Thursday, March 20, 2014

029- SUJJADAR RAFKANNUWA (KABALIYYAH DA BA’ADIYYAH)


 Gabatarwa: Ayanzu da izinin Allah muna son mu kawo bayanaine da suka shafi sujjar rafkannuwa wacce ake kira Kabaliyyah ko ba’adiyya da fatan Allah ya anfanar da mu da wadannan bayanai, kuma ya sanya ya zama sanadiyyar tsira duniya da lahira.
  Wadannan bayanai za su kunshi me ake nufi da sujjadar rafkannuwa ko mecece kabaliyyah sannan mecece ba’adiyyah, sannan a kawo bayanai na abinda ke sabbaba wadannan sujjadu.
Sujjadar Rafkannuwa: Sujjadune guda biyu da mutum yake yinsu bayan ya kammala sallah kafin sallama ko bayan sallama saboda kari ko ragi ko kokwanto da ya yi a cikin sallah.
   Wannan ta’arifi da ya gabata ya fayyace mana me ake nufi da sujjadar rafkannuwa kuma ya yi bayanin abinda yasa ake yenta da kuma lokacin da ake yenta da kuma dadi nawa ake yi.
Kabaliyyah: Sune sujjadu biyu da ake yi bayan tahiyyah kafin sallama, kasancewa ana yinta kafin sallama shi yasa ake kiranta kabaliyyah wato ‘Kabals Salam’.
Ba’adiyyah: Sune sujjadu biyu da ake yi bayan an sallame daga sallah, saboda ana yinsu ne bayan an yi sallama shi yasa ake kiranta da ba’adiyyah wato ‘Ba’das Salam’.
Yadda Ake Yin Kabaliyyah/Ba’adiyyah: Idan saujjadar kabaliyyah ta kamaka to kada ka manta zaka yi ta ne bayan ka kammala tahiyyah ta biyu wato ka karanta tahiyah kuma ka yi salatin Ma’aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- sannan ka nemi tsari daga abubuwa hudunnan ya kallama addu’oinsa, ba’abinda ya rage masa sai sallama to sai ya yi kabbara zuwa sujjada sannan sai ya dago tare da kabbara sannan sai ya sake komawa sujjadar tare da kabbara sannan sai ya sake dagowa tare da kabbara sai ya yi tahiyah sai ya sallame.
   Idan kuma Ba’adiyyace to zai yi wadannan sujjadune tare da bakarbarinsu bayan ya sallame daga sallah, sannan sai ya sake yin tahiya ya yi sallama.
Abubuwan Dake Sa Sujjadar Rafkannuwa: Abubuwan da suke haifar da sujjadar rafkannuwa wato kabaliyyah ko ba’adiyyah a dunkule malamai sukace abubuwa guda uku:
1.    Kari.
2.    Ragi
3.    Kokwanto.
Idan mutun ya yi kari a sallarsa, misali sallah mai raka’a biyu sai ya kara da mantuwa suka zama uku to anan sujjadar rafkannuwa ta kamashi.
  Haka kuma mutum da ya yi ragi, misali mutuminda ya manta bayan ya yi raka’a biyu sai bai zauna ya yi tahiyaba sai ya mike, ka ga anan ya rage zaman tahiyyah.
  Hananma mutum da kokwanto ya samishi alokacin yana cikin sallah, misali mutumin da yake kokwanto wannan raka’ar da yake yi itace ta uku ko itace ta hudu? Ya riga ya rikice bai san wacce yake ciki ba, to shima wannan sujjadar rafkannuwa ta kamashi, saboda haka da izinin Ubangiji zamu kawo muku bayanai na wadannan abubuwa da suke haddasa rafkannuwa da irin sujjadar da za’a yi wa kowanne nau’i. Kada ka manta ba’a sallame sallah domin a sakota daga farko saboda ka rikice a cikinta, a’a abinda ake so shine ka gyarata, bawai ka sallame ka sakeba, saidai a inda akace sallah ta baci.
Kammalawa: Dafatan mun fahimci inda aka sa gaba domin anan an kawo bayananne a dunkule, musamman kan abinda ake nufi da sujjadar da kuma yadda ake yenta da sabuban da suke janyota, da izinin Allah a nan gaba zamu kawo bayanai akan abinda yake janyo kabaliyyah a fayyace, kuma a babi mai zaman kansa, sannan mu kawo kuma akan abinda yake janyo ba’adiyyah shima a babi mai zaman kansa. Da fatan Allah ya kaimu lokacin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com


3 comments: