Wednesday, February 12, 2014

022- WURARAN DA BA'A SALLAH A SU


Gabatarwa: Bayan da bayanai suka gabata akan abinda ya shafi lokutan sallah da kuma yadda ake hada salloli, a yanzu bayanai zasu zo ne akan wuraran da ba'a sallah a su, domin mutum ya kiyayi wurin domin ya tabbatar da sallarsa ta karbu a wurin Allah madaukakin sarki.
Matashiya: Yana daga cikin falalar da Allah madaukakin sarki ya yi wa wannan al'umma ta ma'aikin Allah yadda ya sanya mata kasa ta ko ina ta zama wurin sallah, inbanda wadansu wurare da aka hana yin sallah a su. Mutanan da suka gabacemu basa sallah sai sun je inda aka tanada musu, amma mu ko amota kake ko  a gona ko tsakiyar daji… sai ka gabatar da sallarka, ko anan kusa baka ganin kiristoci sai sun je coci.
   Saboda haka a yanzu muke fatan kawo bayanai na wuraran da aka hana ka yi sallah a su kamar haka:
1.       Shadda (Masai): Shine inda aka ta nada domin yin bayan gida, wannan ya kasance wurine mara tsarki, kuma mun san tsarkin wuri sharadine daga cikin sharuddan sallah. Haka kuma ba'a sallah ana fuskantar bangwan dake dauke da najasa, kamar bangwayen da ake fitsari a jikinsu.
2. Wurin Wanka: Shima dakin da aka ware domin wanka, kasan akan ware wurin wanka daban wurin bayan gida shima daban, ba'a sallah a ciki, domin ana bayyanar da al'aura a wurin, kuma shima matattarane na aljanu.
3. Makabarta: Bai halatta mutum ya yi sallah a inda yake makabartace, domin ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya hana, yana kuma cewa ''Allah ya tsinewa Yahudawa da Nasara domin sun dauki kaburburan Annabawansu masallatai''. Lalle irin wannan al'amari da ya kai madaukakin sarki ya yi wannan tsinuwa to lalle ba karamin al'amari bane, saboda haka bai halatta a binne kabari a cikin masallaciba, ko kuma a gina masallaci a kabarin wani ko wataba, domin yanada matukar hatsari. Hakanan bai halatta mutum ya yi sallah yana fuskantar kabariba domin nan inda yake sallar sunansa masallaci, hadisai masu tarinyawa da kuma tsoratarwa duk sun tabbata akan haka, wannan fa ba wai don su najasa bane, a'a, kada ka manta wadancan kaburburan Annabawa suka mayar masallatai Allah ya tsine musu kuma kowa ya san Annabawa ba najasane, ai dun mumini ba najasabe ballantana Annabawa.
  Ya halatta ayiwa mutum bayan ya rasu sallah a makabarta, kamar ace an binne shine ba'a yi mishi sallah ba
4. Wurin Da Aka Yi Azaba: Dukkan wurin da kasan Allah ya yiwa wasu azaba awurin ko ta hanyar ruftasu ko ma wadansu nau'uka na azaba da Allah yake yiwa wadanda suka saba masa. Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yana cewa dangane da inda Allah ya halakar da Samudawa: '' Kada ku shiga inda waddannan mutanan suke sai in kun kasance masu kuka, kuma indai baku kasance masu kukaba to kada ku shiga wurinsu domin kada irin abinda ya samesu ya sameku''. Bukhari ya ruwaito wannan Hadisin a Kitabus Salah babin: Yin sallah aka kifar da su ko aka yi musu azaba. Akan haka ne wasu daga cikin malamai sukace bai halatta ayi tsarki da ruwan wurinba. Kuma an ruwaito daga Aliyu ibnu Abidalib Allah ya kara masa yarda ya wuce inda aka kifar da mutane a Babila bai yi sallah ba sai day a wuce.
   Amma wadansu malaman na ganin ya halatta domin babu wani dalili ingantacce da yake nuna cewar sallar ta baci, domin cewar ibada bata yi yana bukatar dalili mai karfin gaske. Akashin gaskiya nisantar irin wannan sabani sha yafi.
5. Turken Rakuma: Shine dukkan wurin da yake makwantar rakumane  wato nan suke kwana, ma'aikin Allah yana cewa '' Ku yi sallah a turakun awaki, kada ku yi sallah a turakun rakuma''. Tirmizine ya ruwaitoshi, a dansu ruwayiyon an sami cewar wurin matattace ta shaidanu.
6. Bola: Bai halatta mutum ya yi sallah a inda yake bolace, domin kowa ya san bola matattarace da najasa da shaidanu. Wannan ya fi faruwa a lokacin da sahu ya kure ko kokarin samun jam'i musamman aranar juma'a, to lalle ya kamata mu sani ba'a sallah a bola.
7. Mayanka: Hakanan ba'a sallah a mayanka domin wurine da yake dauke da najasa ta jinin yanka.
8. Saman Ka'abah: Hakanan ba'a sallah akan ka'aba domin abinda aka shar'anta shine a fuskanceta, to mutumin da ya hau kan Ka'abah ina ya fuskanta kenan.
9. Coci: An ruwaito daga wurin malamai cewa ba'a sallah a wuraran ibadar Yahudawa da kuma Coci wurin ibadar Nasara. An ruwaito hakan daga Umar da Ibnu Abbas da Malik, wasu malaman suka a'a sai dai idan Cocin akwai hotuna ko gumaka.
10. Mutummutumi: an hana ayi sallah ana fuskantar mutummutumi domin hakan zai zama ana kwaikwayar wadanda suke bautawa irin wannan mutummutumin. Kenan saboda kariyar da musulunci yake baiwa tauhidi aka hana sallah a makabarta da ire-iren wadannan wuraran.
11. Inda Aka Kwata: Wurin da aka kwata malamai sukace bai halatta a yi sallah a wurinba domin zama ma bai halattaba ballantana sallah. Jamhurdin malamai sukace sallar ta yi laifin kuma yana ga wanda ya kwata amma sallar wanda ya yi sallah a wurin ta yi.
12. Masallacin Cutarwa: Shine dukkan masallacin da aka ginashi domin cutar da al'amma cutarwar da musulunci ya tabbatar da ita, to irin wannan masallacin bai halatta ayi sallah acikin shiba, bayaninshi ya zo a cikin Suratut Taubah daga aya ta 108 zuwa ta 110.
13. Wurin Dake Da Hotuna: malamai sun kyamaci yin sallah matukar kyamata a wurin da ke an manna hotuna, amma abin takaici sai ka ga an manna hoto a jikin masallaci a wasu wuraran har a cikin masallaci, wannan bai kamata ace dakin Allah ake kawo wadannan abubuwaba, abin gudu shine sannu-a-habkali sai hankalin mutane ya fara komawa ga wadannan hotunan, wanda yake hakan sanannene, kuma shine sanadiyyar shirka, ka duba kissar Waddu da Yagusa da Ya'uka da Nasrah da suka zo cin Suratu Nuh. Allah ya sa mudace, amin.
Kammalawa: Daga takaitattun wadannan bayanai ya bayyana a garemu cewa akwai wuraran da ya zama wajibi a kula dasu alokacin da mutum zai yi sallah domin akwai inda aka hana, kuma munsan irin hadarin da ake ciki a yanzu na ginegine da ake yi akabarbaruka wanda yake ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya hana.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

No comments:

Post a Comment