Wednesday, February 12, 2014

023- HUKUNCE-HUKUNCEN RAMUWAR SALLAH


Tambihi: Bai halatta mutum yana cikin hankalinsa ya bari lokacin sallah ba tare da ya gabatar da ita iba. Ayanzu za'a kawo bayanaine akan abinda ya shafi ramuwar sallar da ta wuce ko sallolin da suka wuce tare kuma da neman gafarar Allah, ya Allah ka gafarta mana. Sau dayawa sakaci da ko'inkula shi ke sa mutum ya bar salloli su wuce, wata sai bayan ta yi aure take cika sallah, alhalin sallar ta wajaba akanta tun lokacin da ta balaga wato tun lokacin da ta fara ganin jinin al'ada ko ta fitar da maniyyi...' haka ma maza wasu sai sun yi aure, wanda wannan kuskurene.
   Su dai sallolin da suka wucewa mutum, kodai su wuce masa yana halin tafiya ko kuma yana halin zaman gida.
   Idan sallolin sun wuce masa yana halin tafiyane to zai ramasu a yadda mai tafiya yake sallolinsa kodako yanzu yana gidane,  wato zai ramasu raka'a biyu biyu azahar da la'asar da lisha.
   Idan kuma sun wuce shine alokacin zaman gida to zai ramasune raka'oi hudu hudu sawa'un yana halin zaman gidane lokacin ramuwar ko yana halin tafiya, kenan kowacce sallah za'a ramatane a yadda ta wuce, wato lokacin da ta wuce ake la'akari da shi ba lokacin da za'a ramaba.
Yadda Ake Rama Salloli:
 Idan ana bin mutum salloli hudu ko abinda bai kai huduba to sai ya gabatar da sallolin da ake binsa kafin ya yi wacce ake cikin lokacinta, jerantosu a haka wajibine.
   Amma idan sallolin da ake binsa sunfi hudu to anan kawosu a jere tare da wacce ake cikin lokacinta bai zama dole ba, ya samu ya gabatar da wacce ake cikin lokacinta sannan ya kawo sallolin da ake binsa.
   Kada mu manta dukkan wanda yasa ana binsa salloli mace ko namiji wajibine ya tashi tsaye domin biyan wadannan salloli da suke a kanshi, domin ya sani shi kadaine zai iya biyansu babu wanda zai biya masa ko bayan ya rasu, wannan sallah ba karamar ibada bace. Hakanan su sallolin da ake bin mutum su zai iya gabatar da su a kowanne lokaci ko da bayan la'asarne ko bayan sallar asuba, ba wanda yace idan mutum azahar din yau ta wuceshi wai ba zai ramaba sai idan azahardin gobe ta zo, wannan bayanin kitaburra'asine.
   Wanda ake binsa salloli da dama wajibine ya tashi tsaye domin ya ga ya biya wadannan sallolin da suka wuce masa kamar yadda bayanai suka gabata, idan ana bin mutum salloli da yawa ya samu a kowacce rana ya biya bashin salloli biyar, idan ya yi haka to bai yi sakaciba amma idan ya biya kasa da salloli biyar to zai shiga cikin masu sakaci Allah ya tsaremu. Yadda kuma zai biya salloli biyar biyar shine, idan ya yi sallar asubahi ta yau ya gama, sai ya mike ya kawo sallar kwana guda cikin wadanda suka wuce, wato ya kawo asubahi da azahar da la'asar da magariba da lisha, shikenan sai ya tafi neman abincinsa, idan ya yi sallar azahar ta yau yagama, sai ya mike ya kawo sallar kwana guda cikin wadanda suka wuce kamar yadda bayani ya gabata, wato ya kawo asubahi da azahar da la'asar da magariba da lisha, shikenan sai ya tafi nemana abinci, to idan ya kammala sallar la'asar ta yau sai ya kawo sallar kwana guda daga cikin kwanakin da yake ramawa zai faro kowacce daga asubahi zuwa lisha, haka zai yi idan ya kammala magaribar yau da sallar ishar yau, sai ya zamana alokacin da ya kammala sallar ishar yau kuma itace sallah ta biyar a yau kuma bayan kowacce sallah ya yi sallar kwana guda cikin wadanda suka gabata sai ya zama ya kammala sallolin kwanaki biyar da zarar ya kammala bayan sallar ishar yau, haka zai dinga gabatarwa har ya biya dukkanin sallolin da ake binsa, ya kuma ci gana da rokon Allah gafara Allah ya gafarta mana. 
  Idan mutum ana binshi sallolin da bai san adadinsuba sai ya yi sallah gwargwadon yadda zai tabbatar da ya biya su, misali yana kokwanton watanni takwasne ko tara, to da zarar ya yi ramuwar watanni tara to ya tabbatar da ya biya sallolin sai rokon gafarar Allah da ya yafe.
   Idan anabin mutum salloli to ba zai yi sallar nafilaba, domin farillar da take kansa ita ake so ya biya, masu iya Magana sukace wanda ake bi bashi ai baya kyauta, malamai sukace ba abinda yake halatta ya yi sai dai Shafa'i da wuturi da raka'oi biyu kafin sallar asubahi da sallolin idi guda biyu wato karamar sallah da babbar sallah, da sallar kisfewar rana da kuma sallar rokon ruwa.
