Saturday, September 15, 2012
Tuesday, May 1, 2012
Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Kisa) 3/7#
Kisa: A yanzu za mu yi bayani akan abu na uku cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakarwa, wannan abu kuwa shine Kisa. Allah madaukakin Sarki ya haramta kisa haka kawai ba tare da dalili na shara'a ba, kuma Ya sanya nau'ukan narkon azaba ga dukkan wannada ya aikata kisa.
Karkasuwar Kisankai:
Kashi na Farko: Mutum Ya Kashe Kanshi Da Kanshi.
Allah Madaukakin sarki Yana cewa a cikin littansa Alkur'ani 'Kada ku kashe kawunanku, lalle Allah Ya kasance mai rahama ne a gareku. To duk wanda ya aikata haka (ya kashe kanshi) dan kiyayya da zalinci to da sannu zamu konashi da wuta, hakanko ya kasance a wurin Allah abune mai sauki" Suratun Nisa'I aya ta 29-30. Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- 'Duk wanda ya kashe kanshi da wani abu to da wannan abun za'a azabtar da shi' hakan nan da ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yake cewa 'Duk wanda ya kasha kanshi da guba to zai zo ranar kiya yana ta hambadar wannan gubar ackin wuta, hakanan duk wannda ya kasha kanshi da wuka zai zo ranar kiya da wuka a hannunsa yana ta caka wa jikinshi a cikin wuta'. Ibnu Kasir ya kawo wadannan hadisai alokacin da yake fassara wadancan ayoyin na da suka gabata. Tabbas wannan yana nuna mana cewa kwata-kwata bai halattaba don mutum ya samu kanshi cikin bakin ciki da damuwa da tashin hankali ya ce zai rataye kanshi kodai a fankar dakinshi ko ya tafi daji ya rataye kanshi a wata bishiya, ko ya fada cikin kogi, ko yah au katuwar kada ya diro, mace ko namiji, Allah Ya tsaremu baki daya amin.
Shin Ya Hallata Ayi Masa Sallah?
Ya hallata ayi mishi sallah domin bai kafitraba, saidai malamai da masu fada aji basu halarci sallar da binne shi ba, don kada yaba sauran mutane dammar aikata irin wannan danyan aiki, amma bai hana su koka mishi gafarar Allah a inda suke tsakaninsu da Allah.
Kashi Na Biyu: Kisan Ganganci:
Kisan gangaci shine 'Mutum ya yi nufin kasha wani sannan ya dauki abin da yake kisa ya kashe shi'. Allah madaukakin Sarki Yana cewa " Kuma duk wanda ya kashe mumini da gangan to sakamakonsa Jahannama kuma zai dawwama acikinta kuma Allah Ya yi fushi da shi, kuma Ya tsine masa, kuma Ya yi mishi tattalin azaba maigirma.'' Suratun Nisa'I, aya ta:93. (Allah ya tsaremu, amin)
Hukuncin Kisan Ganganci: irin wanna kisan na ganganci Allah madaukakin sarki ya yi bayaninsa a cikin Alkur'ani mai tsarki inda Allah Ya ke cewa a Suratul-Bakar 'Ya wadanda suka yi imani, an wajabta muku ramuwa dan gane da wadanda aka kashe' Bakara, ayata:178. haka kuma Allah Ya ce 'Kuma mun wajabtamusu acikinta (Attaura) Lalle ana kashe rai idan ran nan ta kashe' (wata rai) Suratul Ma'idah, aya ta:45. Ma'anar Kisasi (wato ramuwa) shine yadda wanda aka kashe ya dandani tacin mutuwa to shima wanda ya yi kisan ya dandana, irin wannan hukuncin shi zai tabbatar da zaman lafiya domin duk mutumin da yasan indai ya kashe to tabbas za'a kashe shi ko shi waye to lalle zai shiga taitayinsa, wanda hakan zai sanya rayuwa ta aminci tsakanin al'umma. Amma farfagandar da ake da sunan kare hakkin dan'adam na cewa shara'ar musulunci ta tsaurara domin bata kula da hakkin dan'adam ba, irin wannan maganar tana nuna jahiltar menene hakkin dan'adam ?! domin ai shima wanda aka kashe dan'amne kuma yana da hakki, yanzu dan ankwatar masa hakkinsa sai ace donme?
Yafiya:
Idan 'yan'uwan wanda aka kashe suka ce sun yafe, to shikenan ba za'a kashe wanda ya yi kisanba sai ya bada diyya ga su 'yan'uwan wanda aka kashedin, sannan kuma ya yi azumi sittin ajere.
Kashi Na Uku: Kisan Kuskure:
Kisan kuskure shine 'Kisan da aka yi ba tare da anyi nufiba' kamar maharbi ya hangi barewa bayan ya kamala shiri ya sakar mata kibiya kawai sai kibiyar nan ta wuce ta sami wani can daban yana noma ko ya zo wucewa.
