Gabatarwa: Bayan da bayanai
suka gabata akan abinda ya shafi lokutan sallah, da kuma cewar kowacce sallah
da lokacin da mahalicci ya sanya ayi ta, to a wannan lokaci zamu kawo bayanai
na wadansu lokuta da shara'a ta sawwaka akan hada salloli biyu alokacin daya a
gabatar da su, har ma shari'a ta tabbatar da wajibcin hakan a wasu wuraren.
Sallolin Da Ake
Hadawa:
Mu sani dan ance hada salloli biyu bashi ke
nuna mutum ya hada kowacce da wacce ya ga damaba, a'a muslunci ya haskaka mana
yadda ake hadawa da kuma wadanda ake hadawa.
1. Azahar da
La'asar.
2. Magariba da
Lisha.
Kenan ba'a hada isha da asuba, ko asuba da
azahar ko la'asar da magariba, hakanan ba'a hada juma'a da la'asar.
Nau'ukan Hadawar:
Malamai sun kasa
hadawar zuwa gida uku, wato:
1. Hada azahar da
la'asar a lokacin azahar, ko hada magariba da isha a lokacin magariba, shi
malamai suke kira ' Jam'u Taqdeem' domin an janyo ta biyu an yi ta a
lokacin ta farko.
2. Hada azahar da
la'asar a lokacin la'asar, ko magariba da isha a lokcin isha, shi wannan
malamai suke kira da 'Jam'u Ta'akheer' domin an jinkirtar da ta farko
har zuwa lokacin ta biyu.
3. Yin sallar farko
akarshen muhtarinta wanda yake ana gamawa farkon muhtarin sallah ta biyu ya
shiga sai a yita ita sallah tabiyun, wanda bai luraba sai yace an hada salloli
biyune alokacin daya alhali kuma kowacce an yi ta a lokacinta, amma a surar an
hadane shi yasa malamai suke kiran wanna 'Jam'us Suuree'.
Wuraran Da ake Hada
Salloli:
Mu sani asali shine kowacce sallah ayi ta
akan lokacinta, bai halatta ka tashi daga wannan asali sai kana da dalilai da
malamai suka karanta maka masu kwarin gaske, ba wai dalilan da kai ka karanta
da kankaba, wadannan wurare sune kamar haka:
1.Arafat: Idan maniyyaci
yana a filin Arafat ranar tara ga watan Zul Hajj, to zai hada azahar da
la'asarne a farkon lokacin azahar, kenan da lokacin azahar sai a kira sallah
ayi ikamah a sallaci azahar raka'a biyu, sannan sai a mike a kira sallah kiran
la'asar kenan sai kuma ayi ikama sai a sallaci la'asar a wannan lokacin, wannan
shi ake kira 'Jam'u Taqdeem', yin haka kuma sunnace wajibah in ji mai
risalah.
2. Muzdalifah: Sannan bayan ya
kammala tsaiwar Arafat rana ta fadi ba zai sallaci magariba sai ya jinkirta sai
ya kai muzdalifa sai ya hada magariba da isha ya sallace su a lokacin isha, ko
wacce da kiran sallah da kuma ikama, sai dai idan an yi sallah amma su basu yi
ba to anan ba za su kira sallah ba sai su yi ikama su sallaci magariba raka'a
uku isha kuma raka'a biyu. Wannan jinkirta magariba da aka yi a ka sallaceta a
lokacin isha shi ake kira 'Jam'u Ta'akheer' kamar yadda bayani ya
gabata.
3. Ruwan Sama: Haka nan kuma ida
ya zama ruwan samane ko kuma duhune da tabo to anan wadanda ke masallaci sai su
hada magariba da lisha sai kowa ya wuce gida, ga yadda ake hadawar:
'Za'a kira sallar
magariba a farkon lokacinta a wajan masallaci (wato da lasifika) sannan sai a
dan jinkirta sallar kadan, sannan sai a tada ikama sai a sallaceta. Sannan sai
a kira sallar isha a cikin masallaci (kenan ba tare da lasifikaba) sai a tada
ikama a sallace raka'a hudu, a lokacin akwai haske shafaki bai baceba kowa sai
ya koma gida'.
Anan sai a kiyaye wasu kwata-kwata ba
ruwansu da wani abu waishi hada sallolin magariba da lisha saboda ruwan sama.
Wasu kuma da zarar hadari ya daga ko ya kai
yadda ya kamata ayi tunanin hadawa ko bai kaiba sai ace an hada salloli a su,
wannan kuskurene, hadawar saukine musulunci ya zo da shi, yin kowacce sallah a
lokacinta wajibine, to kada ka tashi daga wannan wajibin zuwa ga wannan saukin sai
kana da dalilai masu kwari.
