Gabatarwa: Ayanzu da izinin
Allah muna son mu kawo bayanaine da suka shafi sujjar rafkannuwa wacce ake kira
Kabaliyyah ko ba’adiyya da fatan Allah ya anfanar da mu da wadannan bayanai,
kuma ya sanya ya zama sanadiyyar tsira duniya da lahira.
Wadannan bayanai
za su kunshi me ake nufi da sujjadar rafkannuwa ko mecece kabaliyyah sannan
mecece ba’adiyyah, sannan a kawo bayanai na abinda ke sabbaba wadannan sujjadu.
Sujjadar Rafkannuwa: Sujjadune
guda biyu da mutum yake yinsu bayan ya kammala sallah kafin sallama ko bayan
sallama saboda kari ko ragi ko kokwanto da ya yi a cikin sallah.
Wannan ta’arifi
da ya gabata ya fayyace mana me ake nufi da sujjadar rafkannuwa kuma ya yi
bayanin abinda yasa ake yenta da kuma lokacin da ake yenta da kuma dadi nawa
ake yi.
Kabaliyyah: Sune sujjadu biyu
da ake yi bayan tahiyyah kafin sallama, kasancewa ana yinta kafin sallama shi
yasa ake kiranta kabaliyyah wato ‘Kabals Salam’.
Ba’adiyyah: Sune sujjadu biyu da
ake yi bayan an sallame daga sallah, saboda ana yinsu ne bayan an yi sallama
shi yasa ake kiranta da ba’adiyyah wato ‘Ba’das Salam’.
Yadda Ake Yin Kabaliyyah/Ba’adiyyah:
Idan saujjadar kabaliyyah ta kamaka to kada ka manta zaka yi ta ne bayan ka
kammala tahiyyah ta biyu wato ka karanta tahiyah kuma ka yi salatin Ma’aikin
Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- sannan ka nemi tsari daga
abubuwa hudunnan ya kallama addu’oinsa, ba’abinda ya rage masa sai sallama to
sai ya yi kabbara zuwa sujjada sannan sai ya dago tare da kabbara sannan sai ya
sake komawa sujjadar tare da kabbara sannan sai ya sake dagowa tare da kabbara
sai ya yi tahiyah sai ya sallame.
Idan kuma
Ba’adiyyace to zai yi wadannan sujjadune tare da bakarbarinsu bayan ya sallame
daga sallah, sannan sai ya sake yin tahiya ya yi sallama.
Abubuwan Dake Sa Sujjadar Rafkannuwa:
Abubuwan da suke haifar da sujjadar rafkannuwa wato kabaliyyah ko ba’adiyyah a
dunkule malamai sukace abubuwa guda uku:
1. Kari.
2. Ragi
3. Kokwanto.
Idan mutun ya yi kari a sallarsa, misali sallah mai
raka’a biyu sai ya kara da mantuwa suka zama uku to anan sujjadar rafkannuwa ta
kamashi.
Haka kuma mutum
da ya yi ragi, misali mutuminda ya manta bayan ya yi raka’a biyu sai bai zauna
ya yi tahiyaba sai ya mike, ka ga anan ya rage zaman tahiyyah.
Hananma mutum da
kokwanto ya samishi alokacin yana cikin sallah, misali mutumin da yake kokwanto
wannan raka’ar da yake yi itace ta uku ko itace ta hudu? Ya riga ya rikice bai
san wacce yake ciki ba, to shima wannan sujjadar rafkannuwa ta kamashi, saboda
haka da izinin Ubangiji zamu kawo muku bayanai na wadannan abubuwa da suke
haddasa rafkannuwa da irin sujjadar da za’a yi wa kowanne nau’i. Kada ka manta
ba’a sallame sallah domin a sakota daga farko saboda ka rikice a cikinta, a’a
abinda ake so shine ka gyarata, bawai ka sallame ka sakeba, saidai a inda akace
sallah ta baci.
Kammalawa: Dafatan mun fahimci
inda aka sa gaba domin anan an kawo bayananne a dunkule, musamman kan abinda
ake nufi da sujjadar da kuma yadda ake yenta da sabuban da suke janyota, da
izinin Allah a nan gaba zamu kawo bayanai akan abinda yake janyo kabaliyyah a
fayyace, kuma a babi mai zaman kansa, sannan mu kawo kuma akan abinda yake
janyo ba’adiyyah shima a babi mai zaman kansa. Da fatan Allah ya kaimu lokacin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Jazakumullahu khair
ReplyDeleteJazakumullahu khair
ReplyDeleteAllah ya saka da mafificin lada Akramakallah
ReplyDelete