Wednesday, March 12, 2014

024- FARILLAN SALLAH


Shinfida: Ita sallah ibadace mai matukar mhimmanci da kuma girma a wurin Ubangiji mai girma da daukaka, saboda haka ya zama wajibi akan kowanne mutum daga cikin mu ya kyautata wannan sallah ta hanyar cika farillanta da kuma sunnoninta da mustahabbanta.
   Farillan Sallah: Idan akace wannan abun farillane to dole ka aikata shi, rashin aikatashi zai janyo matsala a wannan ibadar. Idan ake farillan sallah to anan nufin abubuwa masu matsayi na farko a cikin sallah ta yadda rashin aikata wannan farilla yana zama sanadiyyar rugujewar sallar mutum, kenan ya zama wajibi mu san wadannan farillai da kuma yadda ake aikata su a cikin sallah, domin su ko kabali da ba'adi ba'a yi musu, wadannan farillai sune kamar haka:
1.    Niyya: Ana kudurta tane a zuciya ba wai ana furtata da baki bane, abinda ake so adaidai lokacin da zaka yi kabbarar harama zuciyarka ta nufaci sallar da zaka yi. Abinda zai nuna maka ba'a furta lafazin Niyyah kuma furtata bashi da tasiri shine; Idan zaka yi sallar azahar sai zuciyarka ta nufaci azahar din amma bakinka ya furta la'asar to da na zuciyarka za'a yi la'akari saboda haka sai ace sallarka ta yi.
2.    Kabbarar Harama: Wato fadin lafazin ''Allhu Akbar'', an kirata da kabbarar haramane domin da ita ake shiga cinkin hurumin sallah, da zarar mutum ya yi ta to cid a sha da Magana …' duk sun haramta agareshi har sai ya yi sallama.
3.    Tsayuwa Domin Kabbarar Harama: Kenan sai ka tsaya a tsaye cur sannan ka fadi wannan kabbarar, da yawa zaka ga wasu sai sun sunkuya suke yinta domin son su riski wannan raka'ar wannan kuskurene.
4.    Karatun Fatiha: Karatun fatiha farillane a kowacce kuma a kowacce raka'a, kuma mutum ya karantata da kyau idan bai iyaba ya sami wani ya koya, ba'a irin wannan hali ake jin kunya ba, domin wani akan titi ya tsinci karatun fatihar ba zai iya tuna wani malami da ya kowa masaba, sabo da haka yake karantata yadda yaga dama.
5.    Karantata A Tsaye: Kenan ba'a karatun fatiha a zaune, sai dai idan mutum ba shi da lafiya saboda haka ba zai iya tsayawaba ko kuma saboda wani dalili shar'antacce to anana sai ya karantata a yadda ta sawwaka.
6.    Ruku'u: Wato sunkuyawa ba tare da ka daga kai ba ko kuma ka sunkuyar da shi ba, wannan yana daga cikin abinda ake koya a gaban malami ido-da-ido saboda sai a kusanci malumma.
7.    Tasowa Daga Ruku'i: Kenan bayan da mutum ya kammala zikiran da zai yi a ruku'I ba wucewa zai yi zuwa sujjadaba, a'a sai ya mike tsaye ya tsaya cur, sannan ya tafi zuwa sujjada. Amma yadda wasu suke yi da sun yi ruku'I sai su wuce sujjada kai tsaye ba tare da sun tasoba wannan laifine mai girman gaska.
8.    Sujjada: suddaja tana cikin farillan sallah kuma wajibine mutum ya yi ta kuma sujjdar sau biyu ake yinta akowacce raka'a. yadda ake yinta shine ka tabbata goshinka ya taba kasa da kuma karan hancinka da tafukan hannayanka biyu da kuma gwiwoyinka biyu sannan ka kafe yatsun kafafuwanka a kasa. Da yawa ana tafka kura-kurai a wurin sujjada, wani ko goshinsa baya sawa a kasa saidai hanci wannan bai yi sujjadaba, wani kuma tsakiyar kansa yake sawa, wani kuma maimakon ya kafe yatsun kafarsa sai ya daga kafafuwan sama, akwai kura kurai masu tarin yawa maganinsu shine yin kusa da inda ake karantarwa kodai inda kowa yake biya littafinsa ko kuma inda ake sa littafi abiya baki daya kamar bayan magariba ko bayan asuba ko bayan la'asar da dai yadda kowa yake sa lokacin karatunsa.
9.    Dakuma Tasowa Daga Sujjada: Wasu yadda tsuntsuwa ko kaza take cin abinci haka  suke yin sujjadarsu, kuma abinda ake Magana anan shine idan ka yi sujuda ka dago zaka zaunane tukunna sai dukkan gabbanka sun koma inda suke sannan ka koma zuwa sujjada ta biyu.
10. Daidaituwa: Shine mutum ya daidaita, wato idan yana tsaye kowa ya ganshi ya san yana tsaye haka idan yana ruku'i ko sujjada, kenan ya tabbata ko wacce gaba ta koma inda take kafin ya je zuwa ga wani mataki na gaba.
11. Natsuwa: Shine mutum ya tabbata ya natsu ya mayar da hankalinsa wurin sallah, banda soshe-soshe, ko wasa ko makamantan haka.
12. Jeranto Farillai: Wannan shima yana cikin farillan sallah ya kasance ka kawo su a jere, wato inda mutum zai yi sujjada sannan ya kawo ruku'i to hakan bai yi ba.
13. Sallama: Yin sallama farillane wato inda mutum zai gama salla amma bai yi sallamaba to sallar bata yi ba, domin bai kammala taba, kuma ga kadan daga yadda ake yin sallamar:
- Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah
- Assalamu Alaikum.
Kurakuran da ake samu a sallama suna da yawa, wani cewa yake yi: Salamma'alaikum, wannan kuskurene, kenan itama sai an koya daga bakin malamai domin ananne za'a banbance maka da sallamar da ake yi a sallah da kuma wacce ake yi lokacin gaisuwa.
14. Zama Domin Sallama: Kenan a zaune akeyin sallama ba'ayin sallama a tsaye, to wannan zaman da ake yi wanda ake.
Kammalwa: Daga wadannan bayanai da suka gabata mun fahimci cewa lalle ya kamata mu tashi domin gyara inda yake da kuskure a cikin farillan sallah, wadansu malaman suna sanya ‘Shigar Lokaci’ cikin farillan sallah sai ya zama shabiyar kenan, wasu kuma suna sanya shine cikin ‘Sharuddan Sallah’ kamar yadda bayanai suka gabata, da fatan Allah ya anfanar da mu wadannan bayanai, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
        

26 comments:

  1. Assalam, Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.yabo da junjina ya tabbata ga Annabi Muhammad (SAW) shugaban hallitu.
    Bayan haka INA mai godewa malam da ya rubuta wannan fatwa akan farillan sallah, haqiqa naji dadin wannan fatwa acikin harshen Hausa,INA kira ga malamai da sucigaba da yin fatwa kaman yadda malam yayi domin tanada matuqar amfani, sau dayawa zakaga mutane Na buqatar haske akan wani Abu Na addini amma bakasamun cikakken bayani to gaskiya naga an daukihanya mai ficewa . Allah yasaka da alkhairi.

    ReplyDelete
  2. Allah ya saka da alheri malam, ya kai ladan kabari.

    ReplyDelete
  3. Enter your comment...Allah Ya saka da alheri

    ReplyDelete
  4. Masha Allah. Allah yabada lada

    ReplyDelete
  5. Alhamdullilah! Jazakallahu khair

    ReplyDelete
  6. Remain me always in my religion

    ReplyDelete