Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan
jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki
daya. Bayan haka:
A
wannan lokacin kuma za mu yi bayani ne akan abinda ya shafi hukunce hukuncen
azumin watan Ramadan, kama daga falalarsa da sauran bayanai da za su zo
akan abinda ya shafi hukunce hukuncensa, da fatan Allah ya yi mana jagora ya
kuma datar da mu ya kuma anfanar da mu.
FALALAR AZUMIN RAMADAN.
Azumun watan Ramadan azumin ne da yake da
matukar falala, babu wani azumi day a kai shi falala a cikin dukkanin nau’ukan
azumi da ake da su, kadan gada cinkin falalar azumin watan Ramadan:
(1) Rukuni ne daga rukunan addinin
Musulunci, wato addinin Musulunci bai cika said a azumin watan Ramadan, wanda
yake kasancewar azumin Ramadan yana daya daga cikin shika-shikan Musulunci guda
biyar ya isheshi falala, Mala’ika Jibrilu ya tambayi Ma’aikin Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi akan menene Musulunci ? sai Ma’aikin Allah
ya ce:
((الإسلام أن تشهد أن
لا إله إلا الله، وأن محمدا رسول الله، وتقيم الصلاة، وتؤتي الزكاة، وتصوم رمضان،
وتحج البيت إن استطعت إليه سبيلا)). رواه مسلم.
Ma’ana: “Musulunci shi ne ka shaida da babu abin
bautawa da cancanta sai Allah, kuma lalle Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, ka
tsayar da sallah, kuma ka bayar da zakkah, ka yi azumin Ramadan, ka yi aikin
Hajji idan ka sami ikon haka”. Muslim ne ya ruwaito. Sai wannan ya nuna
mana azumin Ramadan daya ne daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar.
(2) Yadda Ma’aikin Allah – tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi – ya fayyace falalar wannan azumin, ya ce: “A
aljanna akwai wata kofa babu mai shigarta sai masu azumi”. Kana Ma’aikin Allah
– tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi – ya ce:
((من صام رمضان إيمانا واحتسابا، غفر له ما تقدم
من ذنبه)). رواه البخاري.
Ma’ana: “Duk wanda ya azumci Ramadan yana mai imani
da kuma neman lada an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubinsa”. Bukhari
ya ruwaito.
Lalle wannan yana nuna mana irin girma da
falala da daraja da azumin watan Ramadan yake da shi, shi ne azumin da yake gaba
da kowanne azumin, kana shi ne azumin da ya fi kowanne azumi falala da daraja. Bannan
abinda ake so shi ne mutum ya yi wannan azumi na Ramadan yana mai imani da Allah
da Manzonsa, yana kuma mai kaunar lada a wurin Allah. Saboda haka koda kana kwadayin
yin azumin nafila amma ana binka wani azumin na Ramadan to lalle ilalla shakka babu
na Ramadan da ake binka shi zaka fara gabatarwa tukunna, domin shi ya fi kowanne
azumi falla, daga nan ink agama ranka wanda ake binka sai ka yin a nafilar da kake
son yi.
AKAN WA AZUMIN RAMADAN YA WAJABA?.
Idan watan Ramadan ya kama akawai wadanda
azumin ya zama wajibi akan sun an take da zarar an ga wata, akwai kuma wadanda azumin
bai haukansu ba anan take, wasu za su rama shi bayan wucewar watan wasu daga cikin
su kuma ba za su rama ba, anan za mu yi bayan kowanne.
Wanda azumin watan Ramadan yake wajaba akansa
shi ne: “Dukkan wanda yake musulmi, baligi, mai hankali, mai lafiya wanda ba
a halin tafiya yake ba”.
Musulmi: Da muka ce dukkan wanda yake musulmi, kenan
an fitar da duk wanda yake ba musulmiba. Azumin Ramadan yana wajaba ne akan musulmi
mace ko namiji banda wanda ba musulmi ba. Idan wanda ba msulmi ba ya yi azumi to
azumin bai yi ba, sannan kuma idan wanda ba musulmi ba ya musulunta to ba zai rama
azumin da ya wuce ba, idan ya musulunta cikin watan Ramadan ne da rana to da zarar
ya musulunta sai ya dakatar da cin abin ci da kuma shan abin sha, amma an so bayan
azumi ya wuce ya rama wannan guda dayan, na ranar da ya musulunta wannan idan ya
musulunta da rana kenan, amma idan ya musulunta bayn shan ruwa ko kafin sahur wannan
kai tsaye za’a tashi da shi ne da azumi.
Baligi: Azumin Ramadan na zama wajibi ne akan wanda ya
balaga, idan yaran da ba su balaga ba suka yi azumi azumin ya yi, kuma ba zai rama
adadin azumin da bai yi ba kafin ya balaga.
Kadan daga alamomin balaga akwai: Fitar maniyyi
daga mace ko namiji, bayyanar gashin mara mace ko namiji, jinin al’ada ga mace kadai,
ciki ga mace kadai…’’. To da zarar daya daga cikin wadannan alamomi sun bayyana
to lalle hukunce hukuncen shari’a sun hau kan mutum ciki kuma har da azumin watan
Ramadan, saboda haka sai iyaye da malamai su kula. Domin irin yadda ake barin balagaggun
yara ba sa azumi suna ci suna shad a rana, wai ai ba su yi aure ba, ko kuma ai yau
suna da aiki a gida ko a gona koma dai a inane wannan ba karamin laifi ba ne.
Mai Hankali: Idan mahaukaci ya yi azumin watan Ramadan
to azumin bai yi ba, domin sharadi ne na mai azumin ya zama mai hankali.
Mai Lafiya: Idan mara lafiya ya yi azumi to azumin ya
yi, idan kuma ya aji ye azumin to sai ya rama adadin kwanakin da ya sha, babu wani
abu akansa bayan haka.
Matafiyi: Shi ma matafiyi iadan ya yi azumin a halintafiyar
ta sa to azumin ya yi, idan kuma ya aji ye hakamma ya yi, sai ya rama adadin kwanakin
da ya ajiye bayan sallah.
Kammalawa: Da wannan takai taccan bayanin, ya bayyana
a garemu yadda falalar azumin watan Ramadan take, da kuma wadanda azumin ya wajaba
akan su, kana da hukunce hukuncen haka.
Aliyu
Muhammad Sadisu,
Minna
Jahar Neja, Nijeriya.
Za'a
iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma
a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a
ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
No comments:
Post a Comment