Shinfida: Su wadanann abubuwa
su malamai suke kira ‘Makruhatus Salah’ wato abubuwan da ba’a so
ayi su a cikin sallah, domin yinsu yana matukar ragewa mutum ladan sallarsa,
dudda sallar bat abaci ba ta yadda za’a ce sai ya sake, kuma ba zai yi
kabaliyyah ko ba’adiyyah saboda ya yisu ba, saboda haka sai a kiyaye kada mutum
ya yi wasa da sallarsa, Hssan dan Atiyyah yake cew: ‘’Lalle mutane biyu za
su iya kasancewa a cikin sallah guda, amma tazarar dake tsakaninsu na falala ya
fi nisan sama da kasa’’.
Lalle wannan ba
karamar Magana bace indai har mutane biyu za su kasance a sallah guda bayan
limami guda amma banbancin dake tsakaninsu ya dara tazarar dake tsakanin sama
da kasa, to kan lalle bakaramin banbanci bane, sannan tambaya anan itace: Me ya
janyo wannan banbanci na falala?.
Natsuwa kwantar
da hankali kankar-da-kai, da kuma sanin me mutum yake yi da nisantar abinda
ba’a so mutum ya yi a cikin sallah, wadannan kadanne daga cikin abubuwan da za
su banbanta falalar masallata, ga kadan daga cikin abubuwan da ba’a so a yi su
a cikin sallah:
1.Waiwaye: Shi waiwaye ya kasu
kasha buyu; Kashi na farko shine ‘waiwayen zuciya’ wato zuciyar mai sallah ta
kasance ba anan take ba ta kada ta yi wani wuri, wannan nau’i na waiwaye yana
matukar rage ladan sallah, saboda haka kullum sai ka yi kokarin hana zuciyarka
tafiya wani wuri lokacin sallah. Waiwaye na biyu shine ‘waiwayen jiki’ wato
mutum ya tunga waige yana sallah, ya waiga dama ya kuma waiga hagu, wani
lokcimma ya daga kai sama, Allah ya sawwake.
2. Rufe Ido: Ida
nana sallah bude idanuwa ake yi ba’a rufesu domin rufe idanuwa ba’a ibada dashi
a musulunci.
3. Tsayawa Akan Kafa Guda:
Wani ida yana sallah sai ya bada karfinsa akan kafarshi guda, wani ya dauki
kafar ya dorata akan dayar, wannan ba’a son shi a cikin sallah. Saidai malamai
sukace idan tsayuwarce ta yi tsawo to wannan ba komai.
4. Hada Kafafuwa:
Wasu idan suna sallah sai su hada kafafuwansu maimakon su ware su, wannan hada
kafafuwa da suke yi kuskurene a sallah, saboda haka kullum a dinga kusantar
malamai domin sanin hukunce-hukuncen sallar nan.
5. Tunani Akan Duniya:
Abinda ake so idan kana sallah ka dainga tunani kan ayoyin da kake karantawa a
sallar ko limaminku yake karantawa. Wannan zai sa ba zaka shiga cikin tunanin
duniyaba, kada ka manta shaidan a koda yaushe so yake ya samu rabonsa a
ibadarka, domin kuwa wani tunanin bai zuwa maka sai ka fara sallah, saboda haka
kai kuma ka nemi taimakon Allah akan ba zaka bashi wannan damarba.
6. Kin Kashe Waya: Kin
kashe waya yana cikin abubuwan da suke ragewa mutum ladan sallar shi, domin ta
yi kararnan tana dauke hankalinka da na liman da na sauran masallata ashe
bakaramin hatsari bane kin kashe waya a lokacin sallah. Abinda ake so anan
shine da zarar ka kama hanyar masallaci ana rubuta maka ladane saboda haka sai
ka kashe wayarka ka fara tanadarwa kanka natsuwa, koda kana cikin sallah sai ka
tuna baka kashe wayarkaba ya halatta ka cirota ka kashe, ko ka ji an kira wani,
shi yasa malamai sukace ‘’Da nisantar dukkan abinda zai shagaltar das hi
daga barin anboton Allah’’. Wato ya bar duk abinda zai hana mishi wannan.
7. Kaya A Aljihu:
Hakanan ba’a bukatar mutum ya zuba kaya a cikin aljihunsa wanda zai iya daukar
hankalinsa ya shagaltar da shi, wani sai ya cika aljihunshi da mangwaro ko lemo
ko wayoyi ko mabudan kofa, abinda ake Magana akai shi fa masallaci yana gaban
Ubangijine saboda haka ake bukatar ya samu cikakkiyar natsuwa.
8. Motsa Yatsu: Shi
kuma wani yana sallah yana motsa yatsunsa sunawa; kas,kas, wani kuma yana ta
wasa da gemu ko a gogo ko ya cire hula, wani kuma hannunsa yake sawa a kugunsa,
wanda yake kamar yadda bayanai suka gabata shaidan yana son sai ya rage maka
ladan sallarka ne.
9. Bayan An Kawo Abinci:
Hakanan an fi so ka ci abinci idan har an kawoshi kafin ka fara sallah musamman
idan kana matukar son ka ci abincin, amma wannan bas hi ke nuna cewa ‘Ci na
gaba da sallah ba’.
10. Ware Wani Abu Domin Yin Sujjada Akan Shi:
Kuma ba’a so mutum ya ware wani abu ya zama akan shi zai dinga yin sujjada
domin yin haka koyine da masu bin addinin Shi’a, kuma ba’a yarda kai ka yi ko
yi da su ba.
11. Share Hannu Ko Hanci:
Ba’a so ba aduk lokacin da ka yi sujjada ace sai ka share hannuwanka da kuma
hancinka a lokacin da kake cikin sallah, amma idan bayan ka idar da sallar ne
to wannan ba komai.
12. Inda Yake Da Hotuna:
Hakanan an kyamaci ka yi sallah a inda yake da hotuna an manna su a bangone ko
an jingine su ne, domin hakan ko yi ne da masu bautar gumaka, kuma ko yi ne da
Nasara.
13. Shinfida Hannu:
Kuma ba’a so a lokacin da kake sujjada kamar yadda kare yake shinfida
hannuwansa, abinda ake so shine ka shinfida tafukan hannuwanka.
14. Rashin Natsuwa: Ba’a so mutum ya fara sallah alhalin
bai natsuba, saboda haka kada ya fara sallah yana mai matse tusa, ko fitsari ko
bayangida ko kuma matsanancin kishin ruwa da matsananciyar yunwa.
Kammalawa: Wadannan bayanai sun
nuna mana cewa lalle mu tashi tsaye domin cire rabon shaidan daga cikin
ibadarmu, Allah Ya taimaka mana.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
No comments:
Post a Comment