuka.
(2) Salloli A Kan Lokaci: Lalle wanda ya sami kanshi a wannan birni mai albarka kada ya kuskura ya sake da sallah, to yanzu wanda ya yi sake da sallah a inda aka saukar da sallar to a inane ba zai yi sake da itaba, musamman a cikin wannan masallaci maitarin albarka.
(3) Yawaita Karatun Alkur'ani: anan ba wai sai ka haddace ba ko ka sauka a'a iya inda ka iya ka nace da karanta shi, wannan ba karamin alkhairi bane.
(4) Yawaita Zikiri, Istighfari, Salatin Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) Zikiran safe  da na yamma, kada ka manta saboda wadannan al'amura kabar kasarka, wurin aikinka, ka rufe shagonka kada mutum ya yi wasa da wadannan ayyuka musamman a cikin wannan masallaci da ake nunnunka ayyuka.
(5) Taimakon Juna: Lalle kada zuciyarmu ta yi nesa da taimakawa juna abune mai mahimmanci tabangaren guzuri shawara nasiha ga juna, zaburar da juna, neman …''
Wuraren Ziyara Da Takaitaccan Tarihinsu: Yana dakyau mu tsaya mu yi karatun ta-natsu a kan abinda ya shafi ziyara a makka ko a madina kada harkar ziyara tasa ka rasa sallah a cikin wadannan masallatai wadanda suke sune jigo uban-tafiya. Yanzu za'a lissafo wuraren ziyara, kamar haka:
(1) Masallacin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi). Wannan masallaci ma'aikin Allah Ya sayi filin wurinne da kudinsa sannan ya aza harsashin gininshi da hannayen sa masu albarka, masallacin ya zama nanne wurin sallah nanne kuma makaranta inda yake karantarwa kuma ananne yake alqalanci (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), anan yake tarbar baqinshi.
  Yadda Ake Ziyara a wannan masallaci shi ne, dazarar kun isa madina ankaiku masauki kowa ya aje kayansa sai a nufi wannan masallaci maialbarka idan akaje sai afara gabatar da kafar dama lokacin shiga, sai kai addu'a kace:
بِسْمِ اَللهِ، وَالصَّلاَةُ وَالسَّلاَمُ عَلَى رَسُولِ اَللهِ، اَللَّهُمَّ اَفْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ
Sannan sai ka yi sallah raka'a biyu, idan ka tarar ana farilla sai kabi ta wadatar maka, idan kuma ka isa an idar da sallah  sai ka yi farillar.
(2)  Kabarin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) Da manyan sahabbanshi biyu: wadannan kabarurruka suna cikin dakin sayyida Aisha ne –Allah ya kara mata yarda- kamar yadda kowa ya sani ne masallacin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) daban yake dakunan iyalanshi ma daban suke wato gini ya rabasu, bayan da Allah ya karbi yaruwar wannan Annabi mai daraja a dakin Sayyida Aisha sai aka yi masa kabari a dakin, haka kuma wadannan manyan sahabbai nashi guda biyu wadanda zaka ji yana cewa na kasance ni da Abubakar da Umar na yi  kaza ni da Abubakar da Umar, Allah ya kara musu daukaka da karamci da kuma yarda, amin.
     Yadda Ake Ziyara anan mutum zaizo ta gaba sai ya fuskanci qabarin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) sai yace:
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا رَسُولَ اَللهِ وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكَاتُهُ صَلَّى اَللهُ وَسَلَّمَ وَبَارَكَ عَلَيْكَ، وَجَزَاكَ أَفْضَلَ مَا جَزَى نَبِيَّا عَنْ أُمَّتِهِ.
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareka ya ma'aikin Allah da rahamarsa da albarkarsa, Allah ya kara maka salati da aminci da kuma albarka, ya sakanka maka da mafificin abinda ya sakankawa wani Annabi dangane da al'ummarsa.
Mutum zai yi hakane ba tare da daga murya ba, domin ba'a daga wa ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) murya yana da rai ko bayan ya rasu, ka duba Suratil-Hujrat aya ta (2-3).
Sannan sai ya dan yi dama kadan sai yace:
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا أَبَا بَكْرِ اَلصِّدِّيقَ
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareka ya Abubakar maigaskiya.
sannan sai ya danyi dama kadan, sai yace:
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا أَبَا حَفْصٍ عُمَرَ اَلْفَارُوقَ
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareka ya wannan gwarzo Umar.
Sai mutum ya yi musu adda'a domin sun yiwa wannan addini hidima da duk abinda za su iya, Allah ya kara musu daukaka.
(3) Makabartar Baki'a: ita wannan kushewa bata da nisa da masallacin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) bai wuce taku kadan ba, itace babbar kushewar madina nan aka binne su Nana Aisha da Nana Fafima da Sayyina Usman da manya-manyan sahabban ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), nan kuma aka binne su Imamu Malik, Allah ya kara musu yarda, amin.
   Idan mutum yaje wannan makabarta zaicene :
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكُمْ دَارَ قَوْمٍ مُؤْمِنِينَ وَإِنَّا إِنْ شَاءَ اَللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، يَغْفِرُ اَللهُ لَنَا وَلَكُمْ
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareku ya mutanan wannan gida da suke muminai, muma in Allah ya yarda munanan zamu tarar da ku, Allah ya gafartama ya gafarta muku.
(4) Shuhada'u Uhud: Kushewar shahidan Uhudu kushewace dake dab da dutsan Uhudu, anan ne aka yiwa sahabban ma'aikin Allah wadanda suka yi shahada a wannan yaki mai cike da darussa janaza, wanna a cikinsu akwai Sayyidina Hamza wanda Allah yaba da labarinsa a cikin suratul Ali-Imrana.
  Siffar yadda ake ziyara anan itace irin yadda aka yi a baki'a, wato idan kaje makabartar sai kace:
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكُمْ دَارَ قَوْمٍ مُؤْمِنِينَ وَإِنَّا إِنْ شَاءَ اَللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، يَغْفِرُ اَللهُ لَنَا وَلَكُمْ
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareku ya mutanan wannan gida da suke muminai, muma in Allah ya yarda munanan zamu tarar da ku, Allah ya gafartama ya gafarta muku.
(5) Masallacin Kuba: Wannan shine masallacin da ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya gina kafin ya shiga birnin madina, domin ya yi kwanaki anan kafin ya shiga, anan ne kuma ya yi sallar juma'a ta  farko a musulunci.
 Falalar Masallacin Kuba: wannan masallci yana da falala ta musamman da ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya bayya, Abdullahi dan Umar (Allah ya kara masa yarda) yace: ''Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya kasance yana zuwa masallacin Kuba a duk ranar asabar wani lokacin ya tafi a kafa wani lokacin kuma ya hau abin hawa sai ya yi sallah raka'a biyu''                                                               Bukhari da Muslim.
  Hakanan ankarbo daga Sahal dan Hunaif (Allah Ya kara masa yarda) yace Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yace:
           ''Duk wanda ya yi tsarki daga gidanshi sannan ya je (masallacin) Kuba ya yi sallah a cikin shi to ya kasance yana da ladan Umarah''  Ibnu Majah da wasu suka ruwaito.
           Wadannan sune wuraran ziyara shar'antattu su biyar (5), biyu masallatai (Masallacin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) da masallacin Kuba), uku makabartu.
          Amma akwai wasu wurare da mutane suke zuwa da sunan ziyara wadannan wurare sun kasu kashi biyu:
(1)            Akwaishi A Tarihi: Kamar kiblatai, wannan a kwai shi a tarihi sai dai masallacin da ake kira kiblataini a yau shine wanda tarihin ya nuna ? to wannan malamai masana Sira da Tarihi sun karawa juna sani akan haka.
(2)            Babu Shi A Tarihi: a kwai wuraren da suke inda zaka karade littafai dakyar ka ji duriyarsu domin babu su, an same su ne a zamanin wadansu dauloli da suka wuce.
Shawarwari:
Ni ina gabatar da nasiha ga 'yan-uwa kamar haka:
1.    Rikon abinda ya kaika.
2.    Kada ka dauki wannan tafiya a matsayin yawon bude ido.
3.    Lizimtar Ibada a wadannan masallatai.
4.    Sanya lokacin ziyara ya kasance da safe, domin kada ka rasa sallah a masallacin ma'aiki (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi).
5.    Kimanta lokaci.
6.    Abokantaka da wanda yake da himma.
7.    Barin shiga kasuwa sai an idar da sallar isha.
8.    Daraja wannan wuri domin Allah ya daraja shi
9.    Ba'a dawafi a madina domin a ka'aba kawai ake dawafi, kamar yadda ya fada a Suratul-Hajj
Kira ga wannan gidauniya  da ta ci gaba da gudanar da irin wannan bita, da fatan Allah ya sanya mata albarka, ya kuma karbi ayyukammu.
وصلى الله وسلم على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
 e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu