Gabatarwa: Bayan da bayanai
suka gabata akan abinda ya shafi lokutan sallah da kuma yadda ake hada salloli,
a yanzu bayanai zasu zo ne akan wuraran da ba'a sallah a su, domin mutum ya
kiyayi wurin domin ya tabbatar da sallarsa ta karbu a wurin Allah madaukakin
sarki.
Matashiya: Yana
daga cikin falalar da Allah madaukakin sarki ya yi wa wannan al'umma ta
ma'aikin Allah yadda ya sanya mata kasa ta ko ina ta zama wurin sallah, inbanda
wadansu wurare da aka hana yin sallah a su. Mutanan da suka gabacemu basa
sallah sai sun je inda aka tanada musu, amma mu ko amota kake ko a gona ko tsakiyar daji… sai ka gabatar da
sallarka, ko anan kusa baka ganin kiristoci sai sun je coci.
Saboda haka a yanzu muke fatan kawo bayanai
na wuraran da aka hana ka yi sallah a su kamar haka:
1.
Shadda (Masai): Shine inda aka ta
nada domin yin bayan gida, wannan ya kasance wurine mara tsarki, kuma mun san
tsarkin wuri sharadine daga cikin sharuddan sallah. Haka kuma ba'a sallah ana
fuskantar bangwan dake dauke da najasa, kamar bangwayen da ake fitsari a
jikinsu.
2. Wurin Wanka: Shima dakin da aka
ware domin wanka, kasan akan ware wurin wanka daban wurin bayan gida shima
daban, ba'a sallah a ciki, domin ana bayyanar da al'aura a wurin, kuma shima
matattarane na aljanu.
3. Makabarta: Bai halatta mutum
ya yi sallah a inda yake makabartace, domin ma'aikin Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi ya hana, yana kuma cewa ''Allah ya tsinewa
Yahudawa da Nasara domin sun dauki kaburburan Annabawansu masallatai''.
Lalle irin wannan al'amari da ya kai madaukakin sarki ya yi wannan tsinuwa to
lalle ba karamin al'amari bane, saboda haka bai halatta a binne kabari a cikin
masallaciba, ko kuma a gina masallaci a kabarin wani ko wataba, domin yanada
matukar hatsari. Hakanan bai halatta mutum ya yi sallah yana fuskantar kabariba
domin nan inda yake sallar sunansa masallaci, hadisai masu tarinyawa da kuma
tsoratarwa duk sun tabbata akan haka, wannan fa ba wai don su najasa bane, a'a,
kada ka manta wadancan kaburburan Annabawa suka mayar masallatai Allah ya tsine
musu kuma kowa ya san Annabawa ba najasane, ai dun mumini ba najasabe
ballantana Annabawa.
Ya halatta ayiwa mutum bayan ya rasu sallah a
makabarta, kamar ace an binne shine ba'a yi mishi sallah ba
4. Wurin Da Aka Yi
Azaba: Dukkan wurin da kasan Allah ya yiwa wasu azaba awurin ko ta hanyar
ruftasu ko ma wadansu nau'uka na azaba da Allah yake yiwa wadanda suka saba
masa. Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yana cewa
dangane da inda Allah ya halakar da Samudawa: '' Kada ku shiga inda
waddannan mutanan suke sai in kun kasance masu kuka, kuma indai baku kasance
masu kukaba to kada ku shiga wurinsu domin kada irin abinda ya samesu ya
sameku''. Bukhari ya ruwaito wannan Hadisin a Kitabus Salah babin: Yin
sallah aka kifar da su ko aka yi musu azaba. Akan haka ne wasu daga cikin
malamai sukace bai halatta ayi tsarki da ruwan wurinba. Kuma an ruwaito daga
Aliyu ibnu Abidalib Allah ya kara masa yarda ya wuce inda aka kifar da mutane a
Babila bai yi sallah ba sai day a wuce.
Amma wadansu malaman na ganin ya halatta
domin babu wani dalili ingantacce da yake nuna cewar sallar ta baci, domin
cewar ibada bata yi yana bukatar dalili mai karfin gaske. Akashin gaskiya
nisantar irin wannan sabani sha yafi.
5. Turken Rakuma: Shine dukkan wurin
da yake makwantar rakumane wato nan suke
kwana, ma'aikin Allah yana cewa '' Ku yi sallah a turakun awaki, kada ku
yi sallah a turakun rakuma''. Tirmizine ya ruwaitoshi, a dansu
ruwayiyon an sami cewar wurin matattace ta shaidanu.
6. Bola: Bai halatta mutum
ya yi sallah a inda yake bolace, domin kowa ya san bola matattarace da najasa
da shaidanu. Wannan ya fi faruwa a lokacin da sahu ya kure ko kokarin samun
jam'i musamman aranar juma'a, to lalle ya kamata mu sani ba'a sallah a bola.
7. Mayanka: Hakanan ba'a
sallah a mayanka domin wurine da yake dauke da najasa ta jinin yanka.
8. Saman Ka'abah: Hakanan ba'a
sallah akan ka'aba domin abinda aka shar'anta shine a fuskanceta, to mutumin da
ya hau kan Ka'abah ina ya fuskanta kenan.
9. Coci: An ruwaito daga
wurin malamai cewa ba'a sallah a wuraran ibadar Yahudawa da kuma Coci wurin
ibadar Nasara. An ruwaito hakan daga Umar da Ibnu Abbas da Malik, wasu malaman
suka a'a sai dai idan Cocin akwai hotuna ko gumaka.
10. Mutummutumi: an hana ayi sallah
ana fuskantar mutummutumi domin hakan zai zama ana kwaikwayar wadanda suke
bautawa irin wannan mutummutumin. Kenan saboda kariyar da musulunci yake baiwa
tauhidi aka hana sallah a makabarta da ire-iren wadannan wuraran.
11. Inda Aka Kwata: Wurin da aka kwata
malamai sukace bai halatta a yi sallah a wurinba domin zama ma bai halattaba
ballantana sallah. Jamhurdin malamai sukace sallar ta yi laifin kuma yana ga
wanda ya kwata amma sallar wanda ya yi sallah a wurin ta yi.
12. Masallacin
Cutarwa: Shine dukkan masallacin da aka ginashi domin cutar da al'amma cutarwar da
musulunci ya tabbatar da ita, to irin wannan masallacin bai halatta ayi sallah
acikin shiba, bayaninshi ya zo a cikin Suratut Taubah daga aya ta 108 zuwa ta
110.
13. Wurin Dake Da
Hotuna: malamai sun kyamaci yin sallah matukar kyamata a wurin da ke an manna
hotuna, amma abin takaici sai ka ga an manna hoto a jikin masallaci a wasu
wuraran har a cikin masallaci, wannan bai kamata ace dakin Allah ake kawo
wadannan abubuwaba, abin gudu shine sannu-a-habkali sai hankalin mutane ya fara
komawa ga wadannan hotunan, wanda yake hakan sanannene, kuma shine sanadiyyar
shirka, ka duba kissar Waddu da Yagusa da Ya'uka da Nasrah da suka zo cin
Suratu Nuh. Allah ya sa mudace, amin.
Kammalawa: Daga takaitattun
wadannan bayanai ya bayyana a garemu cewa akwai wuraran da ya zama wajibi a
kula dasu alokacin da mutum zai yi sallah domin akwai inda aka hana, kuma
munsan irin hadarin da ake ciki a yanzu na ginegine da ake yi akabarbaruka
wanda yake ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya hana.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar
Neja, Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
No comments:
Post a Comment