Sunday, December 22, 2013

015- SALLAH GINSHIKIN ADDINI


Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya, bayan haka; A yanzu kuma za mu fara kawowa masu karatu bayanai ne da suka shafi hukunce hukunce Sallah bayan da muka kawo bayanai da suka shafi tsarki.
   Ita dai Sallah itace tafi komai girma a musulunci akan dukkan wanda yake musulmi, kenan ta fi hajji da azumi da zakka…' hakika anshar'anta sallah a mafi kyawun tsarin ibada, kuma ita wannan sallah ta kunshi nau'ukan ibada masu tarin yawa, kama daga Zikiri da karatun Alkur'ani da tsayuwa gaban Ubangiji da ruku'I da sujjada da addu'a da tasbihi da kabbara, babu wata shari'a ta wani manzo daga daga cikin manzannin Allah da babu sallah a ciki.
   Tabbas Allah madaukakin sarki ya faralantata ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi a daran mi'iraji a sama, sabanin sauran hukunce-hukunce, kenan wannan yana nuni ga girman da wannan sallah take da shi da kuma irin matsayin da take da shi a wurin Allah.
  Hakika bayanai na ayoyi da ingantattun hadisai sun tabbatar da falalar sallah da kuma wajibcinta akan kowa, wajibcin sallah wannan sanannene a musulunci, mai littafin Iziyyah yana cewa:
 '' Dukkan wanda ya yi musun cewa sallah ba wajibiba ce ko wani abu na wajibabbunta ko wani abu na rukunan musulunci guda biyar to wannan kafirine wanda ya yi ridda, za'a nemi ya tuba tsawan kwanaki uku, idan ya tuba shikenan idan ko bai tuba ba sai a kasheshi. Wanda kuma ya yadda wajibice (ita sallar) amma ya ki ya yi za'a saurara masa har zuwa abinda zai saura na lokacinta na laruri gwargwadon raka'a cikakkiya, idan har hakan ya faru bai yi sallar ba sai a kasheshi da takobi a matsayin haddi''.
   Wannan zai kara fayyace maka yadda malamai suka yi bayanin sallah da kuma yadda suka san matsayinta a musulunci.
Mecece Sallah: A gundarin vakin larabci idan akace sallah ana nufin: Addu'a. Amma shar'ance idan akace sallah ana nufin:
'' Ibadace data kunshi maganganu da ayyuka kebantattu, ana budeta ne da Kabbara a kuma rufeta da Sallama''.
  Hakika an faralanta wadannan salloli guda biyarne a kowanne yini da dare bayan shigar lokacin ko wacce a kan kowanne musulmi wanda hukunce-hukuncen shara'a suka hau kansa.
  Allah madaukakin sarki yana cewa: '' Lalle ita sallah ta kasance akan ko wanne mumini wajibice wacce aka yiwa lokaci''. Suratun Nisa'I, aya ta: 103. ma'ana farillace alokutan da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya bayyana da maganganunsa da kuma ayyukansa. Ayoyi masu tarin yawa a cikin Alkur'ani mai garima sunyi bayanin sallah da matsayinta, duk wanda lokacin sallah ya yi alhalin yana da hankalinsa kuma ya balaga to wannan sallah ta wajaba akanshi sai dai kawai da mai al'adace ko mai jinin biki wadannan bata hau kansuba kuma ba zasu rama ba.
  Ya hau kan dukkan wanda yake kula da karamin yaro day a umarceshi da yin sallah idan ya kai shekara bakwai dudda bata wajaba akansaba, sai dai domin ya san muhimmancinta ya kuma saba da ita, kuma za'a rubuta masa shi yaron da kuma mai kula da shin lada. Yana zama wajibi ga dukkan wanda ke kula da yaro ya dakki yaron idan ya yi wasa da sallar a lokacin da ya kai shekaru goma, domin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa:
'' Ku umarci 'ya'yanku da sallah tun suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dakke su akanta idan sun kai shekaru goma, kuma ku raba musu wurin kwanciya''. Abu Daud: 494, Tirmizi: 407.
   Bai halatta mutum ya jinkirta sallah daga barin lokacinta, mai littafin Akhdari yake cewa: Duk wanda ya jinkirta sallah har lokacinta ya fita to yana da zunubi mai girmangaske sai dai idan mantuwace ko bacci.
   Bai halatta mutum ya jinkirta sallah sai dai kawai wanda yake son ya hadata da wacce ta biyota idan sun kasance wadanda ake hadawanne kuma ya kasance cikin wanda aka halatta musu hadawar kamar yadda bayanai zasu zo. Amma jinkirta salloli rana akaisu dare ko sallolin dare a kaisu rana ko sallar asuba sai rana ta fito du wannan bai halattaba ta ko wanne irin hali ko saboda janaba ko najasa duk bai halattaba, mutumdai zai sallacetane alokacinta gwargwadon halinsa, amma ka ga wani a masallaci dab da rana za ta fadi yana sallah wacce yake yi to? balle ace ana biki ko aikin gona ko aikin ofis, wata da aka kaita dakin miji ta fito tana alwala zata yi sallah sai ake mamaki wai amarya zata yi sallah ba'a kammala bikiba, Tsarki ya tabbata ga Allah, wani kuma ma'aikacine baya sallar azahar da la'asar a wurin aiki sai bayan ya kammala ya koma gida sai ya hadasu duka, Allah ya tsaremu.
   Wasu kuma da jahilci ya yi musu katutu idan basu da lafiya suna kwance a gida ko a asibiti to ba'a maganar sallah wai ai ba zai iya sakkowa daga gadon asibiba ko ba zai iya canza tufafin dake jikinsaba saboda najasa ko ba wata kasa da zai yi taimama da ita ko bai sami wanda zai kawo mishiba sai ya jinkirta sallah yana ganin sai ya sami sauki sannan ya rama wani sai ya tara sallolin kwanaki hamsin ko goma gwargwadon rashin lafiyar wannan abune mai hatsarin gaske, wani kuma sabo da antsareshi a bayan kanta yana ganin ai tufafinsa akwai najasa watakilama ya yi mafarki yana da janaba, sannan shi kuma bai yi tambayaba, abinda yake wajibi ya yi sallah a gwargwadon yadda ya sami kansa awannan lokacin kuma sallarshi ta yi, ba zai sake ba. To ya mantane ai a sallar zai roki Allah ya fitar da shi daga cikin halin day a sami kansa.
  Da yawa malamai suna cewa dukkan wanda ya bar sallah don bai dauketa komaiba da kasala da yawa malamai sukace ya bar musulunci, saboda Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:
''Abindake tsakanin mutum da kafirci shine barin Sallah'' Muslim:82.
'Yan-uwa mu tashi tsaye mu kara kula da sallah mu sani babu rabo na aljanna ga dukkan wanda ya bar sallah, ba'a jinkirta sallah saboda hayaniyar biki ko aiki ko hadahadar kasuwa, sallah wajibice mu zaburar da kawunammu da na iyalammu baki daya, Allah ya karba mana ya sa mu dace, amin.
Kammalawa: Daga wadannan takaitattun bayanai ya bayyana a fili cewa sallah ba wata al'ada bace da aka gada iyaye da kakanniba da za'a yi a lokacin da aka dama, wannan ibadace da Allah yake sakankawa akanta, Allah ya yi mana jagora.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Minna Jahar  Neja, Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com   

No comments:

Post a Comment