Da sunan Allah mai yawan rahama mai
yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga ma'aikin Allah. Bayan haka
lalle wannan masifa da ta aukawa kasarnan a wannan gagarumin aiki wanda yake
rukunine daga cikin rukunan addinin musulunci abin a tsaya ai nazarinta ne domin
aga ta ina ta fito kuma ya za'a tunkareta ta yadda ba zata sake aukuwaba, domin
ace mutum ya isa kasa mai tsarki lamilafiya amma kuma a dawo da shi kai wannan
ba karamin tashin hankali bane Ya Allah muna rokonka da kada musake ganin
maimaituwar wannan al'amari. Kamar yadda na fada lalle ya kamata mu tsaya mu yi
wa wannan lamari karatun ta-natsu, mabudin wannan karatu itace ayar dake cikin Suratus
Shura aya ta 30. ''Kuma duk abinda ya sameku na kowacce irin masifa to fa
saboda abinda kuka gabatarne, kuma (Allah) Yana ga abubuwa masu tarin yawa''.
Lalle
la'akari da wannan ayar yana dakyau mu tsaya muga me aka gabatar da ya haifar
da wannan al'amari don asan matakin da za'a dauka don hana aukuwar irinshi nan
gaba. Ni a ganina wadannan al'amurra sune kamar haka:
1. Mahrami: Shine mutumin da yake haramunne ya auri matar da yake tare
da ita (kamar uba mahramine na 'yarshi, ko kaka ko siriki) shi yasa sai ace
mahrami ko miji, Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-
yana cewa: Bai halatta ga dukkan matar da tai imani da Allah da ranar
lahira da ta yi tafiya kwana guda ba tare da maharraminta ba'' Hadisai
da suka zo daga ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-
a kan haka suna da matukar yawa da fayyace al'amurra a fili da suke nuna irin
gatan da musulunci ya yi mace lura da cewa ita mai raunice baibukar taimakoce a
koda yaushe kuma ko wanne iri. An
ruwaito cewa wani daga cikin Sahabban ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- an sanyashi cikin wadanda za su
tafi yaki sai yace medakinshi zata tafi aikin hajji sai ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace acire sunansa ya tafi ya je ya
yi aikin hajji tare da maidakinshi. Kuma wannan al'amarii sannannene cewa
alokacin da mace take tare da mahraminta ko mijinta zata dada kamewa doruwa
akan wacce take da ita, in kuma ba kamammiya bace to zata kame da izinin Allah,
kuma zata zama tana da abokin hira a wannan tafiyar, hikimomi da zaka iya
zakulowa cikin muhimmacin mahrami a tare da mace a Halin tafiya ba karamin
al'amari bane, duk wanda ya taba yin aikin Hajji zai tabbatar da muhimmancin
mahrami tare da mace, ba Mijin-Biza ba domin akwai halin da ake shiga na
sai ka rike mata hannu ko jiki, wanda yake haka ba zai yiwuba idan ba
maharramaka bace. Malamai sun karawa juna sani kan abinda ya shafi aikin Hajji
shin idan aka sami tawaga amintacciya
mace zata iya tafiya a cikinsu ko dab a mahraminta? Sai wannan tawaga ta
zama kamar mataimaka a gareta? Malamai da yawa sun tafi akan haka,
Maganar
mahrami maganace da ta taso a aikin Hajjin wannan shekarar ta 1433 Hijira ko
2012 miladiyya, a inda akan hakanne hukumar kasar Saudiya ta dawo da mahajjata
mata masu tarin yawa daga kasar, na farko da maganar mahrami tabbatacciiyace a
shara'a domin ta fitone daga bakin Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ba Magana bace da hukumar kasar
Saudiya ta kirkiri bam domin na ji Nura Das Ahirarsa da jaridar Leadership
Hausa bugu na 313, a shafi na 25 yana cewa Ba kowanne mahajjaci
bane ke bin akidar Wahabiyaci, Su a mazahabinsu na Ja'afariyyah wanda aka fi
sani Shi'a mace idan ta amincewa kanta ko waliyyanta sun amince mata zata iya
tafiya ko inane, wannan Magana tasu ta nuna abinda acewa su Shi'a ba abinda ya
hada su da karantarwar ma'aikin Allah, in banda ina maganar bin tafarkin
ma'aikin Allah ina kuma maganar wahabiyanci?. Maganar maharami manace data
mamaye kafafan yada rabaru a kasarnan kuma maganace da take bukatar a tsaya a
yi mata karatun-ta-tsau domin sanin hikimomi da tausayawa da musulunci ya yiwa
'ya mace, kafafan yada labaru sun cancanci yabo yadda suka tunubi malumma akan
wannan al'amari wato suka maida al'amarin zuwa ga masu shi. To amma
hanzari-ba-gudu-ba maganar da kafofin yada labarai suke yi na cewa anya maganar
mahramce kadai tasa wannan al'amari ya faru koko akwai lauje cikin nadi domin
mata 'yan Nijeriya kawai aka dawo da su banda 'yan wadansu kasashen? Wannan
maganar ya kamata a yi la'akari da ita, wannan ya kaimu abu na biiyu wato.