4. Halin Tafiya: Idan mutum ya fara
tafiya kafin lokacin sallah ta farko a sallolin da ake hadawa ya shiga kuma ga
shi sun kan tafiya sun samu su jinkirta ta farkon su yita a lokacin ta biyu,
idan kuma sun sami dama sai su yi ta biyun alokacin ta farko, ma'a ko su yi 'Jam'u
Taqdeem' ko kuma su yi 'Jam'u Ta'akheer', misali; mutum ya bar gida
karfe: 10:30am na safe ai lokaci azahar bai yiba sai suke ta tafiya ba'a tsaba
sai 2:30 na rana to anan sai su hada azahar da la'asar ko ba'a tsaya ba sai
kafe 4:30pm na yamma duk anan ba komai sai su hada azahar da la'asar kowacce
raka'a biyu biyu, ba sai an sami matsala da direbaba, domin su mutane sun dauka
kowacce sallah sai an tsaya an yi ta a lokacinta, ai ida kana halin tafiya zaka
iya hada azahar da la'asar, ko kuma magariba da lisha a lokacin kowacce daya
daga cikinsu, amma ba'a hada azahar da la'asar da magariba a lokacin isha,
bayanai sun gabata.
Al'amarin addinin musulunci al'amarine mai
saukin gaske, kuma kullum gwargwadon yadda ka fahimceshi gwargwadon yadda yake
da sauki a gareka, Allah mun gode maka.
Saboda haka koda tsayawa aka yi domin aci
abinci sai kake ganin lokacin ba zai ishekaba sai ka yi sallah a lokacin
abincin ka saya ka ci a cikin mota.
Idan kuma yanzu zaku fara tafiya kuma gashi
lokacin azahar ya yi shikenen sai ku sallaci azahar raka'a hudu bayan kun yi
sallama sai ku mike ku kawo la'asar itama raka'a hudu. Haka kuma ida lokacin
magaribane sai ku yita raka'a uku sai kuma ku mike ku kawo isha raka'a hudu sai
akama hanya, Allah ya sakeku lafiya.
5. Rashin Lafiya: idan mutum bashi
da lafiya ya samu ya jinkirta sallar farko zuwa karshen muhtarinta wanda yake
shine farkon muhtarin sallah ta biyu, sai ya sallace su, ma'ana ya yi sallar
farko a lokacinta sallah ta biyu ma a lokacinta wannan malamai suke kira '
Jam'us Suuree', hakanan ma idan za'a yi mishi fida ya zama idan an jira lokcin
sallah ya yi babu wata damuwa sai ajira domin ya sallace su duka, misali idan
aka jira azahar ta yi sai ya yi azahar ya kuma kawo la'asar idan ya fi kusa da
su, ko a jira magariba sai ya yi ta ya kuma kawo lisha idan dasu ya fi kusa,
sannan sai ayi masa aiki, amma idan jinkirin zai kawo masala alafiyarsa sai ayi
mishi aikin ba tare da an jira lokacinba.
Hadisi ya tabbata a ruwayar Muslim da Imam
Ahmad da Tirmizi da Nasa'i da Abu Daud cewar ''Ma'aikin Allah Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi ya hada azahar da la'asar, ya kuma hada
magariba da lisha a birnin madina ba tare da tsoroba ba kuma ruwan sama ba''
sai aka tambayi Abdullah ibu Abbas akace; ''Me yake nufi da hakan kenan? Sai
ibnu Abbas yace: ''Yana son kada ya kuntatawa al'ummarsa''.
Sai malamai sukace wannan ya nuna halaccin
jinkirta sallah zuwa karshen muhtarinta sannan a sallaceta wanda yake nuna
shine kuma farkon muhtarin sallah ta biyu sai wanda bai luraba yace an hada su,
Eh, an hada kuma an raba, an yi kowacce a lokacinta wannan ya nuna an raba, an
yi ta farko sai aka mike aka kawo ta biyu wannan yake nuna an hada shi yasa
malamai suke kiran wannan da 'Jam'us Suuree'.
Saboda haka wannan baya nuna haka kawai mutum
ya tashi da zarar an kammala azahar ya kawo la'asar ko da zarar an kammala
magariba ya kawo lishi dogaro da wannan hadisin domin yin haka ya sabawa
fahimtar magabata a kan hadisin.
Kammalawa: Lalle wannan ya
nuna mana irin gatan da musulunci ya yi ma da irin yadda Allah yake nufatar
wannan al'umma da sauki bad a tsanani ba, ta yadda dudda cewar shigar lokaci
sharidine na sallah amma aka sami wasu wurare da musulunci ya yarda da a hada
wadannan salloli, wannan kuma saukine a garemu, Ya Allah mun gode.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar
Neja, Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Mashaa Allah, wannan ilmantarwa da tunatarwa da gargadi da akai mana, ina fatan Allah ya kai mizani ya kuma karo budi da basira da ilimi mai albarka da amfani Amen.
ReplyDeleteDaga; Muzaffar Muhammad
Allah ya Saka da alkhairi
ReplyDeleteAss. Munyi sallar azahar sai aka barke da ruwa Mai yawa. Shin zamu iya kawo la'asar kowa ya watse? Kodai andoge akan magariba da ishane kawai
ReplyDeleteAslamualyk wai shin y halatta mutum y hada ishai d magrib saboda tsananin sanyi da akeyi
ReplyDeleteMasha Allah
ReplyDeleteJAZAKALLAHU BI KHAIR
ReplyDeleteJazakallahul khari
ReplyDelete