Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan
jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki
daya. Bayan haka:
A daidai
wannan lokacin kuma muna son ci gabaa ne da bayani akan hukunce hukuncen azumin
watan Ramadan, kama daga abinda ya shafi ganin wata da sauran bayanai da
za su zo akan abinda ya shafi hukunce hukuncensa, da fatan Allah ya yi mana
jagora ya kuma datar da mu ya kuma anfanar da mu.
Allah madaukakin sarki Shi ne wanda ya
wajabta azumin Ramadan, inda ya ce a cikin Suratul Bakara:
((يا أيها الذين
ءامنوا كتب عليكم الصيام كما كتب على الذين من قبلكم لعلكم تتقون * أياما
معدودات....)). البقرة.
Ma’ana: “Ya ku wadanda suka yi imani! an wabta muku
azumi kamar yadda aka wajabtawa wadanda suka zo kafinku, domin hakan zai sa ku
ji tsoron Allah. Wasu kwanaki ne kididdigaggu….” Bakarah.
Sai kuma Allah madaukakin sarki ya
bayyana wadannan kwanaki da suke kididdigaggu, a inda ya ce:
(( شهر رمضان الذي
أنزل فيه القرآن هدى للناس وبينالت من الهدى والفرقان، فمن شهد منكم الشهر
فليصمه)). البقرة.
Ma’ana: “Watan Ramadan ! wanda aka saukar da
Alkur’ani a cikinsa, shiriya ce ga mutane, kuma bayanaine na shiriya da kuma
rarrabewa, to duk wanda ya halarci watan (na Ramadan) daga cikinku to ya azumce
shi”. Bakarah.
Sai Ubangiji mai girma da daukaka ya
sanya watan da za’a yi azumi a cikinsa shi watan Ramadan, sai kuma Ma’aikn
Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:
((صوموا لرؤيته
وأفطروا لرؤيته، فإن غم عليكم فاقدروا له)) وفي روية ((فأكملوا شعبان ثلاثين)). رواه
البخاري ومسلم.
Ma’ana: “ Ku dauki azumin idan kun
ganshi (jinjirin watan Ramadan) kuma ku ajiye idan kun ganshi (jinjirin watan
Shawwal), idan an shamakance muku shi to ku cika”. A wata riwayar “Ku
cika Sha’aban kwana talatin”. Bukhari da Muslim suka ruwaito.
SHIGAR WATAN RAMADAN.
A wannan hadisi da ya gaba ya bayyana a
fili hanyoyin shigar watana Ramadan guda biyu ne:
Hanya Ta Farko: Ganin jinjirin watan Ramadan a lokacinda
Sha’aban yake da kwanaki ashirin da tara.
Hanya Ta Biyu: Cika lissafin watan Sha’aban kwana
talatin, idan ba’a jinjirin watan na Ramadan ba a lokacin da Sha’aban din yake
da kwanaki ashirin da tara.
Idan ya zama an ga jijirin watan Ramadan,
kuma wadanda alhakin sanarwa ya hau kansu suka sanar to ya zama waji kowa ya
dauki a zumi.
Ya halatta a yi anfani da na’urar kawo
nesa kusa domin neman wata, domin dai koda wacce na’ura aka yi anfani ba za’a
ganshi ba sai idan shi jinjirin watan ya fito.
Amma idan mutum ya ga wata kuma
shugabanni ba su karbi ganinsa ba to shi ne ya zama wajibi akan sa ya dau azumi,
ko iyalansa da ‘ya’yansa da almajiransa ba zai sa su su dauka ba, domin hakan
ba huruminsa ba ne. kuma ba wajibi ba ne idan ka ce ka ga wata dole sai an
yarda ganinka.
Ba’a yin anfani da Calendar wajan
tabbatar da shigar watan Ramadan ko fitarsa, misali inda Kalanda za ta nuna
cewa Sha’aban kwana ashirin da tara zai yi, sai kuma muka duba wata a ranar
ashirin da taran ba mu ganshi ba, to lalle ya wajaba mu cika Sha’aban talatin,
mu saki lissafin kalanda. Magana dai anan ita ce kodai aga wata koda ta hanyar
na’ura ne ko kuma a cika shi kwana talatin.
