Saturday, April 3, 2010

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa 1#

MUNBARIN-MUSULUNCI.blogspot.com
Don bayyana yadda Musulunci ya haskaka mana dukkanin rayuwarmu

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa.1#

Gabatarwa: Awannan lokacin da izinin Allah mai kowa mai komai muna fatan kawo wadansu abubuwa bakwai masu halakarwa, wadannan abubuwa Ma'aikin Allah-Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- Shine yace masu halakarwa ne. Lalle dukkanin abinda Ma'aikin Allah ya ce 'Abu kaza mai halakarwane' To lalle ya kamata mutum musulmi ya yi kokarin sanin wannan abin, tun da sauran nunfashinshi. Ma'aikin Allah- Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- Ya ce "Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa ! (Sai Sahabban shi -Allah ya kara musu yarda suka ce) 'Wadanne abubuwane wadannan ya Ma'aikin Allah?. Sai Ma'aikin Allah- Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- Ya ce " Shirka da Allah, da Asiri da Kashe raid a Allah ya haramta a kashe ba tare da hakki ba, da Cin Riba da cin Dukiyar Maraya da Ja-da-baya lokacin gumurzu, da Yiwa mace mumina wacce ta kame kanta wacce bata san ya ake barna ba mutum ya yi wa irin wannan macan kazafi." Wannan Hadisi Bukhari ya ruwaitu a wurare da dama a cikin littafinsa. To wadannan fa sune abubuwa bakwaidin da ma'aikin Allah- Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- ya gargadi wannan al'umma, yace ku yi nesa da su kada ku kuskura ku yi kusa da su.
Ayanzu wadannan abubuwa bakwai su muke fatan zamu yi bayaninsu daya bayan daya, da yardarm Allah, muna rokonShi da sunayanSa kyawawa da siffofinshi madaukaka da ya yi mana jagora.

Abu Na Farko: Shirka da Allah. Itace 'hada bautar Allah da wani' wannan ya nuna cewa bautawa Allah Shi kadai, shine abinda yake daidai, amma hada Allah da wani, bai taba halatta. Wannan yasa Allah madaukakin sarki ya dinga turo Annabawa da Manzanni do min su tabbatar da tsan-tsar Tauhidi, haka kuma Annabawan da Manzannin suka tsaya tsayin daka domin tabbatar da sun isar da wannan aike da aka yi musu, muna shaidawa da cewar Annabawan Allah da Manzannin shi sun isar da sakon da ya aikosu da shi.
Ma'aikin Allah ya dauki tsawan she karu goma cur yana kira zuwa ga tsantsar Tauhidi acikin shekaru ashirin da uku da ya yi yana raye bayan aiko shi a matsayin Manzo, wanda hakan ya ke nuna mana matsayin tauhidi. Ya tura wakilai da yawa wurare daba-daban, misali ya tura Mu'azu Dan Jabal zuwa kasar Yaman yace "Lalle kai zaka je wurin mutanan da suna dauke da littafi, Farkon Abin da zaka kira su akai shine su kadaita Allah'' wannan Hadisi Bukhari ya ruwaitoshi. Wannan bayani zai tabbatar mana da cewa lalle ya wajaba mu tsaya domin karanta da karantar da Tauhidi, domin da Tauhidi ne mutane za su rabauta duniya da lahira, da shi ne kuma za'a sami hadinkan a'ummar musulmi baki dayanta, ta zama 'Tsintsiya madaurinki daya' wanda wannan shi ne matan ko wanne musulmi.
Ita shirka da Ma'aikin ya fara lissafata acikin jerin gwanon wadannan abubuwa guda bakwai, tana da matukar hadarin gaske, daga cikin manyan hatsarinta wanda ba wanda ya ke so ya afka, ita shirka tana tabbatar da mutun cikin azabar Allah har'abada. Tana sa Mutun ya rasa ceton Manzan Allah Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi. Tana sa mutum ya yi asarar dinbin ayyukan alheri da ya yi a duniya, kamar taimakawa nakasassu, sadar da zumunci…'. Saboda haka dukkan wani aikin ibada da Allah da Manzanshi su ka yi umurni da ayi to mutum ya tabbatar ya yi shi ga Allah kadai kada ya hada kowa tare da Allah. Kuma idan akace Ibada ana nufin 'Gamamman suna ne da yake tara dukkan abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi' to kaga anan muna da nau'ukan ibada masu tarin yawa kamar, Karatun Kur'ani, Sallah, Azumi, Salatin Annabi, Is'tigfari, Hailala, Sada zumunci,Gaida mara lafiya, Yanka, Neman tsari, Neman Agaji, Tawakkali, Kauna, So da sauran su, wadanda ba'a ambata ba dukkan su na Allah ne Kadai kada mutum ya kuskura ya karkatar da wani nau'i guda zuwa ga wanin Allah, domin Allah yana cewa 'Ku bautawa Allah (Shi kadai) kada ku hada shi da komai' Suratun-Nisa'i, aya ta 36, da kuma fadin Allah adai cikin Surar 'Lalle Allah baya gafarwa idan akai Shirka da shi, yana gafarta abinda bai kai haka ba, dukkan wanda ya yi shirka da Allah to hakika ya kirkiri Zunubi mai girma' Suratun –Nisa'I aya ta 48. wanna yasa Annabawa da Manzanni ba su bari anhada su da Allah wurin bautaba domin sun san basu can-canta ba, Allah kadai mabuwayi shine ya can-canta Maganganun Annabi Isah –Amincin Allah ya tabbata a gare shi- cikin suratul Ma'idah sun tabbatar da haka. Hakanan maganganun Ma'aikin Allah cikin Hadisanshi ingantattu haka kuma.

