Gabatarwa: Wannan wani
babine mai girman gaske dudda cewa dukkan wadannan bayanai suna da matukar
muhimmanci. Su lokutan sallah saninsu yana da matukar muhimmanci, domin ba'a
yin sallah sai lokacinta ya yi kuma ba'a bari lokacinta ya fita ba'a yi ba,
asalima shigar lokaci sharadine daga cikin sharuddan sallah kamar yadda bayanai
suka gabata kuma mukace da izinin Allah zamu kawo bayanai akan abinda ya shafi
lokutan sallah.
Lokutan Sallah: Kowacce sallah
daga cikin wadannan salloli wajibabbu guda biyar tana da lokacinta da Allah
madaukakin sarki ya iyakance mata ba za'a yi ta kafin lokacinta ya yi idan kuma
lokacin ya yi ba za'a bari sai ya fitaba, Allah madaukakin sarki yana cewa ''
Lalle ita salla ta kasance akan muminai wajibice kuma abar gayyadewa lokaci''
Suratun Nisa'i, aya ta: 103. Umar dan Khaddab Allah ya kara masa yarda yana
cewa 'Sallah tana da lokaci da Allah ya sansa bata inganta sai a wannan
lokacin'. Sallah tana zama wajibine idan lokacinya ya shiga kamar yadda
ayoyi masutarin yawa suka nuna, gabadayan malamai sun yi ijima'I akan falalar
dake cikin yin sallah a farkon lokaci a dunkule, Allah madaukakin sarki yana
cewa '' Ku yi rige-rigen aikata alheri'' Bakara, aya ta:148 wanda
yake sallah itace babba akan dukkan wani alheri da musulmi zai gabatar.
Kowacce sallah daga cikin salloli biyar din
nan tana da lokacinta da Allah ya kayyade mata wanda kuma ya yi daidai da halin
da bayinsa suke, ta yadda zasu gabatar da wadannan salloli a kan lokutansu ba
tare da wani abu ya tsare sub a asalima zata taimaka musu ne, kuma ta kankare
musu zunubai, ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya
kamantata da ruwa da yake gudu wanda mutum a kullun yake wanka a cikinsa sau
biyar kana tsammanin zaka ga wani datti a tare da shi!.
1. Lokacin Sallar
Azahar: Lokacin sallar azahar shine daga lokacin da rana ta karkata daga
tsakiyar sama ta koma zuwa bangaren yamma, zaka gane hakane ta yadda inuwarka
zata koma bangaren gabas bayan ada baka gantaba. Wato yadda al'amarin yake
alokacin da rana take gabas zaka ga inuwa ta na yammane, lokacin da rana take
kara dagowa lokacin inuwar take kara ragewa harzuwa lokacin da rana zata zo
tsakiyar sama daidai, za kuma tad an tsaya kadan, to adaidai wannan lokacin da
take atsakiya cif zaka ga ba wata inuwa, domin sai ranar ta karkata wani
bangarene sannan inuwar ta bayyana a wani bangaren. To daga lokcin da ranar ta
ci gaba da tafiya zuwa yamma to daga lokacin inuwa zata ci gaba da bayyana
bangaren gabas, ranar tana kara yin yamma inuwar tana kara tsawo bangaren
gabas. Daga lokacin da ranar ta karkata zuwa bangaren yamma kuma alamar hakan
itace ka ga inuwarka ta bayyana bangaren gabas to da ganin haka lokacin sallar
azahar ya yi, ba abinda ya rage sai dai a sallah ce ta, sai dai idan lokacin
ana fama zafin rana sai a jinkirta kadan, ma'aikin Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gareshi yana cewa: ''
Idan zafi ya tsananta to kudan sanyaya sallah, domin tsananin zafin nan daga
nunfashin jahannama ne''. Bukhari da Muslim da Malik a Muwatta'u.
Wannan shine loakcin sallar azahar har kuma
zuwa inuwar komai ta zama kamar tsawonsa.
Kenan anan ba wata sallah mai suna karfe
biyu ko karfe daya, kamar yadda lokuta suke canzawa a tsawon shekara to haka
lokutan sallah suke canjawa, duk mun san wani lokaci magariba akan yita kusa
bakwai na yamma wani lokacin kuma kusan shida da wani abu na yamma, to ashe
kamar yadda muka yarda lokacin magariba yana canzawa to hakanan na sauran
sallolin, kuma fa duk wannan a wasu yankunane kadan fa domin inda mutum ya je hajji
ko umarah a inda aka saukar da sallar to da yaga wani lokacimma tuni karfe daya
an gama sallah kuma da shi aka yi ta, amma idan ya dawo gida yace sai ta nuna.
2. Lokacin Sallar
La'asar: Lokacinta yana farawane daga lokacin da inuwar kowanne abu ta zo kamar
tsawonsa, kenan inda zaka kafa tsinke a kasa sannan sai ka ja layi a karshen
inuwar to daga lokacin da tsawon tsinken ya doru kadan kan inuwar to lokacin
sallah ya yi, daga nan har zuwa lokacin da inuwar kowanne abu zata ninka shi
sau biyu, amma kada ka manta yinta a farkon lokaci shine abinda ya fi.
Anan ana samun manyan kura-kurai guda biyu,
kuskure na farko shi yafi ko wanne muni shine daukan lokacin sallar la'asar
shine: karfe uku da rabi (3:30pm), wannan kuskurene domin dayawa masu
irin wannan sallar za su yita tun kafin lokacinta ya yi, kenan basu da sallah
domin sun yita kafin lokaci. Kuskure na biyu kuma shine jinkirtata bayan
lokacin ya shiga waishi ai yana ganin ance har inuwa ta ninka gida biyu.
3. Lokacin Sallar
Magariba: Lokacin sallar magariba yana farawane daga lokaci da kaskon rana ya
bace bakidayansa to daga wannan lokacin magariba ta yi ko da ana ganin haske,
kuskuren da ke yi anan shine jinkirta sallar har sai dare ya yi alhali kuma
lokacinta takaitaccene, daga lokacin da rana ta fadi har zuwa bacewar shafaki,
shi kuma shafaki: wani haskene da yake gauraya da ja anan sai jan ya bace ya
bar hasken sai shima hasken ya bace.
An fi so a gabatar da kowacce sallah a farko
lokacinta to hakama ita sallar magariba.
4. Lokacin Sallar
Isha: Shi lokacin sallar lisha yana farawane daga lokacin da shafaki ya bace,
wanda yake shine karshen muhtarin magariba har zuwa kashi daya cikin uku na
dare, zuwa nan muhtarin lisha ya tsaya, amman dai lokaci na laruri yana kaiwane
harzuwa lokacin da alfijiri na biyu ya kyato, wanda yake kuma shine farkon
muhtarin asubahi.
Shi babban kuskuren da ake samu a sallar
lisha shine wasu wuraran sun dauki karfe bakwai da rabi (7:30pm) shine
lokacinta wanda yake nuna sauda yawa ana yinta kafin shigar lokacinta.
5. Lokacin Sallar
Asubahi: shi lokacin sallar asubahi yana
farawane daga hudowar alfijiri na biyu kuma zai ci gaba har zuwa fitowar rana,
saidai kada ka manta anfi so a gabatar da ita da zarar an tabbatar da fitowar
alfijir.
Kuskuren da ake samu a sallar asubahi shine
yadda wasu suka maida lokacin shine karfe biyar da rabi na asuba (5:30am)
wanda yake wannan babban kuskure domin sauda yawa wasu lokutan alfijir yana
fitowane tun kafin biyar, ballema a wasu yankunan, kuma Karin hatsarin akwai
masu azumi na nafila ko ramuwa kuma sun dogarane da kiran sallah shi kuma mai
kiran sallar bai kiraba gashi kuma alfijir ya dade da fitowa.
Wadannan sune lokutan sallah kuma idan muka
lura zamu ga kowacce sallah tana da lokutai guda biyu; Muhtari da kuma Laruri.
Muhtari: shine zababban lokaci da
aka zaba domin ka gabatar da wannan sallar, ba'a yarda ka shiga lokacin
laruriba sai inda larura kuma musulunci ya fayyace me ake nufida larurar,
sannan shima muhtarin yin sallah a farkonshi tafi lada da samun matsayi a wurin
Allah mai girma da daukaka.
Kammalawa:
Atakaitaccan wannan bayani ya bayyana a fili cewar lokutan sallah lokutane da
musulunci ya sanya, jindadi da walwala shine abi wadannan lokuta da musulunci
ya kayyade, bai al'ummar musulmi su yi wasa da sanin lokutan sallah ba musamman
ladanai domin da kiran sallar su ake barin sahur da shi kuma ake shan ruwa. Nan
gaba zamu kashi na biyu na lokutan sallah, da izinin Allah.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna
Jahar Neja, Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
No comments:
Post a Comment