Thursday, January 30, 2014

018- SHARUDDAN SALLAH


Gabatarwa: Abinda ake nufi da sharadi anan shine: wadansu abubuwa da musulunci ya gicciyasu da sai sun samu kafin ai hukunci akan sallar ta yi ko bata yi ba, kenan wadannan abubuwa ana bukatar duk wanda yake musulmine ya tabbatar da sun cika kafin fara sallah.
Karkasuwa Sharuddan Sallah:
Sharuddan sallah sun kasu kashi biyu, akwai wadanda ake kira da 'Sharuddan Wajibci' akwai kuma wadanda ake kira da 'Sharuddan Inganci'.
Kashi Na Daya: Sharuddan Wajibci: Abinda ake nufi da sharuddan wajibci shine, su wadannan sharuddai duk wanda ya cika su to sallah ta zama wajibi akanshi, idan ya kuskura ya batta to ya jefa kanshi cikin mummunan hatsari, sune kamar haka:
1.Hankali: Dukkan wanda yake da hankali ya ci sharadi na farko daga cikin sharuddan wajibcin sallah, domin samuwar hankali al'amarine da musulunci yake lura da shi kafin dora hukunci, kenan mahaukaci ko mahaukaciya sallah bata wajaba akan kowannensuba, kuma koda ya yi bata yi ba.
2. Musulunci: Kenan dukkan wanda ba musulmibane koda ya yi sallah sallar bata yi ba, domin babban abinda ake nema daga gareshi shine musulunci tukunna. Malamai sun karawa juna sani akan sallar ta wajaba akanshi ko bata wajababa?, Magana ta farko cewar bata wajababa domin abinda ya wajaba akanshi a daidai wannan lokaci shine ya yi musulunci. Magana ta biyu kuma sallar ta wajaba akanshi amma koda ya yi ba za'a karbaba domin bai cika sharadiba, kuma in ya isa alkiyama sai an yi mishi azabar kin yin musulunci da kuma azabar ki yin sallah, Allah mun gode maka da ka yi mu musulmai, ya Allah ka dauki rayuwar mu muna musulmai.
3. Balaga: Idan mutum ya balaga mace ko namiji to sallah ta wajaba akanshi, babu wanda yace sai ya yi aure ko sai ta yi aure, amma irin halin da samari da 'yanmata suke shiga na rashin kula da sallah wai sai an yi aure wannan jefa kaine cikin mummunan hatsari, kuma mun yi magana akan alamomin balaga a bayanan da suka wuce. Idan yaro bai balagaba ya yi sallah sallar ta yi kuma akwai lada akai, idan bamu manta ba ai ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce ''Ku umarci yaranku da sallah tun suna shekara bakwai, kuma ku dakke su akan ta idan sun kai shekara goma''. Abu Daud: 495, Tirmizi:407. Amma mu yanzu muna Magana ne akan lokacin da sallar zata zama wajibi akansu ance su tashi su yi ko ba'ace ba.
4. Shigar Lokaci: Idan lokacin bai shigaba sallah bata wajababa kuma koda mutum ya yi ta bata yi ba, saboda Allah madaukakin sarki ya sanyama kowacce sallah lokaci, bai yadda ayi ta kafin lokacinba, hakanan kuma bai yadda abari har lokacin ya fita batare da an yi ta ba, bayanai na musamman zasu zo akan abinda ya shafi lokutan sallah da izinin Allah.
5. Isar Kiran Ma'aikin Allah: (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), kenan wadanda labarin ma'aikin Allah bai kai musuba kwatakwata to wadannan sallah bata wajaba akansuba, saidai akwai maganganun malamai akan hakan, kamar yadda bayanai suka gabata akan wanda ba musulmiba.
6. Tsarkaka Daga Jinin Al'ada/Biki: Ya kasance tana cikin tsarki, kenan idan tana al'ada ko biki sallah bata wajaba akantaba, kuma ko ta yi sallar bata yiba, kuma ta yi laifi sai ta nemi gafarar Allah.
  Wadannan sune sharuddan da idan mutum ya cika su to sallah ta zama wajibi akanshi.
 Kashi Na Biyu: Sharuddan Inganci: Wadannan sune sharuddan da idan mutum ya cika su ne za'a ce sallar shi ta yi, amma idan bai cika su ba kaitsaye zaka ce sallar shi bata yi ba.
1. Tsarki: Dolene masallaci mace ko namiji ya tabbatar da tsarkin jikinsa da kuma tufafin da zai yi sallah da shi, sannan ya tabbatar da tsarkin wurin da zai yi sallar, idan mutum ya yi sallah da najasa a jikinsa ko a tufafinsa ko kuma a wurin da ya yi sallar yana sane kuma yana da ikon ya gusar da ita amma bai gusar da najasar ba to sallar shi bata yi ba, dirkashi!, saudayawa mata suna sallah da zanin da yara suka yi fitsari sai suce ai sallar maigoyo Allah ne ke karbarta ai hakama ta mara goyon Allah ne ke karbarta amma ta sani sallarta bata yi ba.
   Ya kamata mu yi la'akari da wadansu kalmomi biyu da muka yi anmafani da su wato ' Yana sane' da 'Yanada ikon gusar da ita'. Idan ya manta kwatakwata da najasar a jikinsa ko tufafinsa ko kuma wurin day a yi sallar, sai daga baya ya tuna to idan lokacin sallar bai fitaba sai ya sake sallar, idan kuma lokacin sallar ya wuce shikenan ba komai akansa, misali a sallar azahar hakan ya faru amma bai tunaba sai bayan sallar magariba, kaga anan shikenan ba komai akan shi.
   Amma idan mutum ya shiga wani hali da ba zai iya gusar da najasarba kamar ace an kulleshi kuma gashi jikinsa da tufafinsa duk suna da najasa, wannan ba komai akansa sai ya yi sallar a yadda ya samu kanshi, haka namma koda yana da janaba bai sami yadda zai yi wanka ba, Ya Allah kakubutar da dukkan wani musulmi da yake cikin mawuyacin hali, amin.
   Idan mutum yana da janaba a jikinsa amma ya manta bai yi wankaba sai bayan ya yi sallah kuma lokacin sallar ma ya wuce sannan ya tuna to wannan sai ya sake wadannan sallolin da ya yi da janaba, idan kuma ya yi limanci a cikinsu to ba abinda ya shafi sallolin mamun.
