Gabatarwa: Ayanzu za’a kawo
bayanaine akan abubuwan da suke sanya kabaliyyah kadai, sannan bayan haka a
kawo bayanai akan abubuwan da suke sanya ba’adiyyah suma su kadai, fatammu a
tsaya a karanta bayanan a natse kuma a fahimcesu, idan akwai abninda ya shigewa
mutum yana da dama ya yi tambaya, da fatan Allah ya ganar da mu.
Abubuwan Da Suke Kawo Kabaliyyah:
Manyan abubuwan da ke sawa a yi sujjadar Kabaliyyah su ne;
1. Ragi.
2. Ragi
Da Kari.(Alokaci guda)
Dukkan mutumin da ya yi ragi a sallar sa to kabaliyyah ta
kamashi, kamar:
1. Karatun Sura:
Idan mutum ya manta a raka’ar farko ko a ta biyu bai karanta suraba kawai shi
da ya karanta fatiha sai ya yi sujjada, to wannan kabaliyyah ta kamashi.
2. Asurtawa A Inda Ake Bayyanawa: Duk
wanda ya yi karatun sallah sirrance a inda ake bayyanawa, to wannan shima
kabaliyyah ta kamashi.
3. Fadin ‘’Sami’allu Liman Hamidah’’
haka wanda ya manta da fadin wannan kalma kabaliyyah zai yi domin rage.
4. Tahiyar Farko: Duk
wanda ya barta to ya yi ragi a sallarsa kabaliyyah zai yi.
5. Zama Domin Tahiyyar Farko:
Haka duk wanda ya manta da zaman tsakiya shima kabaliyyah zai domin ai shi ya
rage manyan sunnonine ma guda biyu. Zama domin tahiyyar da kuma ita kanta
tahiyyar.
6. Tahiyyar Karshe:
Itama dukkan wanda ya manta bai yi ta ba to kabaliyyah ta kamashi.
7. Zama Domin Wannan Tahiyyar Ta Karshe:
Shima zaman duk wanda ya manta ya barshi to kabaliyyah zai yi. Kada ku sha’afa
zaman da ya karu akan gwargwadon sallama shine ake Magana, amma shi zama gwargwadon
sallama wannan wajibine, idan mutum ya barshi kabaliyyah ko ba’adiyyah bata
daukeshi.
Sannan dukkanin
wadannan abubuwa da aka bari, ana maganane idan akabarsu da mantuwa ba wai
daganganba.
Ragi
Da Kari. (Alokaci guda)
Hakanan dukkan mutumin da ya yi ragi a cikin sallah kuma
ya yi kari a cikin sallar to shima kabaliyyah zai yi, misali mutumin da ya
manta bai yi zaman farkoba wato da ya kammala raka’a biyu maimakon ya zauna ya
yi tahiyyah sai ya manta ya mike zuwa raka’a ta uku, sannan kuma da ya raka’oin
mai makon ya zauna sai ya ci gaba ya kara wata raka’ar ta zama hudu idan a
magaribane ko ta zama biyar idan a azaharne ko la’asar ko lisha. To ka ga
wannan a sallah guda ya yi ragi domin bai yi zaman farkoba kuma ya yi Karin
raka’a to shima kabaliyyah zai yi shikenan ya gyara sallar shi.
Wanda sujjadar
kabaliyyah ta kamashi amma sa ya manta bai tuna ba sai bayan da ya yi sallama,
shikenan sai ya yi ta a wannan lokacin ta zama ba’adiyyah kenan kuma sallar ta
yi, to amma idan bai tuna da hakanba sai bayan wani lokaci ko ma har ya fita
daga masallaci to anan sujjadar ta baci, haka itama sallar zata iya baci idan
ya rage sunnonin da suka kai uku ko sama da haka.
Rafkannuwar da
mamu ya yi alokacin yana bayan liman to liman ya dauke masa, saidai idan mamun
ya rage farillane kama ya bar sujjada, ko sallama..’’.
Idan mamu ya yi
rafkannuwa ko ya yi gyangyadi ko ma aka matse shi bai sami damar yin ruku’i ba
sannan kuma ba’a raka’ar farko bace to anan idan ya tabbatar zai iya samin
liman kafin ya dago daga sujjada ta biyu ta wannan raka’ar sai ya yi ruku’in ya
riski limamin, amma idan ya tabbata ba zai same shi ba, sai ya bar ruku’un,
wannan raka’ar kuma sai ya ajiyeta gefe guda sai ya rama wata raka’ar a
matsayin wannan din bayan sallamar limamin nasa, babu kabaliyyah ko ba’adiyyah.
Idan kuma ya yi
rafkannuwane ya bar sujjada ko aka matseshi ko ya yi gyangyadi har liman ya
tashi zuwa wata sabuwar raka’ar to anan idan ya tabbatar zai riski liman kafin
ya yi ruku’i sai ya yi sujjadar, amma idan ya tabbata ba zai iya riskar liman
ba sai kawai ya hakura ya ci gaba da bin limamin sai ya rama raka’ar da bai yi
mata sujjada ba, bayan liman ya sallame.
Kada mutum ya yi
mamaki ya ji an ce ‘an matse shi’ ka dauki al’amarin da fadi bawai iya
garin ku ba, domin idan Allah ya kaika kasa mai tsarki zaka ga irin cunkoson da
ake yi alokutan sallah, musamman idan ya yi daidai alokacin Hajji ka je ko
Umarah.
Kammalawa:
Wadannan kadan kenan daga cikin abubuwan da suke sabba sujjadar Kabaliyyah, da
mun anfana kuma zamu kara kusantar malamai, a karo na gaba za’a kawo bayanaine
akan abinda ya shafi sabuban sujjadar ba’adiyyah, da fatan Allah ya kai mu
lokacin ta re da imani, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
No comments:
Post a Comment