Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan
jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki
daya. Bayan haka:
A
wannan lokacin kuma za mu yi bayani ne akan abinda ya shafi hukunce hukuncen
azumi, kama daga ta’arifinsa da kuma falalarsa da kuma nau’ukansa, da sauran
bayanai da za su zo akan abinda ya shafi hukunce hukuncensa, da fatan Allah ya
yi mana jagora ya kuma datar da mu ya anfanar da mu.
AZUMI.
Idan aka ce azumi a hausa to shi ake cewa
(SWAUMU/SWIYAMU) da larabci, a larabci idan aka ce ((Swam)) To ana nufin
kamewa ne, amma a shar’ance shi ne:
هو الإمساك عن شهوتي البطن والفرج يوما كاملا بنية التقرب إلى الله تعالى
قبل الفجر أو معه في غير زمن الحيض والنفاس وأيام الأعياد.
Ma’ana: Shi ne kamewa daga barin sha’awar ciki da
kuma farji cikakken yini da niyyar neman kusanci ga Allah, wacce niyyar za’a yi
ta ne kafin hudowar alfijr ko daidai lokacin da alfijirdin yake fitowa, ba a
lokacin jinin al’adaba ba kuma na biki ba, kuma ba lokacin bukukuwan sallah ba.
SHARHI.
A wannan ta’arifi na azumi yana kunshe da
asalin abinda ake bukata daga mai azumi, ta yadda da zarar an rasa daya daga
ciki to wannan abin bai zama shar’an taccen azumi, wadannan abubuwa sune kamar
haka:
(1) Kamewa daga barin sha’awar ciki.
Kenan wanda bai bar sha’awar cikinsa ba, wacce take ko wannan sha’awar ita ce
abinci ko abin sha, ko kuma dukkan wani abu da zai zatsaya matsayin abinci ko
abin sha to wannan ba shi da azumi. Ba zai taba yiwu wa ba mutum ya ce yana
azumi sannan kuma yana cin abinci ko yana shan abin sha ba.
(2) Kamewa daga barin sha’awar farji.
Sha’awar farji kuwa ita ce ko dai saduwa wato jima’i, ko kuma fitar da maniyyi
ko maziyyi, wadannan abubuwa uku su ne sha’awar farji, kuma duk mai azumin da
ya yi daya daga cikin wadannan abubuwa uku wato ya yi jima’i ko ya fitar da
maniyyi ko maziyyi mace ko na miji to ba shi da azumi, domin kowanne daya daga
cikin su sha’awace ta farji. Kuma Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce – a lokacin yana bayyana falalar azumi – ya ce Allah
madaukakin sarki ya ce:
((الصوم لي، وأنا
أجزي به، يدع طعامه وشربه وشهوته من أجلي)). ((رواه البخاري)).
Ma’ana: Azumi nawa ne, kuma ni zan bada sakamakonsa,
(mai azumi) yana barin abin cin sa da abin shansa da sha’awarsa saboda ni”.
Bukhari ya ruwaito. Domin duk wanda ya fitar da maniyyi ko maziyyi to lalle
wannan bai bar sha’awarsa ba.
(3). Cikakken Yini. Abinda ake
nufi da cikakken yini shi ne tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana.
Idan aka sami gibi akan haka to azumi bai yi ba, domin Allah madaukakin sarki
cewa ya yi:
((وكلوا واشربوا حتى
يتبين لكم الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر، ثم أتموا الصيام إلى اليل)).
البقرة
Ma’ana: Kuma ku ci ku sha, har sai silin farin
zare ya bayyana daga silin bakin zare na alfijr, sannan kuma ku cika azuminku
zuwa dare.” Bakarah.
Wannan ya nuna inda jinin al’ada zai zo
mata minti kadan kafin shan ruwa to ba tad a azumin wannan ranar saboda ba ta a
zumci yinin ba ki daya ba. Haka kuma inda jinin al’adar zai dauke mata minti
kadan bayan fitowar alfijir to haka shi ma yake ba ta a zumin wannan yinin,
dalili kuwa shi ne ba ta azumci yinin baki yaba, kuma abinda Allah ya fada shi
ne azumtar yinin baki yada.
