Friday, April 25, 2014

0033. RAFKANNUWA A SALLOLIN NAFILA


Gabatarwa: A wannan karon zamu kawo bayanaine akan abinda ya shafi yin kabaliyyah ko ba’adiyyah a salloli na nafila.
Shinfida: Da farko mu sani cewar duk abinda yake farillane a sallah kuma akabarshi to kabaliyyah ko ba’adiyyah bata gyarashi, to haka hukuncin yake a salloli na nafila?. Haka kuma duk abinda mustahabbine a sallah to shima ba’a yi masa kabaliyyah ko ba’adiyyah.
  Dukkan rafkannuwa da aka yi ta a lokacin da ake ramuwar sallah to hukuncinta kamar sallar da ake yenta ne a cikin lokaci, kenan ba banbanci da sallolin ramuwa da kuma wadanda ake yinsu cikin lokaci.
 Yin rafkannuwa a sallar nafila hukuncinsa kamar yin ranfannuwa ne a sallolin farilla in banda mas’aloli guda shida ananne nafila ta banbanta da farilla, sune kuma kamar haka:
(1) Karatun Fatiha: Duk wanda ya manta da karatun fatiha a sallar nafila bai tunaba sai bayan ya yi ruku’u sannan ya tuna to anan zai ci gaba da sallar shine sai bayan ya kammala ya yi kabaliyyah, sabanin sallar farilla da zai cire wannan raka’ar ya kawo wata makwafinta sannan ya yi ba’adiyyah idan ba’a biyun farko bane, ko kabaliyyah idan hakan ya farune a biyun farko na farilla.
(2) Karatun Sura.
(3) Bayyanawa.
(4) Sirrantawa.
 Idan mutum ya manta karatun sura bayan fatiha a cikin sallar nafila, ko kuma ya bayyana a inda ake asurtawa ko ya sirranta a inda ake bayyanawa kuma bai tunaba sai bayan da ya yi ruku’i to zai ci gaba da sallar shine, amma duka a cikin nafila to babu komai akansa, wato ba kabaliyyah kuma ba ba’adiyyah, sabanin inda sallar farilla ce.
(5) Tashi Zuwa Raka’a Ta Uku: Dun wanda ya kammala raka’o’I biyu a sallar na fila sai bai zaunaba ya mike zuwa raka’a ta uku to idan ya tuna kafin ya kulla ruku’u to anan zai dawo ya zauna ya yi tahiya ya yi sallama, sannan kuma ya yi ba’adiyyah, amma har idan ya kulla raka’a ta uku to zai ci gabane da sallar sai ya karat a zama raka’o’I hudu sannan sai ya yi kabaliyyah, sabanin sallar farilla.
(6) Manta Rukuni: Duk wanda ya manta rukuni a sallar nafila kamar ruku’i ko sujjada kuma bai tuna ba har ya yi sallama kuma abin ma ya yi tsawo to anan ba zai sake sallar ba, sabanin sallar farilla, domin inda farillace to da zai sake sallarne har abada.
Kammalawa: Wadannan sune wuraren da aka dan sami banbanci tsakanin salloli na farilla da salloli na nafila akan abinda ya shafi hukunce-hukuncen rafkannuwa, da fatan Allah ya anfanar da mu.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

4 comments:

  1. Allah yasakada alkairi yasa aljannace makoma amen.

    ReplyDelete
  2. Enter your comment...allah datar damu ameen allah yasaka da alkeri.bayan dan allah inda irin wannan group din a whatsAPP dan allah asakani 07017224591.

    ReplyDelete
  3. Assalam Mallam idan mutum yazauna a rakaa na farko cikin sallan tarawihi bayan kammala rakaa na biyu zaiyi qabli kenan?

    ReplyDelete