Wednesday, December 16, 2009

Wasu daga: Manufofin Addinin Musulunci

MUNBARIN-MUSULUNCI.blogspot.com Don bayyana yadda Musulunci ya haskaka mana dukkanin rayuwarmu WASU DAGA CIKIN : MANUFOFIN ADDININ MUSULUNCI !Gabatarwa : Dasunan Allah Mai yawan rahama maiyawai jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabbanshi baki daya. Bayan mun gabatar da kasidu akan abinda ya shafi Takaba, Rabuwar aure da Idda a musulunci, cikin taimakon Allah Madaukakin sarki yau kuma munzo da wata sabuwar kasidar sai dai ba akan aure ko Takaba takeba, wannan makalar zata bayyana mana wasu daga cikin manya-manyan manufofin addin musulunci, wanda hakan zai nuna mana cewa dukkan wanda ya kallaci addinin musulunci kallo na adalci to kan zai tabbatar da kulawar musulunci ga Bani-adama dama sauran halittun Allah, kuma lalle zai dada bayyana mana cewa musulunci yana da cikakken tsari na tafiyar da dukkanin al'amurammu sannan tsarinsa yana iya tafiyar da duniya bakiyanta, wanda hakamma ya kasance a baya. Anan nake cewa akwai wadansu muhimman abubuwa guda shida da zamu bayya yadda musulunci ya basu kariya sosai da sosai domin sune kashin bayan bil'adama wadda rasa daya daga cikin wadannan abubuwa shida ga mutun a matsayin shi na mutun to lallekan akwai Magana balle ace anrasa daya ko biyu daga cikinsu. Ayanzu mai karatu saiya biyomu sannu a hankali domin bayyanasu daya-bayan daya in Allah ya yarda.
Abu na Daya : Kariya ga Addini.Dan-Adam a yadda Allah ya kaddari halittarShi ga reshi bazai iya rayuwa ba ba tare da bin addini ba na kwaraine ko akasin shi, wannan sai ya nuna mana yadda addini yake da tasiri ga Bil'adama, amma cikin rahamar Allah sai ya sanya addinin Muslunci shi ne addini zababbe kuma karbabbe ingantatte a wurinshi, kuma ya bayyana cewa dukkan wanda ya isa farfajiyar ranar lahira bada wannan addinin ba to tabbas yana cikin masu asara Allah ka tsaremu, Allah yana cewa " Ayau na cika maku Addinin ku, kuma na cika muku ni'ima ta, na yardar muku da musulunci shi ne addini." Suratul-Ma'ida, aya ta : 3, haka kuma Allah yake cewa "Dukka wanda yabi addinin da ba musulunci ba baza'a taba karba ba kuma shi aranar lahira yana cikin masu asara". Suratul-Ali-imran, aya ta : 85, ayoyi masu tarin yawa sunyi bayanin bin addinin musulunci kuma bayanine filla-filla daki-daki, sannan wannnan ya nuna mana shi musulunci ba addini ne na gargajiya ba ta yadda mutun zai'iya wadatuwa da abinda ya taso yaga ana yi a matsayin musulunci ba tare da ya karanta musuluncin a gaban malamai ba, ta inda gargajiya ce mutun zai iya wadatuwa da abinda ya taso yaga ana yi, koma ya ce yanzu ya samu ci gaba da wayewa ba sai ya bi shi, haka zalika ba addini ne na wata kabila ba kadai, wannan gabar tana dakyau mufahimce ta sosai, domin aduniyance wasu na ganin wannan addinin na Larabawa ne alarabawamma na gabas-ta-tsakiya wannan ya sa duk abinda akaiwa musulunci sai ace larabawa na kallo, kuma wannan yasa ake ganin kamar su Allah yaba kulawa da addinin, wanda kowa ya san ba haka bane, wannan ya sake sawa ake nunawa wasu ai al'adallarabawa ne su kuma ba larabawa bane, in kuma a najeriyance ne ace addinin Hausawa ne ko al'adarsu wanda kowa ya san ba haka bane kuma bazai taba zama hakaba. Shi Addinin musulunci addinine na kowa da kowa babu wani wanda aka ware, saboda haka idan za'aikira sai akira dukkanin mutane ba wata al'umma ba kadai, Allah yana cewa " Kace Yaku mutane! Ni Ma'aikin Allah ne zuwa gare ku bakidayan ku" Suratul-A'araf, aya ta :158, haka wurare da yawa ake bude kiran da 'Yaku mutane'! ko kuma 'Ya ku wadanda sukai imani' ba tare da anware wani ba, muma dada fahimtar wannana addini addini ne da ya shafi harduniyar Aljanu, domin ayoyi masu tarin yawa sunyi banin hakan daya-ba-yan daya, daga cikin su akwai sura guda wacce take dauke da bayanin su Al'janudin da al'adun su da kuma yadda wasu suka bar wadannan