Kammalawa: Daga takaitattun bayanan da suka gabata ta bayyana a garemu muhimmancin wadannan salloli da Ubangiji ya dora mana su, kuma da yadda ake ramuwarsu idan har ma sun wuce da kuma cewa ko shekarune sai mutum ya biyasu, Allah ya sawwake ya taimaka mana wurin kula da wannan sallar, wadanda kuma ke kan hanyar ramawa ko za su fara to Allah ya sawwake musu su gama lafiya, sannan wannan yana nuna muhimmancin koya ma yara sallah tun kafin ta wajaba akansu domin su saba da ita ko da lokacin da ta waja akansu din ya yi da ma sun saba tuni, shi yasa ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace a umarcesu da yin sallah tun suna shekara bakwai, adakkesu akan ta idan sunkai shekara goma.  
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

022- WURARAN DA BA'A SALLAH A SU


Gabatarwa: Bayan da bayanai suka gabata akan abinda ya shafi lokutan sallah da kuma yadda ake hada salloli, a yanzu bayanai zasu zo ne akan wuraran da ba'a sallah a su, domin mutum ya kiyayi wurin domin ya tabbatar da sallarsa ta karbu a wurin Allah madaukakin sarki.
Matashiya: Yana daga cikin falalar da Allah madaukakin sarki ya yi wa wannan al'umma ta ma'aikin Allah yadda ya sanya mata kasa ta ko ina ta zama wurin sallah, inbanda wadansu wurare da aka hana yin sallah a su. Mutanan da suka gabacemu basa sallah sai sun je inda aka tanada musu, amma mu ko amota kake ko  a gona ko tsakiyar daji… sai ka gabatar da sallarka, ko anan kusa baka ganin kiristoci sai sun je coci.
   Saboda haka a yanzu muke fatan kawo bayanai na wuraran da aka hana ka yi sallah a su kamar haka:
1.       Shadda (Masai): Shine inda aka ta nada domin yin bayan gida, wannan ya kasance wurine mara tsarki, kuma mun san tsarkin wuri sharadine daga cikin sharuddan sallah. Haka kuma ba'a sallah ana fuskantar bangwan dake dauke da najasa, kamar bangwayen da ake fitsari a jikinsu.
2. Wurin Wanka: Shima dakin da aka ware domin wanka, kasan akan ware wurin wanka daban wurin bayan gida shima daban, ba'a sallah a ciki, domin ana bayyanar da al'aura a wurin, kuma shima matattarane na aljanu.
3. Makabarta: Bai halatta mutum ya yi sallah a inda yake makabartace, domin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya hana, yana kuma cewa ''Allah ya tsinewa Yahudawa da Nasara domin sun dauki kaburburan Annabawansu masallatai''. Lalle irin wannan al'amari da ya kai madaukakin sarki ya yi wannan tsinuwa to lalle ba karamin al'amari bane, saboda haka bai halatta a binne kabari a cikin masallaciba, ko kuma a gina masallaci a kabarin wani ko wataba, domin yanada matukar hatsari. Hakanan bai halatta mutum ya yi sallah yana fuskantar kabariba domin nan inda yake sallar sunansa masallaci, hadisai masu tarinyawa da kuma tsoratarwa duk sun tabbata akan haka, wannan fa ba wai don su najasa bane, a'a, kada ka manta wadancan kaburburan Annabawa suka mayar masallatai Allah ya tsine musu kuma kowa ya san Annabawa ba najasane, ai dun mumini ba najasabe ballantana Annabawa.
  Ya halatta ayiwa mutum bayan ya rasu sallah a makabarta, kamar ace an binne shine ba'a yi mishi sallah ba
4. Wurin Da Aka Yi Azaba: Dukkan wurin da kasan Allah ya yiwa wasu azaba awurin ko ta hanyar ruftasu ko ma wadansu nau'uka na azaba da Allah yake yiwa wadanda suka saba masa. Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yana cewa dangane da inda Allah ya halakar da Samudawa: '' Kada ku shiga inda waddannan mutanan suke sai in kun kasance masu kuka, kuma indai baku kasance masu kukaba to kada ku shiga wurinsu domin kada irin abinda ya samesu ya sameku''. Bukhari ya ruwaito wannan Hadisin a Kitabus Salah babin: Yin sallah aka kifar da su ko aka yi musu azaba. Akan haka ne wasu daga cikin malamai sukace bai halatta ayi tsarki da ruwan wurinba. Kuma an ruwaito daga Aliyu ibnu Abidalib Allah ya kara masa yarda ya wuce inda aka kifar da mutane a Babila bai yi sallah ba sai day a wuce.
   Amma wadansu malaman na ganin ya halatta domin babu wani dalili ingantacce da yake nuna cewar sallar ta baci, domin cewar ibada bata yi yana bukatar dalili mai karfin gaske. Akashin gaskiya nisantar irin wannan sabani sha yafi.
5. Turken Rakuma: Shine dukkan wurin da yake makwantar rakumane  wato nan suke kwana, ma'aikin Allah yana cewa '' Ku yi sallah a turakun awaki, kada ku yi sallah a turakun rakuma''. Tirmizine ya ruwaitoshi, a dansu ruwayiyon an sami cewar wurin matattace ta shaidanu.
6. Bola: Bai halatta mutum ya yi sallah a inda yake bolace, domin kowa ya san bola matattarace da najasa da shaidanu. Wannan ya fi faruwa a lokacin da sahu ya kure ko kokarin samun jam'i musamman aranar juma'a, to lalle ya kamata mu sani ba'a sallah a bola.
7. Mayanka: Hakanan ba'a sallah a mayanka domin wurine da yake dauke da najasa ta jinin yanka.
8. Saman Ka'abah: Hakanan ba'a sallah akan ka'aba domin abinda aka shar'anta shine a fuskanceta, to mutumin da ya hau kan Ka'abah ina ya fuskanta kenan.
9. Coci: An ruwaito daga wurin malamai cewa ba'a sallah a wuraran ibadar Yahudawa da kuma Coci wurin ibadar Nasara. An ruwaito hakan daga Umar da Ibnu Abbas da Malik, wasu malaman suka a'a sai dai idan Cocin akwai hotuna ko gumaka.
10. Mutummutumi: an hana ayi sallah ana fuskantar mutummutumi domin hakan zai zama ana kwaikwayar wadanda suke bautawa irin wannan mutummutumin. Kenan saboda kariyar da musulunci yake baiwa tauhidi aka hana sallah a makabarta da ire-iren wadannan wuraran.
11. Inda Aka Kwata: Wurin da aka kwata malamai sukace bai halatta a yi sallah a wurinba domin zama ma bai halattaba ballantana sallah. Jamhurdin malamai sukace sallar ta yi laifin kuma yana ga wanda ya kwata amma sallar wanda ya yi sallah a wurin ta yi.
12. Masallacin Cutarwa: Shine dukkan masallacin da aka ginashi domin cutar da al'amma cutarwar da musulunci ya tabbatar da ita, to irin wannan masallacin bai halatta ayi sallah acikin shiba, bayaninshi ya zo a cikin Suratut Taubah daga aya ta 108 zuwa ta 110.
13. Wurin Dake Da Hotuna: malamai sun kyamaci yin sallah matukar kyamata a wurin da ke an manna hotuna, amma abin takaici sai ka ga an manna hoto a jikin masallaci a wasu wuraran har a cikin masallaci, wannan bai kamata ace dakin Allah ake kawo wadannan abubuwaba, abin gudu shine sannu-a-habkali sai hankalin mutane ya fara komawa ga wadannan hotunan, wanda yake hakan sanannene, kuma shine sanadiyyar shirka, ka duba kissar Waddu da Yagusa da Ya'uka da Nasrah da suka zo cin Suratu Nuh. Allah ya sa mudace, amin.
Kammalawa: Daga takaitattun wadannan bayanai ya bayyana a garemu cewa akwai wuraran da ya zama wajibi a kula dasu alokacin da mutum zai yi sallah domin akwai inda aka hana, kuma munsan irin hadarin da ake ciki a yanzu na ginegine da ake yi akabarbaruka wanda yake ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya hana.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Thursday, February 6, 2014

021- HUKUNCIN HADA SALLOLI BIYU


Gabatarwa: Bayan da bayanai suka gabata akan abinda ya shafi lokutan sallah, da kuma cewar kowacce sallah da lokacin da mahalicci ya sanya ayi ta, to a wannan lokaci zamu kawo bayanai na wadansu lokuta da shara'a ta sawwaka akan hada salloli biyu alokacin daya a gabatar da su, har ma shari'a ta tabbatar da wajibcin hakan a wasu wuraren.
Sallolin Da Ake Hadawa:
  Mu sani dan ance hada salloli biyu bashi ke nuna mutum ya hada kowacce da wacce ya ga damaba, a'a muslunci ya haskaka mana yadda ake hadawa da kuma wadanda ake hadawa.
1. Azahar da La'asar.
2. Magariba da Lisha.
   Kenan ba'a hada isha da asuba, ko asuba da azahar ko la'asar da magariba, hakanan ba'a hada juma'a da la'asar.
Nau'ukan Hadawar:
Malamai sun kasa hadawar zuwa gida uku, wato:
1. Hada azahar da la'asar a lokacin azahar, ko hada magariba da isha a lokacin magariba, shi malamai suke kira ' Jam'u Taqdeem' domin an janyo ta biyu an yi ta a lokacin ta farko.
2. Hada azahar da la'asar a lokacin la'asar, ko magariba da isha a lokcin isha, shi wannan malamai suke kira da 'Jam'u Ta'akheer' domin an jinkirtar da ta farko har zuwa lokacin ta biyu.
3. Yin sallar farko akarshen muhtarinta wanda yake ana gamawa farkon muhtarin sallah ta biyu ya shiga sai a yita ita sallah tabiyun, wanda bai luraba sai yace an hada salloli biyune alokacin daya alhali kuma kowacce an yi ta a lokacinta, amma a surar an hadane shi yasa malamai suke kiran wanna 'Jam'us Suuree'.
Wuraran Da ake Hada Salloli:
  Mu sani asali shine kowacce sallah ayi ta akan lokacinta, bai halatta ka tashi daga wannan asali sai kana da dalilai da malamai suka karanta maka masu kwarin gaske, ba wai dalilan da kai ka karanta da kankaba, wadannan wurare sune kamar haka:
1.Arafat: Idan maniyyaci yana a filin Arafat ranar tara ga watan Zul Hajj, to zai hada azahar da la'asarne a farkon lokacin azahar, kenan da lokacin azahar sai a kira sallah ayi ikamah a sallaci azahar raka'a biyu, sannan sai a mike a kira sallah kiran la'asar kenan sai kuma ayi ikama sai a sallaci la'asar a wannan lokacin, wannan shi ake kira 'Jam'u Taqdeem', yin haka kuma sunnace wajibah in ji mai risalah.
2. Muzdalifah: Sannan bayan ya kammala tsaiwar Arafat rana ta fadi ba zai sallaci magariba sai ya jinkirta sai ya kai muzdalifa sai ya hada magariba da isha ya sallace su a lokacin isha, ko wacce da kiran sallah da kuma ikama, sai dai idan an yi sallah amma su basu yi ba to anan ba za su kira sallah ba sai su yi ikama su sallaci magariba raka'a uku isha kuma raka'a biyu. Wannan jinkirta magariba da aka yi a ka sallaceta a lokacin isha shi ake kira 'Jam'u Ta'akheer' kamar yadda bayani ya gabata.
3. Ruwan Sama: Haka nan kuma ida ya zama ruwan samane ko kuma duhune da tabo to anan wadanda ke masallaci sai su hada magariba da lisha sai kowa ya wuce gida, ga yadda ake hadawar:
'Za'a kira sallar magariba a farkon lokacinta a wajan masallaci (wato da lasifika) sannan sai a dan jinkirta sallar kadan, sannan sai a tada ikama sai a sallaceta. Sannan sai a kira sallar isha a cikin masallaci (kenan ba tare da lasifikaba) sai a tada ikama a sallace raka'a hudu, a lokacin akwai haske shafaki bai baceba kowa sai ya koma gida'.
   Anan sai a kiyaye wasu kwata-kwata ba ruwansu da wani abu waishi hada sallolin magariba da lisha saboda ruwan sama.
   Wasu kuma da zarar hadari ya daga ko ya kai yadda ya kamata ayi tunanin hadawa ko bai kaiba sai ace an hada salloli a su, wannan kuskurene, hadawar saukine musulunci ya zo da shi, yin kowacce sallah a lokacinta wajibine, to kada ka tashi daga wannan wajibin zuwa ga wannan saukin sai kana da dalilai masu kwari.
4. Halin Tafiya: Idan mutum ya fara tafiya kafin lokacin sallah ta farko a sallolin da ake hadawa ya shiga kuma ga shi sun kan tafiya sun samu su jinkirta ta farkon su yita a lokacin ta biyu, idan kuma sun sami dama sai su yi ta biyun alokacin ta farko, ma'a ko su yi 'Jam'u Taqdeem' ko kuma su yi 'Jam'u Ta'akheer', misali; mutum ya bar gida karfe: 10:30am na safe ai lokaci azahar bai yiba sai suke ta tafiya ba'a tsaba sai 2:30 na rana to anan sai su hada azahar da la'asar ko ba'a tsaya ba sai kafe 4:30pm na yamma duk anan ba komai sai su hada azahar da la'asar kowacce raka'a biyu biyu, ba sai an sami matsala da direbaba, domin su mutane sun dauka kowacce sallah sai an tsaya an yi ta a lokacinta, ai ida kana halin tafiya zaka iya hada azahar da la'asar, ko kuma magariba da lisha a lokacin kowacce daya daga cikinsu, amma ba'a hada azahar da la'asar da magariba a lokacin isha, bayanai sun gabata.
    Al'amarin addinin musulunci al'amarine mai saukin gaske, kuma kullum gwargwadon yadda ka fahimceshi gwargwadon yadda yake da sauki a gareka, Allah mun gode maka.
   Saboda haka koda tsayawa aka yi domin aci abinci sai kake ganin lokacin ba zai ishekaba sai ka yi sallah a lokacin abincin ka saya ka ci a cikin mota.
   Idan kuma yanzu zaku fara tafiya kuma gashi lokacin azahar ya yi shikenen sai ku sallaci azahar raka'a hudu bayan kun yi sallama sai ku mike ku kawo la'asar itama raka'a hudu. Haka kuma ida lokacin magaribane sai ku yita raka'a uku sai kuma ku mike ku kawo isha raka'a hudu sai akama hanya, Allah ya sakeku lafiya.
5. Rashin Lafiya: idan mutum bashi da lafiya ya samu ya jinkirta sallar farko zuwa karshen muhtarinta wanda yake shine farkon muhtarin sallah ta biyu, sai ya sallace su, ma'ana ya yi sallar farko a lokacinta sallah ta biyu ma a lokacinta wannan malamai suke kira ' Jam'us Suuree', hakanan ma idan za'a yi mishi fida ya zama idan an jira lokcin sallah ya yi babu wata damuwa sai ajira domin ya sallace su duka, misali idan aka jira azahar ta yi sai ya yi azahar ya kuma kawo la'asar idan ya fi kusa da su, ko a jira magariba sai ya yi ta ya kuma kawo lisha idan dasu ya fi kusa, sannan sai ayi masa aiki, amma idan jinkirin zai kawo masala alafiyarsa sai ayi mishi aikin ba tare da an jira lokacinba.
  Hadisi ya tabbata a ruwayar Muslim da Imam Ahmad da Tirmizi da Nasa'i da Abu Daud cewar ''Ma'aikin Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya hada azahar da la'asar, ya kuma hada magariba da lisha a birnin madina ba tare da tsoroba ba kuma ruwan sama ba'' sai aka tambayi Abdullah ibu Abbas akace; ''Me yake nufi da hakan kenan? Sai ibnu Abbas yace: ''Yana son kada ya kuntatawa al'ummarsa''.
  Sai malamai sukace wannan ya nuna halaccin jinkirta sallah zuwa karshen muhtarinta sannan a sallaceta wanda yake nuna shine kuma farkon muhtarin sallah ta biyu sai wanda bai luraba yace an hada su, Eh, an hada kuma an raba, an yi kowacce a lokacinta wannan ya nuna an raba, an yi ta farko sai aka mike aka kawo ta biyu wannan yake nuna an hada shi yasa malamai suke kiran wannan da 'Jam'us Suuree'.
  Saboda haka wannan baya nuna haka kawai mutum ya tashi da zarar an kammala azahar ya kawo la'asar ko da zarar an kammala magariba ya kawo lishi dogaro da wannan hadisin domin yin haka ya sabawa fahimtar magabata a kan hadisin.
Kammalawa: Lalle wannan ya nuna mana irin gatan da musulunci ya yi ma da irin yadda Allah yake nufatar wannan al'umma da sauki bad a tsanani ba, ta yadda dudda cewar shigar lokaci sharidine na sallah amma aka sami wasu wurare da musulunci ya yarda da a hada wadannan salloli, wannan kuma saukine a garemu, Ya Allah mun gode.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com       

020- LOKUTAN SALLAH (2)


Muhtarin Salloli Da Larurinsu:
1. Muhtarin Sallar Azahar shine daga lokacin da rana da gusa daga sararin sama zuwa bangaren yamma inuwa kuma ta bayyana ta bangaren gabas harzuwa loakcin da inuwa zata kai tsawon kowanne abu. Larurin azahar kuma shine daga lokacin da inuwarka ta kai tsawanka zuwa dab da faduwar rana.
2. Muhtarin Sallar La'asar daga lokacin da inuwarka ta kai tsawonka zuwa loakcin da rana zata yi fatsi-fatsi. Larurinta kuma zuwa faduwar rana.
  Kenan azahar da la'asar suna tarayya a wani bangare na lokacin sallah, wannan kuma yana da matuka muhimmanci a fahimceshi saboda bayanan da zasu zo nan gaba, da izinin Allah.
3. Muhtarin Sallar Magariba: daga lokacin da rana tadi (ta bace kwata-kwata) zuwa gwargwadon abinda ka sallata, ba'a bukatar a jinkirtata. Larurinta har zuwa dab da fitowar alfijir.
4. Muhtarin Sallar Isha: daga lokacin da shafaki ya bace har zuwa kashi daya biya ukun dare. Larurinta har zuwa fitowar alfijir.
   Kenan magariba da lisha suna tarayya awani yanki na lokacin sallah.
5. Muhtarin Sallar Asubahi: daga lokacin da alfijiri ya keto zuwa gari ya waye (ya yi haske tangaran) zuwa fitowar rana.
  Kenan asubahi ita kadai take da lokacinta babu wata sallah da ta yi tarayya da ita.
 Ba'ayarda mutum ya jinkirta sallah har zuwa lokacin laruriba sai idan yana da larurar da shara'a ta bayyana, idan mutum ya kuskura ya bar sallah har lokacinta ya fita to ya tafka laifi mai girman gaske, Allah madaukakin sarki yana cewa '' Sai wadansu masu mayewa suka maye musu suka wulakantar da sallah suka bi holewarsu da sannu zasu hadu da gayyah (wani kwarine a cikin wutar jahannama). Sai dai kwai wanda ya tuba'' Suratu Maryam, aya ta:59-60 Allah ya tsare mu.
Larura:
Ya zama dole mu tsaya mu fahimci mecelarurar domin kada ka dauki abinda ba larura bane a shar'ance ka bashi matsayin larura.
1. Mantuwa: Duk wanda ya manta da sallah, ya dauka kamar ya yi ashe bai yi ba sai daga baya ya tuna to sai ya tsahi ya sallace ta a wannan lokacin da ya tuna, ko da lokacin sallar ya fita, kamar ya manta da azahar sai bayan ya yi sallar isha ya tuna, sai ya tashi ya kawo sallar azahar din,yin ta a wannan lokacin shine kaffarar.
2. Bacci: Idan lokacin sallah ya yi mutum sai ya yi sallah kafin ya kwanta, idan kuma lokacin sallah bai yi ba sai ya kwanta bacci bai tashiba sai da lokaci ya fita, to a wannan lokacin da ya tashi sai ya sallaceta babu wani jinkiri. Akan abinda ya shafi mantuwa da bacci Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yake cewa:    '' Duk wanda ya manta wata sallah, ko kuma ya yi bai yita ba, to ya sallaceta idan ya tunata babu wani abu da yake kaffara sai yin hakan''. Muslim,684. kenan ba maganar wai sai lokacin na gobe ya dawo, wannan babu shi a musulunci duk lokacin da ka tuna da sallah to a wannan lokacin zaka sallace ta.
3. Musulunta: idan mutum ya musulunta bayan muhtarin sallah ya wuce, kamar ya musulunta lokacin da rana ta yi fatsi-fatsi, to a wannan loakcin zai yi sallar azahar da la'asar, tunda sun yi tarayyar lokaci.  
4. Balaga: idan ya zama yarone ya fitar da maniyyi a barci ko a farke ya zama wannan fitar maniyyin shine balagarshi a wannan lokacin to sai ya yi wanka ya sallaci azahar da la'asar idan a loakcin su ne, ko magariba da lisha idan suma a lokacin su ne.
5. Hauka: ko kuma mutumne yake fama da cutar tabin hankali sai bai sami saukiba sai abinda ya saura kafin alfijir ya fito za'a sami raka'a hudu to sai ya sallaci magariba da isha.
