Tuesday, April 2, 2013

004- ABUBUWA MASU TSARKI


Bayanda a darasin da ya gabata aka kawo bayanai da suka shafi abubuwan da suke su karankansu najasane, a yanzu za'a kawo abubuwan da suke masu tsarkine.
Kandagarki:
Mu sani cewa abubuwan da suke kadan sune suke da saukin lissafawa, amma abubuwan da suke da yawa akwai matukar wahala a lissafesu, shi yasa aka lissafa abubuwan da suke najasa amma lissafa abubuwan da suke da tsarki zai yi wahala. Annan za'a bada wadansu ka'idojine da za su taimaka maka kwarai da gasket wurin tantance najasa ko rashinta, sannan kuma za'a lissafa wadansu abubuwan da za'a iya ganinsu kamar najasane alhali kuma ba najasa bane.
Ka'idoji:
(1) Kasa: Duk inda doron kasane kake so ka ibada sai kake ganini kamar akwai najasa ko babu to asali shine babu najasar banda: bola, mayanka, bandaki da makabarta domin ba'a sallah a ita.
(2) Dutse: Hakanan dutse ko kamfa kake kokwanton yana da najasa ko bai da ita, to asali shine bai da najasa, sai ka sami tabbas in kuma baka samu ba to ka yi ibadarka wurin mai tsarkine.
(3) Tufafi: Shima alokacin da samu kanka cikin kokwaniton yana da tsarki ko baida tsarki kuma baka sami tabbas hakaba to sai ka koma asali shine mai tsarki ne, sai ka yi ibadarka da shi.
(4) Ruwa: Asali akan ruwa shine mai tsarkine har sai an sami tabbataccan dalili akan canzawar launinsa ko dandanonsa ko shisshinarsa, saboda haka dazarar an baka ruwa kada ka tsaya kai ta tambaya sai ka yi hukunci da wadannan abubuwan da suka gabata, domin kada ka je ka cika tambaya ka haramtarwa da kanka ruwan ba tare da wani dalili shar'antacceba, Umar dan Khattab (Allah Ya kara masa yarda) sun biyo ta gidan wata mata da musulma bace ta fito musu da ruwa sai abokin tafiyar ta Umar ya kama tambaya kan ruwan sai Umar hanashi.  
Abubuwa Masu Tsarki:
Na daya: Gawar mutum. Na biyu: Gumi/Zuffarsa. Na uku: Yawun mutum. Na hudu: Majinarsa. Na biyar: Hawayensa. Na shida: Kwai muddindai bai zama biragurbiba (wato mai wari). Nonon mutum. Na bakwai: Nonon dabbobin da ya halatta a ci, kamar saniya rakuma, akuya…'. Na takwas: Fitsari da Kashi na dabbobin da basa cin najasa, kamar fitsarin saniya da na akuya, rago muddin dai ba sacin najasa, kenan ya halatta asha ko ashafa kamar yadda akan idan kazzuwa ta kama mutum domin ba najasa ba ne, kamar yadda wadansu mutane suka zo wurin Ma'aikin Allah suna fama da wasu cututtuka 'sai ya tura su wurin da ake daure rakuman sadaka da su sha fitsarin rakuman da nonon su, amma sauran dabbobi fitarinsu da kashinsu yana bin hukuncin namanne, idan cin namansu halasne to fitsarinsu da kashinsu ba najasa bane. Haka namma ragowar ruwan da suka sha, da abincin da suka rage, idan bai halatta cin namansu ba to ragowar ruwansu da abincinsu ya zama najasa, kamar kare, jaki,alade….'.  Na tara: mataccan abinda bai da jijni mai gudana a jikinsa, kamar: kuda, tururuwa. Hakanamma laima-laimar da ke a gaban mata wanda yake ba wadanda aka ambata ba, domin dakyar za'a rasa laima a gaban mace.
   Shi kuma maniyyi mun yi Magana yadda malamai suka karawa juna sani akanshi, amma zance mafi karfin dalili shi ne 'maniyyi ba najasa bane' kamar yadda Abdullahi bn Abbas yace ''Aikamar majina ne''. Amma kuma idan ya fita ya zama wajibi a yi wanka, shi kuma maziyyi ba a yi masa wanka saidai tsarki.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata mun kara fahimtar abubuwan da suke ba najasa bane ko da ko ka kyamace su, amma kuma hakan ba ya sa mutum ya barsu a jiki, domin ita tsafta cikon addinice kamar yadda bayanai za su zo akan haka a rubutu na gaba.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna, Jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

No comments:

Post a Comment