Hukuncin Kisan Kuskure:
Hukuncin kisan kuskure shine 'Za'a bayar da diyya ga dangin wanda aka kashe, sannan za'a 'yanta baiwa/bawa mummunai, idan ba'a samu ba sai ayi azumin kwanaki sittin ajere, Allah Ya karemu, amin.
Tambihi/Fadakarwa:
Yana da kyau musan wadanda suke da hakki akan wanda aka kasha:
Na farko: Allah Madaukakin Sarki, domin shi ne wanda ya halicce shi sannan wani ya zo ya kashe mishi bawansa ba tare da izinin shiba, hakkin Allah madaukakin sarki shi ne ' wanda yayi kisan ya 'yanta baiwa/bawa' idan ba'a samu ba sai ya yi azumin kwanaki sittin a jere ba tare ta ya shaba, domin Allah Yana cewa:'' …Kuma da 'yanta baiwa (ko bawa) mumina, to duk wanda bai samuba to sai ya yi azumin watanni biyu masubibitar juna don neman tuba a wurin Allah.' Suratun Nisa'I, aya ta: 92.
Na biyu: 'yan-uwan wanda aka kasha:
Suma 'yan-uwan wanda aka kashe suna da hakki domin an kasha musu dan-uwansu kuma Allah ya basu dammar su tashi su nemi hakkin su, Allah yana cewa a cikin Suratul-Isra'I, a 33 ayata : Kuma duk wanda aka kashe shi a halin an zalince shi to munsanyawa danginsa karfi (na su nemin hakkinsu) to amma kada ayi barna wurin kisa' (ta yadda za'a wanda bai da lefi). Saboda haka duk wanda ya yi kisa da ganganci za su taru shi danginsa su bayar da diyyah ga 'yan-uwan wanda aka kashe, domin Allah Yana cewa ''Bai kasance ga wani muminiba ace ya kashe mumini saidai da kuskure, to duk wanda ya kashe mumin da kuskure to zai 'yanta bai mumina (Hakkin Allah) da kuma diyyah da za'a mikata ga dangin wanda aka kashe sai dai in sun yafe" Suratun Nisa'I, aya ta: 92.
Na Uku: Wanda Aka Kashe:
Shi kuma wanda aka kashe aranar kiyama zai ruko wuyan wanda ya kashe shi ya zo da shi gaban Allah yace '' Ya Allah tambayeshi akanme ya kashe ni?''.
Tambaya:
A yanzu idan aka tambayeka akace 'Shin irin mahaukacin lodin da direbobi suke yi a mota, kamar ace mota zata dauki buhu hamsin na kaya sai aloda mata buhu sittin sannan mutane su hau da anje kan kwana ko wani tudu ko gangara sai motar ta balle ayi asarar rayuka wane irin kisane? Kuma way a yi kisan? Allah Ya tsaremu amin.
Idan ba'asan wanda ya yi kisaba:
Amusulunci idan ba'asan wanda ya yi kisaba to gwamnatice zata bayar da diyya ga 'yan-uwan wanda aka kasha, domin itace wajibin tsare rayukan al'umma ya rataya a wuyanta.
Kammalawa:
Awannan dantakaitaccan rubutun ya bayyana agaremu yadda musulunci ya baiwa ran bil'adama kulawa, da kuma yadda Ma'aikin Allah ya sanya kisan kai cikin abubuwan da suke halaka wanda ya aikata su. Sannan ya bayyana agaremu cewa koda mutum ya yi kisa anan duniya anbashi kariya ta kowanne irin al'amari to ya sani wannan kariyar bazata anfaneshiba a gaban Allah Madaukakin Sarki. Kenan yanzu dole mutum ya kula da duk irin aikin da za'a sashi da kuma irin alkawarin da za'a yi masa, domin koda ya tsira anan duniya to ya sani fa a kwai lahira, Allah madaukakin sarki yak are rayukan al'ummar musulmi bakidaya, ya tsaremu ya tsare mana imanimmu, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda.
Minna, jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Wednesday, April 25, 2012
Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(ASIRI) 2/7#
ASIRI: A yanzu za mu yi bayani akan abu na biyu cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Yace suna halakarwa, wannan abukuwa shi ne SIHIRI (ASIRI). Asiri shi ne abu na biyu da Ma'aiki Allah ya lissafa cikin abubuwa bakwai masu halakarwa bayan shirka da Allah. Sihiri/Asiri yana daga cikin abinda yake raba bawa da Allah cikin kankanin lokaci, mutum ya dauke dogaron shi da Allah ya sanya shi ga siddabaru ko wani mai siddabaru, wanda hakan zai iya kai mutum ya rasa addinnisa bakidaya. Idan mai karatu yana beye da tarihin musulunci ya san yadda Annabi Musa Alaihissalam ya yi fama da masihirtan zamaninsa mabiya Fir'auna, wadanda Fir'aunan ya gayyato daga ko'ina domin su kalubalanci Annabi Musa. Wannan ya nuna lalle Matsafa sunci karansu ba babbaka a zamanin Fir'auna, amma cikin taimakon Allah alokacin da suka ga Mu'ujizar Annabi Musa suka yi imani da shi sai suka watsar da dukkan kayan tsafe-tsafensu, ba irin barazanar da Fir'auna bai yi musu ba amma suka ce "Ka yi duk abinda zaka yi'' wannan ya nuna mana tarihin matsafa dadadde ne, kuma a haryanzun nan suna nan. Abinda ake so daga dukkan wanda yake musulmi shi ne ya sani Allah ya haramta tsafi/sihiri/asiri/tsubbu/bokanci/duba da dukkanin jinsin wadannan al'amurra, harma ga shi Ma'aikin Allah ya sanya shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa, Lalle Ma'aikin Allah ya isar da Manzanci. Lokaci ba zai bari mukawo dukkanin halayan matsafa ba amma daga ciki asani 'Tintiran Makaryata ne' domin missalan da suke nuna haka, al'ummar da suka zo kafin wannan al'ummar ta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Allah ya bamu bayanin su a cikin littansa mai tsarki Alkur'ani, inda a Suratul-Bakara a aya ta 101 -102 yake bamu labarin wadansu inda yake cewa " Kuma alokacin da wani Manzo (Maigirma) ya zo musu daga wurin Allah mai gasgata dukkan abinda yake tare dasu, (Alokacin da wannan manzon ya zo musu) sai wasu daga cikin wadanda aka baiwa littafi sukai watsi da littafin Allah can bayan su kamar kace basu sani ba. Suka bi abinda shaidanu suke karanta musu akan mulkin (Annabi) Sulaimana, Kuma (Annabi) Sulaimana bai kafirci ba, saidai shaidanune suka kafirce, (domin) suna koyawa mutane Asiri…'' wannan yanuna mana cewa dukkan irin labarinda ake bayarwa na cewa Annabi Sulaiman ya mulki mutane ne da aljanu ta hanyar Asiri karyane tsantsa, wadda wadancan shaidanu suka dinga rura wutarta har yakai aka kirki wadansu hatimai ake sayarwa/bayarwa ga dukkan masu mulki ko masu san mulki wai Hatimin Annabi Sulaiman! Aji tsoron Allah asani za'a tsaya a gaban Allah ranar kiyama, ko kuma hatimin Annabi Yusufu –Alaihissalam- wai maganin farin jinni.
Anan koda ace wani abu ya faru sai wani boka yace aje wuri kaza a tona za'aga abukaza da kaza, kuma aka tona din aka gani a sani fa karya ne, domin zai iya tsarawa ya aiki aljanin da suke aiki tare yaje ya aikata hakan sannan yace maka/ki wanene/wance suka aikata maka/ki..
Abin mamaki da ban takaici shine kaga mutum ya yi karatu digiri na daya koma har ya kai ga digirin-digirgir amma kaga wani mutum ne yake juya shi, wanda watakila mutumin ka ganshi ba arabi ba boko, ko wani alhaji bai da dama ya sayi wani abu sai ya gayawa wai malaminsa, har abin ya shiga cikin jikin mutane idan Allah ya yi maka budi na Karin girma ko abin hannu ko ilimi da dai sauran su, sai kaji ana cewa tofa sai ka tashi tsaye, ko kuma mace ce megidanta zai kara aure, wata kila wanda yake wannan maganar wakiline (agent) na wani boka da suke hada-hada tare, Allah Ya tsare al'ummar musumli daga sharrukansu, amin.
Saudayawa abinda yasa ake cewa ka tashi tsaye wai saboda magabta da mahassada, anan nake cewa addinin musulunci baibarmu haka kara zubeba, ya tsara mana hanyoyin da ake bi don kaucema sharrin masharranta.
Hanyoyin Neman Tsari:
Idan aka kallaci hanyoyin za'a rabasu gida biyu.
Hanya Ta Farko: Adunkule wannan hanya ita ce lizimtar dukkanin abubuwan da Allah Malicci Ya yi umarni da ayi daidai gwargwado, kamar tsayar da Sallah akan lokacin a cikin kyakkyawan tsarki, da yawan nafifilin da Shara'a ta zayyana da yawan karatun Al'kur'ani mai girma ya zamana akullum kana da abinda zaka karanta ba wai sai watan Ramadan ba, da Is'tighfari da kula da zikiran bayan Salloli, da addu'o'in shiga bandaki, domin bandaki yana daga cikin wuraren da suke matattara aljanu, mafi kyawun littafi na zikiri da aka rubuta anan kurkusa shine Hisnul Muslim zaka/ki same shi awuraren masu saida littafai na bakin titi ko na cikin shaguna, an fassarashi zuwa Hausa da Ingilishi.
