Thursday, March 13, 2014

028- ABUBUWAN DA SUKE BATA SALLAH


Gabatarwa: Anan za’a kawo bayanaine na kadan daga cikin abubuwan da suke bata sallah ta yadda ba abinda ya ragewa mutum saidai ya sake wannan sallar, kabaliyyah ko ba’adiyyah basa magance matsalar da aka samu. Wannan ya nuna cewa lalle wannan maudu’i yanada matukar muhimmanci ga kowanne mutum musulmi. Ga kadan daga cikinsu:
1. Dariya: Dariya tana daga cikin manyan abubuwan da suke bata sallah ko an yi ta da gangan ne ko kuma da mantuwa wato ya manta cewar shi yana sallah, ai ba mai dariya a sallah sai rafkananne, saboda haka mu sani sallah ba karamar ibada bace ba’a dariya a cikin sallah kuma duk wanda ya yi dariya a cikin sallah to sallar shi ta baci sai ya sake ta.
2. Kari Dagangan: Idan mutum ya yi Karin raka’a ko ruku’u ko sujjada dagangan to anan sallarsa ta baci, domin kuma ya dauki addinin da wasa da wargi, wanda yake addinin musulunci bai ginu akan hakaba. Amma idan rafkana ya yi har ya yi kari to anan sallar shi bata baciba bayanan yadda zai gyra za su zo ababin kabaliyyah da ba’adiyyah idan Allah ya kaimu.
3. Ci Ko Sha: Duk mutumin da ya ci ko ya sha yana cikin sallah to sallar shi ta baci, domin da zarar ka yi kabbarar harama to ka shiga cikin haramin sallah duk wadannan sun haramta a gareka, saboda haka duk wanda ya ci ko ya sha yana cikin sallah to sallar shi ta baci sai ya saketa.
4. Magana Dagangan: Idan mutum ya yi Magana da gangan kuma maganar bata gyaran sallah bace to sallar shi ta baci. Kenan idan ba dagangan ya yi maganarba to sallar shi nanan, amma zai yi ba’adiyyah domin ya yi kari a cikin sallah. Haka kuma idan ya yi maganarne dagangan amma ya yi ta ne domin gyaran sallah to sallar shi nanan, misali liman ne sallah ta rikice masa ya rasa yadda zai yi sai yace ‘Ina muke ? ko ‘Raka’a nawa muka yi ?’ anan maganar da ya yi ta halatta kuma maganar wanda ba yashi amsa ita ta halatta domin an yi ne saboda gyaran sallah.
   Amma idan maganar ta yi yawa to sallar zata baci, saboda haka da zarar wani ya bada amsa to kais a ka yi shiru, domin ba wata majalisa za’a budeba da za’a ce kowa sai ya fadi albarkacin bakinsa.
5. Hadasi: Da zarar mutum yana cikin sallah sai ya yi hadasi to sallar shi t abaci sai ya sake, shi kuma hadasi shine; dukkan abinda yake fita ta mafita guda biyun nan al’aurar gaba da dubura, kamar; tusa, fitsari, maziyyi…’’ .
6. Tuna Sallar Baya: Idan mutum yana cikin sallah sai ya tuna ai bai yi sallar da ta wuceba to wannan sallar da yake yi ta baci, misali yana cikin sallar la’asar sai ya tuna ai bai yi azaharba to anan la’asardin ta baci. To maye abin yi ? abin yi anan idan shi kadai yake sallar sai ya karo raka’a su zama biyu sai ya sallame ya maida su nafila kenan, sannan ya kawo wacce ta wucedin sai kuma ya maida wannan da cikakkun raka’o’inta, idan kuma yana bayan limanne sai ya ci gaba da bin liman din, idan an sallame sai ya kawo wacce ta wucedin sannan ya maida wannan da ya yi tare da liman. Amma idan bai tuna da sallar da ta wuce ba sai bayan da ya kammala sallar da ta biyo bayanta to anan wacce ta wuce kawai zai kawo ita kadai ba zai sake wacce ta biyo bayan nata ba.
7. Kara Kwatankwacin Sallar: Idan mutum ya yi rakannuwa har ya kara kwatankwacin raka’o’in wannan sallar to sallar ta baci, misalin sallah mai ra’a biyu ya karo biyu su zama hudu da rafkannuwa ai sallar ta baci sai an sake, ko masu raka’o’I hudu ya kara wasu hudun suka zama takwas ko mai uku ya karo wasu ukun suka zama shida to anan sallolin sun baci. Wannan fa ana bayanine idan da rafkannuwane domin abinda da aka kara ba zai yiwu a yi kabaliyyah ko ba’adiyyah ba, amma Karin raka’a guda da ganganci yana bata sallah, saboda haka a banbance.
  Kammalawa: Wadannan kadan kenan daga cikin abubuwan da suke bata sallah wanda hakan yake zama wajibi sai an sake ta, da fatan mun karu, kuma Allah ya karba mana ibadummu, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
      

6 comments: