Tuesday, September 24, 2013

010- YADDA AKE WANKAN TSARKI


Matashiya: Bayanda bayanai suka gabata akan abubuwan da suke wajabta wanka, ayanzu za mu kawo bayani akan yadda ake gabatar da waken da izinin Allah.
   Da farko dai mu sani shi wannan wanka amanace daga cikin tarin amanar dake tsakanin bawa da mahaliccinsa, saboda haka ya zama wajibi ka kiyaye wannan amanar, kuma ka himmatu da sanin hukunce hukuncen wannan wanka, domin ka gabatar da shi a yadda musulunci ya tsara, abinda ya rikice maka sai ka yi tambaya, kada kace wai kunya zata hanaka, jin kunya a irin wadannan al'amurra abune da musulunci bai yarda da shiba, kuma wani nau'ne na tsoro da shaidan yake tsoratar da mutane da shi, kuma ya sanyawa mutum kasalar da ba zai iya gudanar da cikakken addiniba. Al'amarin hukunce-hukuncen tsarki al'amarine mai girman gaske, sakaci a cikin wannan lamari yana da matukar hadari, domin kada ka manta hukunce-hukunce sallah ya ratayune fa da tsarki wacce kuma sallar nan itace ginshikin addini.
Farillan Wanka: Ka/Ki sani shi wankan tsarki yana da farillai da kuma sunnoni dama mustahabbai, amfanin saninsu shine domin duk abinda yake farillane sai baka yi shi to wankan bai yiba, amma idan sunnah ka bari wankan ya yi saidai ka rage lada. Su farillan guda biyarne;
(1) Niyya: Abinda ake nufi shine ka kudurce a zuciyarka/ki yanzu hakannan wankan janaba zaka yi ko zaki yi, ko kuma na daukewar al'ada ko biki…', wannan itace niyya, ba wadansu abubuwa ake karantawaba, niyya kuma tana da matukar muhimmanci, ai kaga shi yasa ta zo a farko.
(2) Game Jiki Da Ruwa: Ana so ka tabbatar ko ina a jikinka ya sami ruwa, kada ka manta da dukkan mahadar gaba.
(3) Cuccudawa: Ka tabbata ka cuccuda ka gurza ko ina da gwargwadon hali, kada ka manta da kasan hammata da dukkan matse-matsi…'.
(4) Tsefe Gashi: Ka tabbata ruwa ya shiga ko ina a cikin gashin kanka ko kanki, Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa: ''Karkashi ko wanne gashi akwai janaba, ku wanke gashi, ku kuma tsaftace jiki''. Abudaud, 248, Tirmizi: 106, Ibnu Maja: 597.
(5) Yi Lokaci Guda: Wannan shi ake nufi 'Muwalat' ma'ana idan ka fara to kada wani abu ya katseka sai ka kammala.
   Wadannan sune farillai ka tabbata sun cika a duk lokacin da kake wanka, kada ka manta shi wankan tsarki anayin shine da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa ken an banda mai sabulu. Ka samu idan kana da janaba kuma kanason ka yi wankan tsarki da kuma wankan zuwa wurin aiki ko kasuwa da sauransu, sai ka fara gabatar da wankan tsarki tukunna, idan ka gama sai ka sa sabulu ka ci gaba da wankanka.
Siiffar Wankan Janaba: Da farko za ka yi niyya a zuciyarka (kamar yadda bayani ya gabata). Sannan ka ce: Bismillah, sai ka wanke hannayanka biyu sau uku, sai kuma ka wanke gabanta (al'aura), hannun dama na zuba ruwa na hagu yana wankewa, sannan sai ka goge hannun naka a bango, sai ka gabatar da cikakkiyar alwala, sannan sai ka kamfaci ruwa ka zuba a kanka domin ka kosar da gashin kanka zaka yi hakanne sau uku. Sannan sai ka dibi ruwa ka kwarara a jikinka kana cuccudawa domin rowan ya kai ko ina, Shikenan ka gama.
   Kana da dama ka wuce zuwa sallah kai tsaye batare da ka yi alwalaba, sai dai idan wani abu cikin abubuwan da suke karya alwala ya faru. Kada ka manta koda kana cikin wanka alwalarka ta karye wankanka nanan ba abinda ya sameshi, sai idan kana so ka yi sallah to sai ka yi alwala.
   Banbanci Janaba Da Al'ada: Anan ana so ki gane wankan janaba da wankan daukewar jinin al'ada ko biki duk iri dayane, inda suka banbanta kadanne. Wuri na farko: Niyya, domin da ita ake banbace ibada da ibada kamar wannan da muke Magana kai. A wankan janaba mace ba sai ta kwance kitson ta ba domin hakan zai zama akwai wahalarwa sai ya wajaba ta tabbata ruwa ya shiga asalin tushan gashin kai, amma a wankan daukewar al'ada ko na biki ya halatta ta kwance kitson dake kanata, amma ba wajibi bane, a dai tabbata ruwa ya shiga ko ina wannan kuma ya shafi maza kamar yadda ya shafi mata, akwai maza masu yawan gemu da suma to dolene a tabbata ruwa ya kai ga asalin tushan gashi, a cuccuda ko ina da ina, idan mutum yana sanye da zobe ya tabbata ruwa ya shiga karkashin zoben, akyautata wanka a kuma karanta ruwa. Allah ya sa mu dace.
   Idan mace al'adarta ta dauke kuma ga wankan janaba akanta, to wanka guda za ta yi sai ta gwama niyyar kamar yadda wadansu malamai suka fada, domin wankan janaba dana al'ada duka wajibine kuma komai nasu dayane…'.
   Idan mutum yana da janaba kuma ga wankan juma'a, to anan ya samu ya shgar da wankan juma'a cikin na janaba, ba wai ya shigar da na janaba cikin na juma'aba, domin na janaba wajine, amma na juma'a ba wajibibane a mafi yawan maganganun malamai.
   Idan ka yi wankan janaba sai kuma ka manta baka yi alwalaba wankanka ya yi, kuma ka samu ka yi sallah ko da baka yi alwalaba muddin ba wani abun da ke karya alwala da ya faru, domin alwalar ta shiga wanka duk inda zaka wanke a alwala ka wanke shi a wanka, kuma kamar yadda alwala take wajibi kafin sallah haka wanka yake wajibi ga mai janaba.
   Amma idan mutum ya yi wankan juma'a to sai ya yi alwala kafin sallah.
  Ya hallata miji da mata su yi wankan janaba tare, kamar yadda aka ruwaito daga daya daga matan ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana yi.
   Ka samu ka jinkirta wanka amma sai ka yi alwala domin alwalar na rage kaifin janaba, kuma tana kara kuzari idan za'a sake saduwa.
  Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata ya bayyana a fili yadda addinin musulunci ya kula da tsarkaka da kuma lafiya, domin janaba bakaramin al'amari bace, saboda haka aka shar'anta wanka, kuma aka kawo siffar wankan daki-daki domin ka fahimci a musulunci ba'a yin abu da ka, fatammu shine Allah ya karba mana kurakurai kuma ya gafarta mana, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
    