Hanya Ta Biyu: Kayyadaddiyar addu'a: kamar Ayatul Kursiyyi Ma'aikin Allah Yace duk wanda ya karanta ta alokacin da zai kwanta Allah zai sanya mishi/mata mai kula da shi/ita har gari yaw aye. Hakanan Amanar Rasulu (Ayoyi biyun Karshen Suratul Bakara) alokacin da mutum zai kwanta bacci, addu'a ta uku itace: zaka/ki buda hannayanka/ki biyu sai ka/ki karanta Kulhuwa sai ka/ki tofa a hannuwannaka/ki sannan sai ka/ki karan ta Falaki, ita ma ka/ki tofa, sannan sai ka/ki karanta Nasi ita ma ka/ki tofa, sannan sai ka/ki shafo jikinka/ki daga sama (kai) zuwa inda ka tsaya, sannan sai ka maimaita Kulhuwa da Falak da Nas, kana tofawa a hannayan naka/ki sannan ka/ki shafa a jiki, sannan sai ka/ki sake maimaitawa, sau uku kenan. Dukkan wadannan addu'o'in ana matukar bukatarsu zaka/ki samesu cikin wannan littafin na Hisnul Muslim. Allah ya karemu daga dukkan sharrin masharranta, amin.
Wadannan wadansu hirzine da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin su tabbata a gareshi – ya karantar da wannan al'umma tashi, domin matsafa ba irin hanyar da baza su bi ba domin suga sun cutar da al'umma.
Nau'ukan Sihiri: Sihiri yana da nau'uka iri daban daban da akebi, kuma ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi – ya haramta hakan:
Canfi: yana cikin irin abinda al'umma ta dade tana ta'amuli da shi a matsayin wata hanya ta samun alhairi ko akasin haka, akan canfa tsuntsu ko kukansa ko mutum ko makaho ko gurgu, Ma'aikin Allah –Tsira da amincin su tabbata a gareshi – yace 'Bai daga cikimmu duk wanda ya yi canfi, ko aka camfa shi'.
Zaburar Da Tsuntsaye: shima wannan wani camfi ne da ake yi da tsuntsaye, mutum idan zai yi tafiya zai fita da duku-duku zuwa inda bishiyar da tsuntsaye suke taruwa ya raka ihu ta yadda zai tarwatsasu inda suka nufa to nanan sa'a take, wannanfa tun zamanin jahiliyyah, Allah Ya tsaremu, domin wannan yana bayyanar da haukan mutum a fili.
Zane a kasa: shima wannan nau'ine na Sihiri a yi zane akasa domin gano wani alheri ko sharri, wato duba.
Dabo/Rufa ido: suma waddannnan manyane anau'ukan Sihiri.
Annamimanci: Shima wani nau'ine na sihiri dubi yadda dauke-dauken maganganu suke canza hakikanin al'amurra ya mai da maigaskiya makaryaci ko ya maida makaryaci maigaskiya.
Ahadisin AbuHurairata Ma'aikin Allah –Tsira da amincin su tabbata a gareshi – Yace '' Duk wanda ya je wajan dan-duba ko boka, ya kuma gasgatashi dangane da abinda ya fada masa, tofa tabbas ya kafircewa duk abinda aka saukarwa (Annabi) Muhammad –Tsira da amincin su tabbata a gareshi –)) lalle wannan ya isa halaka, domin akan haka Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya lissafa shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa.
Kammalawa: Lalle wannan takaitaccan bayani ya nuna yadda Asiri yake halakar da wanda ya yi da wanda aka yiwa, da kuma yadda yake nuna mu'amala da boka ko danduba yana cikin abinda yake warwarewa mutum imaninsa da Allah, domin duk wanda ya yi imani da Allah da Kaddara ba zai aikata wannan danyan aikinba. Allah ya tsaremu, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda.
Minna, jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Saturday, April 3, 2010
Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa 1#
MUNBARIN-MUSULUNCI.blogspot.com
Don bayyana yadda Musulunci ya haskaka mana dukkanin rayuwarmu
Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa.1#
Gabatarwa: Awannan lokacin da izinin Allah mai kowa mai komai muna fatan kawo wadansu abubuwa bakwai masu halakarwa, wadannan abubuwa Ma'aikin Allah-Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- Shine yace masu halakarwa ne. Lalle dukkanin abinda Ma'aikin Allah ya ce 'Abu kaza mai halakarwane' To lalle ya kamata mutum musulmi ya yi kokarin sanin wannan abin, tun da sauran nunfashinshi. Ma'aikin Allah- Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- Ya ce "Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa ! (Sai Sahabban shi -Allah ya kara musu yarda suka ce) 'Wadanne abubuwane wadannan ya Ma'aikin Allah?. Sai Ma'aikin Allah- Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- Ya ce " Shirka da Allah, da Asiri da Kashe raid a Allah ya haramta a kashe ba tare da hakki ba, da Cin Riba da cin Dukiyar Maraya da Ja-da-baya lokacin gumurzu, da Yiwa mace mumina wacce ta kame kanta wacce bata san ya ake barna ba mutum ya yi wa irin wannan macan kazafi." Wannan Hadisi Bukhari ya ruwaitu a wurare da dama a cikin littafinsa. To wadannan fa sune abubuwa bakwaidin da ma'aikin Allah- Tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi- ya gargadi wannan al'umma, yace ku yi nesa da su kada ku kuskura ku yi kusa da su.
Ayanzu wadannan abubuwa bakwai su muke fatan zamu yi bayaninsu daya bayan daya, da yardarm Allah, muna rokonShi da sunayanSa kyawawa da siffofinshi madaukaka da ya yi mana jagora.
Abu Na Farko: Shirka da Allah. Itace 'hada bautar Allah da wani' wannan ya nuna cewa bautawa Allah Shi kadai, shine abinda yake daidai, amma hada Allah da wani, bai taba halatta. Wannan yasa Allah madaukakin sarki ya dinga turo Annabawa da Manzanni do min su tabbatar da tsan-tsar Tauhidi, haka kuma Annabawan da Manzannin suka tsaya tsayin daka domin tabbatar da sun isar da wannan aike da aka yi musu, muna shaidawa da cewar Annabawan Allah da Manzannin shi sun isar da sakon da ya aikosu da shi.
Ma'aikin Allah ya dauki tsawan she karu goma cur yana kira zuwa ga tsantsar Tauhidi acikin shekaru ashirin da uku da ya yi yana raye bayan aiko shi a matsayin Manzo, wanda hakan ya ke nuna mana matsayin tauhidi. Ya tura wakilai da yawa wurare daba-daban, misali ya tura Mu'azu Dan Jabal zuwa kasar Yaman yace "Lalle kai zaka je wurin mutanan da suna dauke da littafi, Farkon Abin da zaka kira su akai shine su kadaita Allah'' wannan Hadisi Bukhari ya ruwaitoshi. Wannan bayani zai tabbatar mana da cewa lalle ya wajaba mu tsaya domin karanta da karantar da Tauhidi, domin da Tauhidi ne mutane za su rabauta duniya da lahira, da shi ne kuma za'a sami hadinkan a'ummar musulmi baki dayanta, ta zama 'Tsintsiya madaurinki daya' wanda wannan shi ne matan ko wanne musulmi.
Ita shirka da Ma'aikin ya fara lissafata acikin jerin gwanon wadannan abubuwa guda bakwai, tana da matukar hadarin gaske, daga cikin manyan hatsarinta wanda ba wanda ya ke so ya afka, ita shirka tana tabbatar da mutun cikin azabar Allah har'abada. Tana sa Mutun ya rasa ceton Manzan Allah Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi. Tana sa mutum ya yi asarar dinbin ayyukan alheri da ya yi a duniya, kamar taimakawa nakasassu, sadar da zumunci…'. Saboda haka dukkan wani aikin ibada da Allah da Manzanshi su ka yi umurni da ayi to mutum ya tabbatar ya yi shi ga Allah kadai kada ya hada kowa tare da Allah. Kuma idan akace Ibada ana nufin 'Gamamman suna ne da yake tara dukkan abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi' to kaga anan muna da nau'ukan ibada masu tarin yawa kamar, Karatun Kur'ani, Sallah, Azumi, Salatin Annabi, Is'tigfari, Hailala, Sada zumunci,Gaida mara lafiya, Yanka, Neman tsari, Neman Agaji, Tawakkali, Kauna, So da sauran su, wadanda ba'a ambata ba dukkan su na Allah ne Kadai kada mutum ya kuskura ya karkatar da wani nau'i guda zuwa ga wanin Allah, domin Allah yana cewa 'Ku bautawa Allah (Shi kadai) kada ku hada shi da komai' Suratun-Nisa'i, aya ta 36, da kuma fadin Allah adai cikin Surar 'Lalle Allah baya gafarwa idan akai Shirka da shi, yana gafarta abinda bai kai haka ba, dukkan wanda ya yi shirka da Allah to hakika ya kirkiri Zunubi mai girma' Suratun –Nisa'I aya ta 48. wanna yasa Annabawa da Manzanni ba su bari anhada su da Allah wurin bautaba domin sun san basu can-canta ba, Allah kadai mabuwayi shine ya can-canta Maganganun Annabi Isah –Amincin Allah ya tabbata a gare shi- cikin suratul Ma'idah sun tabbatar da haka. Hakanan maganganun Ma'aikin Allah cikin Hadisanshi ingantattu haka kuma.