2. Fuskantar Alkibla: Sharadine daga cikin sharuddan sallah kafin ka yi ta Allah ya karba saika fuskanci alkibla, yana dakyau mufahimci me ake nufi 'Alkibla' akace, ba'ace gabas ko yammaba kudu ko arewaba, a'a cewa akayi alkibla, abinda ake nufi Ka'abah, dukkan wanda yake ganin Ka'aba to ba'ace ya kallaci ko inaba sai asalin ita Ka'abar kai tsaye, amma mutumin da yake wajen inda Ka'abar take to zai kallaci inda Ka'abar take, shi kuma mutumin dake wajan birnin makkah zai kallaci jihar da Ka'abar take, wannan yasa mu da muke Nigeria muke kallon gabas domin nannce jihar da Ka'aba take a garemu, wanda yake inda za'aka madina ko ingila ko amurka ko Pakistan ko wasu kasashen afrika abin zai zama ba hakabane. Ko da kuna kikin birnin makkah ba lalle bane mutanan waccan unguwa alkiblarsu da taza daya da wadanda ke waccan unguwa, saboda koda kana birnin makkah sai kaje wata unguwar da ba takuba to kamata yayi ka yi tambaya inace alkibla, haka nan kuma ko tafiya ka yi daga garunku zuwa wani garin ya kamata kayi tambaya kuma musulmi zaka tambaya kafin ka fara sallah, domin wani lokaci sai mutum yadan rikice musamman a sallar magariba da isha da kuma asuba, adansu Otel akansa alamar kibiya da take nuna inda alkibla take.
  Alkibla itace inda Allah ya yi umarni da a fuskanta alokacin da mutum zai yi sallah, sai dai ida mutum yana cikin wani mawuyacin hali kamar gudun kwatar rai ruwa ya biyosu aguje ko wuta ko namun daji ko 'yanfashi dadai sauransu to duk inda suka fuskanta nance alkiblar sai su yi sallah a hali na wannan gudu da suke yi ba sai sun nemi alkiblaba.
  Maralafiya dab a zai iya juyawa ya fuskanci alkiblaba kuma babu wanda zai fuskantar da shi alkibar sai ya yi sallah a haka, wanda kuma aka daureshi ko gini ya rufto mishi shima sai ya yi sallar ahakan, anan fuskantar alkiblar aka dauke mishi ba sallar ba, ba'a daukewa mutum sallah muddin yana cikin hankalinshi.
   Idan mutum ya yi ikar kokarinsa domin ya tabbatar da alkibla sai kuma bayan ya yi sallar sai ta bayyana agareshi ai ba alkibla ya kallaba a sallar da ya yi to anan idan lokcin sallar bai wuce ya samu ya sake sallar idan kuma ya wuce shi kenan ba komai akanshi.
3. Suturce Al'aura: Dolene kafin sallar masallci ta yi ya zamana ya suturce al'aurarsa bakidaya da tufafi mai kauri wanda bayanuna tsiraici, domin wani tufafin sharasha yake kai kace ba abinda yake boyewa, wannan kuma ya shafi maza kuma ya shafi mata. Al'aurar namiji itace daga cibiyarshi zuwa gyaiwa, ya tabbata ba inda ya bayyana alokacin da yake sallah na wadannan wurare, amma irin rigar da samari suke sawa ta yadda idan suka yi ruku'i sai gadan bayansu ya bayyana wani lokaci ma har sai tsagin duburar su ya banna wannan yana da matukar hatsari ga sallar su.
   Al'aurar mace kuwa shine dukkan jikinta. Malamai sun karawa juna sani akan tafukan hannu da kuma fuska, kenan ya zama dole mace ta tabbata ta rufe dukkan jikinta. Imamut Tirmizi yana cewa:
    ''Malamai sun tafine kuma akanshi suke aiki cewa idan mace ta kawo girma sannan ta yi sallah wani abu na al'aurarta yana bude to sallarta bata yi ba.''
   kama daga sangalin hannu da kwaurin kafa da ko'ina, domin sai ta yi hakane za'a ce ta rufa al'aurarta, wannan kuma ya shafi 'yammata da matan aure da zawarawa domin dayawa mata suna banbanta abinda Allah bai banbantaba, sannan kuma suturar ta zama mai kauri ba mai shara-sharaba.
   Wanda ya kasance tufafin da zai yi sallah da shi yana da najasa kuma bai sami waniba, sannan kuma bai sami rowan da zai wanke najasar ba, ko bai sami wanda zai sa ba kafin ya wanke wannan sai ya yi sallah da shi hakanan da najasar, kwatakwata bai halatta mutum ya bar sallah ta wuce ba saboda bashi da tsarki duk wanda ya yi to ya bawa Allah madaukakin sarki.
   Idan kuma mutum ne bai sami tufafin da zai suturta al'aurarsa da shi ba watakila an taure shi ne tsirara sai ya yi sallah hakanan, ba tare da suturarba, Allah ya sawwake.
   Shar'a ta kyamaci mutum ya yi sallah da dogon wando kadai ba tare da ya sanya rigaba, wai yana ganin ai ya janyo wandon ya rufe masa cibiya.
4. Barin Ayyuka Masu Yawa: Baya cikin tsari na wanda yasan sallah ace yana sallar yana wadansu ayyuka, domin yin hakan yana bata sallah sai dai idan hakan yamana kadanne, kamar kashe waya kana cikin sallah sai aka kiraka sai ka dakko wayar ka kashe, ko ka ji an kira wani sai hakan ya tuna maka baka kashe ta ka ba, sai ka dakko ka kashe, wadannan ayyuka basa bata sallah sai dai suna rage lada.
5. Barin Magana: Duk mutumin ana sallah yana Magana da gangan to wannan bashi da sallah domin ya rasa sharadi daga cikin sharuddan ingancin sallah.
   Kammalawa:
Daga wadannan bayanai da suka gabata ya kara tabbata a garemu cewar itafa sallah wata ibadace da Allah madaukakin sarki ya zabeta kuma ya girmamata ya sanya mata falala masu tarin yawa, ya isa sallah falala cewa ita rukunice daga cikin rukunan sallah, amma duk da haka sauke wannan wajibci na sallah ba zai tabbata sai mutum ya cika wadannan tukunna, ashe al'amarin sallah al'amarine mai girman gaske, Allah ya yi mana jagora.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Wednesday, January 29, 2014

017- TADA IKAMAR SALLAH


Matashiya: Abinda ake nufi da tada ikamar sallah shine: Sanar da wadanda kenan an fara sallah da lafuzza kebantattu. Wannan sai ya nuna mana akwai banbanci tsakaninta da kiran sallah ta fuskoki da dama, daga ciki: Shi kiran sallah sanar da jama'a lokacin sallah ya shiga shi yasa lafuzan kiran sallah suka fi na na ikama yawa, ita ikama ana hadatane da sallah ba'a bukatar jinkiri sabanin kiran sallah shi ana bukatar adan jinkirta saboda jama'a su halarta.
   Tada ikamar sallah al'amarine da ya shafi maza da mata, wato kamar yadda namiji zai tada ikamar sallah lokacin da zai yi sallah to hakama mace zata tada ikama lokacin da zata yi sallah, saidai idan zata bi jam'ine to ikamar da aka tayar ta isar mata, kamar yadda ta isarwa namiji idan shima zai bi sallah ne.
  Muna dada jaddadawa wadannan lafuzza na kiran sallah da ikama koyansu ake yi agaban malami kada mutum yace ya ji ya iya akan titi saboda haka ba sai ya je gaban malam ba.
  Lafuzzan Ikamar Sallah: Lafuzzan tada ikamar sallah sune kamar haka:
اَللهُ أَكْبَرُ، اَللهُ أَكْبَرُ، أَشْهَدُ أَ لاَّ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ، أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اَللهِ، حَيَّ عَلَى اَلصَّلاَةِ، حَيَّ عَلَى اَلْفَلاَحِ، قَدْ قَامَتِ اَلصَّلاَةُ، اَللهُ أَكْبَرُ، اَللهُ أَكْبَرُ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ.

