Shinfida:
Su
sunnonin sallah su ne ke biye da farillan sallah wurin matsayi a cikin sallah,
saboda haka kamar yadda bai kamata ka yi wasa da farillan sallah ba to haka
yake bai kamata ka yi wasa da sunnonin sallah ba. Wasu da zarar sun ji ance abu
kaza sunna ne to basa daukan shi da girma domin suna ganin rashin sa ba zai
hana musu sallah ba, alhali kuwa wannan kuskurene mai girman gaske, ai ko ba’a
sallah ba duk abinda ka ji an ce sunnane to bai kamata ka yi wasa da shiba.
Su wadannan sunnoni na sallah kamar yadda
bayani ya gabata matsayinsu baikai na farilla ba domin idan ka bar farilla daya
a raka’a sai dai ka ajiye wannan raka’ar ka kawo wata makwafinta kamar yadda
bayanai za su zo da izinin Allah a lokacin bayani kan kabaliyyah da ba’adiyya.
Kennan su sunnonin sallah ba haka bane, idan mutum ya cika su to sallar shit a
cika, idan ko bai cika su ba to sallar shi bata cika ba ko da ko ba zai sake ta
ba. Saidai su sunnonin sallah asune ake samun damar kyaran sallah ta hanyar yin
kabaliyyah ko ba’adiyyah, amma ita farilla ba’a yi mata hakan.
Sunnonin Sallah: su
sunnonin sallah suna da yawa, sun fi farillan sallah yawa, ga kadan daga cikin
su:
1.Tada
Ikamar Sallah: Ita ikamar sallah ta shafi mai sallah shi
kadai ko wadanda za su yi ta cikin jam’i, kuma bayananta sun gabata a Babi Na
shabakwai (017).
2.
Karatun Sura Bayan Fatiha: Kasancewar shi karatun Fatiha yana
cikin farillan sallah to yanzu shi karatun sura bayan fatiha yana cikin
sunnonin sallah ne, kuma wadannan bayanai sun shafi maza da matane baki daya,
domin duk abinda aka umarci maza da shi an umarci mata das hi saidai abinda
shar’a ta ware tace banda mata. Kuma mutum ya tashi ya koyi karatun sallah daga
bakin malamai. Sannan mu sani shi karatun sura bayan fatiha ana yin shi ne a
raka’o’i biyun farko, kenan banda na karshe, kamar haka: Asuba ana yi a duka
raka’o’in, Azahar ana yi ne a raka’o’I biyun farko banda biyun karshe, la’asar
ma haka, haka namma magariba banda dayar karshe, sannan ita ma isha banda biyun
karshe.
3.
Tsayuwa Domin Karatun Sura: Kenan kamar yadda karatun surar yake
sunnane to hakama yin karatun a tsaye, kenan ba’a karatun sura a zaune sai dai
idan akwai larura da shari’a ta yadda da ita.
4.
Sirrantawa A Inda Ake Sirrantawar: Abinda ake nufi da
sirrantawa shine ka motsa harshe domin yana furta karatun Alkur’ani, wato
bakinka na motsi kenan, amma idan mutum ya yi shiru yai dunkum ba’a kiran
wannan asurtawa. Inda ake surrantawa kuma sune: Azahar da la’asar bakidaya
raka’oinsu, sai kuma raka’ar karshe ta magariba da kuma raka’oi biyun karshen
Lisha. Haka kuma nafilfilin rana suma ana asurta su ne.
5.
Bayyanawa A Inda Ake Bayyanawa: Idan kuma akace bayyanawa
ana nufin ka jiyar da kanka da kuma wanda yake kusa da kai, wannan idan kai
kadai kake sallah kennan, amma idan kai limanne to zaka daga murya yadda kowa
zai ji, ai domin karatun limanne aka hana mamu su yi na su karatun.
Kuskuren da ake samu anan shine, idan mutum
ya shigo masallaci zai yi sallah ko kuma ya mike yana ramo raka’o’in da suka
wuce shi sai ya bude baki yana karatun sallah da karfi, wanda wannan yana shiga
cikin karatun wani, yana kuma hargitsawa wani nashi karatun, inda kowa zaibi
yadda bayan suke to da an yi komai cikin jin dadi da walwala, zuwa inda ake
karatu shi zai magance wadannan matsalolin.
Wuraran da ake bayyana karatun sallah kuma
sune kamar haka; Karatun sallar asuba baki-dayanta, raka’ar karshe ta sallar
magariba, da kuma raka’o’in karshe na sallar lisha.
6.
Kabarbari: Dukkanin kabarbarin sallah sunnane in banda kabbarar farko
wacce take ita farillace wato kabbarar harama. Saidai malamai sun karawa juna
sani akan cewa; shin dukkanin kabarbarin a dunkule suke sunnan guda koko
kowacce kabbara sunnace mai zaman kanta?.
7.
Tahiyyah: Itama tana cikin abinda ya kamata mutum ya koya daga
bakin malami kai tsaye, yana karantawa kana karantawa, domin ana samun kura
kurai masu tarin yawa a lokacin mutane suke karantata.
8.
Zama Domin Tahiyyah: Ashe itama ba’a yinta a tsaye, kuma inda
mutum zai zauna amma bai karantata ba to yabar sunnah guda daya, idan kuma ya
manta bai yi zaman farkoba misali to yabar sunnoni biyu kenan, karatun tahiyyar
da kuma zama domin karatunta.
9.
Gabatar Da Fatiha Kafin Surah: Inda mutum zai zai fara
karanta surah sannan ya zo ya karanta fatiha to da ya bata tsarin sallah, domin
yadda ake so shine ka fara gabatar da fatiha sannan ka sai ka karanta surah.
10.
Bayyanar Da Sallama: Kenan ita sallama ba’a asurce ake yenta ba,
ana bayyana tane, anan mu ban-bance shi yin sallamar wajibine, amma yenta kuma
a bayyane sunnane daga cikin sunnonin sallah.
11.
Salati Ga Ma’aikin Allah: Yin salati ga manzon Allah –tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi- yana daga cikin sunnonin sallah. Kuma shi
salati ga ma’aikin Allah yana da muhimmanci da lada da kuma falala mai zaman
kanta, malamai sun kawo sigogi na salati ga ma’aikin Allah a kicin littafansu
kamar mai littafin Ashmawi ya kawo haka nan ma mai littafin Iziyyah da kuma mai
Risalah, mafi kyawun littafi da aka rubuta domin bayanin salati ga ma’aikin
Allah shi kadai, shine littafin ‘Jila’ul Afham’, zaka same a
shagunan da ake sayar da littafan musulunci.
12.
Suturah: Duk wanda yake sallah shi kadai ko shine liman to anan
ana bukatar ya sanya suturah a gabanshi, domin baiwa mai wucewa damar wucewa ta
bayan suturar, amma shi mamu baya sanya sutura domin suturar liman ta wadatar
masa, saboda haka idan kuna sallah da liman sai wani ya wuce ta gabanku babu
komai inda ba ya wuce ta tsakanin liman da suturarshi bane.
Kammalawa: Adaidai nan zamu da
katata, dafatan wadannan takaitattun bayanai sun wadatar, sannan kuma zamu ci
gaba da kara kusantar malumma. Kula da wadannan ayyuka a cikin sallah bakaramin
aiki bane, domin shi ke sa mutum ya samin dandano na zakin sallah, domin ya
bata kulawa ta hanyar lura da farillanta da kuma sunnoninta, dudda cewa anan
kadan muka kawo, a karo na gaba zamu kawo bayanaine akan Mustahabban Sallah,
sai Allah ya kai mu.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Jazakallahu khairan.Malam ina kara mika kokon baran Neman Karin sanin sauran Sunnonin Sallah.ko da kuwa a kasida ta gaba a sanyo mana sauran iya Gwargwado.Allah shi taimaka ya Kuma sa muyi tarrayya alada amin Thumma amin.
ReplyDelete
ReplyDeleteMasha Allah
Allah ya saka da alheri
ReplyDeleteGaskiya naji dadin wannan bayanin, Allah yasa mudace
ReplyDeleteAllah ya saka wa Malam da mafificin Alkhaeri. Ya kuma sa mu gama da duniya lfy. Akramakallah mun ji dadin kasancewa da wannan karatun. Allah ya saka da gdn Aljannah
ReplyDelete