al'adudin suka musulunta suka shiga yin wa'azi ga wadan da basu musulunta ba. Kuma acikin Suratul-An'am aya ta : 19, Allah yana cewa " Kuma (kace) an yi min wahayin wannan Alkur'anin ne domin In yi muku gargadi da kuma dukkanin wanda (Alkur'anin) ya je masa". Wanna ya nuna babu wani wanda zaice wannan alkur'anin na shi ne ko na kabilar su saboda haka wannan addinin na musulunci addinine na dukkanin wanda ya bi shi, kuma babu wanda zaice shi musulmine amma wani abu na hukun-hukuncen musulunci bai haukanshi ba, sai dai in da larura bashi da lafiya yasha azumi in ya sami sauki ya rama. Hakika Allah ya baiwa wannan addini kariya ta manya-manyan bangarori guda biyu, bangare na farko shine ta waje, bangare na biyu kuma ta ciki, abinnufi da bangare na farko wato ta waje, musulunci ya baiwa kan shi kariya ta yadda bai yadda wani ya ci zarafin shi ba, ko yaki yarda da ai musuluncin ko kuma sanya mishi kowanne irin cikas, sabo da haka aka wajabta Jihadi, domin abaiwa musulunci da musulmai cikakkiyar kariya, domin kamar yadda musulunci bai yadda musulmai su afkawa wadanda ba musulmai ba, to haka musulunci bai yadda a afkawa musulmai ba, Allah (S.W.A) yana cewa "Kuma ku yake su haddai awayi gari babu sauran wata fitina, kuma addini kafdin shi ya zama na Allah ne" Suratul-Anfal, aya ta :39, sannan kuma ba wani sabon abu bane domin duk wani mai wani tsari sai ya baiwa wannan tsarinna shi kowacce irin kariya, ba tare da la'akari da 'yancin daya bangaran ba sabanin musulunci, kai ka san wannan hali da duniya take ciki na yake-yake da karya tattalin arzikin kasashe dan anfi karfinsu ana yin su ne don cimma manufa da kare manufofi wadanda sam musulunci bai goyi bayan haka ba, amma karfi-da- yaji ake tursasa al'umma akan sai sun bi, amma abin mamaki musulunci shi ne abinda kowa ya ke kallo, wai ya yi kaza ya tsara abu iri kaza, kuma tabbas kowa ya shaida in da gwamnatin wata kasa zata dauki nauyin mutun tundaga haihuwar shi har ya yi makarantar Faramari da sakandare yai jami'a, ta samammashi aiki taimai aure, sannan wannan mutumin ya zana yana yiwa wannan gwamnati makarkashiyar ganin bayanta, kai kasan idan ta dankeshi sai an yi mashi kisan da ba'ataba samun irinshi a tarihi ba. saboda haka musulunci ya wajabta hakanne don baiwa kanshi da mabiyanshi kariya. Kariya ta biyu da musulunci ya baiwa kanshi wato ta ciki, ita ce babu kari babu ragi a cikinshi, domin kari da ragi suna cikin manyan al'amuran da suka bata wasu addinai da suka gabata, domin muddin za'ai kari to wata rana za'abar hakikanin abinda yake shi ne musuluncin a kama bin wadannan kare-karen da sunan wai addini ake yi, wannan sai yasa a koma gidan jiya, haka kuma in akace za'a rage to fa zara bata barin dami wata rana sai a wayi gari an bar addinin kwata-kwata Allah ya kiyaye, amin. Akan wannan ne Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa "Dukkan wanda ya kago wani abu acikin addininnan na mu wanda babu shi to an mayar mishi" wannan Hadisin Bukhari da Muslim suka ruwaito shi, sanan a farkon wannan makala tamu mun kawo ayar da Allah yake cewa " Ayau na cika muku Addinin ku, kuma na cika muku ni'ima ta, na yardar muku da musulunci shi ne addini." Suratul-Ma'ida, aya ta : 3, wannan ya nuna tunda an cika to babu wurin kari. Sannan yana daga cikin kariyar da akaiwa wannan addini na cewa ba addinin wasa bane saboda haka ba'a yarda mutun ya shiga ya fita ba, idan zai yi ya yi idan kuma yana ganin ba zai iya ba to shikenan, amma ya shiga yau ya fita gobe musulunci sam bai yarda da wannan ba, kuma ya dauki matakai gamsassu don hana guda nuwar irin hakan, Tsar ya tabbata ga Allah ah, baka ganin idan mutun yana wannan jam'iyyar siyasar yau sai ya canza wata gobe, jibi kuma ya fita ya canza wata ko ya koma tada ya 'yan Siyasa zasu ganshi?! Akan haka ne akai bayanin hukunce hukuncan ridda, Allah ya tsare al'ummar musulmi, amin.
Abu na Biyu : kare Rai. Kasancewar Ran Dan-Adam yana da matukar kima kuma zubadda jinin shi ba karamar barna bace a bayan kasa, dubi Suratul-Ma'ida, bayan da Allah ya bada labarin 'ya'yan Annabi Adam su biyu da yadda dayan su ya kashe daya yadda Allah Mai girma da daukaka ya munana al'amarin, sannan ya ce " Saboda haka muka rubutawa Banu-Isra'ila cewa dukkan wanda ya kashe wata rai ba tare da ta kashe rai ba, ko tai barna a bayan kasa to kamar ya kashe mutane ne baki daya, haka kuma dukkan wanda ya rayar da wata rai to kamar ya rayar da mutane ne baki daya" musulunci ya dauki matakai don kare rayuwar bil-adama baki daya, nan da nan musulunci ya shar'anta Kisasi wato ramuwa a kan dukkan wanda ya yi kisan kai da gangan shima a kashe shi, wannan ita ce hanya mafi sauki wurin tabbatar da rayuwar dan-adam, domin dukkan mutumin da ya zaro wuka ko bindiga zai harbi wani ko ya dabama wani ya tabbatar yana kashe shi, shima za'a kashe shi tokan zai aje hannun shi anan an sami rayuwar al'umma, Allah yana cewa " Kuna da cikakkiyar rayuwa wurin yin kisasi (wato ramuwa)" Suratul-Bakara, aya ta : 179, da kuma fadin Allah " Ya ku wadanda sukai imani ! an wajabta muku yin kisasi (ramuwa) cikin dukkanin wadanda aka kashe" Suratul-Bakara, aya ta : 178, wannan ya ke nuna kulawar musulunci ga rayuwar al'umma, domin dukkan wanda yasan in ya kashe za'a kasha shi tokenan babbas zai hakura, kuma wata miza ta musulunci ba banbanci dan babban mutun in ya kashe dan talaka shima sai an dandana mishi kisan Allah ya tsare mu, amin. Sanna idan bincike ya nuna kisan na kuskure ne anan abubuwa biyu sun zama wajibi a kan wanda ya yi kisan: abu na farko ya 'yanta baiwa mumina idan kuma bai samu ba sai ya yi azimin watanni biyu a jere kamar yadda ayar Suratun-Nisa'I aya ta 92, ta yi bayani, anan ba maganar ciyar da miskinai sittin domin kisan kai ne domin in aka ce a ciyar da miskinai da yawa mutane ba zasu ji komai ba, kawai dayan ya 'yanta baiwa mumina in bai samu ba ya dunfari azumin watanni biyu a jere, wannan hakkin Allah kenen, Abu na biyu ya bayar da Diyya ga dangin wanda ya kasha musu dan'uwa, sai dai in sun yafe, anan zamu fahimci cewa ran dan-adan yana da muhimmanci sosai da sosai, kuma yana daga cikin manyan manofin musuunci kare rayuwar dan-adam. Ran dan-adam ya tara hakkoki kamar haka : hakkin wanda aka kashe, hakkin 'yan-uwan shi, hakkin Allah mahaliccin shi, dankari ! anan an sami hakki uku akan dan-dam, ma'ikin Allah yana cewa 'Dukkan mutumin da ya kashe wani, ranar alkiyama sai wanda aka kashe ya shako wuyan wanda da ya kashe shi, yace ya Allah tambaye shi domme ya kashe ni?!" saboda haka kwata-kwata musulunci bai yadda wani ya kashe wani ba, ko kuma mutum ya kashe kan shi, Ma'aikin Allah yana cewa "Dukkan mutumin daya kashe kan shi da kowacce irin wuka to wukar ta shi na hannun shi zai dinga cakawa cikin shi ita ranar alkiyama cikin wutar jahannama yana mai dawwama a cikin ta har abada, kuma dukkan mutumin da ya kashe kan shi da wata guba to gubar nan ta shi tana hannun shi yana kamfatar ta cikin wutar jahannama yana mai dawwama a cikin ta har abada, kuma dukkan mutumin da ya fado daga saman dutse ya kashe kan shi to haka zai dinga gangarawa cikin wutar jahannama mai dawwama a cikin ta har abada". Allah ya sawwake, mutun bashi da hakkin kashe kan shi da kan shi a musulunci, domin ba shi kadai yake da hakkin ba, bayan nashi a kwai na Allah mahaliccin shi a kwai kuma na 'yan-uwan shi (danginshi) kamardai yadda bayanai suka gabata. To yanzu ya kaga wanda zai tara matasa su zama 'yan-bangar shi yace 'su kashe kisan shi ne' Lalle wadannan bayanai suna nuna mana yadda musulunci ya kula da rayuwar al'umma, kuma aka dauki matakan da suka dace da kare rayuwar bil'adama. Yanzu dauki gajeran misali, kalli kisan kuskure, wanda shara'a ta tabbata kuskure ne kallaci irin diyyar da za'a bayar dudda cewa shi kisan kuskure dama babu ramuwa cikin shi saidai bada diyya, irin wannan diyyar lalle zata kawo karshen irin tuki da mugun wasa da dai sauran miyagun dabi'u, wadanda musulunci ya yi tur da su, amma dauki misali yadda ake tuki a kasar nan, ko lodin kaya, gudu wani in ya kama gudu kamar zai tashi sama, wasu direbobin kuma kajan hakuri, dadai sauran al'amura masu bantakaici wadanda tuni musulunci yai maganin abin, zaka ga yadda ake salwantar da rayukan al'umma basu-jiba-basu-ganiba, Allah ya sawwake, amin. Kuma Allah ya baiwa dangin wanda aka kashewa dan'uwa ya basu karfi, akan su tsaya tsayin daka kan hakkin dan'uwansu da aka kashe, sannan kuma ya yi musu alkawarin zai tai maka musu, Allah yana cewa "Dukkan wanda aka kashe shi da zalinci to hakika mun baiwa dangin shi wani karfi, saboda haka kada ai barna wurin kisan, lallekan shi ya kasance wanda za'a taimaka" Suratu-Isra'I, aya ta :33, hakika wadan nan bayanai sun nuna mana manufar addinin musulunci wurin kare rayuwar bil-adama da kuma irin matakan da aka dauka domin tabbatuwar hakan, hakika in dai anbi hakan to kan lalle za'a sami cikakkiyar rayuwa mai aminci, domin kowa ya san yana kashewa za'a kashe shi in gangancine, wannan sai yasa yaiwa kan shi kiyamullali, ya kubutar da rayuwar shi da kuma ta dan'uwan shi, ko kuma yasan zai dandani kudar shi wurin biyan diyya idan kisan kuskure ne, ko ya san zai dandani azaba idan shi ya kashe kanshi-da-kanshi, wannan zaisa don mutun na bakin ciki ko damuwa ba zai katobarar kashe kanshi-da-kanshi ba, balle ya sha guba, ko ya rataye kan shi ko ya hau katuwar gada ya fada, wai don damuwa da bacin rai na nan duniya Allah ya kiyaye mu amin, wani ya ce 'Da kunyar duniya gwanda ta lahira saboda bai san lahirar ba, amma inda ya san lahirar ai ba zai mafarkin fadin hakan ba.
Manufa ta Uku : Kiyaye Hankali. Yana daga cikin manyan manufofin musulunci kiyayewa Dan-adam Hankalin shi, domin hankali bakaramar kima yake da ita ba, wannan nasan ko ba'a kawo ayoyi da hadisai a kan haka ba kowa ya shaida, dan'uwa mai karatu hakika musulunci ya baima hankalin dan-adam hakikanin kulawa ta yadda ya tsaftace shi daga barin dukkan abinda zai gurbata masa hankali, akan wannane musulunci ya haramta dukkan abinda yake gusar da hankali kamar :, Giya, Wiwi, Koken da dukkan wani abu da za'a sarrafa ta kowacce irin hanya muddin yana taba hamkali to haramunne, Ma'aikin Allah yana cewa "Dukkan abinda ke sa maye giya ne, kuma dukkanin giya haramun ce" Bukhari da Muslim suka ruwaito, sannan koda baya sa maye sai an sha da yawa to ko kadan ne haramun ne kamar yadda Ma'aikin Allah yake cewa "Dukkan abinda meyawan shi ya ke sa maye to kadan dinshi ma haramun ne" wannan fa shine hakikanin gatan da musulunci yayi mana, domin yadda giya da mukarrabanta muggan kwayoyi suke cutar da gangar jiki likitoci sun yi ittifaki akan haka da kuma yadda take sanadiyyar aukuwar cututtuka masu hatsarin gasket wasu suna kaiwa ga salwntar rayuwa, yan zu mutum ya sha wadan nan kwayoyi sun yi sana diyyar rasuwar shi haka zai zo ranar kiyama yana kamfatar wadan nan kwayoyi kamar yadda bayanai suka gabata, ga yadda take bata dabi'u, wani yara suyi mishi 'Ta yi Marisa ta sha kafso' wani kuma ya kwararawa iyalin shi fitsari a kwance, wannan ya zama amalala, da kuma yadda take bata hankali ta kurbata tunani, domin kowa yasan wadan su muggan lefukan da ake tafkawa basa yiwuwa cikin cikakken hankali sai an bugu, Allah ya sawwake amin, wannan yasa malamai suka yi sabani kan aukuwar sakin mai-maye idan ya saki matar shi yana cikin ta yi Marisa ta sha kafso. Sabo da haka kamar yadda bayani ya gabata aka haramta dukkan wani abu da akai mai kowacce irin dabara ta yadda ya ke sa maye, ko meye kuwa, koda fura ce akai mata wata dabara ta zama tana sanya maye to ta zama haram, kamar yadda hadisin da mukai bayani ya nuna.
Manufa ta Hudu : Kiyaye Dangantaka. Hakika daga ciki manyan manufofin musulunci kiyaye dangantaka,domin tana da kima da daraja, misali ya mutun zai ji a ce yau ba'asan mahaifin shi ba?! domin kiyaye zuriyar kowa musulunci ya shar'anta Idda domin kada a dauki dan wani gida a kai wani gidan, kamar yadda bayanai suka gabata a makalolimmu, aka shar'anta Takaba, domin zai iya yiwuwa lokacin da mutun ya rabu da iyalinshi kodai ta hanyar saki ko ta rasuwa ya zamana tana da juna-biyu sati daya koma kwana daya, wannan na daga cikin dalilan da suka sa aka tabbatar da iddah da kuma Takaba, sannan domin tabbar da haka aka haramta Zina! Kuma aka dauki tsauraran matakai domin hana aukuwar hakan, in kuma hakan ya auku aka sanya hukuncin da mutun zai yi wuya ya sake anan gaba, domin Zina mummunar dabai'ace tana lalata zamantakewa ta wargatsa al'umma. Daga cikin matakan da aka dauka domin hana aukuwar hakan sune : Hana kadaituwa da macen da ba maharrama ba (wato wacce musulunci ya hana yin aure tsakanin ku kamar uwa, 'ya, kanwa d.s) Ma'aikin Allah yake cewa "Kada dayan ku ya kadaitu da mace lalle sai na ukun su ya kasance Shedan ne" domin kowa yasan tsakanin mace da namiji kamar mayan karfe ne, masu iya Magana na cewa 'maganin kada a ji kada a fara' domin an hana ma yin kusa da ita balle yin ta, Allah yana cewa "Kuma kada ku kusanci zina domin ta kasance alfasha ce kuma mummunar hanya" Suratul-Israi, aya ta : 32, lalle kan ka san kadaituwa da mace a shago ko ofis d.s yana cikin abinda aka hana, amma abin mamaki da takaici mutun yana zaune agari da iyalan shi sai aiki ko kasuwanci ya kaishi wani wuri wai sai abokin shi ya zo wurin matar suna hira da shewa su kadai a daki wai yana debe mata kewa! aannan ba ana cewa don megidan ta bayanan ba za'a ziyarce ta a ji labarin lafiyar su ba, mekuma suke bukata wannan musulunci ya kwadaitar da shi, kuma ya tsara yadda za'a gudanar da hakan yake cewa "Kuma idan zaku tambaye su wadansu abin bukata to ku tambaye su ta bayan shamaki" Suratul-Ahzab, ina jin wannan yasa iyayammu idan za suyi gini sai ayi zaure, kana cikin shi ita kuma tana daga cikin gida. Kuma yana daga cikin matakan da aka dauka aka hana mace ta sanya matsattsun kaya, wanda hakan cikin kankanin lokaci zai canza tunanin Da-namiji, domin kasan ba falwaya ba ne, ma'aikin Allah yake cewa "…Gasu sun sa tufafi kuma tsirara suke suna rangwada, ba za su sami kanshin aljanna ba" haka nan aka hana mutum ya kalli mace ko ta kale shi, kowa ya rintse idon shi, domin ka sani a jikin mace ba wurin yarwa, kuma masana sun ce ba mace mummuna! Domin dukkanin wadannan hanyoyi ne da suke kai mutun su baro cikin kankanin lokaci dama wadanda ba'a an bata ba, kowa ya san su. Kuma musulunci ya sanya Bulala 100 (dari) a kan dukkan saurayin da ya afka cikin wannan danyan aikin, ya sanya kuma hukunci kisa ta hanyar jefewa ga dukkan magidanci da ya afka cikin irin wannan dabi'a, bayan alkali ya tabbar da haka, wannan kuwa shine mafi dacewa, domin dai wannan saurayi wata kila gafin gwaauranta tasa ya afka cikin wannan hali to ana fatan daga wannan bulala ya tuba, ammafa magincin da bai wadatu da iyalan shi ba, harma aka bashi damar yin mata hudu amma bai hakura ba to wannan ya zama annoba cikin al'umma in ba'ai maganin shi ba to zai lalata al'umma baki daya, kamar yadda kasan ana yanke gaba a jikin dan-adam domin kada sutar ta mamaye sauran jikin, to haka al'amari yake dan ba abinda zai sa ya daina in har ya dandana saidai gyaran Allah. Wannan yana daga cikin abinda wasu suke ganin wai ba'a kare hakkin dan-adamba dirkashi! Sun manta irin bakar masifar da zai tsunduma al'umma ciki, yanzu dai bincike ya babbatar da cewa babbar hanyar yaduwar cutar HIV,(kanjamau) ita ce ta hanyar zina, kusan sama da 90% na hanyar yaduwar wannan cuta ita ce ta zina kamar yadda bayani ya gabata, kuma kaga yadda take aikawa da mutane lahira ba kakkautawa, anan ba wai duk mai dauke da wannan cuta wai manemin mata ba ne a'a sam, wata kila ya kamu ne ta sauran hanyoyin da mawuyaci in sunkai 10%, yanzu kana ganin asalin wanda yake dauke da ita da an kammala da shi ai da yanzu cutar bata zo tana kammalawa da al'umma ba, kuma ashelantawa al'umma haramcin Zina anki ance suna da 'yanci !, shi kallon da akewa musulunci akan hukuncin zina bahagon kallo suke yi, ita fa saduwa ko ta hanyar halas ce abin kyamane a ce an ga mutun da iyalinshi a hali iri kaza, balle haram!!, saboda haka wannan hukuncin shi yafi dacewa da shi, kuma in banda shi babu wani hukunci irin shi, ka tuna lokacin da Ma'aikin Allah yake mubaya'a da mata yake gicciya musu sharuddan mubaya'ar daga ciki ya an baci kada suyi zina, adaidai lokacin Hindu ta ce " Ya Ma'aikin Allah ! yanzu 'Ya zatai zina?!!" wanda ya nuna ko azamanin jahiliyya 'ya'ya mata basa zina saidai bayi, kasancewar ta da irin wannan halin kowa yasan lokacin da shugaban kasar Amurka Bill kilantu ya dunga kwarar da zuffa yana amsa tambayoyi kan zargin da ake mishi na ya yi lalata da Munikalawiski, ku kallace su ku kallaci tsarin da suke bi, wanda in da zargin ya tabbata da barin gidan shugaban-kasa zai yi, ai ma nan kasa da shekara guda wani Gwamna na wata jaha a Amurkadin ya sauka saboda irin wannan mummunan halin, saboda irin barnar da take haifarwa
aka dauki matakai domin magance ta akama hana yin kusa da ita kamar yadda bayanai suka gabata, kuma aka shar'anta yin aure domin kowa ya samu natsuwa da abokin zaman shi aka kuma halattawa mutum ya auri mata hudu duka dai dan kaucewa wannan bala'in da kuma tabbatar da ziriya tagari halattacciya tsaftatacciya, amma abin mamaki shi kuma auran muka cika shi da al'adu wadanda musulunci bai sanda su ba, suka kuma zame mana katangar karfe tsakanimmu da auren, domin kai kasan yawan 'yan-mata da zawarawa da ake dasu galibi ba an rasa masu son auran bane, irin tatsar da za'aiwa mutum idan ya je ita ake tsoro, wanda in da za'a sassauto ayo kasa-kasa da an rage adadi mai yawa a kuma kara da wadatar zuci, amma wata budurwar sai ta goya yaro dan shekara shabiyar, in da za'a sami saukin wadannan al'adun sai marasa aure kaga sun fantsama masu daya-daya kuma su kara hakanan masu biyu ko uku, sai a wayi gari an rage adadi masu yawan gaske, Allah ya taimaka mana, amin.
Abu na Biyar : Kare Mutunci. Hakina yana cikin manyan manufofin addinin musulunci kare mutuncin mutane, kamar yadda Ma'aikin Allah ya bayyana a hajjin Shi na bankwana yake cewa "Lalle jinin ku da dukiyoyin ku da mutuncin ku haramun ne…" saboda kare mutuncin mutane aka haramta Gulma, Zunde, Yafice Annamimanci da dukkan munanan dabi'u da suke zubarwa da mutun mutunci, har Allah Madaukakin sarki ya ke bayyana munin Gulma yake cewa "Yanzu dayan ku zai so cin naman dan-uwan sa matacce? Hakika kun kyamaci hakan" Suratul-Hujrat, aya ta :12, aka kuma haramta mana sanya munanan sunaye, sai kaga mutun ga sunan da mahaifin shi ya sanya mishi amma sai ya sanyawa kan shi wani sunan na daban wai sunan gayu. Sabo da kare mutunci aka hana Kazafi kuma a shar'anta hukunci wanda ya dace da dukkan wanda ya aikata wannan mummunan aikin, domin kamar yadda bayani ya gabata akan mummunar dabi'arnan ta lalata haka kawai a wari gari mutun baisan hawaba baisan sauka ba a ce ya aikata wannan aiki ya kake ganin mutuncin shi zai kasan ce a idon mutane, ka ko san mutunci madara ne, saboda haka musulunci ya gindaya sharadin dukkan wanda ya jefi wani da zina to sai ya kawo shaidu hudu, maza, musulmai, kuma baza'a kirga da shiba domin shi maikai kara ne, sannan idan bincike na alkali ya tabbatar da hakan sai aimai hukun zina kamar yadda bayani ya gabata, in kuma bai tabbata ba kowannan su sai ai mai bulala tamani (80), abu na farko kenan, abu na biyu kuma Baza'a sake karbar shedar su ba har'abada, abu na uku kuma Kuma wadannan sune fasikai, sai dai kawai wadanda suka tuba. Mekaratu dubi yadda musulunci yadauki matakai domin kare mutuncin mutun, domin in ba hakaba sai mutuncin ya zama ba abakin komaiba, da kunyi sabani da mutum sai yai ma kaharu amma in yasan akwai bulala 80 a doron bayan shi dole ya shiga taitayinshi, haka kuma aka shar'anta Li'ani (Tsinuwa tsakanin miji da mata) wanda yana kasancewa idan mutum ya jefi matar shi da lalata kuma bai iya kawo shedu hudu kamar yadda mukai bayani adazu ba, ko kuma ya yi musun dan-data Haifa ko take dauke da shi, mace tana da hakkinta ba zai aikata wannan danyar Magana ba a kyale shi, abu na farko ya kawo shedu hudu kamar yadda bayanai suka gabata, idan babu su sai ya yi rantsuwa hudu yana cewa 'Wallahi tallahi billahillazi La'iha illahuwa ta yi zina ko wannan dan ba nashi ba ne ko wannan cikin ba nashi bane' zai maimaita sau hudu sannan ta biyar yace 'idan karya ya yi mata to Tsinuwar Allah ta tabbata akan shi' sannan sai ya koma gefe ita kuma matar ta zo ta rantse kamar yadda ya yi tana cewa 'Wannan dan na shi ne ko wannan cikin na shi ne ko cewa da ya yi ta yi lalata karya ne, haka zata fada bayan kowacce rantsuwa har sai ta yi sau hudu, sannan ta biyar tace 'Idan abinda ya fada gaskiya ne to Fishin Allah ya tabbata akan ta, dankari! Idan kowa ya rantse shikenan sai ajingina dan gareta ace wane dan wance, a takaddun shi na makaranta da komai-da komai na shi, duk wanda yace mishi shege to bulala 80, idan kuma ta ki ta rantse shikenan sai ai mata hukunci masu zina, idan kuma shi mijinne yaki ya rantse sai ya karbi bulala 80 domin ya yi mata kazafi, Allah ya kiyaye amin, amma don rashin sanin kimar mutunci sai mutun ya rubuta takarda ya fitar da wani daga cikin 'ya'yanshi wai ba danshi bane saboda haka ba zai ci gadon shi ba kuma sai ya boye takardar sai bayan mutuwar shi aita kace-na-ce, ba wata Magana yaro gadon shi zai ci, har idan sauran 'ya'yan sun fahimci addini ai bazasu bayyana wannan takardar ba, domin me yasa bai bayyana ba tun yana da rai ya kare kanshi, mutnci fa ba abin wasa bane. Allah ya sawwaka amin.
Abu na Shida : Kare Dukiya. Kasancewar dukiya kashin bayan rayuwa ya kasance yana daga cikin manufofin musulunci baima tukiya kariya, saboda haka aka haramta dukkanin abinda zai gurgunta Tattalin arziki, kamar Sata Caca Fashi-da-makami Riba (bashi-da-ruwa) Cin-hanci-da-rashawa da dukkan wata hanya da shara'a bata yadda da ita ba, aka haramta Tauye mudu (wato dukkan wani abin'awo hatsi ko yadi ko manja ko litar fetur d.s…) kuma musulunci ya halatta kasuwanci domin kusan shi ne babbar hanya ta karuwar tattalin arziki aka kuma hana yaudara da algus da kara baka da dukkan wani salon yaudara nada da na yanzu, aka kuma dauki matakai don ganin an kare dukiyar al'umma, kasancewa afagen sata hannu shine ja-gaba sai akai umarni da idan mutun ya yi sata ta kai nisabi ta kuma cika sharuddan sata da a yanke hannun, don inba hakaba sai mutum guda ya sace abinda mutune dubu-dari zasu rayu da shi ya barsu cikin halin kaka-ni-kayi, aka kuma dauki tsattsauran mataki kan hana fashi-da-makami domin yana jefa al'umma cikin bakin tashin hankali da asarar rayuka da karya tattalin arziki cikin kankani lokaci, aka kuma bayya azaba maibala'in gaske ga maciya Riba wato bashi-da-ruwa, domin karshen rashin tausayi kenan mutun yana cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai sannan a kara mishi kan abinda aka bashi bashin shi, domin idan kana lissafa abubuwan da kewa tattalin arziki dukan kawo wuka Riba zata zo ajin farko, kuma kowa ya shaida yadda tattalin arzikin duniya yake tangal-tangal, dudda cewar wasu kasashen sun yanke shawarar rage bashi-da-ruwa daga bankunansu ba wai dan musulunci ya hana ba a'a don dai kawai yana mayar da tattalin arziki baya sosai-da-sosai.
Kammalawa: daga dukkanin bayanan da suka gabata ya bayya afili manufofin Addinin musulunci wadanda malamai suke kiran su da 'Addharuriyyat' wanda ya zama dole al'umma ta samu kariyar wadannan abubuwan, domin da su al'ummar zata sami kafuwa ta kuma zama mai cikakken 'yanci. Sannan wadanda suke ganin ba haka ba to ina ganin tsabagyan adawace da suke yi da addinin ko kuma sun jahilci musuluncin kuma wani abu ya hana su su karanci hakikanin shi, wasu kuma addinin ya je musu ne a baibai saboda haka ya zama wajibi atashi a fahimtar da su hakikanin me nene adddinin, kuma dukkanin wadannan manufofi na musulunci babu wata manufa data keta hakkin Dan-adam, sai idan mutun ne ya keta alfarmar shi, hasalima musulunci bai yadda da keta hakkin dan-adam ba, babban abinda wasu suke gani shi ne hukuncin kisa, wanda wannan gata ne musulunci ya yi wa al'umma, kuma dudu-du abubuwa nawa ne ke sa a zartar da hukuncin kisa a musulunci? Amma ka kalli sauran tsarin da ba musulunci ba, a wata kasarfa cin-hanci hukuncin kisa ne, yaga tutar kasa, cin-amanar kasa, za'a iya tunawa a wasu shekaru da suka wuce aka kashe wasu a Chana saboda sun kashe giwaye! Balle laifin juyin-mulki, dukkan wadannan hukuncin kisa ake zartarwa amma kirga abubuwan da musulunci ya tabbatar musu da hukuncin kisa da kuma yadda alherin haka yake a gare mu, kamar yadda muka ambata shifa mutumin da ya kashe mutun da ganganci idan baku kautar dashi ba daga cikin al'umma to zai zama dan-bindiga-dadi, kuma irin wannan sace-sacen yara da manya da ake yi da yawan kisan kai a gida ko a waje, balle fashi-da-makami dukkan musulunci bai yadda da su ba kuma ya dauki matakan da suka dace da su. Allah ya sawwaka kuma ya zaunar mana da kasarmu lafiya ya kuma nunawa shugabanni abinda yake daidai ya kuma basu ikon bi, amin.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda Minna, jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a  08064022965,

 ko kuma a Imei : aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

3 comments:

  1. Loved your site, Lee! Thanks for sharing Kami menyediakan berbagai macam obat seperti Obat kondiloma , Kencing Nanah , Wasir , Sipilis , Herpes , Diabetes

    ReplyDelete
  2. Assalamu alaikum I love this site much more, because is the best meaningful site in hausa language, Allah yasaka da alkhairi

    ReplyDelete