Bayanda a darasin da ya gabata aka
kawo bayanai da suka shafi ruwa, a yanzu za'a kawo abubuwan da ake yi da ruwan,
akan haka za'a fara da najasa da yadda ake gusar da ita da ruwa da sauran
hukunce hukuncen ita najasar, Allah Ya yi mana jagora amin.
Abubuwan Da Suke
Najasa:
Na farko: Fitsari. (Na mutum) Na
babba ko na karami na mace ko na namiji, ya fara cin abinci ko bai faraba. Na
biyu: Bayangida (Kashi na mutum). Na uku: Mushe, shine abinda ya mutu da karan
kansa, ko aka yankashi ta hanyar da bata musulunci ba. Na hudu: Nonon dabbar da
ta yi mushe. Na biyar: Nonon dabbar da aka haramta cin ta, kamar nonon karya,
ko alade ko jaka...' Na shida: Fitsarin dabbar da aka haramta cin ta, kamar
fitsarin jaki, ko kare…' Na bakwai: Kashin dukkanin dabbar da aka harantata,
kamar kashin alade (alhanzir), kashin jaka/jaki..' Na takwas: Kashi da fitsari
na dukkanin dabbar da take cin najasa. Na tara: Giya. Na goma: Jini, saboda
haka bai halatta a tari jinin da aka yanka dabba ba wai ace za'a gasa shi ko a
soya ko ayiwa dabbobi abinci da shi ba domin najasa ne (in banda jinin da ake
samu a cikin dabba bayan anyankata wanda bai fitaba, ai dakyar a rasa jini a
cikin dabba). Na sha-daya: Ruwan ciwo. Na sha-biyu: Maziyyi, shi kuma ruwane da
yake fari yana da laushi yana fitane lokacin motsawar sha'awa ta mace ko namiji
ta hanyar wasa ko kallo ko nitsewa cikin tunani, amma idan sha'awa ta kara
karkafafa to maniyyine ke fita, shi kuma maniyyi ana jin fitarshi sabanin maziyyi,
sannan shi kuma maniyyi yana da kauri sabanin maziyyi shi yana da laushine,
bayanai za su zo akan shi nan gaba kada idan Allah Ya yarda. Na sha-uku:
Wadiyyi, shi kuma ruwane fari yana kauri sau da yawa yana fine akarshen
fitsari, ta sanadiyyar daukar kaya mai nauyi, ko matsanancin sanyi, ko kullewar
ciki. Na sha-hudu: Ragowar ruwa ko aminci na dabbar da ba'a ci, kamar rowan da
jaki ya sha ya raje, in banda mage. Na goma sha-biyar: Yawun kare da na alade,
ko na dukkan babbar da ta samu ta hanyar su. Na goma sha-shida: Amai, alokacin
da canza daga yanayin abinci, kenan idan aka ci abin ci yanzu sai kuma aka
harar da shi wannan harawwar ba najasa bace. Wadannan sune abubuwan da suke
najasa, amma akwai wadansu da malamai suka karawa juna sani akansu kan najasa
ne ko ba najasa ne ba, kamar ragowar ruwa na wanda ba musulmi bane ya sha,
hakanan akan maniyyi.
Shidai Maniyyi na namiji: Ruwa ne da yake fari maikauri yana tunkudar
junansa alokacin da zai fita, idan ka shinshina shi ya yi kama da hudar dabino,
kuma ya yi kusa da kanshin kulli, amma idan ya bushe yana kasancewa kamar
karnin fasasshan kwai. Wannan shine galibin yadda maniyyin namiji yake
kasancewa, wani lokacin ya kanzo sabanin wadannan bayanai da suka gabata. Yana
fitane lokacin matsananciyar sha'awa ta sanadiyyar kallo ko wasa ko matsanancin
tunani ko lokacin saduwa. Shi kuma Maniyyin mace, shi ma: Ruwane fatsi-fatsi
yana da laushi. Wannan ya tabbatar da cewa mace ma tana da maniyyi kuma da shi
ne da na namiji Allah Yake halitta da su.
Wasu malamai sunce maniyyi najasa ne domin yana fitane ta mafitar
fitsari wanda yake shi kuma fitsari najasane, wasu malaman kuma sukace ba
najasa bane domin da shi ne Allah Ya halicci dan'adam kuma a cikinsu akwai
Annabawa da Manzanni, kenan ya za'a mutum da Allah ya karramashi da yaukaka shi
har ya fitar da Annabawa da Manzanni ace kuma da najasa aka yi shi??. Wadannan
sune abubuwan da suke najasa da kuma wadanda malamai suka yi wa juna Karin
fahimta.
Hukuncin Najasa:
Wajibine gusar da najasa daga jiki da tufafi da wurin da za'a yi sallah,
idan mutum yana da ikon gusar da ita kuma yana sane bai gusar da ita dinba ya
yi sallah da ita to ba shi da sallah. Addinin musulunci addinin tsaftane abinda
musulunci yake so shine akoda yaushe ka sance cikin tsarki, mafificin tsarki
kuma shi ne tsarkin zuciya a kakkabeta daga barin shirka da zalinci da hassada
da munafunci da dukkan wata mummunar dabi'a, idan aka samu tsarkin zuciya kuma
ga tsarkin tufafi da ganganjiki da kuma mahalli to lalle wannan shi ke nuna
kammaluwar mutum.
Yadda Ake Gusar Da
Najasa:
Idan ka ga inda najasar take a jikinka ko a tufafinka to iya inda yake
iya nan zaka kama ka wanke, sabanin yadda wasu matan suke yi wai dukkanin
tufafin da tasa alokaci da take al'ada to sai ta wanke su, kama daga dankwali
da zani da riga…' wannan musulunci bai zo da shi ba, inda kwai kika ga jini iya
nan kawai za ki wanke. Idan kuma najasar ta rikice maka baka ganta ba, amma ka
tabbata akwaita ajikin tufafin na ka shikenan sai ka wanke tufafin gabadaya. Amma
idan najasa ta fantsamo sai kake kokwanton ta tabaka ko bata taba ka ba, kuma
kai baka ganta ba kuma ka duba mai Ahlari yace sai ka yayyafa ruwa a wurin.
Amma kuma idan wani abu ya fallatso maka sai kake kokwanto wannan abun
najasane ko ba najasa ba ne, to awannan lokaci ba wani hukunci akanka, ba yayyafa
ruwa ballantana wankewa, domin mafiyawan abubuwa masu tsarki ne, najasa kadanne
shi yasa ake iya lissafe su.
Idan inda najasar take kuma filine ko bango ko wani dutse sai aka yi ruwan
sama ko kuma aka kwarara ruwa mai tsarki akai shikenen an gusar da wannan
najasar. Amma idan ta kasace yawun karene wato karene ya baki a kwano ko a
kwarya to za'a zubar da abinda yake ciki sannan a wanke sau bakwai sannan asa
kasa a daya daga cikin bakwai din. Amma najasar da ba wannan ba sai a wanke ya
wanku sabanin yadda ake yi, da yaro ya yi fitsari sai ace wai za'a yayyafa ruwa
alhali wankewa akace a yi, wani ruwamma da aka yayyafa kamar karawa fitsarin
yawa aka yi, Allah ya sawwake. Ya zama wajibi a tshi tsaye a gusar da najasa a
tsaftace muhalli, musulmi ya kasance tsaftattace tsafta cikon addini ai ta fi
ace ita ciko ce, ita sharadice sai mutum ya tsarkaka daga wadannan najasar
ibadar shi zata karbu.
Abubuwan Da Najasa
Take Hanawa:
Anan za'a anbaci wadansu abubuwa ne
da basu halatta ga dukkan mara tsarki ya aikata su saboda darajarsu da
matsayinsu, kuma hadasin babbane ko karami, wadannan abubuwa sune:
(1) Taba Alkur'ani: Bai halatta ga
mara tsarki ya taba Alkur'ani, har sai ya yi tsarki inda so samune ma ya yi
alwala musamman idan ya kasance ba mai yawan daukan Alkur'ani bane.
(2) Sllah: Hakanan bai
halatta ga mara tsaki ya yi sallah ba farillace ko nafila, har sai ya tsarkaka
ya kuma yi alwala, kamar yadda Ma'aikin Allah-tsira da amincin Allah su tabbata
a gareshi- yace: '' Allah ba zai karbi sallar wanda ya yi hadasiba har
sai ya yi alwala'' Bukhari:135, Muslim:225. Hakanan kuma ko da mutum
yana da tsarki amma tufafinsa ko wurin sallar baida tsarki to delene ya
tsarkake su kafin fara sallar, saidai idan bai saniba ko ya manta cewa a
tufafinsa ko wurin da ya yi sallah akwai najasa sai kuma da lokacin sallar ya
fita sannan ya gani ko ya tuna to anan ba komai sallar shi ta yi.
(3) Tawafi: Kuma dukkan
mutumin da bashi da tsarki to bai halatta ya yi Tawafin Ka'aba ba, daman kuma
ananne kadai ake dawafi a sararin duniyar nan.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata munsan abubuwan
da suke najasa ta yadda ko yanzu akace ka kawo biyar zaka iya cikin gaggawa, da
kuma hanyoyin da akebi wurin gusar da wannan najasa, wanda yake gusar da ita
din wajibine domin munji abubuwan da bai halatta mara tsarki ya yi ba, akaro na
gaba zamu kawo bayanai akan wadansu abubuwa da ake ganinsu kamar najasane
alhali kuma ba najasa bane.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Ahamdulillah wannan yayi
ReplyDeleteMALAM WASU MALAMAN SUNA CEWA RUWA GIDA 2 KAWAI YA KASU:MAI TSARKI DA MARAS TSARKI.TO YAYA HUKUNCIN YAKE?
ReplyDeleteNa kira ba a dauka ba tambayata itace shin farcen/kunba da aka yanke najasa ce ko ba bajasa bane. Nagode
ReplyDelete