Karkasuwar Shirka:
Malamai sun yi bayanin cewa shirka ta kasu kashi biyu; Kashi na farko: Shirkar da Take futar da mutum da musulunci (Allah ya Tsare mu) Kashi na biyu Shirkar da bata fitar da mutum daga musulunci, Amma tana da mummunan Hatsari (Allah ya tsare mu ya kare mu da su baki daya) malamai sukan yi missali kamar:
Riya (Yi don again) Wannan shine mutum ya yi dukkan wata ibata ga Allah amma yana son agani domin a yaba, ko ace yana da kokari ko ya burge. Mutum ya san cewa idan ya yi aiki domin a gani ya sani ya yi riya, sai ya nemi Allah ya yafe (Allah ya yafe mana baki daya) wannan yana shafan ayyuka sai ai fatan ki yayewa, haka kuma Jiyarwa: wato mutum ya yi don aji kodai ace yana da murya ko makamantan haka, ko kuma ya yi ibadar shi daga shi sai mahaliccin shi sai yazo yana bada labari, ko ana fira sai aka ganshi yana gyangyadi aka ce mallam lafiya? sai ya kada baki ya ce 'Ai na kwana na yi ina nafilfili ko ina karatun Kur'ani ko Zikiri, da sauransu, ko ana zaune yace azuminnan yana banwahala al'hali ba watan Ramadan ake ciki ba 'ka ji yana cewa ai azumin litinin da alhamis baya wuceni, da dai makamantansu, asani ba muna hukunci akan ayyukan mutane bane amma 'Gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba' sabo da haka ayi kokarin ankyautata ayyuka domin Allah. Anan sauda yawa mutum yakan yi yunkurin zai aikata wani kyakkyawan aiki wanda Allah yake so sai ya ji kamar mutane zasu gani su yaba saboda haka bari ya hakura? Idan mutum ya samu kanshi cikin irin wannan hali ya aikata aikin da yake so ya aikata wannan tsoron da yaji shi ake bukata shaidanne yake son ya yi amfani da shi domin ya hana shi. Saboda haka kowa ya yi kokari yaga asalin niyyar sat a zama domin Allah, sauda yawa magabata sun sha yin Magana akan 'Ikhlasi' wato yi domin Allah, muna fatan Allah ya karba mana.
Rantsuwa da wanin Allah. Rantsewa da wanin Allah yana daga cikin dinbin abubuwan da Ma'aikin Allah ya hana, domin babu wani mai girma da za'a rantse da shi Inba Allah ba. Ma'aikin Allah cewa ya yi "Duk wanda zai rantse to ya rantse da Allah ko kuma ya yi shiru'' hasali ma duk wanda ya rantse da wanin Allah rantsuwar bata yi ba (bata kulluba) kuma sai ya yi gaggawar tuba zuwa ga Allah. Amma Allah, Sarki mabuwayi mai girma da daukaka mai ikone akan ya rantse da komai, domin babu wanda zai tambaye Shi, akan haka Allah Ya rantse da rayuwar Manzan Shi Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kuma rantse da rana, wata, hantsi, dare. Da dai suransu.
Kammalawa : Awannan takaitaccan bayani da yagabata na munsan hatsarin dake cikin Shirka da Allah wacce Ma'aikin Allah ya tsoratar da mu ita, da irin alherin da yake cikin Tauhidi. Akaro na gaba bayani zai zo akan abu na biyu da Ma'aikin Allah ya ce munisanta kada mu kuskura mu yi kusa da shi wato Sihiri (Asiri) Allah ya karemu ya kuma tabbatar da akan karantarwar Ma'aikin Annabin Tsira Annabi Muhammad Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda.
Minna, jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a +2348064022965, ko kuma a
aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com