2. Gurbacewar Tarbiya: A gaskiya Najeriya tana da matukar
kima da daraja a idanun kasar Saudiya, amma a gaskiya halayyar da 'yan Najeriya
suke nunawa a wadannan wurare masu tsarki musamman ma a birnin Makkah birni
mafi tsarki da daraja gaskiya a kwai bantakaici, mata nawane suka tsallake
mazajensu su kai zaman dirshan a birnin makkah, me ya kaita? me take yi? Asalin
Magana a musulunci mace bata ciyar da kanta kwata-kwata, idan ta yi aure
mijinta ya ciyar da ita idan batai aure ba mahaifinta ko waliyyinta ya ciyar da
ita. Duk mutumin da ya tabayin aikin hajji zai ga irin halayya da sutura ta
rashin mutunci da wasu matan -wasu cikin mahajjata- suke nunawa a ranar sallah
matsattsun kaya wasanni marasa kyau tun kafin a gama zaman mina, ballantana a
gidan da alhazai suka sauka ka ga yadda ake da 'yan-tuwo-tuwodin abin zai baka
mamaki kamar ba a kasa mai tsarki ake ba, idan akai maganar dogon-gida ko
Sara-Mansur abirni Makkah da sauran unguwanni kamar su Jabal abin ba'a cewa
komai. Ni inagani ya kamata ofishi Najeriya ya shirya wata bita da karantar da
'yan Najeriya da tarbiyantar da su a biranan Makkah da Jiddah da kuma Madina,
kuma ya tashi tsaye yaga 'yan Najeriya suna zaune akasar a bisa doka, anan ba
ina cewa duka 'yan Najeriya haka suke ba a'a kwata-kwata, akwai tsayayyu, amma
mu sani idan fitina ta zo ba tana takaituwa bane ga wadanda suka janyota kamar
yadda muka gani a wannan shekarar, zaka iya samun macan da bata ganin jirgin
sama a kasaba sai wannan karon amma gashi bala'in wasu ya janyo mata, Allah
Madaukakin sarki yana cewa:
''Kuma ku ji tsoron fitina wacce
ba ta samun danda suka yi zalunci daga cikinku kadai, kuma ku sani lalle ne
Allah Mai tsanani ukuba ne'' Sutul-Anfalm aya ta 25.
Mai karatu idan kana jin abinda 'yan
Najeriya suke aikata a kasa mai tsarki musamman mata abin zai dauure maka kai
matuka da gaske, yanzu idan aka ce maka dukkan matan da suka je Umarar nan data
wuce sun dawo nan Najeriya? Me zakace ko kuma ka tambaya.
Sannan suma
hukumar alhazai ta Najeriya ya kamata ta tashi haikan wurin sanyawa maniyyata
tsoron Allah da kula da dokokin Sa, a samu malamai masu tsoron Allah wadanda ba
himmarsu a biya musu kujeraba, wadannan dakakkun malamai sukasance na
dindin-din ko kaso mai yawa daga cikin su sannan abasu damar gudanar da aikin
nasu.
3. Mace mai Juna-biyu: Lallekan akwai maganar wahala ga
mace mai juna-biyu a aikin hajji mutum ma yana shi kadai ya yacika, amma irin
matakin da hukuma ta dauka na haramtawa mace mai juna-biyu aikin hajji wai koda
kuwa na wata dayane gaskiya ya kamata a sake duba wannan Magana idan andubeta
ta bangaren kiwon lafiya a dubeta ta bangaren addini, babu wani dalili aduk
abinda malamai sukai ijima'i aka kafa dalili da shi da ya nuna cewa mace mai
juna-biyu bata da damar zuwa aikin hajji, ni ina jin tsoro kada irin wannan
hani da aka yiwa wadannan matan yasa aka wannan dayyar matsalar, kada mu
sha'afa maganar addini ake yi asalima shi aikin hajjin ginshikine daga cikin
shika-shikan musulunci guda biyar, saboda haka kada ka kuskura ka hana wani
wannan aiki ba tare da kanada kakkarfan dalili da zaka gabatarwa Allah ba a
ranar kiyama, a shekarar da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su kara
tabbata a gareshi- Ya yi aikin Hajji wanda shine kuma akekira da hajjin
bankwana, adaidai lokacin da Ma'aikin Allah ya isa Zul-Hulaifah inda nan ne
mikatin mutanan madina yana zuwa wurin medakin Sayyidina Abubakar ta sauka
(tahaihu), kaga kenan ta fito ne ma da tsohon ciki, awannan tafiya da ake akasa
ko a doki ko a rakumi, wanda ba za'a hada hakan da jirgin-sama ba ko na ruwa ko
mota ba. Wannan matsananciyar dokar data zamar da mata da yawa Hajji Haram ya
kamata a sake dubata, wadda ta sanadiyyar ta ake ruwaito mata da yawa suna
zubar da cikinsu, irin wannan mataki na anfani da na'urori masu gani harhanji
masu ganin-kwakwaf na cewar indai har anbankado cewar tana da ciki to Hajji
Haram ya kamata a sake dubawa.
Shawarwari/Mafita: Ni ina ganin bin wadannan shawarwari zai zama wata
mafita ga rashin sake maimaituwar irin wannan al'amari, da muke rokon Allah Ya
kiyayemu daga maimaituwar wannan alamari:
1.
Tsayawa da tabbatar da mahrami shar'antacce muddin akwai
yadda za'a same shi ba abinda ake cewa
mijin-biza ba.
2.
Gabatar da cikakkiyar bita akan mece ''Rifka
Ma'amuna'' sannan suwaye, a kuma gabatar musu da bita ta sanin makamar
aikin ''Rifka Ma'amuna''.
3.
Tashi tsaye domin a wayar da kan mutane dangane da matsayin
mahrami a shara'a, da kuma bayanin gatan da musulunci ya yiwa mata akan sanya
musu mahrami da ya yi.
4.
Kimsawa maniyyata tsoron Allah madaukakin sarki, da kuma
falalar da maibin Allah yake da ita da kuma narkon sabawa Allah, a gida
Najeriya ko a kasa mai tsarki.
5.
Kimsawa maniyyata bin tafarkin Ma'aikin Allah da kuma cewar
rabauta duniya da lahira ta tattarune akan tsantsanta biyayya ga reshi.
6.
Karfa halartar maniyyata
wuraran bita.
7.
Samar da wata manhaja ta baidaya kakkarfa akan abinda ya sha
fi bita.
8.
Kara samarwa malamai masu tsoron Allah gurabu a harkar
hajji, da kuma basu karfin fada aji.
9.
Kara sa ido da dokar da ta dace ga duk wanda ya yi fitsara a
duk wurin da ya shafi Hajji tun daga wuraren bita har kamala aikin hajji.
10. Sanya ido ga dukkanin
jahar da ta bari wani alhajinta ya ki dawowa.
11. Karamin ofishin
jakadancin Najeriya dake birinin Jiddah ya samara da wata ganawa da 'yan
Najeriya dake Makkah, Jiddah da Madina domin karantar da su da kuma kara nuna
musu tsarkin wurin da suke zaune.
12. Daukar matakin
ladabtarwa ga duk dan Najeriyar da ya karya ittifakiyar da aka yi da kasar
Saudiyyah.
13. Sake duba maganar mace
me juna-biyu, domin kada mu manta tun kafin Saudiya su nemi su zamar da wasu
mata Hajji Haram tuni Najeriya ta zamar da wasu.
Allah madaukakin sarki ya tsaremu ya
tsare mana imanimmu, ya kawo mana karshen wannan kiki-kaka da ake yi da alheri,
Allah ya kai alhazammu mata da maza kasa mai tsarki lafiya ya kuma dawo mana da
su lafiya. Ya Allah katsare mana kasarmu ka zaunar da mu lafiya da dukkanin
kasashen musulmi bakiya, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu,
bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar
Neja Nijeriya.
Za'a iya
tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu
Muhammad Sadisu
www.youtube.com/Aliyu
Muhammad Sadisu
No comments:
Post a Comment