Wednesday, May 8, 2019

0036. HUKUNCE HUKUNCEN AZUMIN RAMADAN (3).


SAHUR DA BUDA-BAKI
Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi  Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki daya. Bayan haka:

 A daidai wannan lokacin da muke kawo bayanai akan hukunce hukuncen azumin watan Ramadan, to a wannan muna son mu kawo bayanai akan abinda ya shafi hukunce hukuncen sahur da mude baki, da fatan Allah ya yi mana jagora ya kuma datar da mu ya kuma anfanar da mu.

SUHUR.

Shi ne abin ci ko abin sha da mai azumi yake kusa da fitowar alfijr na biyu. Lokacin kuma shi ake kira da lokacin suhur.
Kenan anan duk abinda mai azumi ya ci ko ya sha a daidai wannan lokaci shi ake cewa suhur.

FALALAR SUHUR.

Suhur yana da matukar falala da albarka, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
((تسحروا فإن في السحور بركة)). رواه البخاري ومسلم.
Ma’ana: “Ku yi suhur domin a cikin suhur akwai albarka”. Bukhari da Muslim suka ruwaito.

Wannan na nuna matsayi da daraja kana da falala ta suhur, ba gwaninta ba ce ko birgewa mutum ya ce ai shi ba ya sahur, lalle mutum Musulmi ya yi iya kokarinsa wurin cin sahur a kowanne azumi na farilla ko na nafila, koda ruwa ne ya sha.

LOKACIN CIN SAHUR.

Ana cin suhur ne akarshen dare ba’a farkon dare ba, ba kuma a tsakiyar dareba, domin kada mutum ya ci abin ci a farkon dare ko a tsakiyar dare ya ce ya ci suhur, wannan dai ya ci abin ci amma ba sahur ba.

Kowacce kasa da kuma birane kana da karkara akwai lokacin da alfijir yake fitowa, domin babu wani takamamman lokaci na karfe nawa alfijr yake fitowa.
 Babban abinda ake so a sani shi ne, alfijir ya kasu kashi biyu:

Kashi Na Farko: Wanda yake fitowa bada dadewa ba kuma yake bacewa, to wannan ba ya hana cin abincin suhur, kuma ba ya sawa a yi sallar asuba.
Kashi Na Biyu: Wanda shi ne yake fitowa ya tokare sasannin sama, to wannan shi ke hana mai sahur cin abin ci, kuma shi ke sawa a yi sallar asuba.

FADAKARWA.

Ba’a bukatar mai azumi ya kure lokacin cin sahur, ana bukatar barin tazara mai dan dama, kamar kuma yadda ba’a bukatar mutum ya ci shi can cikin dare.

ASSALATU.

Wadansu masallatan suna kiran ASSALATU a kiran farko, wasu kuma suna kiranta ne a kira na biyu. Babban abin da ake so agane anan shi ne, masallacin kusa da kai a yaushe ne suke kiran ASSALATU ? a kiran farko ne ko a kira na biyu ?.

Shi lafazin ASSALATU ba fadin shi ne yake sa wa adaina cin abin ci ba, fitowar alfijir ita take tasa a daina cin abin ci, saboda haka sai ka tsaya ka natsu ka ga wane ladani za ka yi aiki da kiransa, domin akwai dubban matsaloli a wannan bangaren, wani ladanin fa sai wani masallacin ya fara sallah sannan shi zai kira, tirkashi!.

BUDA BAKI.

Shi ne abinda mai azumi yake ci ko sha bayan faduwar rana. Ke nan abinda ake so anan shi ne da zarar rana ta fadi kawai sa ka sha ruwa, wannan shi ne karantarwa musulunci domin rana na faduwa an shiga farkon dare, kuma Allah madaukakin sarki cewa ya yi:
((وكلوا واشربوا حتى يتبين لكم الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر، ثم أتموا الصيام إلى اليل)). البقرة
Ma’ana: Kuma ku ci ku sha, har sai silin farin zare ya bayyana daga silin bakin zare na alfijr, sannan kuma ku cika azuminku zuwa dare.” Bakarah.

Anan Allah madaukakin sarki ya yi bayanin farkon azumin da kuma karshensa, farkonsa shi ne fitowar alfijir, karshen sa kuma faduwar rana.

Sannan a karantarwar musulunci suhur jinkirta shi ake yi, wato ba’a yin shi a farkon dare ko tsakiyar dare, kamar yadda bayani ya gabata. Shi kuma buda baki gaggauta shi ake yi, wato da zarar rana ta fadi.

Ba birgewa ba ce mutum ya ce ai shi sai an yi sallar magariba yake shan ruwa, a’a abinda ake so shi ne da zarar lokacin shan ruwa ya yi ka sami wani abu ko kadan ne ka sa a bakinka. An fi so ya zama dabino in ba’a samuba sai ruwa.

BUDA BAKI A LOKACIN DAMINA.

Ya zama dole a dunga lura musamman lokacin damina, domin idan gari ya rufe da hadari, domin wasu ladanan kawai sai su danno kiran sallah da kusan banbancin minti goma ko talatin wani lokacin ma awa daya akan yadda suka kira jiya. Saboda haka dole ka tsaya ka natsu domin sanin wanne ladani za ka bi a bude baki da kuma suhur.

BUDA BAKI A JIRGIN SAMA.

Akan abinda ya shafi buda baki a cikin jirgin sama to bayanan za su kasance ne kamar haka:

(1) Idan kuka ta shi daga filin jirgin sama sai kawai kuka dare to shikenan lokacin san ruwanku ya yi, ba za ka yi la’akari da inda kuka taso ba cewar ai ba’a sha ruwa ba, tunda dai yanzu inda kuke rana ta fadi shikenan sai ku sha ruwa.

(2). Idan said a kuka sha ruwa, sannan sai kuma jiginku ya tashi, jirgin yana tashi sai kuma ga rana a sama, to anan malamai suka ce za ku ci gaba da cin abincin ku ne kawai babu wata matsala, domin tun farko kun ajiye azuminku a bisa ka’ida ta shari’a.

(3) Idan ya zama rana ba ta fadi ba kuka tashi, sai ya zama kuma ga ranar nan kuna gani, to anan fa babu yadda za’a yi a yi buda baki sai rana ta fadi, ba za ku yi la’akari da kasar da kuka baroba ko kuma kasar da za ku je, cewar an sha ruwa a can ko ba’a sha ba, duk ba za’a la’akari da wannan ba, kawai hukuncinku shi ne hukuncin nan wurin da kuke. Ka’ida fa a babin azumi dauka ko ajiyewa shan ruwa ko suhur shi ne hukuncin nan inda kake, sauda yawa zai zama kuma tafiya kuna bin rana, to shakka babu tsawon lokacin buda bakinku zai karu, ko kuma kun juwa rana baya to kuma tsawon lokacinku na shan ruwa zai ragu.

TSAWON LOKACI KO GAJARTARSA A BUDA BAKI.

Idan kasar da kake rana na fitowa kuma ta fadi, to anan sahur dinka da buda bakinka ya ginune akan fitowar alfijir a daina sahur, fadur rana kuma a yi buda baki, sabo da fadin Allah madaukakin sarki:
   ((وكلوا واشربوا حتى يتبين لكم الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر، ثم أتموا الصيام إلى اليل)). البقرة
Ma’ana: Kuma ku ci ku sha, har sai silin farin zare ya bayyana daga silin bakin zare na alfijr, sannan kuma ku cika azuminku zuwa dare.” Bakarah.

Idan misali inda kake rana tana fitowa ne tsawon awa biyar sannan ta fadi, sannan kuma dare ya zo awa shatara, to haka za ku yi azuminku cikin wadannan awannin, ta yadda da rana ta fadi shikenan sai ku yi buda baki.

Haka kuma idan inda kuke rana ce take fitowa tsawon awa shatara misali ko ma sama da haka to fa ba makawa a wadannan awannin zaka yi azumi, koda a ce awa ashirin da biyu ne arana, awa biyu kuma dare, to awadannan awannin ashirin da biyu a shi ne za ku yi zumi, suma sauran awa biyun a su ne za ku yi buda baki da magariba da isha da tarawih da kuma sahur, saboda waccan ayar da aka anbata a sama. Wannan yana nuna mana cewar ya zama dole mu tashi mu koyi sanin hukunce hukuncen ayyukammu na addinin musulunci ta yadda duk inda ka sami kanka to kasan hukuncin day a kamaka, domin kada mutum ya dauki hukuncin kasarsa ya ce da shi zai yi aki a ko’ina. 

Kammalawa: Da wannan ne muka karshen wannan bayani akan abinda ya shafi sahur da kuma bude baki, da kuma abubuwan da suke da alaka da su. 

Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com




Sunday, May 5, 2019

0036. HUKUNCE HUKUNCEN AZUMIN RAMADAN (2).

                                      GANIN WATA

Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi  Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki daya. Bayan haka:

 A daidai wannan lokacin kuma muna son ci gabaa ne da bayani akan hukunce hukuncen azumin watan Ramadan, kama daga abinda ya shafi ganin wata da sauran bayanai da za su zo akan abinda ya shafi hukunce hukuncensa, da fatan Allah ya yi mana jagora ya kuma datar da mu ya kuma anfanar da mu.
Allah madaukakin sarki Shi ne wanda ya wajabta azumin Ramadan, inda ya ce a cikin Suratul Bakara:

((يا أيها الذين ءامنوا كتب عليكم الصيام كما كتب على الذين من قبلكم لعلكم تتقون * أياما معدودات....)). البقرة.

Ma’ana: “Ya ku wadanda suka yi imani! an wabta muku azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka zo kafinku, domin hakan zai sa ku ji tsoron Allah. Wasu kwanaki ne kididdigaggu….” Bakarah.

Sai kuma Allah madaukakin sarki ya bayyana wadannan kwanaki da suke kididdigaggu, a inda ya ce:

(( شهر رمضان الذي أنزل فيه القرآن هدى للناس وبينالت من الهدى والفرقان، فمن شهد منكم الشهر فليصمه)). البقرة.

Ma’ana: “Watan Ramadan ! wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa, shiriya ce ga mutane, kuma bayanaine na shiriya da kuma rarrabewa, to duk wanda ya halarci watan (na Ramadan) daga cikinku to ya azumce shi”. Bakarah.
Sai Ubangiji mai girma da daukaka ya sanya watan da za’a yi azumi a cikinsa shi watan Ramadan, sai kuma Ma’aikn Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:

((صوموا لرؤيته وأفطروا لرؤيته، فإن غم عليكم فاقدروا له)) وفي روية ((فأكملوا شعبان ثلاثين)). رواه البخاري ومسلم.

  Ma’ana: “ Ku dauki azumin idan kun ganshi (jinjirin watan Ramadan) kuma ku ajiye idan kun ganshi (jinjirin watan Shawwal), idan an shamakance muku shi to ku cika”. A wata riwayar “Ku cika Sha’aban kwana talatin”. Bukhari da Muslim suka ruwaito.

SHIGAR WATAN RAMADAN.

A wannan hadisi da ya gaba ya bayyana a fili hanyoyin shigar watana Ramadan guda biyu ne:

Hanya Ta Farko: Ganin jinjirin watan Ramadan a lokacinda Sha’aban yake da kwanaki ashirin da tara.

Hanya Ta Biyu: Cika lissafin watan Sha’aban kwana talatin, idan ba’a jinjirin watan na Ramadan ba a lokacin da Sha’aban din yake da kwanaki ashirin da tara.
Idan ya zama an ga jijirin watan Ramadan, kuma wadanda alhakin sanarwa ya hau kansu suka sanar to ya zama waji kowa ya dauki a zumi.

Ya halatta a yi anfani da na’urar kawo nesa kusa domin neman wata, domin dai koda wacce na’ura aka yi anfani ba za’a ganshi ba sai idan shi jinjirin watan ya fito.

Amma idan mutum ya ga wata kuma shugabanni ba su karbi ganinsa ba to shi ne ya zama wajibi akan sa ya dau azumi, ko iyalansa da ‘ya’yansa da almajiransa ba zai sa su su dauka ba, domin hakan ba huruminsa ba ne. kuma ba wajibi ba ne idan ka ce ka ga wata dole sai an yarda ganinka.

Ba’a yin anfani da Calendar wajan tabbatar da shigar watan Ramadan ko fitarsa, misali inda Kalanda za ta nuna cewa Sha’aban kwana ashirin da tara zai yi, sai kuma muka duba wata a ranar ashirin da taran ba mu ganshi ba, to lalle ya wajaba mu cika Sha’aban talatin, mu saki lissafin kalanda. Magana dai anan ita ce kodai aga wata koda ta hanyar na’ura ne ko kuma a cika shi kwana talatin.

YIININ KOKWANTO (YAUMUS SHAKKI).

Idan ba’a ba a ga watan Ramadan ba, a yini na ashirin da tara ga watan Sha’aban to yini na talatin ga watan Sha’aban shi ne yinin kokwanto. An kira shi da yinin kokwanto ne domin ana kokwanton wannan yinin talatin ga Sha’aban ne ko kuma daya ga Ramadan, idan ya tabbata anga watan Ramadan a ranar ashirinda tara ga Sha’aban to ka ga washegari ya zamadaya ga Ramadan kenan kai tsaye. Indai bai tabbata anga watan Ramadan a ranar ashirin da tara ga watan Sha’aban ba, to lalle washe gari tanan a ranar kokwanto, saboda kodai ta zama daya ga Ramadan ko kuma talatin ga Sha’aban, domin hakan ne kuma ake kiran ranar da ranar kokwanto, wanda da Larabciake kira da (Yaumus Shakki).

AZUMI A RANAR KOKWANTO.

Bai halatta a yi azumi anar kokwanto domin a lissafishi cikin na Ramadan, idan mutum ya dauki azumi a ranar kokwanto da niyyar in an ga wata to azumin na Ramadan ne, idan kuma ba’a ga wata to azumin na nafila ne to shi ma a irin wannan hali ba shi kowanne daya daga cikin su, bas hi na Ramadan kuma ba shi da na nafilar.

WURARAN DA BA SU DA RANA.

A kwai wadansu kasashe da ba kasafai rana take bayyana musu ba, akwai kasashen da rana takan bace na tsawon watanni ba ta fito ba, haka kuma idan ta fito ta kan jima ta tsawon watanni bata fadi ba. Abinn da malamai suka bada fatawa akan irin wadannan kasashe shi ne za su yi aiki ne da ganin watan kasashen da suke kusa da su, da su rana take fito musu ta kuma fadi.

DAUKAR A ZUMI DA KUMA AJIYESHI.

Hukuncin kowanne mutum wurin daukar da azumi da kuma ajiye azumin shi ne hukuncin inda yake a lokacin dauka da kuma lokacin ajiyewa. Misali idan lokacin daukar azumi ya yi kana Nijeria to yanzu dole kadauki azumi ko kai dan Nijeriya ko ba dan Nijeriya ba, haka kuma idan lokacin ajiyewa yi.

To yanzu a ce ka dauki azumin daga Nijeriya, sai ka tafi Nijar ko Saudiyyah, sai kuma ya zama Nijeriya ta riga su daukar azumi, amma ga shi yanzu salla ta yi kana wadannan kasashe, to anan hukuncinka shi ne hukuncin wadannan kashashe, za ka ci gaba da yin azumi har sai kasar da kake sun ajiye azumi kafin kai ma ka ajiye, ko da kuma kasar da ka fara azumin su tuni sun yi sallah, sannan haka kuma ko kai naka azumin zai kai talatin da daya ne ko da biyu…’.

Sannan haka hukun cin yake idan kasar da ka fi wacce take ta Musulmaice, amma sun riga ku daukar azumin domin sun riga ku ganin wata, to haka za ka yi aiki da ganinsu, idan sun ga watan sallah a ashirin da tara ga Ramadan a lissafinsu, alhalin kai kuma a lissafinka kana da azumi ashirin da takwas ne ko da bakwai haka zaka ajiye azumin naka, idan an yi sallah sai ka rama wadannan kwanakin. Dalilin da malamai suka bayar akan wadannan matsalili shi ne fadin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi:

((الصوم يوم تصومون، والفطر يوم تفطرون)). رواه الترمذي.

Ma’ana: “Azumi shi ne ranar da kuke azumin, sallah ranar da kuke sallah”. Tirmizi ne ya ruwaito. 

Kammalawa: Da wannan ne muka karshen wannan bayani akan abinda ya shafi ganin wata, da kuma abubuwan da suke da alaka da shi.  

Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
        


Saturday, May 4, 2019

0035. HUKUNCE HUKUNCEN AZUMIN RAMADAN (1).


Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi  Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki daya. Bayan haka:
 A wannan lokacin kuma za mu yi bayani ne akan abinda ya shafi hukunce hukuncen azumin watan Ramadan, kama daga falalarsa da sauran bayanai da za su zo akan abinda ya shafi hukunce hukuncensa, da fatan Allah ya yi mana jagora ya kuma datar da mu ya kuma anfanar da mu.

FALALAR AZUMIN RAMADAN.
                                      
Azumun watan Ramadan azumin ne da yake da matukar falala, babu wani azumi day a kai shi falala a cikin dukkanin nau’ukan azumi da ake da su, kadan gada cinkin falalar azumin watan Ramadan:
(1) Rukuni ne daga rukunan addinin Musulunci, wato addinin Musulunci bai cika said a azumin watan Ramadan, wanda yake kasancewar azumin Ramadan yana daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar ya isheshi falala, Mala’ika Jibrilu ya tambayi Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi akan menene Musulunci ? sai Ma’aikin Allah ya ce:

((الإسلام أن تشهد أن لا إله إلا الله، وأن محمدا رسول الله، وتقيم الصلاة، وتؤتي الزكاة، وتصوم رمضان، وتحج البيت إن استطعت إليه سبيلا)). رواه مسلم.

Ma’ana: “Musulunci shi ne ka shaida da babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma lalle Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, ka tsayar da sallah, kuma ka bayar da zakkah, ka yi azumin Ramadan, ka yi aikin Hajji idan ka sami ikon haka”. Muslim ne ya ruwaito. Sai wannan ya nuna mana azumin Ramadan daya ne daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.
(2) Yadda Ma’aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi – ya fayyace falalar wannan azumin, ya ce: “A aljanna akwai wata kofa babu mai shigarta sai masu azumi”. Kana Ma’aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi –  ya ce:
((من صام رمضان إيمانا واحتسابا، غفر له ما تقدم من ذنبه)). رواه البخاري.

Ma’ana: “Duk wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da kuma neman lada an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubinsa”. Bukhari ya ruwaito.

Lalle wannan yana nuna mana irin girma da falala da daraja da azumin watan Ramadan yake da shi, shi ne azumin da yake gaba da kowanne azumin, kana shi ne azumin da ya fi kowanne azumi falala da daraja. Bannan abinda ake so shi ne mutum ya yi wannan azumi na Ramadan yana mai imani da Allah da Manzonsa, yana kuma mai kaunar lada a wurin Allah. Saboda haka koda kana kwadayin yin azumin nafila amma ana binka wani azumin na Ramadan to lalle ilalla shakka babu na Ramadan da ake binka shi zaka fara gabatarwa tukunna, domin shi ya fi kowanne azumi falla, daga nan ink agama ranka wanda ake binka sai ka yin a nafilar da kake son yi.

AKAN WA AZUMIN RAMADAN YA WAJABA?.

Idan watan Ramadan ya kama akawai wadanda azumin ya zama wajibi akan sun an take da zarar an ga wata, akwai kuma wadanda azumin bai haukansu ba anan take, wasu za su rama shi bayan wucewar watan wasu daga cikin su kuma ba za su rama ba, anan za mu yi bayan kowanne.
Wanda azumin watan Ramadan yake wajaba akansa shi ne: “Dukkan wanda yake musulmi, baligi, mai hankali, mai lafiya wanda ba a halin tafiya yake ba”.   

Musulmi: Da muka ce dukkan wanda yake musulmi, kenan an fitar da duk wanda yake ba musulmiba. Azumin Ramadan yana wajaba ne akan musulmi mace ko namiji banda wanda ba musulmi ba. Idan wanda ba msulmi ba ya yi azumi to azumin bai yi ba, sannan kuma idan wanda ba musulmi ba ya musulunta to ba zai rama azumin da ya wuce ba, idan ya musulunta cikin watan Ramadan ne da rana to da zarar ya musulunta sai ya dakatar da cin abin ci da kuma shan abin sha, amma an so bayan azumi ya wuce ya rama wannan guda dayan, na ranar da ya musulunta wannan idan ya musulunta da rana kenan, amma idan ya musulunta bayn shan ruwa ko kafin sahur wannan kai tsaye za’a tashi da shi ne da azumi.

Baligi: Azumin Ramadan na zama wajibi ne akan wanda ya balaga, idan yaran da ba su balaga ba suka yi azumi azumin ya yi, kuma ba zai rama adadin azumin da bai yi ba kafin ya balaga.

Kadan daga alamomin balaga akwai: Fitar maniyyi daga mace ko namiji, bayyanar gashin mara mace ko namiji, jinin al’ada ga mace kadai, ciki ga mace kadai…’’. To da zarar daya daga cikin wadannan alamomi sun bayyana to lalle hukunce hukuncen shari’a sun hau kan mutum ciki kuma har da azumin watan Ramadan, saboda haka sai iyaye da malamai su kula. Domin irin yadda ake barin balagaggun yara ba sa azumi suna ci suna shad a rana, wai ai ba su yi aure ba, ko kuma ai yau suna da aiki a gida ko a gona koma dai a inane wannan ba karamin laifi ba ne.

Mai Hankali: Idan mahaukaci ya yi azumin watan Ramadan to azumin bai yi ba, domin sharadi ne na mai azumin ya zama mai hankali.

Mai Lafiya: Idan mara lafiya ya yi azumi to azumin ya yi, idan kuma ya aji ye azumin to sai ya rama adadin kwanakin da ya sha, babu wani abu akansa bayan haka.

Matafiyi: Shi ma matafiyi iadan ya yi azumin a halintafiyar ta sa to azumin ya yi, idan kuma ya aji ye hakamma ya yi, sai ya rama adadin kwanakin da ya ajiye bayan sallah.

Kammalawa: Da wannan takai taccan bayanin, ya bayyana a garemu yadda falalar azumin watan Ramadan take, da kuma wadanda azumin ya wajaba akan su, kana da hukunce hukuncen haka. 
   
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com


Friday, May 3, 2019

0034. HUKUNCE HUKUNCEN AZUMI

Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi  Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki daya. Bayan haka:
 A wannan lokacin kuma za mu yi bayani ne akan abinda ya shafi hukunce hukuncen azumi, kama daga ta’arifinsa da kuma falalarsa da kuma nau’ukansa, da sauran bayanai da za su zo akan abinda ya shafi hukunce hukuncensa, da fatan Allah ya yi mana jagora ya kuma datar da mu ya anfanar da mu.
AZUMI.
Idan aka ce azumi a hausa to shi ake cewa (SWAUMU/SWIYAMU) da larabci, a larabci idan aka ce ((Swam)) To ana nufin kamewa ne, amma a shar’ance shi ne:

هو الإمساك عن شهوتي البطن والفرج يوما كاملا بنية التقرب إلى الله تعالى قبل الفجر أو معه في غير زمن الحيض والنفاس وأيام الأعياد.

Ma’ana: Shi ne kamewa daga barin sha’awar ciki da kuma farji cikakken yini da niyyar neman kusanci ga Allah, wacce niyyar za’a yi ta ne kafin hudowar alfijr ko daidai lokacin da alfijirdin yake fitowa, ba a lokacin jinin al’adaba ba kuma na biki ba, kuma ba lokacin bukukuwan sallah ba.
SHARHI.
A wannan ta’arifi na azumi yana kunshe da asalin abinda ake bukata daga mai azumi, ta yadda da zarar an rasa daya daga ciki to wannan abin bai zama shar’an taccen azumi, wadannan abubuwa sune kamar haka:
(1) Kamewa daga barin sha’awar ciki. Kenan wanda bai bar sha’awar cikinsa ba, wacce take ko wannan sha’awar ita ce abinci ko abin sha, ko kuma dukkan wani abu da zai zatsaya matsayin abinci ko abin sha to wannan ba shi da azumi. Ba zai taba yiwu wa ba mutum ya ce yana azumi sannan kuma yana cin abinci ko yana shan abin sha ba.
(2) Kamewa daga barin sha’awar farji. Sha’awar farji kuwa ita ce ko dai saduwa wato jima’i, ko kuma fitar da maniyyi ko maziyyi, wadannan abubuwa uku su ne sha’awar farji, kuma duk mai azumin da ya yi daya daga cikin wadannan abubuwa uku wato ya yi jima’i ko ya fitar da maniyyi ko maziyyi mace ko na miji to ba shi da azumi, domin kowanne daya daga cikin su sha’awace ta farji. Kuma Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce – a lokacin yana bayyana falalar azumi – ya ce Allah madaukakin sarki ya ce:

((الصوم لي، وأنا أجزي به، يدع طعامه وشربه وشهوته من أجلي)). ((رواه البخاري)).

Ma’ana: Azumi nawa ne, kuma ni zan bada sakamakonsa, (mai azumi) yana barin abin cin sa da abin shansa da sha’awarsa saboda ni”. Bukhari ya ruwaito. Domin duk wanda ya fitar da maniyyi ko maziyyi to lalle wannan bai bar sha’awarsa ba.   
(3). Cikakken Yini. Abinda ake nufi da cikakken yini shi ne tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana. Idan aka sami gibi akan haka to azumi bai yi ba, domin Allah madaukakin sarki cewa ya yi:

((وكلوا واشربوا حتى يتبين لكم الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر، ثم أتموا الصيام إلى اليل)). البقرة

Ma’ana: Kuma ku ci ku sha, har sai silin farin zare ya bayyana daga silin bakin zare na alfijr, sannan kuma ku cika azuminku zuwa dare.” Bakarah.
Wannan ya nuna inda jinin al’ada zai zo mata minti kadan kafin shan ruwa to ba tad a azumin wannan ranar saboda ba ta a zumci yinin ba ki daya ba. Haka kuma inda jinin al’adar zai dauke mata minti kadan bayan fitowar alfijir to haka shi ma yake ba ta a zumin wannan yinin, dalili kuwa shi ne ba ta azumci yinin baki yaba, kuma abinda Allah ya fada shi ne azumtar yinin baki yada.  
(4) Da niyyar neman kusanci ga Allah, wacce niyyar za’a yi ta ne kafin hudowar alfijr ko daidai lokacin da alfijirdin yake fitowa. A wannan gabar akwai manyan abubuwa guda biyu da ya kamata a yi la’akari da su:
Abu na farko; Niyyar neman kusan ci ga Allah, kenan inda mutum zai ki ci ya ki sha saboda bai sami sarari ba ko sabo da likita ya hana shi ya ci ko ya sha…. Duk wannan ba ya sa ya azumi, shi azumi lalle ne sai idan Allah aka nufata da shi, sannan ne yake amsa sunan azumi shar’antacce.
Abu na biyu: Lokacin da za’a niyyar, lalle dukkan wanda zai ta shi da azumi to ya wajaba akan shi ya kudurce niyyar yin azumin azuciyar shi a cikin daren kafin alfijir ya fito ko kuma daidai lokacin fitowar alfijir din, domin da hakanne zai zama ya azumci cikakakken yini, kamar yadda muka yi bayani a ayar da ta gabata ta Suratul Bakarah, sannan kuma ga Hadisi sayyidah Hafsah – Allah ya kara mata yarda - mai dakin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi:

((لا صيام لمن لم يبيته بالليل)). رواه الترمذي.  ضعيف في رفعه، صحيح في وقفه.

Ma’ana: Babu wani azumi ga dukkan wanda bai kwana da niyyarsa ba da daddare. Tirmi ne ya ruwaito.    
(5) Ba a lokacin jinin al’adaba ba kuma na biki ba, kuma ba lokacin bukukuwan sallah ba. Wannan tsagi na ta’arifin azumi yana bayani ne a kan lokutan da ba’a azumi a cikin su, kuma ko an yi azumin bai yi ba sai an sake kuma an sabawa Allah.
Wadannan lokuta sune kamar haka:
- Lokacin Jinin al’ada, idan mace tana al’ada to ba ta azumi, kuma in ta yi azumin to azumin bai yi ba sai ta sake shi, sannan kuma ta sabawa Allah da Manzonsa.
- Lokacin Jinin Biki (wato jinin haihuwa), idan mace tana jinin biki to ba ta azumi, kuma in ta yi azumin to azumin bai yi ba sai ta sake shi, sannan kuma ta sabawa Allah da Manzonsa. 
- Lokutan Bukukuwan Sallah: Ba’a azumi a ranar karamar sallah ko babbar sallah, duk kuma wanda ya yi azumi a wadannan ranaku to azumin shi bai yi ba kuma ya sabawa Allah da Manzonsa.
Wannan shi ne ta’arifin azumi, sabanin haka to ba azumi ba ne, sannan wannan ya shafi ko wane azumi.
Nau’ukan Azumi.
A zumi ya kasu kashi – kashi, akwai azumin wajibi a kwai kuma wanda ba na wajibi ba.
Azumin Wajibi.
Azumin wajibi shi ne azumin da shari’a ta dorawa mutum, ta yadda idan ya yi wannan azumin to za’a ba shi  lada,idan kuma bai yi ba to zai iya fuskantar ukuba. Azumi na waji bi su ne kamar haha:
1. Azumin watan Ramadan.
2. Azumin Kaffara.
3. Azumin Alwashi.   
Sai kuma azmin da bana wajiba,wanda idan mutum ya yi yana da lada, idan kuma bai yi ba to ba shi da wannan ladan, kuma ba shi zunubi. Kamar:
1. Azumin Ranar Arafat.
2. Azumin Tasu’a Da Ashurah.
3. Azumin Litinin Da Alhamis.
4. Azumin Kwana Uku A Kowanne Wata.
5. Azumi Shida A Watan Shawwal (Sittu Shawwal), Da dai sauransu.
Kammalawa: Adaidai nan za mu dakata, da fatan mun fahimci menene azumi? Menene yake shiga cikin azumin menene kuma ba ya shiga, a karo na gaba za mu kawo bayanai akan hukunce hukuncen nau’ukan azumi, ta yadda za mu fara da Azumin Ramadan.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Niger – Nigeria.
+2348064022965.

e-mail:aliyusadis@gmail.com