Karkasuwar Shirka:
Malamai sun yi bayanin cewa shirka ta kasu kashi biyu; Kashi na farko: Shirkar da Take futar da mutum da musulunci (Allah ya Tsare mu) Kashi na biyu Shirkar da bata fitar da mutum daga musulunci, Amma tana da mummunan Hatsari (Allah ya tsare mu ya kare mu da su baki daya) malamai sukan yi missali kamar:
Riya (Yi don again) Wannan shine mutum ya yi dukkan wata ibata ga Allah amma yana son agani domin a yaba, ko ace yana da kokari ko ya burge. Mutum ya san cewa idan ya yi aiki domin a gani ya sani ya yi riya, sai ya nemi Allah ya yafe (Allah ya yafe mana baki daya) wannan yana shafan ayyuka sai ai fatan ki yayewa, haka kuma Jiyarwa: wato mutum ya yi don aji kodai ace yana da murya ko makamantan haka, ko kuma ya yi ibadar shi daga shi sai mahaliccin shi sai yazo yana bada labari, ko ana fira sai aka ganshi yana gyangyadi aka ce mallam lafiya? sai ya kada baki ya ce 'Ai na kwana na yi ina nafilfili ko ina karatun Kur'ani ko Zikiri, da sauransu, ko ana zaune yace azuminnan yana banwahala al'hali ba watan Ramadan ake ciki ba 'ka ji yana cewa ai azumin litinin da alhamis baya wuceni, da dai makamantansu, asani ba muna hukunci akan ayyukan mutane bane amma 'Gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba' sabo da haka ayi kokarin ankyautata ayyuka domin Allah. Anan sauda yawa mutum yakan yi yunkurin zai aikata wani kyakkyawan aiki wanda Allah yake so sai ya ji kamar mutane zasu gani su yaba saboda haka bari ya hakura? Idan mutum ya samu kanshi cikin irin wannan hali ya aikata aikin da yake so ya aikata wannan tsoron da yaji shi ake bukata shaidanne yake son ya yi amfani da shi domin ya hana shi. Saboda haka kowa ya yi kokari yaga asalin niyyar sat a zama domin Allah, sauda yawa magabata sun sha yin Magana akan 'Ikhlasi' wato yi domin Allah, muna fatan Allah ya karba mana.
Rantsuwa da wanin Allah. Rantsewa da wanin Allah yana daga cikin dinbin abubuwan da Ma'aikin Allah ya hana, domin babu wani mai girma da za'a rantse da shi Inba Allah ba. Ma'aikin Allah cewa ya yi "Duk wanda zai rantse to ya rantse da Allah ko kuma ya yi shiru'' hasali ma duk wanda ya rantse da wanin Allah rantsuwar bata yi ba (bata kulluba) kuma sai ya yi gaggawar tuba zuwa ga Allah. Amma Allah, Sarki mabuwayi mai girma da daukaka mai ikone akan ya rantse da komai, domin babu wanda zai tambaye Shi, akan haka Allah Ya rantse da rayuwar Manzan Shi Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kuma rantse da rana, wata, hantsi, dare. Da dai suransu.
Kammalawa : Awannan takaitaccan bayani da yagabata na munsan hatsarin dake cikin Shirka da Allah wacce Ma'aikin Allah ya tsoratar da mu ita, da irin alherin da yake cikin Tauhidi. Akaro na gaba bayani zai zo akan abu na biyu da Ma'aikin Allah ya ce munisanta kada mu kuskura mu yi kusa da shi wato Sihiri (Asiri) Allah ya karemu ya kuma tabbatar da akan karantarwar Ma'aikin Annabin Tsira Annabi Muhammad Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda.
Minna, jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a +2348064022965, ko kuma a aliyusadis@gmail.com

Thursday, December 24, 2009
TAKABA A MUSULUNCI
Gabatarwa:
Da sunan Allah Maiyawan rahama Mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halitar Allah Annabi Muhammad, da SahabbanSa da Iyalan gidanSa amin. Muna son a wannan lokacin muyi bayanin yadda addinin musulunci ya haskaka duhun da duniya ta dade a ciki, ayayin yin takaba lokacin da mace megidanta ya rasu, ta yadda kowacce kabila take yi yadda ta tashi ta ga haka mutananta ke yi , a irin wannan lokacinne mata suke dan-dana kudarsu, domin suna kan wani tsari da Allah Madaukakin sarki bai turo wani Annabi da wannan tsarin ba. Ayau zamuyi kokarin fayyacewa tsanin zare da abawa ne, akan yadda takaba take a musulunci, da kuma irin gatan da musulunci ya yi wa mata. Asha karatu lafiya Allah yai mana jagora amin.
Mecece Takaba?: Takabadai itace" Zaman da mace zatayi bayan rasuwar megidanta, na wadansu kwanuka sanannu, batare da ado da kwalliya ba, ba kuma da yin wani aure ba, ko yi wa wani alkawari, ko sanya dukkan abinda zai ja hankalin wani ba, na tufafi ko kayan karau." Awanna bayani daya gabata zamu tsinkayi abubuwa masu yawa, wadanda kusan za mu bisu a hankali gaba-gaba domin fayyace su.(anan Takaba ta sha babban da Iddar saki, wadda muke fatan a wani lokaci muyi bayaninta, in Allah ya yarda).
