Sunday, March 24, 2013

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Juya Baya A Lokacin Yaki)6/7#

Ja-Da-Baya Lokacin Gumurzu: A yanzu za mu yi bayani akan abu na shida cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu shine Juya Baya A Lokacin Yaki.
     Jihadi wani al'amarine da musulunci ya shar'antashi ya kuma tsarashi kamar yadda ya tsara rayuwar bil'adama ta duniya da kuma ta lahira. Ayoyi na Alkur'ani mai girma da ingantattun Hadisai Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- duk sun zayyana yadda jihadi yake hanan kuma malamai sun zayyana yadda yaki yake domin habbaka addinin Allah, kuma kamar sauran al'amura sai mutum ya yi kamar yadda aka shar'anta sannan zai sami ladanshi. Yaki domin habbaka addinin Allah shine kololuwar musulunci, kamar yadda Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya bayyana a Hadisin Mu'az.
    Kuma kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya bayyana a cikin Alkur'ani mai girma cewa: ''An wajabta muku yaki alhalin bakwasansa'' Bakara, ayata: 216.
   A wannan dogon hadisi da muke bayani a kanshi, Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa juyawa da nufin guduwa yana daga cikin abubuwa masu halakarwa domin kamar wannan juyawar da mayaki ya yi yana nufin a murkushe musulunci kenan.
   Amma juyawar da zata laifi sai idan yawan musulmai daidaine dana kafirai, ko kuma su wadanda ba musulmanba sun ninka musulmai ribinyi biyu, amma idan yawan wadanda ba musulmai ya ninka yawan musulmai sama da sau biyu to awannan lokaci babu laifi idan musulmi ya juya da baya kamar yadda aya Suratul Anfal ta yi nuni:
   ''Ayanzu Allah Ya sawwaka muku, kuma ya bayyanar da cewa a cikinku akwai masu rauni, idan an sami mutane dari daga cikinku masu hakuri zasu rinjayi mutane dari biyu (daga cikinsu), in kuma an sami mutane dubu daga cikinku zasu rinjayi dubu biyu (daga cikinsu) da izinin Allah, Allah Yana tare da masu hakuri. Ayata: 66.
      Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa ''Kada ku yi fatan haduwa da abokan gaba, ku roki Allah zaman lafiya, idan kuma har kuka hadu da su to ku tabbata, ku sani aljannah tana karkashin inuwar takobi''.
  Ya Allah muna rokonka ka zaunar da mu lafiya, kuma ka dawowa da musulunci izzarsa da kimarsa da darajassa.
Kammalawa: wannan ya nuna yadda musulunci bai yarda da juyawa da bayaba a lokacin da aka yi futo-na-fito, kuma mu sani annan ba wai ana bayanine akan abinda ya shafi hukunce-hukuncen yaki bane (Jihadi) wannan wurinsa daban malamai sun fayyace shi da yadda ya karkasu da matsayin ko wanne kaso daga cikinsu, amma anan an yi bayanine akan abinda ya shafi tserewane afagen fama. Ya Allah ka tsaremu ka tsare mana rayukammu da imanimmu. Amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna, Jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

No comments:

Post a Comment