6.Suma: ko kuma mutumne ya suma ko aljanu suka bigeshi sai bai farfadoba sai a wadannan lokuta na laruri, idan ya zama za'a sami sallar raka'a biyar kafi rana ta fadi sai ya yi sallar azahar sannan ya kawo sallar la'asar, amma idan za'a sami raka'oi hudune kafin rana ta fadi sai ya sallaci la'asar kadai.
7-8. Jinin Al'ada Da Jinin Biki: Zuwan wannan jini da kuma lokacin da ya dauke yana da matukar muhimmanci iyaye mata su kula da shi domin yana da alaka da sallar da zaki rama da kuma wacce ba zaki ramaba.
   Idan jinin ya dauke mata kuma bayan ta yi wanka za'a sami gwargwadon raka'oi biyar kafin rana ta fadi to zata yi sallar azahar da kuma la'asar, idan kuma kafin alfijirine za'a sami raka'oi hudune to zata sallaci magariba da lisha. Tirkashi!. Da yawa wasu matan idan sun sami tsarki da daddare ba abinda suke tsammani sai sallar asuba, idan kuma da ranane basa ilssafa fara sallah sai magariba ta yi, wanda yake wannan danyan kuskurene kuma laifine maigirman gaske.
   Wadannan sune larurorin da shara'a ta yadda da su har mutum sallah ta kai shi loakcin laruri, amma aiki a ofis ko baki balle mitin ko aikin gona ko hada-hadar kasuwanci wadannan ba laruraba a shar'ance, kawai da zarar loakcin sallah ya yi sai ka tashi kaje ka gabatar da ita.
   Sallah itace mafi girman ibada da ake so mutum musulmi ya bata kulawa, ranar alkiyama idan sallah ta gyaru to da izinin Allah komai zai zo da sauki.
   Amma yadda wasu suka dauka na idan sun fita harkokinsu sai sun dawo gida za su hada azahar da la'asar, sannan su biyo da magariba da lisha wannan tsantsar sabon Allah ne, babban abinda ake so mai wannan dabi'a ya tuba zuwa ga Allah ya ci gaba da gabatar da kowacce sallah akan lokacinta.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai mun san muhtarin sallah da kuma larurinta da kuma abainda ake nufi da larurin sune wadannan abubuwa da aka lissafo, kuma mun fahimci gabatar da kowacce sallah a lokacinta shine mafi alheri ga kowa da kowa, Allah ya yi mana jagora.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com      

019- LOKUTAN SALLAH (1)


Gabatarwa: Wannan wani babine mai girman gaske dudda cewa dukkan wadannan bayanai suna da matukar muhimmanci. Su lokutan sallah saninsu yana da matukar muhimmanci, domin ba'a yin sallah sai lokacinta ya yi kuma ba'a bari lokacinta ya fita ba'a yi ba, asalima shigar lokaci sharadine daga cikin sharuddan sallah kamar yadda bayanai suka gabata kuma mukace da izinin Allah zamu kawo bayanai akan abinda ya shafi lokutan sallah.
Lokutan Sallah: Kowacce sallah daga cikin wadannan salloli wajibabbu guda biyar tana da lokacinta da Allah madaukakin sarki ya iyakance mata ba za'a yi ta kafin lokacinta ya yi idan kuma lokacin ya yi ba za'a bari sai ya fitaba, Allah madaukakin sarki yana cewa '' Lalle ita salla ta kasance akan muminai wajibice kuma abar gayyadewa lokaci'' Suratun Nisa'i, aya ta: 103. Umar dan Khaddab Allah ya kara masa yarda yana cewa 'Sallah tana da lokaci da Allah ya sansa bata inganta sai a wannan lokacin'. Sallah tana zama wajibine idan lokacinya ya shiga kamar yadda ayoyi masutarin yawa suka nuna, gabadayan malamai sun yi ijima'I akan falalar dake cikin yin sallah a farkon lokaci a dunkule, Allah madaukakin sarki yana cewa '' Ku yi rige-rigen aikata alheri'' Bakara, aya ta:148 wanda yake sallah itace babba akan dukkan wani alheri da musulmi zai gabatar.
   Kowacce sallah daga cikin salloli biyar din nan tana da lokacinta da Allah ya kayyade mata wanda kuma ya yi daidai da halin da bayinsa suke, ta yadda zasu gabatar da wadannan salloli a kan lokutansu ba tare da wani abu ya tsare sub a asalima zata taimaka musu ne, kuma ta kankare musu zunubai, ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kamantata da ruwa da yake gudu wanda mutum a kullun yake wanka a cikinsa sau biyar kana tsammanin zaka ga wani datti a tare da shi!.
1. Lokacin Sallar Azahar: Lokacin sallar azahar shine daga lokacin da rana ta karkata daga tsakiyar sama ta koma zuwa bangaren yamma, zaka gane hakane ta yadda inuwarka zata koma bangaren gabas bayan ada baka gantaba. Wato yadda al'amarin yake alokacin da rana take gabas zaka ga inuwa ta na yammane, lokacin da rana take kara dagowa lokacin inuwar take kara ragewa harzuwa lokacin da rana zata zo tsakiyar sama daidai, za kuma tad an tsaya kadan, to adaidai wannan lokacin da take atsakiya cif zaka ga ba wata inuwa, domin sai ranar ta karkata wani bangarene sannan inuwar ta bayyana a wani bangaren. To daga lokcin da ranar ta ci gaba da tafiya zuwa yamma to daga lokacin inuwa zata ci gaba da bayyana bangaren gabas, ranar tana kara yin yamma inuwar tana kara tsawo bangaren gabas. Daga lokacin da ranar ta karkata zuwa bangaren yamma kuma alamar hakan itace ka ga inuwarka ta bayyana bangaren gabas to da ganin haka lokacin sallar azahar ya yi, ba abinda ya rage sai dai a sallah ce ta, sai dai idan lokacin ana fama zafin rana sai a jinkirta kadan, ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:  '' Idan zafi ya tsananta to kudan sanyaya sallah, domin tsananin zafin nan daga nunfashin jahannama ne''. Bukhari da Muslim da Malik a Muwatta'u.