Allahu Akbar, Allahu Akabar, Ash'hadu Al Laa'ilaaha Illahu, Ash'hadu Anna Mudammadar Rasulul llahi, Hayya alas Salah, Hayya alal Falah, Qadqamatis Salatu, Allahu Akbaru, Laa'ilaaha illallahu.
Wadannan bayanai malami zai tabbatar maka da ka karanta daidai ko baba karanta daidaiba, ke nan wannan baya wadatarwa sai ka karanta a gaban malami.
  Wadannan lafuzza na kiran sallah da ikama lafuzzane masu girman gaske, sun kunshi tsantsar tauhidi ga Allah madaukakin sarki, da kuma biyayya ga ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, saboda haka ba'a karawa kuma ba'a ragewa.
   Idan mutum ya yi kiran sallah da lfuzza daidai to batayi ba sai ya sake, haka kuma idan ya yi ikama da lafuzza bibiyu baya yi ba sai ya sake, saidai malamai sun karawa juna sani akan '' Qadqamatis Salatu" wadansu sukace sau biyu za'a yi, wasu kuma sukace saudane, ke nan lafuzza na ibada kiyaye su ake yi kada a kara kuma kada a rage, Allah ya karba mana ibadummu.
Kammalawa: wannan ya nuna mana a fili yadda sallah take da muhimammanci da kuma yadda ta kunshi tsantar lafuzza na kadaita Ubangiji da girmamashi, kuma wannan yake nuna mana cewa ashe komai sai ankoya ba daka ake yiba.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com   

Tuesday, January 28, 2014

016- HUKUNCE-HUKUNCEN KIRAN SALLAH


Gabatarwa: Kamar yadda bayanai suka gabata su wadannan salloli wajibabbu wadanda suke guda bayarne a kowanne kwana guda suna da lokutansu sanannu a shar'ance, wanda yake bai halatta a yi sallah kafin shigar lokacin kuma kasancewar ba kowa bane ya san shigar lokacn ko kuma ya sani amma ya shagaltu da wadansu al'amurra, akan haka da wadansu hikimomin aka shar'anta kiran sallah idan lokaci ya yi.
   Menene Kiran-sallah ?: Kiran sallah shine: Sanar da shigar lokacin sallah ta farilla da lafuzza kebantattu.

