Gabatarwa: wannan shine tsagi na
biyu na abubuwan da suke janyo ba’adiyyah a cikin sallah, ta fatan zamu kara
kusantar malamai.
Kokwanto:
Idan mutum ya yi
kokwanton sallarshi ta cika ko bata cika ba sai ya kawo abinda ya yi kokwanton
sannan ba’adiyyah, misali; Idan ya yi kokwanton shin ya yi sujjadar ta cika ko
bata cika ba, sai ka cika sannan ka yi ba’adiyyah.
Idan mutum ya yi
kokwanton wannan raka’ar itace ta hudu ko itace ta uku sai ya barta itace tau
kun sai ya kawo cikon ta hudun sannan ya yi ba’adiyyah.
Mutum mai yawan
wasuwasi to abinda da ake so daga gareshi shine yabar wasuwasin ya kakkabeshi
daga zuciyarsa ba zai kawo abinda ya yi kokwanton akanshi ba, sai bayan ya
sallame sai ya yi ba’adiyyah, shin kokwanton akan karine ko akan ragi. Wannan
yana nuna mana mafita daga mutanan da suke da yawan kokwanto da wasuwasi, Allah
ya yaye musu mu kuma ya tsaremu, amin.
Idan mutum ya yi
shakkun yana da hadasi ko bai da shi? Sannan sai ya dan yi tunani kadan sai
kuma ya samu tabbas akan yana da tsarki to ba komai akanshi, dudda ya yi hakan
ne a cikin sallah.
Yin rafkannuwa a
sallolin da ake ramakwansu daidaine da wadanda ake yin su cikin lokaci ba
banbanci, kenan suma kabaliyyah da ba’adiyyah tana shiga cikinsu.
Idan mamu ya yi
lafkannuwa alokacin yana bayan liman to liman ya dauke masa, misali; da aka yi
zaman tahiya na farko kawai sai ka yi sallama ka dauka an gama sallar, ko kuma
kuna sujjada sai ka ji wani ya yi kabbara sai ka taso daga sujjadar ka dauka liman
sai ka ga ba haka bane sai ka koma sujjadar duk bakomai akanka, saboda kana
bayan liman.
Idan masabuki
(wanda yake ciko sallarsa bayan sallamar liman) ya yi rafkannuwa a lokacin da
yake kawo raka’o’in da suka wuce masa bayan sallamar liman to fa anan
hukuncinsa hukuncin mai sallah ne shi kadai saboda haka ba’abinda liman ya
dauke masa domin tuni liman ya sallame shi, saboda haka idan kabaliyyah ta
kamashi a wannan lokacin sai ya yi ta hakama idan ba’adiyyah ce.
Idan kabaliyyah
ko ba’adiyyah ta kama liman to ta shafi mamu ko tare dashi abin ya faru ko ba
tare da shi bane.
Idan kabaliyyah
ta kamaliman to mamu zai yi tare da liman, sannan idan liman ya sallame sai ya
mike ya kawo ragowar raka’o’insa. Amma idan ba’adiyyah ce to bazaka yi tare da
liman ba har sai ka ciko ragowar abinda ake binka ka yi sallama sannan ka yi
ta, kasan dalilin da liman ya yi ta ko baka saniba.
Idan mutum
ba’adiyyah ta kamashi ta bangaran liman, sannan da ya tashi yana kawo abinda ya
saura akansa sai kuma kabalillah ta same shi to anan idan ya yi kabaliyyar ta
wadatar, ba sai ya yi ba’adiyyar ba.
Wanda ya yi
kokwanton ‘‘shin yanzu yana wuturine ko yana raka’a ta biyun shafa’ine’’?
to sai ya barta itace raka’a ta biyun shafa’in, sannan bayan ya sallame sai ya
yi ba’adiyyah sai kuma ya mike ya kawo wuturin.
Idan kuna sallah
tare da liman sai shi limamin ya yi rafkannuwa ta yadda ya yi kari ko ya rage
to mamu tasbihi zai yi, sai kace ‘’Subhanallahi’’, idan liman ya kara
sujjada ta zama uku to abinda zaka yi shine tasbihi ba zaka yi sujjadar ta uku
tare da shi ba.
Idan liman ya
tashi zuwa raka’a ta biyar to duk wanda ya tabbatar itace ta hudun sai ya
bishi, haka kuma duk wanda yake kokwanto; shin ta biyarce ko ta hudu, to shima
zai mike ya bishi. Amma duk wanda ya tabbatar wannan raka’ar itace ta biyar to
ba zai bi shi ba sai ya yi zamanshi.
Idan liman ya
sallame kafin sallah ta cika, to wadanda ke bayansa sai su yi masa tasbihi wato
su ce ‘’Subhanallah’’, idan liman ya gasgata wanda ya yi tasbihin sai ya
mike ya ciko sallar, sai kuma a yi ba’adiyyah, idan kuwa liman yana kokwanto
akan hakan, sai ya tambayi mutane biyu adilai, kuma ya halatta su yi Magana
anan, idan kuwa shi liman yanada yakini akan sallar ta cika to sai ya yi aiki
da yakinin na sa, ya ajiye tanbayar, saidai idan mutanen dake bayansa sun ta
tasbihi sai ya bar yakinin na sa, ya koma zuwa ga abinda suke a kai, kamar
yadda mai Akhdari ya zayyano.
Kammalawa: Wannan shine
gwargwadon abinda ya samu na bayani akan rafkannuwa a cikin salloli na farilla,
ko na ramuwa ko wadanda ake yin su a lokacinsu, da fatan zamu kara kusantar
inda malamai suke. Akaro na gaba da izinin Allah madaukakin Sarki zamu kawo
bayanaine dangane da rafkannuwa a cikin salloli na nafilfili. Ga dukkan mai
tambaya kofa a bude take, fatammu shine Allah ya karbi ayyukammu ya kuma sanya
mu cikin wadanda ya yiwa rahama.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Jazakallahu khairan
ReplyDelete