Wacece mai yin Takaba?: Matar da zata yi zaman takaba, itace dukkar matar da mijinta ya rigamu gidan gaskiya, tana matarshi, sunyi saduwar aure ko busu yi ba. Anan zamu fahimci cewa muddin akwai igiyar aure a tsakanin su, to za ta yi takaba. Misali (Allah ya kiyaye) idan aka daura auren mutun da karfe 2:30 na rana, sannan bayan minti 30 ko awa guda ya rasu, to fa takaba ta ganta, kuma zata ci gadonshi, domin matar shi ce. Kamar yadda Abdullahi Dan Mas'ud Allah ya kara masa yarda, ya bada amsa lokacin da aka tanbaye shi, akace da shi : "Mutunne ya auri mace amma bai bayyana mata sadakinta ba, kuma bai sadu da ita ba har ya rasu? Sai Dan Mas'udin ya ce" Zan bada amsa da fahimta ta, idan na yi daidai to daga Allah ne, idan kuwa ban yi daidai ba to daga Shaidan ne, Allah da Ma'aikin Shi sun barranta da wannan amsar. Tana da sadakin mata ire-irenta, ba kari ba ragi, kuma za ta yi Takaba, sannan tana da gado". Sai Ma'akil Dan Sinan wanda yake daga kabilar Ashja'a ya mike yace: "Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, ya yi irin wannan hukuncin da ka yi ga Rauh Diyar Washik –wata mace ce daga cikin mu, sai Abdullahi Dan Mas'ud yai farinciki da wannan Magana tashi" Imam Ahmad da Abu-Daud da Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah suka ruwaito wannan hadisin, kuma Tirmizi ya Inganta shi.
Hakanan kuma inda mutun zai rabu da mai dakinshi da saki daya ko biyu, sannan ya rasu kafin ta kammala iddar saki, shikenan sai ta koma takaba, matarshi ce yana da dama yado da ita a ko yaushe muddin bata kammala idda ba.
Gwargwadon kwanakin Takaba: Alokacin da mutun ya rasu, to zaibar iyalin shi a dayan halaye biyu, kodai ta zama tanada Juna biyu ko kuma bata da shi. Idan bata da juna biyu to Takabarta itace "Wata hudu da kwana goma" Kamar yadda Allah yace cikin Suratul-Bakara "Kumma dukkanin mazan dake rasuwa daga cikin ku subar matansu, to matan za su zauna wata hudu da kwana goma" aya ta :234.

To amma idan ya rasu ya barta da juna biyu, a wannan lokacin karshen Takabarta shine ta sauke abinda take daoke da shi, koda ko ranar da ya rasu ne, Misali ya rasu 7:00 na safe ita kuma ta haihu 7:10 na safiyar, shi kenan ta kammala takabarta, idan wani ya gani ya ce yana so aka daura aure 2:30 na ranar aure ya dauru(ana karbar gaisuwa ana daurin aure) dalii kuwa shi ne. fadin Allah a cikin Suratut-Talak aya ta 4 " Kuma dukkanin mata masu juna biyu to lokacinsu shine su sauke abinda suke dauke dashi" da kuma Hadisin Subai'a Al-aslamiyyah, " Ita ta kasance tana auran Sa'ad Dan Khaulah, shi kuma ya fito ne daga gidan Amir dan Lu'ayy, yana daga cikin wadanda suka halarci gwabzawar Badar, sai ya rasu yabarta a hajin bankwana tana da juna biyu, bata ko jima ba bayan rasuwar shi saita haihu, a lokacin data kamma biki sai ta yi kwalliya, sai Abu-Sanabil Dan Ba'akk ya zo wurinta, shi kuma ya fito ne daga gidan Abduddar, sai yace da ita " Lafiya na ga kin cancara ado?, ko kina son ki yi aure ne? Na rantse da Allah lokacin auranki bai yi ba, harsai kin yi wata hudu da kwana goma.
Sai Subai'a ta ce "Yayinda ya fada min haka, maraice na yi sai na tattara kayana naje wurin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, na tambaye shi hakan, sai ya ban amsa da cewa ai na kammala Takabata tun lokacin dana haihu, ya ban dama da inyi aure a duk lokacin da naga dama". Wanna hadisin Bukhari ya ruwaito shi, hadisi na 4909 da kuma na 5318, hakanamma Muslim da Abu-Daud da Tirmizi da Nasa'I, da Ibnu Majah. Inbu Shihab yake cewa : "Bana ganin akwai wani laifi idan ta yi aure lokacin data haihu, koda tana cikin jinin biki, saidai kawai mijin ba zai kusanceta ba sai ta yi tsarki.
To haka kuma idan yarasu ya barta da juna biyu na kimanin wata daya ko ma baikai haka ba, tofa sai ta haihu ka ga wannan Takabarta na neman wata tara koma fiye kenan domin dai sai ta sauka. Zai iya yuwuwa alokacin da maigida yarasu bata samma tanada juna biyu ba, wata kila a saduwarda bai huce masa saura minti 30 aduniya ba ta sami juna biyun, to kaga wannan zata fara lissafin kwanaki ne na Takaba sai daga baya Takabarta ta koma sauraran haihuwa, Allah ya sauketa lafiya shi kuma maigida Allah yajikan shi. Wannan ya nuna mana cewa mutun zai iya rasuwa ya bar matanshi, amma wata ta riga wata kammala Takaba, domin musulunci bai yadda a dauki dan wani gida akai wani gida ba, wannanfa ko da mace mai Takaba ta samu kwanciyar ciki, domin ciki yakan kai shekara 4 ko 6 kamar yadda malamai sukai bayani, duba Tafsirin Adhwa'ul Bayan Suratur-Ra'ad aya ta :8. Abinda ake nufi data sauka shi ne, ta sauke duk abinda ke cikinta, ya zo da rai ko bai zo da rai ba, saboda haka ko bari tayi ta kammala idda ko Takaba idan aka samu shaidu akan hakan, koma ace siffar mutun ta bayyana a tare da shi barin, idan mai Takaba ta haihu sannan ingantaccen bincike yanuna cewa tana dauke da 'ya'ya biyu ne kuma gashi ta haifi daya, tofa bata kammala ba sai ta haifi na biyun, domin abinda ake bukata ta sauke duk abinda take dauke da shi.