 Daga cikin hikimomin shar'anta kiran sallah akwai fatan haduwar mutane, da kuma cewar wannan garin garine na musulmai ko akwai musulmai a cikinsa, akwai kuma bayyanar da alama ta musulunci.
   An shar'anta wannan kiransallah a tun shekarar farko bayan hijira, kuma sanadiyyar shar'antuwarta kuwa shine alokacin sanin lokaci ya ta'azzara ga sahabbai sai aka yi shawara akan wacce alama za'a yi anfani da ita domin sanar da al'aumma shigar lokacin sallah, bayan wadannan shawarwarine sai aka nunawa Abdullahi dan Zaid kiran sallar a mafarki kuma Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tabbatar.
   Dukkanin lafuzzan kiran sallah lafuzzane da suka kunshi zikiri kuma suka kunshi tsantsar akidar musulunci, kama daga girmama Ubangiji da tabbatar da kadaituwarsa kana ga tabbatar da manzanci manzan Allah Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, sannan kuma kiran al'umma zuwa gabatar da sallah wacce take itace ginshikin addini, ga kuma addu'a da fatan samun babban rabo wanda yake shine rabauta da tabbatuwa a cikin ni'ima matabbabaciya, sannan kuma a kammala kiran sallar da girmama Ubangiji da tsantsanta kalmar ikhilasi wacce take tana cikin mafificin zikiri.
   Hadisai masu tarin yawa sun yi bayanin falalar kiran sallah, da masu kiransallar, amma falalar zata tabbatane a lokacin da aka gabatar da kiran a yadda yake, mai kiran sallah ya kusanci malamai domin sanin hukunce-hukuncen kiran sallah, ya dinga tantance lokaci. Idan muka yi la'akari kiran sallah bawai ya takaitu ga sallah bane kadai a'a, da yawa masu azumi suna dakatar da sahur dinsu ne sakamakon kiran sallar asuba, haka nan kuma ba'a gabatar da budabaki sai bayan kiran sallar magariba, kenan idan lokaci bai yi bai kira sallah aka gabatar da budabaki ya kake gani kenan, ko kuma lokacin kiran sallah ya yi domin a dakatar da sahur amma kuma bai kiraba ya zakace, wannan kuma ba wai ya shafi watan Ramadan kadai bane domin ai akwai masu ramuwa akwai masu nafilfili a wajan Ramadan.  
   Bai halatta a kira sallah kafin loakcinta ya yi, domin ai an shar'antatane domin sanar da shigar lokacin sallah, saidai sallar asuba ya halatta a kira sallah kafin lokacin ya yi domin mutane su kintsa su kuma shirya, sannan idan lokacin sallar ya shiga sai a sake kiran sallar, wannan ke nuna mana ita sallar asuba kiran sallah biyu ake yi mata.
   An sunnanta ga dukkan wanda ya ji kiran sallah ya fadi kwatankwacin abinda mai kiran sallar ya fada ba kari ba raji sai dai a lokacin da mai kiran sallah yace ''Hayya alas Salah da Hayya alal Falah'' sai kace ''La haula wala kuwwata illa billah''
Bai halatta ga wanda yake cikin masallaci ya fita bayan an kira sallah ba tare da wani uzuri ba, idan kuma mai kiran sallah ya fara kiran sallah to bai kamata wanda yake a zaune ya tashiba domin kada ya yi kamanceceniya da shaidan. Yanada matukar muhimmanci ga dukkan wanda ya ji ankira sallah ya kama hanyar zuwa masallaci yabar dukkan ayyukan dake gabanshi ya je ya gabatar da na lahira tukunna.
   Bayanai akan kiran sallah suna da dama, wanda hakan yake nuna muhimmancin wannan ibada, sannan kuma kusantar malamai shine abinda zai warwarw dukkan wata matsala, domin shi kiran sallah ba aikine na marasa aikiba. Mun taba gabatar da rubutu na musamman akan abinda ya shafi kurakurai a kiran sallah.
Kammalawa: Takaitattun wadannan bayanai da suka gabata sun tabbatar mana da cewa lalle kiran sallah al'amarine da musulunci ya kula dashi domin yana da alaka da ibadar da tafi kowacce ibada a gurin musulmi, sannan kuma ba'a yenta da kah, ko a koya a kan titi, sai an je makaranta malami ya biya maka ka maimaita a gabansa har zuwa lokacin da zaice ma ya yi daidai, wanda ko ya fara bai koyaba sai ya koma wurin malamai domin su gyara masa.   
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com  