Tuesday, September 17, 2013

009- WANKAN TSARKI (JANABA)


Shinfida: Bayan da bayanai suka gabata akan abinda ya shafi karamin hadasi wanda yake ya takaitune ga tsarki da kuma alwala, sannan bayanai suka zo akan abinda ya shafi kadan daga cikin hukunce-hukuncen alwala, to a yanzu za'a yi bayani ne akan abinda ya shafi babban hadasi wanda yake bai tsaya ga tsarki ko alwalaba a'a, shi tsarkinsa shine ayi wanka shine an tsarkaka, wadannan abubuwa da suke wajabta wanka suna da yawa za mu yi iya kokari damin mu kawo su daki-daki, da fatan Allah ya yi mana jagora, amin.
(1) Janaba: Janaba dayace daga cikin abubuwan da suke wajanta wanka, wanda yake hanyoyin kasantuwa da janaba sune kamar haka:
(a) Fitar Mani: Idan maniyyi ya fita daga mace ko namiji to wanka ya wajaba, amma kafin wankan ya wajaba sai ya zama maniyyin ya fitane ta hanyar jin dadi, kamar kallo ko wasa ko tabe-tabe ko jingina…' amma idan ya fita ba ta hanyar jin dadiba ya fitane ta hanyar wahala, kamar ya taka wuta ko harbin kunama ko kuma watar lantarki ta ja shi…' to wannan wanka bai wajaba a kanshiba saida kawai ya yi alwala. Shi wannan fitar maniyyi da ake Magana akan shi ko dai ya fita a farke ko kuma ya fita ana bacci, idan ya fita ana farke shine ake maganar an ji dadi ko ba'a ji ba, amma idan ya fita ana baccine to ba wata maganar jin dadi wanka ya wajaba.
(b) Shigar Azzakari Cikin Farji: Idan kan kaciyar namiji ya bace cikin gaban mace to wanka ya wajaba. Anan ba'a maganar an fitar da mani ko ba'a fitarba, da zarar hakan ya faru ko macen ce ta fitar amma namijin bai fitarba ko kuma namijin ne ya fitar amma macen bada fitar ba ko ma dukansu basu fitarba wankadai ya kamasu su duka, da wanda ya fitar da wanda bai fitarba, tunda ba maganar fitarwa ake yi ba maganar saduwace, amma inda wasa aka yi ba saduwa ba to wanda ya fitar shi wanka ya wajaba a kanshi.
   Idan aka yi saduwa sannan aka kara yi to idan an tashi wanka wanka guda kawai za'a yi, koda an yi saduwar sau gomane sannan ake so ayi wanka to wanka guda za'a yi ba wanka goma ba.
   Idan mutum ya sadu da mace kuma yake so ya jinkirta wankan janaba zuwa an jima to abinda zai yi shine ya yi tsarki sai ya yi alwala, domin alwalar tana rage kaifin janaba, sannan kuma tana kara kuzari lokacin da ake so akara saduwar.
   Idan mutum ya sadu da mace sai bai fitar da maniyyi ba wanka ya wajaba akanshi kamar yadda bayini ya gabata, to bayan ya yi wankan sai kuma ya ga maniyyi ya zubo, to anan idan wata sabuwar sha'awace ta fitar da wannan maniyyin wani wankan ya kama shi, amma idan janabar da ya yi wa wankace maniyyinta ya zo yanzu to alwala kawai zai yi.
   Abayan da suka gabata mun yi bayani na babbancin maniyyi da kuma maziyyi, sannan kuma da banbance-banbancen maniyyin mace da na namiji. Sannan mu sani wadannan bayanai sun shafi maza da mata, sannan kuma ka'ida ta musulunci itace bayanin abubuwa a yadda suke, domin kada a ga maganganun sun yi tsauri, mahalline na bayanin hukunce-hukunce.
   Fitar maniyyi a farke ko ta hanyar nafarki, kamar mutum ya yi mafarkin yana saduwa da mace, ko mace ta yi mafarkin namiji yana saduwa da ita to wannan al'amari yana tabbatar da abubuwa kamar haka; abu na farko wannan wanda ya fitar da maniyyin janaba ta hau kanshi, abu na biyu; idan wannan shine fitar maniyyinsa na farko to ya sani daga wannan lokacin ya balaga, saboda haka hukunce-hukuncen musulunci sun hau kanshi ko kanta.
   Idan mutum ya yi mafarkin yana saduwa da mace, ko mace ta yi mafarkin ana saduwa da ita, sannan kuma ya farka bai ga maniyyi ba to ba wata janaba akanshi, saboda haka ba zai wanka ba kuma zai yi tsarkiba saboda hakan.
   Wadannan kadan kenan daga cikin bayanan da suka shafi janaba, kuma dole a tashi tsaye domin a karantar da mutane, wani da ake Magana da shi cewa yake yi shi bai san idan mutum ya sadu da matarsa wai sai ya yi wankaba, wai abinda ya dauka shine wanda ya yi zina shine wanda zai yi wanka. Wannan jahilci har ina!.
Abubuwan Da Janaba Ke Hanawa: Bai halatta ga wanda yake da janaba ba ya shiga masallaciba, ko kuma ya karanta Alkur'ani ba, sai aya daya ko biyu domin neman tsari.
   Mutumin da yasan ba zai iya taba rowan sanyi ba to malamai sunce kada ya kusanci iyalinsa sai ya tanadi abinda zai dumama rowan dashi, kamar hita, risho ko itace…'.
(2) Daukewar Jinin Al'ada: Abu na biyu cikin abubuwan da suke wajabta wanka shine daukewar jinin al'ada, kenan idan jinin al'adar mace ya dauke to abu na farko dake gabanta shine wanka. Bayanai akan abinda ya shafi jinin al'ada da hukunce-hukuncensa da alamar daukewarshi da izinin Allah za su zo nan gaba, mudai sani idan jinin al'ada ya dauke to dole mace ta yi wanka, kuma zuwan jinin al'ada lamace dake nuna wannan mai jinin ta balaga musamman ace shine zuwansa na farko a wurinta, bayanai dai za su zo da izinin Allah.   
(3) Daukewar Jinin Biji: Wannan shine abu na uku daga cikin abubuwan da suke wajabta wanka, watau daukewar jinni haihuwa, da zarar mace ta ga jinin haihuwa ya dauke mata ko da ranar data haihune to wanka ya wajaba akanta domin ta fara sallah, ba wanda yace sai mai jego ta yi kwanaki arba'in kafin ta kama sallah, shima bayai akan jinin biji zai zo da izimin mai duka shine Allah, kawai mu sani anan daukewar jinin haihuwa yana wajabta wanka.
(4) Mutuwa: Mutuwa tana wajabta a yiwa wanda ya mutu wanka, shi kuma bayanai kan abinda ya shafi wankan da yadda ake yinsa zai zo ne alokacin da za'a kawo bayanai kan jana'iza da izinin Allah, kuma Allah ya kaimu lokacin, abinda ake so a fahimta anan shine idan mutum ya mutu to dole ayi mishi wanka sai dai idan shahidine da ya rasu a fagen fama.
(5) Musulunta: Wannan yana cikin abinda malamai suka karawa juna sani, shin idan wanda ba musulmiba ya musulunta wajibine sai ya yi wanka? Wasu sukace wajibine domin Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya umarci wasu da suka musulunta da su yi wanka, su kuma wadanda sukace ba wajibi bane wankan sunce ba'a ruwaito cewa Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya umarci dukkan wadanda suka musulunta da cewa kowa sai ya yi wanka ba.
   Kammalawa: A yanzudai munsan abubuwan da idan yada daga cikinsu ya faru to wanka ya wajaba, kuma mun sami takaitaccan bayani akan abinda ya shafi janaba, kama daga hanyoyin da ake samunta, bayanan da zasu zo nan gaba za su kun yadda wankan tsarki yake, wato wankan janaba da kuma na daukewar jinin al'ada (haila) da bambance-bancen dake cikin su, Allah ya kai mu lokacin da sauran kwana da kuma imani.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