YIININ KOKWANTO (YAUMUS SHAKKI).
Idan ba’a ba a ga watan Ramadan ba, a
yini na ashirin da tara ga watan Sha’aban to yini na talatin ga watan Sha’aban
shi ne yinin kokwanto. An kira shi da yinin kokwanto ne domin ana kokwanton
wannan yinin talatin ga Sha’aban ne ko kuma daya ga Ramadan, idan ya tabbata
anga watan Ramadan a ranar ashirinda tara ga Sha’aban to ka ga washegari ya
zamadaya ga Ramadan kenan kai tsaye. Indai bai tabbata anga watan Ramadan a
ranar ashirin da tara ga watan Sha’aban ba, to lalle washe gari tanan a ranar kokwanto,
saboda kodai ta zama daya ga Ramadan ko kuma talatin ga Sha’aban, domin hakan
ne kuma ake kiran ranar da ranar kokwanto, wanda da Larabciake kira da (Yaumus
Shakki).
AZUMI A RANAR KOKWANTO.
Bai halatta a yi azumi anar kokwanto
domin a lissafishi cikin na Ramadan, idan mutum ya dauki azumi a ranar kokwanto
da niyyar in an ga wata to azumin na Ramadan ne, idan kuma ba’a ga wata to
azumin na nafila ne to shi ma a irin wannan hali ba shi kowanne daya daga cikin
su, bas hi na Ramadan kuma ba shi da na nafilar.
WURARAN DA BA SU DA RANA.
A kwai wadansu kasashe da ba kasafai rana
take bayyana musu ba, akwai kasashen da rana takan bace na tsawon watanni ba ta
fito ba, haka kuma idan ta fito ta kan jima ta tsawon watanni bata fadi ba. Abinn
da malamai suka bada fatawa akan irin wadannan kasashe shi ne za su yi aiki ne da
ganin watan kasashen da suke kusa da su, da su rana take fito musu ta kuma fadi.
DAUKAR A ZUMI DA KUMA AJIYESHI.
Hukuncin kowanne mutum wurin daukar da azumi
da kuma ajiye azumin shi ne hukuncin inda yake a lokacin dauka da kuma lokacin ajiyewa.
Misali idan lokacin daukar azumi ya yi kana Nijeria to yanzu dole kadauki azumi
ko kai dan Nijeriya ko ba dan Nijeriya ba, haka kuma idan lokacin ajiyewa yi.
To yanzu a ce ka dauki azumin daga Nijeriya,
sai ka tafi Nijar ko Saudiyyah, sai kuma ya zama Nijeriya ta riga su daukar azumi,
amma ga shi yanzu salla ta yi kana wadannan kasashe, to anan hukuncinka shi ne hukuncin
wadannan kashashe, za ka ci gaba da yin azumi har sai kasar da kake sun ajiye azumi
kafin kai ma ka ajiye, ko da kuma kasar da ka fara azumin su tuni sun yi sallah,
sannan haka kuma ko kai naka azumin zai kai talatin da daya ne ko da biyu…’.
Sannan haka hukun cin yake idan kasar da ka
fi wacce take ta Musulmaice, amma sun riga ku daukar azumin domin sun riga ku ganin
wata, to haka za ka yi aiki da ganinsu, idan sun ga watan sallah a ashirin da tara
ga Ramadan a lissafinsu, alhalin kai kuma a lissafinka kana da azumi ashirin da
takwas ne ko da bakwai haka zaka ajiye azumin naka, idan an yi sallah sai ka rama
wadannan kwanakin. Dalilin da malamai suka bayar akan wadannan matsalili shi ne
fadin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi:
((الصوم يوم تصومون، والفطر يوم تفطرون)). رواه الترمذي.
Ma’ana: “Azumi shi ne ranar da kuke azumin, sallah ranar
da kuke sallah”. Tirmizi ne ya ruwaito.
Kammalawa: Da wannan ne muka karshen wannan bayani akan
abinda ya shafi ganin wata, da kuma abubuwan da suke da alaka da shi.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
No comments:
Post a Comment