Sunday, December 22, 2013

015- SALLAH GINSHIKIN ADDINI


Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya, bayan haka; A yanzu kuma za mu fara kawowa masu karatu bayanai ne da suka shafi hukunce hukunce Sallah bayan da muka kawo bayanai da suka shafi tsarki.
   Ita dai Sallah itace tafi komai girma a musulunci akan dukkan wanda yake musulmi, kenan ta fi hajji da azumi da zakka…' hakika anshar'anta sallah a mafi kyawun tsarin ibada, kuma ita wannan sallah ta kunshi nau'ukan ibada masu tarin yawa, kama daga Zikiri da karatun Alkur'ani da tsayuwa gaban Ubangiji da ruku'I da sujjada da addu'a da tasbihi da kabbara, babu wata shari'a ta wani manzo daga daga cikin manzannin Allah da babu sallah a ciki.
   Tabbas Allah madaukakin sarki ya faralantata ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi a daran mi'iraji a sama, sabanin sauran hukunce-hukunce, kenan wannan yana nuni ga girman da wannan sallah take da shi da kuma irin matsayin da take da shi a wurin Allah.
  Hakika bayanai na ayoyi da ingantattun hadisai sun tabbatar da falalar sallah da kuma wajibcinta akan kowa, wajibcin sallah wannan sanannene a musulunci, mai littafin Iziyyah yana cewa:
 '' Dukkan wanda ya yi musun cewa sallah ba wajibiba ce ko wani abu na wajibabbunta ko wani abu na rukunan musulunci guda biyar to wannan kafirine wanda ya yi ridda, za'a nemi ya tuba tsawan kwanaki uku, idan ya tuba shikenan idan ko bai tuba ba sai a kasheshi. Wanda kuma ya yadda wajibice (ita sallar) amma ya ki ya yi za'a saurara masa har zuwa abinda zai saura na lokacinta na laruri gwargwadon raka'a cikakkiya, idan har hakan ya faru bai yi sallar ba sai a kasheshi da takobi a matsayin haddi''.
   Wannan zai kara fayyace maka yadda malamai suka yi bayanin sallah da kuma yadda suka san matsayinta a musulunci.
Mecece Sallah: A gundarin vakin larabci idan akace sallah ana nufin: Addu'a. Amma shar'ance idan akace sallah ana nufin:
'' Ibadace data kunshi maganganu da ayyuka kebantattu, ana budeta ne da Kabbara a kuma rufeta da Sallama''.
  Hakika an faralanta wadannan salloli guda biyarne a kowanne yini da dare bayan shigar lokacin ko wacce a kan kowanne musulmi wanda hukunce-hukuncen shara'a suka hau kansa.
  Allah madaukakin sarki yana cewa: '' Lalle ita sallah ta kasance akan ko wanne mumini wajibice wacce aka yiwa lokaci''. Suratun Nisa'I, aya ta: 103. ma'ana farillace alokutan da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya bayyana da maganganunsa da kuma ayyukansa. Ayoyi masu tarin yawa a cikin Alkur'ani mai garima sunyi bayanin sallah da matsayinta, duk wanda lokacin sallah ya yi alhalin yana da hankalinsa kuma ya balaga to wannan sallah ta wajaba akanshi sai dai kawai da mai al'adace ko mai jinin biki wadannan bata hau kansuba kuma ba zasu rama ba.
  Ya hau kan dukkan wanda yake kula da karamin yaro day a umarceshi da yin sallah idan ya kai shekara bakwai dudda bata wajaba akansaba, sai dai domin ya san muhimmancinta ya kuma saba da ita, kuma za'a rubuta masa shi yaron da kuma mai kula da shin lada. Yana zama wajibi ga dukkan wanda ke kula da yaro ya dakki yaron idan ya yi wasa da sallar a lokacin da ya kai shekaru goma, domin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:
'' Ku umarci 'ya'yanku da sallah tun suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dakke su akanta idan sun kai shekaru goma, kuma ku raba musu wurin kwanciya''. Abu Daud: 494, Tirmizi: 407.
   Bai halatta mutum ya jinkirta sallah daga barin lokacinta, mai littafin Akhdari yake cewa: Duk wanda ya jinkirta sallah har lokacinta ya fita to yana da zunubi mai girmangaske sai dai idan mantuwace ko bacci.
   Bai halatta mutum ya jinkirta sallah sai dai kawai wanda yake son ya hadata da wacce ta biyota idan sun kasance wadanda ake hadawanne kuma ya kasance cikin wanda aka halatta musu hadawar kamar yadda bayanai zasu zo. Amma jinkirta salloli rana akaisu dare ko sallolin dare a kaisu rana ko sallar asuba sai rana ta fito du wannan bai halattaba ta ko wanne irin hali ko saboda janaba ko najasa duk bai halattaba, mutumdai zai sallacetane alokacinta gwargwadon halinsa, amma ka ga wani a masallaci dab da rana za ta fadi yana sallah wacce yake yi to? balle ace ana biki ko aikin gona ko aikin ofis, wata da aka kaita dakin miji ta fito tana alwala zata yi sallah sai ake mamaki wai amarya zata yi sallah ba'a kammala bikiba, Tsarki ya tabbata ga Allah, wani kuma ma'aikacine baya sallar azahar da la'asar a wurin aiki sai bayan ya kammala ya koma gida sai ya hadasu duka, Allah ya tsaremu.
   Wasu kuma da jahilci ya yi musu katutu idan basu da lafiya suna kwance a gida ko a asibiti to ba'a maganar sallah wai ai ba zai iya sakkowa daga gadon asibiba ko ba zai iya canza tufafin dake jikinsaba saboda najasa ko ba wata kasa da zai yi taimama da ita ko bai sami wanda zai kawo mishiba sai ya jinkirta sallah yana ganin sai ya sami sauki sannan ya rama wani sai ya tara sallolin kwanaki hamsin ko goma gwargwadon rashin lafiyar wannan abune mai hatsarin gaske, wani kuma sabo da antsareshi a bayan kanta yana ganin ai tufafinsa akwai najasa watakilama ya yi mafarki yana da janaba, sannan shi kuma bai yi tambayaba, abinda yake wajibi ya yi sallah a gwargwadon yadda ya sami kansa awannan lokacin kuma sallarshi ta yi, ba zai sake ba. To ya mantane ai a sallar zai roki Allah ya fitar da shi daga cikin halin day a sami kansa.
  Da yawa malamai suna cewa dukkan wanda ya bar sallah don bai dauketa komaiba da kasala da yawa malamai sukace ya bar musulunci, saboda Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:
''Abindake tsakanin mutum da kafirci shine barin Sallah'' Muslim:82.
'Yan-uwa mu tashi tsaye mu kara kula da sallah mu sani babu rabo na aljanna ga dukkan wanda ya bar sallah, ba'a jinkirta sallah saboda hayaniyar biki ko aiki ko hadahadar kasuwa, sallah wajibice mu zaburar da kawunammu da na iyalammu baki daya, Allah ya karba mana ya sa mu dace, amin.
Kammalawa: Daga wadannan takaitattun bayanai ya bayyana a fili cewa sallah ba wata al'ada bace da aka gada iyaye da kakanniba da za'a yi a lokacin da aka dama, wannan ibadace da Allah yake sakankawa akanta, Allah ya yi mana jagora.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com   

014- HUKUNCIN JININ ISTIHALA ( JININ CIWO)


Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna daukene da abinda ya shafi jinin istihala wato jinin ciwo, saboda baya amsa jinin al'ada  wato jinin haila haka kuma ba amsa sunan jinin biki wato jinin haihuwa kenan, wato kenen shi wannan jinin ba jinin al'ada bane ba kuma jinin haihuwa bane saboda haka baya dauke da hukunce-hukuncensu, baya hana sallah da azumi da saduwa kamar yadda wadancan suke hanawa.
Matashiya: Domin yin kandagarki yana da matukar kyau da tsari mace ta lura da abubuwa kamar haka:
(1) Launin Jininta: Ta yi kokari ta gane launin jininta na al'ada wanne kala yake zuwa mata 'Baki ne ko Ja'.
(2) Lokacin Zuwa: Shin al'adarta tana zuwa mata ne a farkon wata ko tsakiyarsa ko karshe.
(3) Kwanakinsa: Kuma ta kiyaye kwanaki nawa yake zuwa mata a duk lokacin da take al'ada.
(4) Shinshina: Wato yanayinsa yana da karnine ko wari.
   Dukkanin wadannan abubuwa ana bukatar ta gane su kuma ta fahimcesu tun lokaci da take lafiya, -Allah ya sawwake – domin idan jini ya ci gaba da zuwa saboda ciwo da wadannancan bayanai za'a yi aiki domin a gano mata kwanakin jininta na al'ada da kuma kwanakin da suke na rashin lafiya.
Jinin Istihala: Shine ballewar jini ba'a lokacinsaba, ta wata jijiya da ake kira 'Azil'.
   Al'amari mai jinin Istihala al'amarine mai rikitarwa domin yadda jinin al'ada yake kama da jinin istihala, to idan jinin ya kasance yana zuba a koda yaushe ko mafi yawancin lokaci to a irin wannan lokaci me zata yi la'akari da shi a matsayin al'ada me kuma zata yi la'akari da shi a matsayin jinin istihala ta yadda ba zatabar azumi da sallah ba saboda shi? Domin mai jinin istihala ana mata hukunci mata masu tsarkine, kada a manta ya kandauki mace tsawan shekaru ko watanni ba al'amarine da za'a yi wasa da shi ba. La'akari da wannan bayani lalle mace mai jinin istihala tanada yanayi guda uku:
Yanayi Na Farko: Ya kasance dama tanada lissafin tsarin al'adarta kafin wannan ciwo na zubar jini ya sameta, kamar ace dama ta kasance kafin jinin istihala tana al'adane tsawan kwanaki biyar ko takwas missali a farkon wata ko a tsakiya kuma ta san adadin lokacin, to wannan zata zauna ne a matsayin mai al'ada gwargwadon yadda ta saba, sai ta bar sallah da azumi domin a wannan lokacin ana mata hukuncin mace mai jinin al'ada, idan al'adar ta dauke (Kwanakin da ta kaddarasu cewa sune na al'adar) sai ta yi wanka ta kuma yi sallah, sai ya zama  jinin da ya ci gaba da zuwa jinin istihalane ba jinin al'adaba, kamar yadda Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yace ma Ummu Habiba '' Ki zauna gwargwadon da al'adarki take zuwa, sannan sai ki yi wanka ki kuma yi sallah'', Muslim 334, hakanan kuma Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya fadawa Fatima diyar Abu Hubaish cewa : ''Ai wannan wata jijiyace, ba al'ada bace idan lokacin al'adarki ya iso sai ki bar sallah'' Bukhari 228, Muslim 333.  
