Thursday, February 6, 2014

020- LOKUTAN SALLAH (2)


Muhtarin Salloli Da Larurinsu:
1. Muhtarin Sallar Azahar shine daga lokacin da rana da gusa daga sararin sama zuwa bangaren yamma inuwa kuma ta bayyana ta bangaren gabas harzuwa loakcin da inuwa zata kai tsawon kowanne abu. Larurin azahar kuma shine daga lokacin da inuwarka ta kai tsawanka zuwa dab da faduwar rana.
2. Muhtarin Sallar La'asar daga lokacin da inuwarka ta kai tsawonka zuwa loakcin da rana zata yi fatsi-fatsi. Larurinta kuma zuwa faduwar rana.
  Kenan azahar da la'asar suna tarayya a wani bangare na lokacin sallah, wannan kuma yana da matuka muhimmanci a fahimceshi saboda bayanan da zasu zo nan gaba, da izinin Allah.
3. Muhtarin Sallar Magariba: daga lokacin da rana tadi (ta bace kwata-kwata) zuwa gwargwadon abinda ka sallata, ba'a bukatar a jinkirtata. Larurinta har zuwa dab da fitowar alfijir.
4. Muhtarin Sallar Isha: daga lokacin da shafaki ya bace har zuwa kashi daya biya ukun dare. Larurinta har zuwa fitowar alfijir.
   Kenan magariba da lisha suna tarayya awani yanki na lokacin sallah.
5. Muhtarin Sallar Asubahi: daga lokacin da alfijiri ya keto zuwa gari ya waye (ya yi haske tangaran) zuwa fitowar rana.
  Kenan asubahi ita kadai take da lokacinta babu wata sallah da ta yi tarayya da ita.
 Ba'ayarda mutum ya jinkirta sallah har zuwa lokacin laruriba sai idan yana da larurar da shara'a ta bayyana, idan mutum ya kuskura ya bar sallah har lokacinta ya fita to ya tafka laifi mai girman gaske, Allah madaukakin sarki yana cewa '' Sai wadansu masu mayewa suka maye musu suka wulakantar da sallah suka bi holewarsu da sannu zasu hadu da gayyah (wani kwarine a cikin wutar jahannama). Sai dai kwai wanda ya tuba'' Suratu Maryam, aya ta:59-60 Allah ya tsare mu.
Larura:
Ya zama dole mu tsaya mu fahimci mecelarurar domin kada ka dauki abinda ba larura bane a shar'ance ka bashi matsayin larura.
1. Mantuwa: Duk wanda ya manta da sallah, ya dauka kamar ya yi ashe bai yi ba sai daga baya ya tuna to sai ya tsahi ya sallace ta a wannan lokacin da ya tuna, ko da lokacin sallar ya fita, kamar ya manta da azahar sai bayan ya yi sallar isha ya tuna, sai ya tashi ya kawo sallar azahar din,yin ta a wannan lokacin shine kaffarar.
2. Bacci: Idan lokacin sallah ya yi mutum sai ya yi sallah kafin ya kwanta, idan kuma lokacin sallah bai yi ba sai ya kwanta bacci bai tashiba sai da lokaci ya fita, to a wannan lokacin da ya tashi sai ya sallaceta babu wani jinkiri. Akan abinda ya shafi mantuwa da bacci Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yake cewa:    '' Duk wanda ya manta wata sallah, ko kuma ya yi bai yita ba, to ya sallaceta idan ya tunata babu wani abu da yake kaffara sai yin hakan''. Muslim,684. kenan ba maganar wai sai lokacin na gobe ya dawo, wannan babu shi a musulunci duk lokacin da ka tuna da sallah to a wannan lokacin zaka sallace ta.
3. Musulunta: idan mutum ya musulunta bayan muhtarin sallah ya wuce, kamar ya musulunta lokacin da rana ta yi fatsi-fatsi, to a wannan loakcin zai yi sallar azahar da la'asar, tunda sun yi tarayyar lokaci.  
4. Balaga: idan ya zama yarone ya fitar da maniyyi a barci ko a farke ya zama wannan fitar maniyyin shine balagarshi a wannan lokacin to sai ya yi wanka ya sallaci azahar da la'asar idan a loakcin su ne, ko magariba da lisha idan suma a lokacin su ne.
5. Hauka: ko kuma mutumne yake fama da cutar tabin hankali sai bai sami saukiba sai abinda ya saura kafin alfijir ya fito za'a sami raka'a hudu to sai ya sallaci magariba da isha.
6.Suma: ko kuma mutumne ya suma ko aljanu suka bigeshi sai bai farfadoba sai a wadannan lokuta na laruri, idan ya zama za'a sami sallar raka'a biyar kafi rana ta fadi sai ya yi sallar azahar sannan ya kawo sallar la'asar, amma idan za'a sami raka'oi hudune kafin rana ta fadi sai ya sallaci la'asar kadai.
7-8. Jinin Al'ada Da Jinin Biki: Zuwan wannan jini da kuma lokacin da ya dauke yana da matukar muhimmanci iyaye mata su kula da shi domin yana da alaka da sallar da zaki rama da kuma wacce ba zaki ramaba.
   Idan jinin ya dauke mata kuma bayan ta yi wanka za'a sami gwargwadon raka'oi biyar kafin rana ta fadi to zata yi sallar azahar da kuma la'asar, idan kuma kafin alfijirine za'a sami raka'oi hudune to zata sallaci magariba da lisha. Tirkashi!. Da yawa wasu matan idan sun sami tsarki da daddare ba abinda suke tsammani sai sallar asuba, idan kuma da ranane basa ilssafa fara sallah sai magariba ta yi, wanda yake wannan danyan kuskurene kuma laifine maigirman gaske.
   Wadannan sune larurorin da shara'a ta yadda da su har mutum sallah ta kai shi loakcin laruri, amma aiki a ofis ko baki balle mitin ko aikin gona ko hada-hadar kasuwanci wadannan ba laruraba a shar'ance, kawai da zarar loakcin sallah ya yi sai ka tashi kaje ka gabatar da ita.
   Sallah itace mafi girman ibada da ake so mutum musulmi ya bata kulawa, ranar alkiyama idan sallah ta gyaru to da izinin Allah komai zai zo da sauki.
   Amma yadda wasu suka dauka na idan sun fita harkokinsu sai sun dawo gida za su hada azahar da la'asar, sannan su biyo da magariba da lisha wannan tsantsar sabon Allah ne, babban abinda ake so mai wannan dabi'a ya tuba zuwa ga Allah ya ci gaba da gabatar da kowacce sallah akan lokacinta.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai mun san muhtarin sallah da kuma larurinta da kuma abainda ake nufi da larurin sune wadannan abubuwa da aka lissafo, kuma mun fahimci gabatar da kowacce sallah a lokacinta shine mafi alheri ga kowa da kowa, Allah ya yi mana jagora.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com      

No comments:

Post a Comment