Tambihi: Bai halatta mutum
yana cikin hankalinsa ya bari lokacin sallah ba tare da ya gabatar da ita iba. Ayanzu
za'a kawo bayanaine akan abinda ya shafi ramuwar sallar da ta wuce ko sallolin
da suka wuce tare kuma da neman gafarar Allah, ya Allah ka gafarta mana. Sau
dayawa sakaci da ko'inkula shi ke sa mutum ya bar salloli su wuce, wata sai
bayan ta yi aure take cika sallah, alhalin sallar ta wajaba akanta tun lokacin
da ta balaga wato tun lokacin da ta fara ganin jinin al'ada ko ta fitar da
maniyyi...' haka ma maza wasu sai sun yi aure, wanda wannan kuskurene.
Su dai sallolin da suka wucewa mutum, kodai
su wuce masa yana halin tafiya ko kuma yana halin zaman gida.
Idan sallolin sun wuce masa yana halin
tafiyane to zai ramasu a yadda mai tafiya yake sallolinsa kodako yanzu yana
gidane, wato zai ramasu raka'a biyu biyu
azahar da la'asar da lisha.
Idan kuma sun wuce shine alokacin zaman gida
to zai ramasune raka'oi hudu hudu sawa'un yana halin zaman gidane lokacin
ramuwar ko yana halin tafiya, kenan kowacce sallah za'a ramatane a yadda ta
wuce, wato lokacin da ta wuce ake la'akari da shi ba lokacin da za'a ramaba.
Yadda Ake Rama
Salloli:
Idan ana bin mutum salloli hudu ko abinda bai
kai huduba to sai ya gabatar da sallolin da ake binsa kafin ya yi wacce ake
cikin lokacinta, jerantosu a haka wajibine.
Amma idan sallolin da ake binsa sunfi hudu
to anan kawosu a jere tare da wacce ake cikin lokacinta bai zama dole ba, ya
samu ya gabatar da wacce ake cikin lokacinta sannan ya kawo sallolin da ake
binsa.
Kada mu manta dukkan wanda yasa ana binsa
salloli mace ko namiji wajibine ya tashi tsaye domin biyan wadannan salloli da
suke a kanshi, domin ya sani shi kadaine zai iya biyansu babu wanda zai biya
masa ko bayan ya rasu, wannan sallah ba karamar ibada bace. Hakanan su sallolin
da ake bin mutum su zai iya gabatar da su a kowanne lokaci ko da bayan la'asarne
ko bayan sallar asuba, ba wanda yace idan mutum azahar din yau ta wuceshi wai
ba zai ramaba sai idan azahardin gobe ta zo, wannan bayanin kitaburra'asine.
Wanda ake binsa salloli da dama wajibine ya
tashi tsaye domin ya ga ya biya wadannan sallolin da suka wuce masa kamar yadda
bayanai suka gabata, idan ana bin mutum salloli da yawa ya samu a kowacce rana ya
biya bashin salloli biyar, idan ya yi haka to bai yi sakaciba amma idan ya biya
kasa da salloli biyar to zai shiga cikin masu sakaci Allah ya tsaremu. Yadda
kuma zai biya salloli biyar biyar shine, idan ya yi sallar asubahi ta yau ya
gama, sai ya mike ya kawo sallar kwana guda cikin wadanda suka wuce, wato ya
kawo asubahi da azahar da la'asar da magariba da lisha, shikenan sai ya tafi
neman abincinsa, idan ya yi sallar azahar ta yau yagama, sai ya mike ya kawo
sallar kwana guda cikin wadanda suka wuce kamar yadda bayani ya gabata, wato ya
kawo asubahi da azahar da la'asar da magariba da lisha, shikenan sai ya tafi
nemana abinci, to idan ya kammala sallar la'asar ta yau sai ya kawo sallar
kwana guda daga cikin kwanakin da yake ramawa zai faro kowacce daga asubahi
zuwa lisha, haka zai yi idan ya kammala magaribar yau da sallar ishar yau, sai
ya zamana alokacin da ya kammala sallar ishar yau kuma itace sallah ta biyar a
yau kuma bayan kowacce sallah ya yi sallar kwana guda cikin wadanda suka gabata
sai ya zama ya kammala sallolin kwanaki biyar da zarar ya kammala bayan sallar
ishar yau, haka zai dinga gabatarwa har ya biya dukkanin sallolin da ake binsa,
ya kuma ci gana da rokon Allah gafara Allah ya gafarta mana.
Idan mutum ana binshi sallolin da bai san adadinsuba
sai ya yi sallah gwargwadon yadda zai tabbatar da ya biya su, misali yana
kokwanton watanni takwasne ko tara, to da zarar ya yi ramuwar watanni tara to
ya tabbatar da ya biya sallolin sai rokon gafarar Allah da ya yafe.
Idan anabin mutum salloli to ba zai yi
sallar nafilaba, domin farillar da take kansa ita ake so ya biya, masu iya
Magana sukace wanda ake bi bashi ai baya kyauta, malamai sukace ba abinda yake
halatta ya yi sai dai Shafa'i da wuturi da raka'oi biyu kafin sallar asubahi da
sallolin idi guda biyu wato karamar sallah da babbar sallah, da sallar kisfewar
rana da kuma sallar rokon ruwa.
Kammalawa: Daga takaitattun
bayanan da suka gabata ta bayyana a garemu muhimmancin wadannan salloli da
Ubangiji ya dora mana su, kuma da yadda ake ramuwarsu idan har ma sun wuce da
kuma cewa ko shekarune sai mutum ya biyasu, Allah ya sawwake ya taimaka mana
wurin kula da wannan sallar, wadanda kuma ke kan hanyar ramawa ko za su fara to
Allah ya sawwake musu su gama lafiya, sannan wannan yana nuna muhimmancin koya
ma yara sallah tun kafin ta wajaba akansu domin su saba da ita ko da lokacin da
ta waja akansu din ya yi da ma sun saba tuni, shi yasa ma'aikin Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi yace a umarcesu da yin sallah tun suna
shekara bakwai, adakkesu akan ta idan sunkai shekara goma.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar
Neja, Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
No comments:
Post a Comment