Matashiya: Abinda ake nufi
da tada ikamar sallah shine: Sanar da wadanda kenan an fara sallah da lafuzza
kebantattu. Wannan sai ya nuna mana akwai banbanci tsakaninta da kiran sallah
ta fuskoki da dama, daga ciki: Shi kiran sallah sanar da jama'a lokacin sallah
ya shiga shi yasa lafuzan kiran sallah suka fi na na ikama yawa, ita ikama ana
hadatane da sallah ba'a bukatar jinkiri sabanin kiran sallah shi ana bukatar
adan jinkirta saboda jama'a su halarta.
Tada ikamar sallah al'amarine da ya shafi
maza da mata, wato kamar yadda namiji zai tada ikamar sallah lokacin da zai yi
sallah to hakama mace zata tada ikama lokacin da zata yi sallah, saidai idan
zata bi jam'ine to ikamar da aka tayar ta isar mata, kamar yadda ta isarwa
namiji idan shima zai bi sallah ne.
Muna dada jaddadawa wadannan lafuzza na kiran
sallah da ikama koyansu ake yi agaban malami kada mutum yace ya ji ya iya akan
titi saboda haka ba sai ya je gaban malam ba.
Lafuzzan Ikamar Sallah: Lafuzzan tada ikamar
sallah sune kamar haka:
اَللهُ أَكْبَرُ، اَللهُ أَكْبَرُ، أَشْهَدُ أَ
لاَّ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ، أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اَللهِ، حَيَّ عَلَى
اَلصَّلاَةِ، حَيَّ عَلَى اَلْفَلاَحِ، قَدْ قَامَتِ اَلصَّلاَةُ، اَللهُ أَكْبَرُ،
اَللهُ أَكْبَرُ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ.
Allahu Akbar,
Allahu Akabar, Ash'hadu Al Laa'ilaaha Illahu, Ash'hadu Anna Mudammadar Rasulul
llahi, Hayya alas Salah, Hayya alal Falah, Qadqamatis Salatu, Allahu Akbaru,
Laa'ilaaha illallahu.
Wadannan bayanai
malami zai tabbatar maka da ka karanta daidai ko baba karanta daidaiba, ke nan
wannan baya wadatarwa sai ka karanta a gaban malami.
Wadannan lafuzza na kiran sallah da ikama
lafuzzane masu girman gaske, sun kunshi tsantsar tauhidi ga Allah madaukakin
sarki, da kuma biyayya ga ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi, saboda haka ba'a karawa kuma ba'a ragewa.
Idan mutum ya yi kiran sallah da lfuzza
daidai to batayi ba sai ya sake, haka kuma idan ya yi ikama da lafuzza bibiyu
baya yi ba sai ya sake, saidai malamai sun karawa juna sani akan '' Qadqamatis
Salatu" wadansu sukace sau biyu za'a yi, wasu kuma sukace saudane,
ke nan lafuzza na ibada kiyaye su ake yi kada a kara kuma kada a rage, Allah ya
karba mana ibadummu.
Kammalawa: wannan ya nuna
mana a fili yadda sallah take da muhimammanci da kuma yadda ta kunshi tsantar
lafuzza na kadaita Ubangiji da girmamashi, kuma wannan yake nuna mana cewa ashe
komai sai ankoya ba daka ake yiba.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna
Jahar Neja, Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Allah ya saka da alkhairy
ReplyDeletemashaallah Allah yasaka da alkairi
ReplyDeleteEnter your comment...Allah Yasa Mudace Da Alkhairi Duniya Da Lahira
ReplyDeleteAllah Ya Yi maka kyakkyawan sakayya.
ReplyDeleteMalam Allah Ya saka da alkhari. Tambaya: Ana Hausa ka Allahu Akbar sau daya ake fadi koko sau biyu? Don na ga sau daya aka rubuta shi. Allah Ya biya. Ahmed Daga Gombe
ReplyDeleteMalam Allah yasaka da gidan Aljanna
ReplyDelete