(4) Da niyyar neman kusanci ga Allah,
wacce niyyar za’a yi ta ne kafin hudowar alfijr ko daidai lokacin da alfijirdin
yake fitowa. A wannan gabar akwai manyan abubuwa guda biyu da ya kamata a
yi la’akari da su:
Abu na farko; Niyyar neman kusan ci ga Allah, kenan
inda mutum zai ki ci ya ki sha saboda bai sami sarari ba ko sabo da likita ya
hana shi ya ci ko ya sha…. Duk wannan ba ya sa ya azumi, shi azumi lalle ne sai
idan Allah aka nufata da shi, sannan ne yake amsa sunan azumi shar’antacce.
Abu na biyu: Lokacin da za’a niyyar, lalle dukkan
wanda zai ta shi da azumi to ya wajaba akan shi ya kudurce niyyar yin azumin
azuciyar shi a cikin daren kafin alfijir ya fito ko kuma daidai lokacin fitowar
alfijir din, domin da hakanne zai zama ya azumci cikakakken yini, kamar yadda
muka yi bayani a ayar da ta gabata ta Suratul Bakarah, sannan kuma ga Hadisi
sayyidah Hafsah – Allah ya kara mata yarda - mai dakin Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi:
((لا صيام لمن لم
يبيته بالليل)). رواه الترمذي. ضعيف في رفعه، صحيح في
وقفه.
Ma’ana: Babu wani azumi ga dukkan wanda bai
kwana da niyyarsa ba da daddare. Tirmi ne ya ruwaito.
(5) Ba a lokacin jinin al’adaba ba
kuma na biki ba, kuma ba lokacin bukukuwan sallah ba. Wannan tsagi na
ta’arifin azumi yana bayani ne a kan lokutan da ba’a azumi a cikin su, kuma ko
an yi azumin bai yi ba sai an sake kuma an sabawa Allah.
Wadannan lokuta sune kamar haka:
- Lokacin Jinin al’ada, idan mace tana
al’ada to ba ta azumi, kuma in ta yi azumin to azumin bai yi ba sai ta sake
shi, sannan kuma ta sabawa Allah da Manzonsa.
- Lokacin Jinin Biki (wato jinin
haihuwa), idan mace tana jinin biki to ba ta azumi, kuma in ta yi azumin to
azumin bai yi ba sai ta sake shi, sannan kuma ta sabawa Allah da Manzonsa.
- Lokutan Bukukuwan Sallah: Ba’a azumi a
ranar karamar sallah ko babbar sallah, duk kuma wanda ya yi azumi a wadannan
ranaku to azumin shi bai yi ba kuma ya sabawa Allah da Manzonsa.
Wannan shi ne ta’arifin azumi, sabanin
haka to ba azumi ba ne, sannan wannan ya shafi ko wane azumi.
Nau’ukan Azumi.
A zumi ya kasu kashi – kashi, akwai
azumin wajibi a kwai kuma wanda ba na wajibi ba.
Azumin Wajibi.
Azumin wajibi shi ne azumin da shari’a ta
dorawa mutum, ta yadda idan ya yi wannan azumin to za’a ba shi lada,idan kuma bai yi ba to zai iya fuskantar
ukuba. Azumi na waji bi su ne kamar haha:
1. Azumin watan Ramadan.
2. Azumin Kaffara.
3. Azumin Alwashi.
Sai kuma azmin da bana wajiba,wanda idan
mutum ya yi yana da lada, idan kuma bai yi ba to ba shi da wannan ladan, kuma
ba shi zunubi. Kamar:
1. Azumin Ranar Arafat.
2. Azumin Tasu’a Da Ashurah.
3. Azumin Litinin Da Alhamis.
4. Azumin Kwana Uku A Kowanne Wata.
5. Azumi Shida A Watan Shawwal (Sittu
Shawwal), Da dai sauransu.
Kammalawa: Adaidai nan za mu dakata, da fatan mun
fahimci menene azumi? Menene yake shiga cikin azumin menene kuma ba ya shiga, a
karo na gaba za mu kawo bayanai akan hukunce hukuncen nau’ukan azumi, ta yadda
za mu fara da Azumin Ramadan.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Niger – Nigeria.
+2348064022965.
e-mail:aliyusadis@gmail.com
Last Shelter: Survival is a management, builder, and survival multiplayer game where you playclick here the role of a commander of a newly built settlement in a zombie ...
ReplyDeleteAllah ya saka wa Malam da alkhairi
ReplyDeleteMasha'allah nima na amfana daga nan Majia Jahar Jigawa
ReplyDelete