008- ABUBUWAN DAKE KARYA ALWALA


Shinfida: Lalle wannan babi yana da matukar muhimmanci, domin bayan da kasan alwala to ya kamata kasan abin da ke warwareta, akan haka ya ka yiwa kanka hukunci idan zaka yi sallah ko abinda dole sai da alwala ake yinsa, saboda haka yana da matukar kyau mu kula da wadannan hukunce-hukunce. Allah ya yi mana jagora.
  Abubuwan da suke bata alwala sunkasu kashi biyu; Hadasi da Sababinsa. Abin nufi anan shine, akwai abinda shi karankan sa yake bata alwala to wannan shi ake kira Hadasi (Al'ahdaas). Akwai kuma wanda shi karankan sa bai warware alwala amma zai kai ka ga abinda yake warware alwalar to wannan shi ake kira, Sabuban Hadasi (Asbabul Ahdas).
   To shi hadasin wato abinda yake karya alwala da karankansa, abubuwane guda shidane, hudu daga cikinsu suna fitane ta gaba, sune kuma; Fitsari, Maziyyi, Wadiyyi da kuma Maniyyi. Wadannan idan suka faru ko dayansu ya faru to tsarki kawai za'a yi a sake alwala in banda maniyyi, Wanda shi maniyyi bayan ya bata alwala sai kuma anyi wanka. Sai kuma guda biyu daga da suke fita daga dubura, sune kuma; Bayangida da kuma tusa. Amma shi bayan-gida tsarki za'a yi sai a sake alwala, sabanin tusa wacce take ita ba'a yi mata tsarki alwala kawai za'a sake.
   Sai kuma abubuwan da suke sabubbane na hadasin wadanda yake suna da wasu bayanai, amma su wadancan da zarar ya diga komai kankantarsa to ya karya alwala inbanda mai fama da cutar yoyon-fitsari, wadannan abubuwa sune;
(1) Bacci: Shi bacci a nan ya kasu kashi hudu;
(a) Dogon bacci mai nauyi, kai tsaye wannan ya karya alwala.
(b) Takaitaccan bacci mai nauyi, shi ma ya karya alwala.
(c) Takaitaccan bacci mara nauyi to shi bai karya alwala ba.
(e) Dogon bacci mara nauyi, bai karya alwala amma an so a sake ta.
Ma'aunin da ake auna bacci da shi domin a gane yana da nauyi ko ba shi da nauyi shine; Idan ka san wanda ya zo da wanda ya tashi to baccinka bai yi nauyi ba, amma idan baka san wanda ya zo ba ko wanda ya tashi ba to baccin ya yi nauyi. Kenan idan kuna fira sai amma kana gyangyadi sai da ka farka sai kace; ina wane? Ko; wane yaushe ka zo? To kasan baccinka ya yi nauyi, Allah ya sa mu dace.
(2) Gushewar Hankali: Idan hankalin mutun ya gushe ta hanyar hauka ko farfadiya ko suma ko maye to mu sani alwalarsa ta karye. Kenan idan mutum ya yi alwala sai ya hau iska ko kuma suka yi hadari kawai sai ganinsa ya yi a asbiti ko kuma ya sha ta yi Marisa-ta sha kafso to alwalar ko wannensu ta karye.
(3) Shafar Azzakari: Idan mutum ya shafi al'aurarsa kai tsaye tafin hannunsa ya taba al'aurarsa bawai ta samani riga ko wandoba ko kuma wani kyalleba to malamai sun karawa juna sani kan makomar al'walarsa, wadansu suke ce kawai alwalarsa ta karye, wasu kuma suka ce idan ya tabane domin ya ji dadi to ta karye amma idan ba wai ya yi hakanne domin ya ji dadi ba alwalarsa nanan, wannan maganar kuwa tana da karfi. Amma dukkanin malamai sun yi ittifaki kan cewa idan ya taba al'aurarsa ba kai tsayeba ko dai ta saman wando ko saman riga ko saman wani kyalle to alwalarsa nanan daram.
(4) Shafar Mace/Namiji: Idan namiji ya shafi mace domin ya ji dadi to ko ya ji dadin ko bai ji ba alwalarsa ta karye, haka kuma al'amari yake idan mace ta taba namiji domin ta ji dadi to ta ji dadin ko bata ji ba alwalarta ta karye, malamai sun kasa shafar zuwa gida hudu;
(a) Idan ya taba domin ya ji dadi kuma ya ji dadin to alwalar ta karye.
(b) Idan ya taba ba don ya ji dadi ba sai kuma ya ji dadin to ta karye.
( c) Idan ya taba domin ya ji dadi sai bai ji da din ba to alwalar ta karye.
(d) Idan ya taba ba domin ya ji dadi ba kuma bai ji dadinba to alwalarshi tanan daram. Wadannan bayanai haka mai Ashmawi ya kawosu. Mu sani wadannan bayanai sun shafi macema idan ita ta yi.
   Akwai wadansu da malamai suka karawa juna sani akan suna karya alwala ko basa karyawa?, wadannan kuma sune:
(5) Shakka Akan Hadasi: Idan mutum ya tabbatar da alwalarsa sai kuma yake kokwanto ya yi hadasi ko bai yi ba? Kenan bashi da tabbas? Wasu malamai sukace; Ai da ya yi kokwanto alwalarsa ta karye domin ba'a sallah da wani abu na shakku. Wasu malaman kuma suke: Idan ya tabbatar da yana da alwala sai daga bayane yake shakka to ai shakka bata ture abinda yake dahir, saboda haka sukace alwalar nanan, Allah shine masani.
(6) Ridda: Shine mutum musulmi ya kafirta (Allah Ya tsaremu). Wadansu malamai sukace da zarar ya bar musulunci to da zarar alwalar ta karye, wasu malaman kuma sukace; A'a, ai ayyukansa da ya yi  ba za su baciba sai in ya mutu bai dawo musulunci ba, wadda alwala na cikin wadannan ayyukan. Mafi kyawu ga wadannan abubuwa mutum ya sake alwalar shi yafi.
   Alwala bata baci idan mutum ya yanke farce (Kunba), ko ya taba marenansa ko duburarsa ko anyi masa kaho ko ya yi dariya ko amai ko kuma tuntube har jini ya fita duk alwala bat abaci saboda wadannan, ko mace ta shafi gabanta amma idan ta sa yatsa a ciki to wasu sunce alwalar ta karye. Idan mutum yana jin fitsari ko tusa ko bayan gida abinda musulunci ya karantar shine mutum ya je ya biya wannan bukatar ta shi tukunna, maimakon ya matse.
  Kammalawa: Alwala tana da muhimmanci matuka saboda haka a kiyayeta a san kuma abinda yake warwareta, kuma wannan yake nuna mana cewa tunda har alwala za'a ce akwai abubuwan da suke warwareta dudda ga laima a jikin mutum amma ace alwalarsa ta warware to lalle yana da kyau musan kuma abubuwan da suke warware musulunci domin kullun mutum ya dinga ba addininsa kariya ta yadda kada ya warware, Allah yak are mana addinimmu, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Thursday, September 12, 2013

007- TSARKI DA YADDA AKE YINSA


Shinfida: Mu sani ya 'yan-uwa masu albarka, wannan addini na musulunci addinine da yake cikakken addini ta kowanne bangare, bai takaitu ga alwala da sallaba kadai, ya shafi kowanne bangare na rayuwa, kamar tsafta kiwon lafiya zamantakewa, kasuwanci taimakon juna, tsare-tsaren gudanarwa dadai sauransu.
   A yanzu zamu kawo bayanaine da suka shafi tsarki, dame-dame ake yiwa tsarki? Me rashin tsarkin yake jawowa? Ya ladubban yin tsarkin suke? Ya ake shiga makewayi? Dadai sauran wadansu batutuwa da suke da alaka da wannan maudu'i, da fatan Allah ya yi mana jagora ya kuma fahimtar da mu.