   Wannan shine loakcin sallar azahar har kuma zuwa inuwar komai ta zama kamar tsawonsa.
   Kenan anan ba wata sallah mai suna karfe biyu ko karfe daya, kamar yadda lokuta suke canzawa a tsawon shekara to haka lokutan sallah suke canjawa, duk mun san wani lokaci magariba akan yita kusa bakwai na yamma wani lokacin kuma kusan shida da wani abu na yamma, to ashe kamar yadda muka yarda lokacin magariba yana canzawa to hakanan na sauran sallolin, kuma fa duk wannan a wasu yankunane kadan fa domin inda mutum ya je hajji ko umarah a inda aka saukar da sallar to da yaga wani lokacimma tuni karfe daya an gama sallah kuma da shi aka yi ta, amma idan ya dawo gida yace sai ta nuna.
2. Lokacin Sallar La'asar: Lokacinta yana farawane daga lokacin da inuwar kowanne abu ta zo kamar tsawonsa, kenan inda zaka kafa tsinke a kasa sannan sai ka ja layi a karshen inuwar to daga lokacin da tsawon tsinken ya doru kadan kan inuwar to lokacin sallah ya yi, daga nan har zuwa lokacin da inuwar kowanne abu zata ninka shi sau biyu, amma kada ka manta yinta a farkon lokaci shine abinda ya fi.
   Anan ana samun manyan kura-kurai guda biyu, kuskure na farko shi yafi ko wanne muni shine daukan lokacin sallar la'asar shine: karfe uku da rabi (3:30pm), wannan kuskurene domin dayawa masu irin wannan sallar za su yita tun kafin lokacinta ya yi, kenan basu da sallah domin sun yita kafin lokaci. Kuskure na biyu kuma shine jinkirtata bayan lokacin ya shiga waishi ai yana ganin ance har inuwa ta ninka gida biyu.
3. Lokacin Sallar Magariba: Lokacin sallar magariba yana farawane daga lokaci da kaskon rana ya bace bakidayansa to daga wannan lokacin magariba ta yi ko da ana ganin haske, kuskuren da ke yi anan shine jinkirta sallar har sai dare ya yi alhali kuma lokacinta takaitaccene, daga lokacin da rana ta fadi har zuwa bacewar shafaki, shi kuma shafaki: wani haskene da yake gauraya da ja anan sai jan ya bace ya bar hasken sai shima hasken ya bace.
   An fi so a gabatar da kowacce sallah a farko lokacinta to hakama ita sallar magariba.
4. Lokacin Sallar Isha: Shi lokacin sallar lisha yana farawane daga lokacin da shafaki ya bace, wanda yake shine karshen muhtarin magariba har zuwa kashi daya cikin uku na dare, zuwa nan muhtarin lisha ya tsaya, amman dai lokaci na laruri yana kaiwane harzuwa lokacin da alfijiri na biyu ya kyato, wanda yake kuma shine farkon muhtarin asubahi.
   Shi babban kuskuren da ake samu a sallar lisha shine wasu wuraran sun dauki karfe bakwai da rabi (7:30pm) shine lokacinta wanda yake nuna sauda yawa ana yinta kafin shigar lokacinta.
5. Lokacin Sallar Asubahi: shi  lokacin sallar asubahi yana farawane daga hudowar alfijiri na biyu kuma zai ci gaba har zuwa fitowar rana, saidai kada ka manta anfi so a gabatar da ita da zarar an tabbatar da fitowar alfijir.
   Kuskuren da ake samu a sallar asubahi shine yadda wasu suka maida lokacin shine karfe biyar da rabi na asuba (5:30am) wanda yake wannan babban kuskure domin sauda yawa wasu lokutan alfijir yana fitowane tun kafin biyar, ballema a wasu yankunan, kuma Karin hatsarin akwai masu azumi na nafila ko ramuwa kuma sun dogarane da kiran sallah shi kuma mai kiran sallar bai kiraba gashi kuma alfijir ya dade da fitowa.
   Wadannan sune lokutan sallah kuma idan muka lura zamu ga kowacce sallah tana da lokutai guda biyu; Muhtari da kuma Laruri.
    Muhtari: shine zababban lokaci da aka zaba domin ka gabatar da wannan sallar, ba'a yarda ka shiga lokacin laruriba sai inda larura kuma musulunci ya fayyace me ake nufida larurar, sannan shima muhtarin yin sallah a farkonshi tafi lada da samun matsayi a wurin Allah mai girma da daukaka.
Kammalawa: Atakaitaccan wannan bayani ya bayyana a fili cewar lokutan sallah lokutane da musulunci ya sanya, jindadi da walwala shine abi wadannan lokuta da musulunci ya kayyade, bai al'ummar musulmi su yi wasa da sanin lokutan sallah ba musamman ladanai domin da kiran sallar su ake barin sahur da shi kuma ake shan ruwa. Nan gaba zamu kashi na biyu na lokutan sallah, da izinin Allah.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Tuesday, February 4, 2014

ABINDA KE WAJABA GA SABON MUSULUNTA YA YI KO YA BARI


بسم الله الرحمن الرحيم
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da aminci su tabbata ga Annabimmu da iyalanshi da kuma sahabbanshi.
   Bayan kaha; Hakika Allah ya halicci halittane domin su bauta mishi, Allah madaukakin Sarki yana cewa; ''Kuma ban halicci aljan da mutumba sai domin su bauta mini''. Kuma ba'a bautawa Allah sai da abinda ya shar'anta, tabbas ya aiko da manzanni domin su yiwa mutane bayanin abinda ya shar'anta, domin bautawa Allah da abinda bai shar'antaba batacciyar ibadace, kuma ya kammala aiko manzanni da manzanshi Muhammad –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, kuma ya wajabtawa mutane binshi, Allah madaukakin sarki yana cewa; ''Kace ya ku mutane lalle ni ma'aikin Allah ne zuwa gareku bakidaya''. Duk wanda bai yi imani da (Annabi) Muhammad ba to ba musulmi bane, kuma addinin (Annabi) Muhammad shine musulunci, Allah kuma bai karbar wani addinin da ba shi ba, Allah madaukakin sarki yana cewa; ''Duk wanda ya bi addinin da ba musulunci ba to ba za'a taba karba daga wurinsa ba, kuma shi aranar lahira yana cikin asararru.
  Shi musuluncin da (Annabi) Muhammad ya zo da shi yana da shika-shikai guda biyar; Shaidawa da babu abin bauta da cancanta sai Allah kuma Muhammad manzon Allah ne, da kuma tsaida sallah, da kuma bada zakkah, da azumin watan Ramadan, da ziyarar dakin Allah mai alfarma tare da ikon hakan (wato aikin Hajji).
Abinda Wanda Yake So Ya Shiga Musulunci Zai Yi:
Zai furta kalmar shahada sannan ya biyo da rukunan musulunci kamar haka;
1. zaice; أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اَللهِ  , zai furta hakan ne a fili.
2. sai ya sallaci salloli biyar; Asubahi da Azahar da La'asar da Magariba da Isha, a kowanne yini da dare tsawon rayuwa, Asubahi raka'a biyu, Azahar raka'a hudu la'asar raka'a hudu magariba raka'a uku isha raka'a hudu, ba kuma zai yi sallar ba sai bayan ya yi alwala, wannanko zai farune ta hanyar wanke fuska da wanke hannuwa zuwa gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa idon sawu da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa.
3. Idan yana da kudi da ya karu akan bukatarsa sai ya fitar da daya bisa arba'in (2.5 %) wannan zakka ce da zai baiwa talakawa da miskinai a kowacce shekara, amma idan ya kasance yana da dukiyar sai dai ba abinda ya karu akan bukatarsa to anan babu wata zakka da zai fitar.
4. Zai azumci watan Ramadan, shi ne kuma wata na tara a kalandar musulunci (Zaibar abinci da abin sha da saduwa da iayali tun daga hudowar alfijr har zuwa faduwar rana) zai kuma ci ya sha ya sadu da iyalinsa da daddare kadai.
5. Idan ya kasance yana da arziki da kuma lafiyar jiki to sai ya yi aikin hajji sau daya a rayuwarshi, idan ko yana da kudi ne amma bashi da lafiyar jiki saboda tsufa ko wani dadadden rashin lafiya to sai ya wakilta wanda zai je ya yi mishi sau daya.
6. Sauran abubuwan da suka rage na biyayya ga Allah to su cuko ne ga wadannan rukunan.
Abinda Yake Lizimtar Musulmi Ya Bari:
1. Yabar shirka da dukkan nau'ukanta, itace kuma bautawa wanin Allah, akwai daga ciki kiran matattau da yi musu yanka da yi musu alwashi.
2. Yabar dukkanin bidi'o'i, wato ibadojin da Ma'aikin Allah (Annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi bai shar'anta ta ba domin yana cewa ''Duk wanda ya aikata wani aiki da bamu sa shi ba to ba za'a karba ba''.
3. Yabar cin riba da caca da cin-hanci-da-rashawa da kuma karya a dukkan mu'amalolinsa da sayar da abinci na haram da kayayyaki na haram.
4. Yabar zina wato saduwa da matar da ba ta shi ba a shar'ance ya kuma bar luwadi wato auren jinsi.
5. Yabar shan giya da cin alade da dukkan abinda aka yanka ba domin Allah ba, ya kuma bar cin mushe.
6. Ya kuma bar auren matan da suke kafirai ne saidai in kiristocine.
7. Ya rabu da matarshi da take ba musulmaba sai dai in kiristace ko kuma ta musulunta tare da shi ko ta musulunta kafin ta gama iddah.
8. Idan kaciya ba zata cutar da shi ba sai likitan da yake musulmi ya masa kaciyar.
9. Idan ya kasance zai iya tashi daga garin da bana musulmaiba ne sai ya tashi, idan kuma ba zai iya barin garinba to sai ya zauna a garin nasa ya kuma yi riko da addininsa.
Wanda ya rubuta:
Sheikh: Salih bn Fauzan Al-Fauzan
Mamba a majalisar manyan malamai. (Saudi Arebiya)
19/3/1433
Fassarar:
Aliyu Muhammad Sadisu (Nigeria - +2348064022965)