Shinfida: Su kuma mustahabbai
su ke biye da sunnoni awurin falala da daraja, suna da ban-bance ban-bance a
hukunci lokacin da mutum ya bar daya daga cikin su, idan mutum ya abinda
farillane a sallah to sallar bata yi ba, kuma abin ya fi karfin ba’adiyya ko
kabaliyyah. Amma idan sunnah daga cikin sunnoni ya bari to anan ne za’a yi
kabaliyyah ko ba’adiyya ba sai an sake sallar ba. Sannan kuma idan mustahabi ya
bari to sallar shi nanan kuma ba ba’adiyyah sannan kuma ba kabaliyyah, ashe
kenan yana da matukar muhimmanci kowannen mu ya zama ya rike abubuwan da suke
farillaine a sallah ko mustahabbaine ko kuma su sunnonine.
Mustahabban
Sallah: Suma mustahabban suna da yawa, kuma matsayinsu a sallah ba karamin
matsayi bane, ga kadan daga cikin su:
1.Daga Hannuwa Lokacin Kabbarar Harama:
Alokcin da mutum zai yi kabbarar harama ana bukatar ya daga hannayansa su zama
sun yi kafada da kunnuwansa, kuma yatsun hannuwan sun mike sama.
2. Fadin Aameen:
Alokacin da ka kammala karanta fatiha ko liman ya kammala sai kace amin, inda
mutum zai manta bai fadi amin din ba sallar shi nanan ba kuma zai yi kabaliyyah
ko ba’adiyyah ba, saidai ya yi asarar dinbin ladan da ake samu.
3. Tasbihi A Ruku’u:
Haka shima yin tasbihi wato tsarkake Ubangiji a ruku’i yana cikin mustahabban
sallah, akwai sigogi na wannan tasbihi daban-daban zaka sami wasu daga cikinsu
a littafin ‘Hisnul Muslim’ ana samunshi a shagunan sayar dalittafan musulunci,
akwai wanda fassarashi zuwa Hausa da Ingilishi…’’.
4. Addu’a A Suddaja:
Haka kuma yin addu’a a lokacin sujjada yana daga cikin mustahabban sallah, kuma
anan nake cewa musani asujjada ne mutum ya fi kusa da Ubangiji saboda haka kada
mutum ya yi wasa wurin yin addu’a.
5. Tsawaita Karatu: An
fi so a tsawaita karatun sallah a sallolin Asuba dana Azahar, kuma an fi so
karatun sallah araka’ar farko a asuba ya fi karatun raka’a ta biyu tsawo, shi
kuma karatun raka’a ta biyu a sallar asuba ya fi karatun raka’ar farko ta
azahar, shi kuma karatun raka’a ta biyu a sallar azahar kada ya kai tsawon
karatun raka’ar farko ta azahardin.
An ruwaito cewar
Umar dan Khattab Allah ya kara masa yarda yana karanta Suratu Yusuf da Suratu
Hajj a sallar asuba, amma ai an fatane a farkon lokaci, kuma dudda haka ana
la’akari da halayan mamu ta bangaren tsufa da masu hanzari…’’.
6. Takaita Karatu:
Kuma an fison takaita karatun sallar la’asar da kuma magariba. Wanda yake shi
kuma karatun sallar lisha anfison a yi shi tsaka-tsakiya wato shi bad a tsawoba
kamar asuba da azahar ba kuma takaitacceba kamar la’asar da magariba, wannan ya
zama dole ga limammu ya zama suna la’akari kuma suna samun bita ta musamman
akan abinda ya shafi limanci, domin shi limanci abune da yake bukatar ilimi da
natsuwa da kuma fahimta, Allah ya sa mu dace ya kuma sakawa limamammu da
alheri.
7. Jeranta Surori: Ana
bukatar lokacin karatu a sallah ya zama an jero karatun surorin a yadda suke a
Kur’ani, ma’ana idan ka karanta Surah ta goma a raka’ar farko kuma kana so a
raka’a ta biyu ka caza Surah sai ka karanta daga ta shadaya zuwa sama ba wai ka
koma ka karanta ta tara ko ta shida ba, misali; Idan ka karanta ‘Alam tara
Kaifa’ a raka’ar farko to a raka’a ta biyu sai ka karanta Li’ilafi zuwa karshen
Kur’ani duk surar da ka zaba ka karanta ya yi, mai makon ka koma ka karanta ‘Wal’Asri’.
Sannan ko da mutum ya yi sabanin hakan sallar shi ta yi, saidai ya yi abinda ba
shi akafi so ba.
8. Addu’a Bayan Tahiyyah Ta Biyu:
Yana daga cikin abinda ake so ka gabatar bayan ka kamma Tahiyah kuma ka yi
salati ga ma’aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- kuma ka
nemi tsari daga wadannan abubuwa hudu wato; Azabar Jahannama da kuma Azabar
Kabari da Fitinar Rayuwa da Mutuwa da kuma Fitina Jujal. Sai kuma ka gabatar da
addu’oinka kafin sallama.
9. Damaita Sallama:
Abin nufi anan shine ka kada fuskarka kadan bangaren dama sai ka yi sallama,
shi ne ma’anar damaita sallama, amma wasu limaman sai bayan sun karanta fatiha
sai su dan yi rangaji kadan bangaren dama da hagu wannan tsan-tsar kuskurene a
sallah.
10. Motsa Yatsa Lokacin Tahiyyh:
Yana cikin mustahabban sallah a loakcin da kake yin tahiyah ka dinga motsa
yatsanka wanda yake shine ‘Yar manuniya’.
11.
Karatun Sallah: Ma’ana anan yana cikin musta habban sallah
idan liman yana karun sallah a asirce kai ma karanta, amma idan yana yi a
sarari sai ka yi shuru.
Kammalawa: Wadannan sune kadan
daga cikin mustahabban sallah, wanda yake cika su bayan cika farillai da
sunnoni yana da matukar girma da falala da kuma Karin lada, sannan kuma barin
su yana rage ladan sallah, dudda ba za’a yi kabaliyyah ko ba’adiyyah, Allah ya
karba mana ibadummu.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
ALLAAH YA SAKA DA ALHERI
ReplyDeleteMuna godiya Allah yasaka amin
ReplyDeleteAllah yasaka da alkhairi
ReplyDeletemuna rokon Allah yasa muyi aiki da wannan karatu Allah ya saka da alkairi yayi albarka...
ReplyDeleteMuna fata wannan yazama sanadiyyar shigan mu aljannah baki daya
ReplyDelete