Abubuwan Da Akewa Tsarki: ana yin tsarki ne daga dukkan abinda ya fito ta daya daga mafitar guda biyu ko ma ta duka inbanda hutu (tusa). Kenan ana yiwa fitsari, bayangida maniyyi maziyyi jinin al'ada….tsarki, kawai dai idan mutum yana da alwala sai ya yi tusa to alwalar kawai zai sake ba sai ya dauki butu ya yi tsarki ba.
Hukuncin Tsarki: Tsarki wajibine, saboda haka dukkan wanda dayan wadancan abubuwa da makamantansu suka same shi to dole ya tabbata ya gabatar da ya yi tsarki.
Abinda Ake Tsarki Da Shi: Abinda ake tsarki da ashar'ance shine ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, wannan shi ake kira Istinja'u. Saidai idan mutum bai sami ruwanba sai ya yi da duwatsu a kalla guda uku, idan ya ga na ukun ya fito a bushe ba wata laima shikenen, idan kuma akwai laima to sai ya kara su kai biyar wuturi ake bukata (3,5,7,9…) wannan kuma ana yinshi a fitsari ko bayan gida, sannan idan ka sami ruwa ba sai ka sake ba, wannan hukunci shi ake kira Istijmari, ka samu ka hada duka a lokaci guda, misali idan ka yi bayan gida sai kasa tsinke ko takarda mara rubutu sai ka share sannan sai ka biyo shi da ruwa. Kenan ba'a tsarki da yawu (miyau).

   Kada asha'afa, idan aka yi la'akari da abinda ya fita da kuma abinda ya fantsamo maka, za'a raba tsarki zuwa gida biyu:
(1) Tsarkin Hadasi: Shine tsarkin abinda ya fita daga dayan mafita guda biyu, kamar fitsari, maziyyi…'.
(2) Tsarkin Kabasi: Shine tsarkake abinda ya taba jiki ko tufafi ko kuma wuri, kuma ko wannensu baya yiwuwa said a ruwa mai tsarki mai tsarkakewa.

   Amma idan aka yi la'akari da girma ko rashin girma za'a kasa tsarki zuwa gida biyu shima:
(1) Babba wanda ake kira Hadasul Akbar: Ankira shi babbane domin ba'a tsarkaka daga gareshi sai an yi wanka, kamar fitar maniyyi, ko saduwa, ko daukewar jinin al'ada ko na biki.
(2) Karami wanda ake kira Hadasul Asghar: wanda yake tsarki ko alwala ta wadatar, kamar fitsari ko maziyyi.
Yadda ake yi: Da farko mutum ya wanke hannunsa na hagu kafin ya sa a wurin da zai wanke, domin hannun sa ya koshi da ruwa, sannan sai ya wanke wurin fitsari. Daga nan kuma sai ya fara wanke wurin bayan gida musamman idan ya kaatse, ana bukatar mutum ya wanke al'aurar sa baki dayanta musamman idan maziyyi ne ya fita.

Ladubban Zagawa (Fitsari Ko Bayangida): Akwai tsari na ladubba da musulunci yake da su a lokacin da mutum ya ke niyyar kewayawa, wannan zai nuna maka cewa musulunci ya karade komai:
(1) Anbaton Allah: Ana bukatar kafin ka shiga ka ambaci Allah domin ba'a anbaton Allah a makewayi, kuma ka nemi Allah ya tsareka da sharrin aljanu, domin irin wadannan wurare matattarace ta su, yace:
بِسْمِ اَللهِ، اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ اَلْخُبُثِ وَالْخَبَائِثِ
Ma'ana: Da sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina neman tsarinka (Ka tsareni) daga aljanu maza da kuma aljanu mata.
Idan kuma zaka fito sai kace:
غُفْرَانَكَ، اَلْحَمْدُ للهِ اَلَّذِي أَذْهَبَ عَنِّي اَلأَذَى وَعَافَانِي
  Ma'ana: (Ina neman) gafarar Ka, Dukkan godiya ta tabbata ga Allah wanda ya rabani da wannan kazantar kuma ya bani lafiya.
    Ka sani ba'a shiga bayi da dukkan wani da yake dauke da sunan  Allah, kamar zobe, ko carbi…'. Hakanan kuma ba'a katse bayangida da dukkan wani abu da yake da sunan Allah.
(2) Fara Gabatar Da Kafar Hagu Lokacin Shiga, kafar dama kuma lokacin fita.
(3) Ayi A Tsugunne: kada mutum ya yi fitsari ko bayan gida a tsaye, sai dai idan wurin kangone ko yana tsoron fitarin ya fallatso masa, sannan ba wanda zai ganshi ya samu ya yi a tsaye.
(4) Tabbatuwa A Cikin Sutura: ana bukatar kada mutum ya yaye al'aurar sa tun yana tsaye, sai ya tsugunna ya yi dab da kasa sai ya daga suturarsa, domin ba'a yarda wani ya ga al'aurar wani ba in ba miji da mataba, amma halin ko unkula da wasu suke nunawa na bayyanar da al'aurarsu ga kowa muddin jinsi gudane wannan baidaceba, sai ka ji wana yace 'Ai duka mazane, abinda kake da shi ina dashi', wannan ba koyarwar musulunci bace, haka namma mata, wannan zai kaika ka ga maza sun tube suna wanka lokaci guda a dakin wanka guda, haka namma mata, wai sun dauka abinda yake haram shine namiji ya ga al'aurar mace ko mace ta ga al'aurar namiji, kai wani lokaci kana tafiya a cikin mota sai kai arba da wani gabjejen kato yana wanka a rafi, wani kuma a gefan titi ya kafe mashin ko ya je kayan tallansa, duk wadannan bakewawan halaye bane, mutum musulmi ya nisance su.
(5) Yafi Bada Karfi A Kafarsa Ta Hagu: Kenan abinda akafi so shine mutum ya fi bayar da karfinsa a kan kafarsa ta hagu.
(6) Ya Bude Tsakanin Cinyoyinsa: kenan kada ya matse, ballantana ya sa matsattsiyar tufa wacce idan yana fitsari na gaban ne kawai zai fita, sannan idan ya mayar cikin wando sauran ya gangaro, Allah ya sawwake.
(7) Ya Nisanci Inda Ruwa Yake: musulunci bai yadda mutun ya yi fitsari ko bayan gida a inda ruwa yakeba ko kusa dashi, dan wannan zai haifar da cututtuka.
(8) Ya Rufe Kansa: Ana son wanda yake bayangida ya rufe kansa a daidai lokacin da yake yi, domin koda wani ya yi kuskuren ganinsa to shi bai ganshiba, abin zai zo da sauki, amma ba zaka ji dadiba kana bayan gida ka hada ido da wani, wanda zai iya zama dalibinka ne ko suruki ko da..,'.
(8) Kada Ayi Magana: anhana mutum yana bayan gida yana Magana, sai dai idan akwai dalili mai kwari, kamar ka ga makaho ya nufi rijiya ko karamin yaro…'.
(9) Kada A Tari Iska: an hana idan mutum zai yi bayan gida a dawa (daji) an hana ya tari iska, domin zai bsowa jama'a warin bayan gidansa, kenan sai ya yi nesa, ya kuma duba ina iska take kadawa.
(10) Kaucewa Rami: Ba'a yarda idan za ka yi fitsari ko bayangida ka yi aramiba saidai idan kai ka haka, domin bakasan mekecikin ramin ba, takan yiwu akwai mugun abu.
(11) Kaucewa Wuraran Tsinuwa: Wadannan wurare sune wuraran da mutane suke yawan tsinema dukkan wanda ya yi musu bayangida a wurin, wadannan wurare sune:
(a) Inda mutane suke zama su huta, jikin bangone ko karkashin bishi komadai inane.
(b) Kan hanya: Akwai rashin mutunci mutum ya zo kan hanya ya gicciya bayangida, wannan dabi'a musulunci bai yarda da ita ba.
( c ) Mashayarruwa: Hakanan baya cikin karantarwar musulunci mutum ya zo inda al'umma suke diban ruwa rafine ko wani gulbi ko gindin fanfo komadai inane ya aikata wannan ta'asa. Wadannan wurare uku musulunci ya hana a aikata wannan danyan aiki a wurin, domin mutum yana jawa kansa tsinuwa, Allah ya tsaremu.
(12) Nesa Da Jama'a: ana bukatar dukkan wanda zai yi bayan gida ya yi nesa da jama'a ta yadda ba za su ganshiba kuma ba za su ji nishin shiba, ba zai yi kyauba ace kana bayan gida mutane suna ganinka ko suna jin nshinka, ko da a bayan bishiya ko ganyan kargo sai ka boye, amma sau da yawa mutane suna tafiya a mota da motar ta tsaya sai ka ga kowa ya tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a barshiba.
(13) Kada Ya Fuskanci Alkibla: wato inda mutum yake kallo lokacin sallah, kuma kada ya juya mata baya, wannan idan a dajine, amma idan a gidane to da sauki.

