بسم الله الرحمن الرحيم
Dukkan godiya ta
tabbata ga Allah, Tsira da aminci su tabbata ga Annabimmu da iyalanshi da kuma
sahabbanshi.
Bayan kaha; Hakika Allah ya halicci
halittane domin su bauta mishi, Allah madaukakin Sarki yana cewa; ''Kuma
ban halicci aljan da mutumba sai domin su bauta mini''. Kuma ba'a
bautawa Allah sai da abinda ya shar'anta, tabbas ya aiko da manzanni domin su
yiwa mutane bayanin abinda ya shar'anta, domin bautawa Allah da abinda bai
shar'antaba batacciyar ibadace, kuma ya kammala aiko manzanni da manzanshi
Muhammad –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, kuma ya wajabtawa
mutane binshi, Allah madaukakin sarki yana cewa; ''Kace ya ku mutane
lalle ni ma'aikin Allah ne zuwa gareku bakidaya''. Duk wanda bai yi
imani da (Annabi) Muhammad ba to ba musulmi bane, kuma addinin (Annabi)
Muhammad shine musulunci, Allah kuma bai karbar wani addinin da ba shi ba,
Allah madaukakin sarki yana cewa; ''Duk wanda ya bi addinin da ba
musulunci ba to ba za'a taba karba daga wurinsa ba, kuma shi aranar lahira yana
cikin asararru.
Shi musuluncin da (Annabi) Muhammad ya zo da
shi yana da shika-shikai guda biyar; Shaidawa da babu abin bauta da cancanta
sai Allah kuma Muhammad manzon Allah ne, da kuma tsaida sallah, da kuma bada
zakkah, da azumin watan Ramadan, da ziyarar dakin Allah mai alfarma tare da
ikon hakan (wato aikin Hajji).
Abinda Wanda Yake
So Ya Shiga Musulunci Zai Yi:
Zai furta kalmar
shahada sannan ya biyo da rukunan musulunci kamar haka;
1. zaice; أَشْهَدُ
أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اَللهِ , zai furta hakan ne a
fili.
2. sai ya sallaci
salloli biyar; Asubahi da Azahar da La'asar da Magariba da Isha, a kowanne yini
da dare tsawon rayuwa, Asubahi raka'a biyu, Azahar raka'a hudu la'asar raka'a
hudu magariba raka'a uku isha raka'a hudu, ba kuma zai yi sallar ba sai bayan
ya yi alwala, wannanko zai farune ta hanyar wanke fuska da wanke hannuwa zuwa
gwiwar hannu da shafar kai da wanke kafafuwa zuwa idon sawu da ruwa mai tsarki
mai tsarkakewa.
3. Idan yana da
kudi da ya karu akan bukatarsa sai ya fitar da daya bisa arba'in (2.5 %) wannan
zakka ce da zai baiwa talakawa da miskinai a kowacce shekara, amma idan ya
kasance yana da dukiyar sai dai ba abinda ya karu akan bukatarsa to anan babu
wata zakka da zai fitar.
4. Zai azumci watan
Ramadan, shi ne kuma wata na tara a kalandar musulunci (Zaibar abinci da abin
sha da saduwa da iayali tun daga hudowar alfijr har zuwa faduwar rana) zai kuma
ci ya sha ya sadu da iyalinsa da daddare kadai.
5. Idan ya kasance
yana da arziki da kuma lafiyar jiki to sai ya yi aikin hajji sau daya a
rayuwarshi, idan ko yana da kudi ne amma bashi da lafiyar jiki saboda tsufa ko
wani dadadden rashin lafiya to sai ya wakilta wanda zai je ya yi mishi sau
daya.
6. Sauran abubuwan
da suka rage na biyayya ga Allah to su cuko ne ga wadannan rukunan.
Abinda Yake
Lizimtar Musulmi Ya Bari:
1. Yabar shirka da
dukkan nau'ukanta, itace kuma bautawa wanin Allah, akwai daga ciki kiran
matattau da yi musu yanka da yi musu alwashi.
2. Yabar dukkanin
bidi'o'i, wato ibadojin da Ma'aikin Allah (Annabi) Muhammad tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi bai shar'anta ta ba domin yana cewa ''Duk
wanda ya aikata wani aiki da bamu sa shi ba to ba za'a karba ba''.
3. Yabar cin riba
da caca da cin-hanci-da-rashawa da kuma karya a dukkan mu'amalolinsa da sayar
da abinci na haram da kayayyaki na haram.
4. Yabar zina wato
saduwa da matar da ba ta shi ba a shar'ance ya kuma bar luwadi wato auren
jinsi.
5. Yabar shan giya
da cin alade da dukkan abinda aka yanka ba domin Allah ba, ya kuma bar cin
mushe.
6. Ya kuma bar
auren matan da suke kafirai ne saidai in kiristocine.
7. Ya rabu da
matarshi da take ba musulmaba sai dai in kiristace ko kuma ta musulunta tare da
shi ko ta musulunta kafin ta gama iddah.
8. Idan kaciya ba
zata cutar da shi ba sai likitan da yake musulmi ya masa kaciyar.
9. Idan ya kasance
zai iya tashi daga garin da bana musulmaiba ne sai ya tashi, idan kuma ba zai
iya barin garinba to sai ya zauna a garin nasa ya kuma yi riko da addininsa.
Wanda
ya rubuta:
Sheikh:
Salih bn Fauzan Al-Fauzan
Mamba
a majalisar manyan malamai. (Saudi Arebiya)
19/3/1433
Fassarar:
Aliyu
Muhammad Sadisu (Nigeria - +2348064022965)
No comments:
Post a Comment