Yanayi Na Biyu: Idan ya zama bata da wani yanayi sananne saidai jinin nata ana banbanceshi yana dauke da siffar jinin al'ada, kamar ya kasance baki ko mai kauri ko ya kasance yana da wata shinshina amma sauran baya kama da siffar jinin al'ada, kamar ya kasance jaa amma bashi da shisshina kuma bashi da kauri, to a irin wannan yanayi za ta yi la'akari da jinin da yake dauke da siffar jinin al'ada a matsayin jinin al'ada sai ta bar sallah da azumi…' sai kuma ta yi la'akari da wanda ba shiba jinin ciwone bana al'adaba, sannan sai ta yi wanka idan wannan jinin da yake dauke da siffar jinin al'adar ya dauke, daga nan kuma sai ayi mata hukuncin mace mai tsarki, kenan sai ta ci gaba da sallah da azumi…' ko dako jinni na zuba, kamar yadda Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya fadawa Fatima diyar Abi Hubaish:
'' Idan ya kasance jinin al'ada, shifa jinine baki akasanshi, to sai ki dakatar da sallah, idan kuma dayanne sai ki yi alwala ki yi sallah''. Abu Daud 286, Nasa'I,220, Ibnu Hibban 1348.
Yanayi Na Uku: Idan ya kasance bata da wani abu da take gane jinin al'ada da shi, kuma babu wata siffa da take banbance jinin al'ada da wanda ba na al'adaba, to anan zata yi la'akarine da mafi yawan kwanakin al'ada a kowanne wata wato kwanaki shida ko bakwai, domin wadannan kwanakin sune mafi yawan kwanakin da mata suke al'ada, wannan ko saboda hadisin Hamnatu diyar Jahash Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi:
'' Abin sani kawai wannan (Jinin ciwon) wani zungurine daga shaidan, saboda haka sai ki yi al'adarki kwana shida ko kwanaki bakwai, sannan sai ki yi wanka, idan kika tsarkaka sai ki yi sallah kwanaki ashirin da hudu ko ashirin da uku, kuma ki yi azumi ki yi sallah, yin haka ya isarmiki, haka za ki dinga yi kamar yadda mata suke al'ada''. Tirmizi: 128, Abu Daud: 287, Ibnu Majah: 627.
   Atakaice: Idan aka yi la'akari da bayan da suka gabata za mu fahimci cewa; mai yanayi tabbatacce zata yi anfani da wannan yanayin ne, wacce take abinda take banbance al'ada da jinin da ba na al'adaba za ta yi anfanine da wannan, amma wacce bata da wata alama to za ta yi al'ada kwanaki shida ko bakwai.
   Abinda kan mai jinin istihala (jiwo): Dudda cewa a hukumce mace mai jinin istihala wato jinin ciwo macece mai tsarki dudda cewa jinni na tare da ita alokaci, saboda haka za ta yi lura da abubuwa kamar haka:
1. Ya zama wajibi ta yi wankan daukewar jinin al'ada bayan wucewar kwanakin da aka yi la'akari da su a matsayin jinin al'ada.
2. Za ta wanke gabanta domin gusar da abinda ya fita alokacin kowacce sallah.
3. Za ta sanya auduga ko makamancinta a gabanta domin hana shi diga kasa, wato zata yi kunzugu kenan.
4. Za ta dinga yin al'awala a kowacce sallah, kenan ba zata yi salloli biyu da al'awala dayaba, saidai idan ramuwace, Allah kadai shine masani.
  Kammalawa: Daga wadannan bayanan da suka gabata ya bayyana a fili yadda musulunci ya kula sosai kan abinda ya shafi hukunce-hukunce jinin dake samun mata, kama daga jinin al'ada jinin biki har zuwa wannan jinni na istihala wato jinin ciwo, kuma wannan yana nuna muhimmancin al'ummar muslmi su tashi tsaye domin sanin wannan al'amari musammanma mata, kuma daga nana za mu dasa aya akan abinda ya shafi tsarki za kuma mu shiga abinda ya sahafi Sallah da izinin Allah.      
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Friday, November 8, 2013

Lum'atu Li'itiqaad (Aliyu M.Sadisu 02)

http://www.youtube.com/v/qkstRJwTayY?autohide=1&version=3&autohide=1&autoplay=1&attribution_tag=7PUFKeugZ8iwupLCX3Nvyg&showinfo=1&feature=share

Monday, November 4, 2013

Lum'atu Li'itiqaad (01)

http://www.youtube.com/v/7ijHOTkvurg?autohide=1&version=3&autohide=1&showinfo=1&autoplay=1&attribution_tag=yXIuAJkv1ltyAjNMUR5Nrw&feature=share