Abubuwan Da Rashin Tsarki Yake Hanawa: kamar yadda bayani ya gabata cewar tsarki wajibine, to mu sani idan mutum bashi da tsarki bai halatta a gareshi wadannan abubuwanba:
(1) Sallah: Bai halatta ga wanda bashi da tsarki ba ya yi sallah nafila ko farillah.
(2)  Dawafi: Kewayan Ka'aba kenan a birnin makkah, saboda haka idan mutum yana dawafi sai ya yi tusa to dawafisa ya warware sai ya sake alwala domin ita tusa ba'a yi mata tsarki.
(3) Sujjadar Tilawa: Wato sujjadar da mutum zai yi ida yana karatun Alkur'ani mai girma sai ya kai wadansu gurare, domin ba shi da tsarki, dudda malamai sun kawa juna sani akai.
(4) Kabli Ko Ba'adi: Bai halatta ga wanda bashi da tsarki ba ya yi kabli ko ba'adiba har sai ya yi tsarki, idan akce kabli ana nufin sujjadar da mutum zai yi kafin ya yi sallama, amma idan ake ba'adi to wacce zai yi bayan sallama. Idan jiya ba'adi ta kamaka sai kuma ka manta baka yi to ya halatta ka yi ta a yanzu idan kana da tsarki.
(5) Daukar Alkur'ani Mai Tsarki: idan mutum bashi da tsarki to sai yi tsarki kafin ya taba wannan littafi mai tsarki.

Kammalawa: ina fatan wadannan takaitattun bayanai sun warkar da abinda ake bukata, kuma sun nuna lallai addinin musulunci gamamman addinine da ya shafi komai ya kuma yi bayani akan komai, domin idan yakai bayan gida sai an nunawa mutum yadda ya kamata ya yi to ashe wannan ba karamin gata musulunci ya yi mana, muna godiya ga Allah.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna, Jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.co

Wednesday, September 11, 2013

006- HUKUNCE-HUKUNCEN ALWALA


Gabatarwa: Alwala ibadace mai zaman kanta wacce Allah madaukakin sarki ya sahar'antata kafin gabatar da wadansu ibadu musammamma sallah, mutum yana samun cikakken ladan alwala idan ya yi ta cikakkiya, Allah madaukakin sarki ya saukar da hukunce-hukuncen alwala a cikin littafinsa mai girma alkur'ani:
'' Ya ku dukkanin wadanda suka yi imani, idan kuka ta shi za ku yi sallah to ku wanke fuskokinku da hannayanku zuwa gwiwar hannu ku kuma shafa kawunanku da kafafanku zuwa idan sawu (idan kafa)…'' Suratu Ma'ida, aya ta:6.

Tabbas wannan aya ta ti bayanin wajibcin alwala lokacin da za'a yi sallah, kuma ta bayyana gabban da ya zama wajibi anwanke ko kuma anshafa, sannan kuma ayar ta iya kance ko wanne mahalli, sannan kuma Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya bayyana siffar yadda alwalar take da maganarsa da kuma aikinsa bayanin da yake gamsasshan bayani.

Ka sani lalle ita wannan alwala tanada falala da kuma sharudda da kuma farillai sannan tana da sunnoni da kuma mustahabbai, sharuddannan da farillai tabbas a tabbata ansame alokacin gabatar da alwala iya gwargwado domin da sune alwala zata zama karbabbiya, amma su sunnoni da mustahabbai suna cika alwalarne ta inda matsayinsu bai kai matsayin sharuddai da farillaiba.

