Gabatarwa: Ayanzu za’a kawo
bayanaine akan abubuwan da suke sanya ba’adiyyah kadai, da fatan Allah ya an
fanar da mu.
Manyan abubuwan da suke haifar da ba’adiyyah, abubuwane
kamar haka:
1.
Kari (Da mantuwa)
2.
Kokwanto
Wadannan sune manyan abubuwan da suke kawo sujjadar
ba’adiyyah, kuma akan su za muyi bayani a wannan karon da izinin Allah.
Idan mutum ya yi
kari a sallah da rafkannuwa ba wai daganganba to ba’adiyyah zai yi, kamar
mutumin da ya kara raka’a a asuba ta zama uku, ko a magariba ta zama hudu, ko
kuma a azahar ko la’asar ko kuma lisha ta zama biyar to hukuncinshi anan ya yi
sujjadar ba’adiyyah domin ya yi kari.
Haka mutumin da
ya kara sujjada a raka’a ta zama uku ko ya kara ruku’i ya zama biyu, amma da
mantuwa shi ma ba’adiyyah zai yi.
Wanda ya yi
Magana a cikin sallah da mantuwa shima ba’adiyyah zai yi, ko ya sallame daga
raka’a biyu da mantuwa, saida ya sallame ya tuna to anan sai ya ciko ragowar
raka’o’in sannan ya yi ba’adiyyah.
Wanda ya karanta
surori biyu ko sama da biyu a raka’a guda, ko ya fita daga surar da yake
karantawa zuwa wata surar ko kuma ya yi ruku’i kafi ya kammala karatun surar
duk anan ba komai akan shi, wato ba kabaliyyah kuma ba ba’adiyyah, haka kuma
wanda ya yi nuni da hannusa ko da kansa kuma yana cikin sallah, saidai yana
rage lada.
Wanda ya maimaita
karatun fatiha a raka’a duga da rafkannuwa to shima zai yi ba’adiyyah.
Amma wanda ya
tuna cewar bai karanta suraba bayan kuma ya sunkuya zuwa ruku’u to anan bazai
koma tsaye domin ya karantaba, saidai bayan sallama ya yi kabaliyyah, saidai
idan ya tuna asurtawane ko bayyanawa kafin ya yi ruku’i to anan zai sake
karatun, idan karatun surane zai sake karatunne ba wata kabaliyyah ko
ba’adiyyah, amma idan karatun fatihane zai sake din amma kuma zai yi
ba’adiyyah.
Wanda kuma ya
mike bayan ya yi raka’a biyu amma kuma bai zauna ba sai ya tuna kafin
hannayansa da gwiwowinsa su bar kasa shikenan sai ya koma ya zauna ba komai
akansa, in ko ha ya rabu da kasane to sai ya ci gaba ba zai dawo ya zaunaba
saidai zai yi kabaliyyah domin ya rage wani abu a sallarshi, idan kuma bayan ya
mikedin ya dawo ya zauna bayan kuma ance da shi ya wuce to anan sallarshi ta yi
sai dai zai yi ba’adiyyah ne saboda ya yi kari na wannan mikewar.
Wanda ya yi
atishawa a cikin sallah baya cewa ‘’Alhamdu Lillah’’ idan kuma har ya
fadadin sallah shi nanan kuma ba komai akanshi, sannan kuma baya maida gaisuwa
ga wanda ya gaida shi saboda yana cikin sallah.
Wanda kuma ya yi
hamma yana cikin sallah sai ya rufe bakinsa shikenan.
Wanda kuma ya sa
wata kalma alokacin da ya karatu wacce ba ta Kur’ani ba zai yi ba’adiyyah ne,
amma idan ta Kur’anice babu komai akanshi, saidai idan ya canza lafazi ko ya
bata ma’ana to anan sai ya yi ba’adiyyah. Lalle wadannan bayanai za su sa
mutsaya mu gyara karatummu na sallah da kuma limamammu, domin ana tafka
kurakurai a karatuttukan sallah.
Amma kuma wanda ya
manta da ruku’i saida yana sujjadah ya tuna to sai ya koma tsaye, sannan an so
ya sake wani abu na karatun sallah, sannan sai ya yi ruku’in ya kuma ci gaba da
sallar, bayan ya kammala sai ya yi ba’adiyyah.
Sannan wanda ya
manta sujjada guda bai yi ta biyun ba, saida ya mike sannan ya tuna to kawai
zai dawo ya zaunane sannan ya yi wannan sujjadar, saidai idan ya yi wannan
zaman kafin ya mike to kawai sai ya wuce zuwa gabatar da wannan sujjadar
kai-tsaye, bayan ya kammala saii ya yi ba’adiyyah.
Wanda kuma ya
manta da sujjadu biyu sai bayan ya mike sannan ya tuna to kawai zai tafi zuwa
gabatar da wadannan sujjadunne ba tare da ya zauna ba, sannan ya yi ba’adiyyah.
Kammalawa: Adaidainan zamu
dakata kan abinda ya shafi yin ba’adiyyah ta sanadiyyar kari da mantuwa, a karo
na gaba bayanai za su zo akan ba’adiyyah ta sanadiyyar kokwanto, da fatan mun
anfana.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
casino-how to play with bitcoin - DRMCD
ReplyDeleteI've seen bitcoin gambling play online for 당진 출장마사지 many years, so 창원 출장안마 I decided to take a break 서귀포 출장마사지 to play games for cash. My 군산 출장안마 first time 동두천 출장안마 playing at a casino in