Tuesday, September 10, 2013

005- TSAFTA CIKON ADDINI


Tare Da:
Aliyu Muhammad Sadisu, Minna, Jahar  Neja - Nijeriya.
(+234)08064022965, e-mail:aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Duk da bayanan da suka gabata na zayyana wadansu abubuwa da akace masu tsarkine wannan ba yana nufin mutum ya barsu a jikinsa ko tufafi ko kuma wurin zamaba, a'a, abin nufi anan ko da ka yi sallah sai ka ga majina a tufafinka ba abinda ya taba sallarka, ko ka ga yawu, amma wannan ba yana nufin kabar majina ko yawu a jikinba, tafta a musulunci ba karamin matsayi take da shiba, anan za'a lissafo wadansu abubuwa kadan daga cikin abinda addinin musulunci yace a tabbatar da tsaftarsu:

(1) Tsaftace Baki: Akan wannan musulunci ya shar'anta asuwaki tun sama da shekaru dubu da dari hudu baya, asuwaki yana tsarkake hakora da baki da dukkan wani datti da kazanta da ta makale a hakori ko dasashi…'' wannan kuma ya shafi mace ya shafi namiji, bai kamata mutum yana magana mutane suna kauda kai saboda warin bakinsa, Allah ya sawwake. Ka ka manta hakoranta da bakin da magogaranka hanyoyine na fitar zancan Allah wato Alkur'ani, saboda haka ka tabbatar da cewa ako da yaushe bakinka a tsaftace yake. Ma'aikin –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa: ''Asuwaki abune da yake tsarkake baki, kuma yake sa Ubangiji ya yarda da mutum''. Kuma yace ''Dabadin kada in tsanantawa al'umma ta ba da na umarcesu da yin asuwaki a kowacce sallah''. Kenan sau biyar a kalla a kowacce rana, Ma'aikin Allah ya kasance ko cikin dare ya tashi sai ya yi asuwaki. Adunga fabatar da asuwaki a kowanne lokaci domin samun lada da kuma tsaftace baki musamman lokacin sallah ta farilla ko nafi, maza ko mata, yara kuma a koya musu su saba tun kafin su girma.

(2) Aske Gashi Mara: Shine gashin-gaba (wanda yake fitowa gefan al'aura), addinin musulunci ya karantar da aske wannan gashi domin samun cikakkiyar tsafta mace ko namiji, bai kamata mutum ya bar wannan gashi a tare da shi ba har ya jima, akalla ace acikin dukkan kwanaki arba'in mutum yana askeshi, akwai mai da ake sayarwa wanda mutum zai iya amfani da shi, koma almakashi ko ma duna abinda zaka yi amfani da shi wanda ba zai cutar da kaiba.
Wani sako da wannan gashi yake isarwa kuma shine tabbatar da balagar wanda wannan gashi ya bayyana a gareshi/ta, wanda hakan ke nuna cewa hukunce-hukuncen shari'a sun hau kanshi/ta ko bai yi mafarkiba.

(3) Kaciya: Itace cire fatarnan data rufe Hashafa, wannan kaciya tana kasancewane tun yaro yana karami, domin yafi saurin warkewa, kuma zai tashi a siffa mafi kamala. Daga cikin hikimomin ita kaciya: Tsarkake al'aura daga najasar da zata iya toshi al'aura dadai sauran fa'idoji masu tarin yawa.

(4) Rage Gashin-Baki: A tsari na addinin musulunci ba'a barin gashi-baki da yawa kamar wani muzuru, ba kuma a shareshi baki daya rageshi ake yi matuka, sannan kuma a bar gemu, wanda shi barin gemu babbar alamace ta banbancewa tsakanin mace da namiji, Kash!! Amma haka zaka ga wani kullum sai ya askeshi ya kankare wai shi dole yarone, ya dauka manyane kadai ke barin gemu.

(5) Yanke Akaifa (Farce): Wannan yana daga cikin da Ma'aikin Allah ya fadakar da wannan al'umma, a lokacin da ka/ki yanke farce ka gusar da dukkan wata kazanta ta zata iya samun wurin zama, sannan kuma baka barshi ya yi zaro-zaro ba kamar na dabbobi, abin mamaki haka zaka ga samari da wasu mata su sabawa wannan karantarwa ta ma'aikin Allah wai suna ganin haka shine wayewa, Allah ya sawwake.

(6) Cire Gashin Hammata: Abinda ake fi so shine 'tsigewa' duddacewa akwai zafi sai dai hakan zai baiwa iska damar shiga wadannan kananan kofofi, amma ko da mutum ya askene ba komai. Baya cikin tsari na addinin musulunci mutum ya bar gashin hammatarsa buzubuzu macece ko namiji, tsari na musulunci shine askewa.
   Wadannan bayanai da suka gabata na abubuwa shida, Ma'aikin Allah ya karantar da wannan al'umma tsaftace su da gyarasu, mun kawo Hadisai akan na farko wanda yake shine asuwaki, akan sauran biyar dinne Ma'aikin Allah ya ce:
''Abubuwa biyar suna cikin tsafta a musulunci: Aske gashin mara da Kaciya da Rage gashin-baki da Tshige gashin hammata da kuma Yanke farce'' Bukhari 5889 Muslim 257.

   Wannan ya tabbatar mana da yadda musulunci yake kula da tsafta, domin dubi yadda aka bayyana tsaftar gangan jiki, to haka yake idan mutum ya zo wanka sai ya tabbatar ya wanke wadannan wurare ya kuma kurza domin kaucewa makalalliyar kazanta.

  Kuma addinin musulunci ya kwadaitar da sanya turare domin kasancewa cikin yana yi mai dadi, ya kuma hana mutumin da yaci tafarnuwa ko albasa da kada ya shiga cikin mutane, domin zai cutar da su da wannan warin na tafarnuwa ko albasa ballantana taba (sigari).

  Bayan wannan dole a kula da tsaftar gida kamar dakin kwana falo dakin girki makewayi (bandaki) tsakar-gida a tabbatar da antsaftace su bai kamata wurin da mutum yake kwana ya kasance ba tsafta babu yana yi na kamshi mai dadi, ko kuma ka ga tsakar gida kaca-kaca ba shara babu tattara kayayyakin aiki wuri guga, ballantaba bayi (makewayi) akwai magunguna da ake sanyawa a bayi bayan anwanke shi domin kara tsaftaceshi koma kananzir aka zuba zai rage kaifin bashin da bandaki yake da shi kuma zai rage kanan kwari sannan ma ga kafur da idan aka sa zai tai maka.

Kammalawa: Daga wadannan bayanan da suka gabata ya bayyana a fili cewar addinin musulunci addinine na tsafta ba addinine na kazantaba, a tsaftace jiki da tufafi da wurin zama/sana'a, domin yawan sutura daban tsafta kuma daba, zaka ga wani ba yawan suturu yake da su ba, amma akwai wanki da guga da sa turare sai ka ganshi a kullun abin sha'awa. Allah ya yi mana jagora.

No comments:

Post a Comment