Falalar Alwala: Dudda cewa alwala wajibice wannan kadai ya isheta samun matsayi a musulunci domin dukkan abinda akace farillane to wannan matsayi ne me zaman kansa, bayan hadisi na 62 a cikin Muwadda'u Malik yana cewa: '' An karbo daga Abdullahi As-Sunaabihi, lalle ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:
  ''Idan bawa mumini ya yi alwala sai ya yi kuskurar baki dukkanin laifukan dake bakin sun fice, idan kuma ya face laifukan (Day a shaka) sun fice, to idan kuma ya wanke fuskarsa laifukan da ke fuskar ta sa sun fice, har wadanda ke karkashi girar shi, idan ya wanke hannayansa laifukan dake hannayansa sun fice, har wadanda ke karkashi faratansa (jam'in farce), to idan kuma ya shafi kanshi laifukan dake kan nashi sun fice har wadandake kunnuwansa, to idan kuma ya wanke kafafuwansa duk laifukan dake kafafuwan nasa sun fice, har wadanda ke karkashi farcen kafafun nashi. Sannan kuma tafiyar da ya yi zuwa masallaci ya zama wani karine da yake da shi''.
    Lalle wannan bakamar falala bace da alwala take da shi, domin mai alwala zai kasance yana kammala alwala zunubanshi suna digewa a kasa, amma gudu ba hanzariba wannan ladan zai tabbata ne ga wanda ya yi alwala da shara'a ta tabbatar da ita ba wacce ya tsinta a kan titi ba.

Sharuddan Alwala: Sharuddan alwala sune abubuwan da ake so mai alwala ya cika su kafin ya fara alwalar, sune kamar haka:
(1) Musulunci, kenan idan wanda ba musulmiba ya yi alwala bata yi ba.
(2) Hankali, idan mahaukaci ya yi alwala itama bata yi ba.
(3) Wayau, idan dan karamin yaro mara dabara ya yi bata yi ba.
(4) Ruwan ya zama mai tsarki, idan ya zama ruwane mara tsarki to alwalar bata yi, bayanai sun gabata akan hukunce-hukuncen ruwa.
 (5) Ruwan ya zama na halas, idan ruwane da mutum ya sata ko ya same shi bata shar'an tacciyar hanyaba to alwalar bata yi ba.
 (6) Ya kasance mai tsarki, idan mai alwala ya kasance ya yi fitsari ko bayan gida misali wato ya kasance mara tsarki kafin alwala to ko ya yi alwalar bata yi ba.
(7) Gusar da duk abinda zai hana ruwa shiga, kenan idan mutum ya kasance yaba sanye da wani abunda zai hana ruwa ya kai ga fatar jiki to dolene ya cire shi, kamar tabo (laka)…'.

Farillan Alwala:
(1) Niyyah: Domin a banbance  wanda ya sa ruwa donin sanyaya jiki, ko domin gusar da datti, duk wannan ba niyyace ta alwalaba.
(2) Wanke Fuska: ita kuma fuska ta bangaren tsawo tana farawane daga matsirar gashin kai (banda sanko) zuwa karshen mukamiki, amma ta fuskar fadi tana farawane daga kunnan dama zuwa kunnan hagu, wannan shine abinda yake amsa fuska, kenan dole mai alwala ya tabbatar ko ina ya sami ruwa kamar kasan haba, gefan ido da gefan kunne da matsa-matsin karan hanci, ayi hattara sosai domin wasu alwalarsu kamar alwalar yarace.
(3) Wanke Hannaye Zuwa Gwiwar Hannu. Mai alwala mace ko namiji ya tabbata ya wanke hannayansa tun daga saman yatsunsa (farce-akaifa) harzuwa gwiwar hannu ya tabbata gwiwar ta shiga inda ya wanke, anamma akwai manya masu alwalar yara.
(4) Shafar Kai: Ka tabbata ka hada yatsunka sannan kuma ka fara shafar daga goshi (daidai matsirar gashi) sannan ka shafa zuwa keya.
(5) Wanke Kafa: Hakanan mai alwala ya tabbata ya wanke kafarsa harzuwa idon sawu, wato wadannan kasusuwan guba biyu dake gefan kafafuwa sun shiga cikin inda aka wanke.
(6) Cudanyawa: Mai alwala ya tabbata ya cudanya duk inda ya wanke ya dirza ruwa ya shiga ko ina.
(7) Yinsu Baidaya: Abinda ake nufi shine alokacin da ka fara alwala to ka dakatar da komai sai ka kammala, amma kana alwala kana kuma wata sabga daban wannan bai yi ba.
   Mai alwala ya tabbata ya gabatar da wadannan ayyuka a lokacin da yake alwala ta yadda idan aka rasa daya daga cikin su to alwalarsa ta shiga hadari.
Sinnonin Alwala:
(1) Wanke Hannaye Kafin A Tsoma Su A Ruwa. Ta yadda mai alwala zai karkato butar alwala domin ya wanke hannayansa zuwa Ku'u wato wuyan hannu.
(2) Kuskurar Baki: mai alwala ya tabbata ya sanya ruwa a bakinsa sannan kuma ya kada ruwan a baki, wannan shi ake kira da kuskurar baki.
(3) Shaka Ruwa: Shine mai alwala ya shaki ruwa ruwan ya shiga hancin sa sosai, sai dai kawai idan yana azumine sai yayi kadan. Amma yadda mutane suke shafar hancinsu wai da sunan shaka ruwa wannan baiba.
(4) Facewa: mai alwala zai shaki ruwanne da hannun dama sai ya sa hannun haku akan karan hancinsa, sannan sai ya fyato ruwan da ya shaka.
(5) Shafar Kunne; Mai alwala ya tabbata ya shafi cikin kunnensa da wajan kunnan, zaka/ki sanya yatsanka 'yar-manuniya a cikin kunnan sannan ka babban yatsa a wajan kunnan sannan sai ka shafa, Dirkashi!.
(6) Sake Taba Ruwa: Alokacin da zaka shafi kunne shin zaka shafi kunnanne da ragowar danshin hannuka da ka yi shafar kai da shi? Ko ko zaka sake taba ruwa na musamman domin shafar kunne, malamai sun karawa juna san, ko wanne ka yi ya yi daidai.
(7) Dawo Da Shafar Kai: Ka tsaya ka fahimta, ita shafar kai farillace, amma dawo da shafar kai sunnace daga cikin sonnonin alwala.
(8) Jeranto Farillai: Ta yadda zaka kawosu daya-bayan-daka kamar yadda aka lissafosu, kada ka dauki na uku ya zama shine na farko sannan ka biyo shi dana biyar, misali…'.
Wadannan matsayisu bai kai matsayin farillaiba, amma suna cikin manyan abubuwan da suke cika alwala.
Mustahabban Alwala:
Wannan shi ke biye da mataki na sunnoni, kenan sunnoni sun fi mustahabbai karfi, wadanda suke dukansu biyun farillai na gabansu, babu daya daga cikin sunnoni ko mustahabbai da mutum zai yi sakaci da su, domin kowannanmu so yake ya yi ibada cikakkiya kammalalliya, to ko tunda hakane bai kamata yace ai wannan mustahabbine ya daukeshi kamar wani kankanin abu.
   Su mustahabban alwala suna da yawa, amma yanzu ga kadan daga cikinsu:
(1) Anbaton Allah yace ''Bismillah'', adaidai loakcin da zaka fara alwala, amma idan mutum ya manta saida yake tsakiyar alwalar ya tuna bakomai sai ya yi a lokacin.
(2) Addu'a bayan kammala alwala, itace kuma kamar haka:
أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، اَللَّهُمَّ اَجْعَلْنِي مِنَ اَلتَّوَّابِينَ، وَاجْعَلْنِي مِنَ اَلْمُتَطَهِّرِينَ.
Ma'ana: ''Ina shaidawa da babu abinbauta da cancanta sai Allah, kuma shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lalle (Annabi) Muhammad bawan Allah ne kuma manzansa ne, Ya Allah ! ka sanya ni daga cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni daga masu neman tsarkaka.''
(3) Karanta Ruwa: Bawai ana nufin mai alwala ya shasshafa gabbansa bane, a'a, ana bukatar ya yi anfani da ruwa amma kada ya malalar da shi, domin yana daga cikin tsarin musulunci tattali da tsimi da tanadi.
(4) Gabatar Da Asuwaki: Bayani kuma dama ya gabata akan asuwaki, ana yi da danye ko da busasshe, idan bai samuba sai ayi da yatsa, amma mu sani asuwaki daban kuskurar baki ma daban. Hakanan kuma ko da mutum lokacin sallah ya yi kuma amma yana da alwala to abinda ake so shine ya yi asuwaki.
(5) Wuri Mai Tsarki: An so inda zaka yi alwala ya zama wurine mai tsarki.
(6) Dama Kafin Hagu: abin nufi shine ka fara wanke hannun dama kafin hannun hagu, hakanan ka fara wanke kafar hagu kafin ta dama.
(7) Jerantawa: Wato jeranta kowacce sunnah tare da 'yar-uwarta, kamar fara gabatar da kuskurar baki kafin shaka ruwa.
(8) Wankewa Sau Uku: Ma'ana wanke wuraran da ake wankewa sau uku, mu sani wankewa sau uku zai zama mustahabbine idain wankewar farko ta game ko ina, amma idan ta farko bata gamaba to ta biyu tananan amatsayin wajibi, haka namma idan ta biyun idan bat agama ba to ta uku tana nan a matsayin wajibi. Ya zama wajibi mai alwala mace ko namiji ya kula sosai ya cuccuda inda ya kamata ya sa ruwa ba tare da barnaba. Amma shi kais au daya ake shafarsa, ba'a shafar kai sau uku. Sannan kuma mutum ya tabbata a wadannan wankewa da akace ya yi sau uku bai kara akan hakan ba, ya yi iya kokarinsa ya ga guda ukun sun kammala.
   Wadannan kadan kenan daga cikin mustahabban alwala, kuma wadannan bayanai sun mata kamar yadda suka shafi maza, sai dai mata su sani gashin kansu da sangalin hannuwansu duka al'aurane, saboda haka bai halatta su bayyanar da su ga maza, ken an idan zaki yi alwala sai ki sami wuri ki kawwame kanki.
   Wadannan bayanai da suka gabata zasu haskaka mana yadda alwala take, amma hanya mafi sauki shi ne a yi maka ita a aikace ka gani domin haka sahabban ma'aikin Allah suka yi, an tambayi Usman dan Affan dan gane da alwala sai yasa aka kawo mishi butar alawala ya yi musu ita a aikace, yace kuma irinta ma'aikin Allah ce.
   Anan nake kira ga dukkanin limamai na juma'a dana sauran masallatai da kuma malamai a jami'oi da kwalejin ilimi da kuma malamai a sakandare da firamare da malaman islamiyyu da malamai masu karantarwa a masallatai da masu wa'azi da sauran wadanda abin ya shafa da su karantar da mutane ita wannan alwalar a aikace kowa ya gani ya kuma yi tambaya, kada ka ga kamar kowa ya gane da zarar ka yi ta a aikace zaka ga abin mamaki, ni na taba gwada hakan, ita ibada sai an koyawa mutum ba wai daka kawai shikenan ya iyaba, ko kuma ai shi iyaye da kakanni duk musulmai ne sabo da haka ba sai ya koyaba, duk wannan maganace ta wanda yake nesa da makaranta, kai da ganin alwalar wani kasan bai je makaranta ba, Allah ya karba mana ibadummu.
   Kammalawa: Lalle wadannan bayanai sun kara tabbatar mana ashe alwa abace da sai an tashi tuku domin a koyeta tana da falala da kuma sharudda sannan ga farillai da sunnoni da kuma mustahabbai, lalle ka nana bukatar malamai daga kowanne bangare su tashi tsaye su karantar da al'umma wannan ibada a aikace, domin a gudu tare a tsira tare.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna, Jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com