Yaushe za'a fara lissafin Takaba?. Za'a fara lissafin maitakaba ne daga lokacin da megida ya rasu, ba wai kamar yadda akebin al'ada ba wai sai ran juma'a, ko dako ya rasu ranar asabar, sannan ai mata wankan shiga Takaba, wannan kwata-kwata ba shi da alaka da addinin musulunci, sannan ace za'aba maitakaba wuka ko sanda, in zata shiga makewayi ta rike, kuma ta tafi a hankali wai mijinta na biye da ita, a firgita baiwar Allah. Saboda haka daga ranar da mijinta ya rasu daga ranar ta fara idda, yana rasuwa ta shiga Takaba. Saboda haka Malamai sun yi maganganu biyu, idan ya rasu bata sami labarin rasuwarshi ba, sai bayan wata hudu da kwana goma, ko bayan haihuwarta sannan ta sami labarin shikenan ta kamala takabarta, adaya daga cikin maganganun, Magana ta biyu kuma shi ne zata fara lissafi daga ranar da labari ya zo mata, in kuma bayan wata biyune da rasuwar shi ta sami labarin rasuwar shi. Sannan kuma babu wani wankan fita daga Takaba a mulunci, da zaran ta kammala wata hudu da kwana goma, ko ta haihu to ta kammala Takaba, saboda haka duk abinda ya haramta a gareta lokacin tana Takaba to yanzu ya halatta ta yi domin ta kammala takaba.
To me ya haramta ga maitakaba? A dunkule abinda ya haramta ga maitakaba shine 'Ado da kwalliya, da kuma yin aure ko yi wa wani al'kawari, ko fita ba tare da wani dalili na Shara'a ba. anan yana da kyau mu banbance tsakanin Kwalliya da Tsafta ya haramta ta yi kwalliya da ado, kamar sa Tozali, Kunshi, sa hoda yin dizayin janfarce janlebe, sanya tufafi na ado sa turare –indai ba bayan ta kammala al'ada ta diga shi akyalle domin tasa agabanta saboda rage karnin jiniba- da dai dukkan wani nau'I na ado ko kwalliya, koda ko rangada kitsone. Amma ita tsafta babu wanda ya hana maitakaba yin ta, yin wanka kullun yin kitso idan bukatar hakan ta taso ba kuma ayi don kwalliyaba, suma sun san na kwalliya kuma kun san wanda za'adan kakkama alallaba, kuma ya halatta ta yi wanki domin duk suna cikin tsafta ba kulliyaba, sannan ya halatta ta share dakinta ba ta zauna kamar wata mai haukaba, sannan dukkanin wadannan abubuwa babu wata rana da aka ajeye musu don gudanar da su, kamar ace 'sai juma'a ko laraba' za ta yi aduk lokacin da bukatar hakan ta samu. Anan nake cewa lallai akwai babbanci wanda ba zai yiwu ahadaba da irin yadda musulunci ya fayyace mana al'amura dalla-dalla ya haskaka mana su, da kuma irin yadda al'adu sukai kane-kane cikin harkar Takaba, Allah ya sauwake.
Kammalawa: daga dukkanin bayanan da suka sauwaka zamu fahimci irin gatan da musulunci ya yi mana shi, irin saukin da ya nema mana, musamman idan muka kalli yadda Allah ya tsara mana kuma muka kalli yadda ake yi a al'ada lallai zamu fahimci ya zama wajibi mu dada godewa Allah akan wannan ni'ima da Ya yi mana.
Aliyu Muhammad Sadisu,Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda Minna, jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a +2348064022965,
ko kuma a Imei : aliyusadis@gmail.com
Ko a yanar gizo, a :htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Littafan da aka duba.
1- Alkur'ani Maigirma.
2- Tafsirin Ibnu Kasir
3-Adhwa'ul-Bayan Na Muhammad Amin As-Shankiti
4- Ahkamul-Kur'an Na Ibnul-Arabi
5- Fat'hul-Bari Na Ibnu-Hajar
6- Al-Mughni Na Ibnu Kudama
7- Taisirul-Allam Na Abdullahi Bassam.
Wednesday, December 16, 2009
RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI #2.
Gabatarwa:Bayanda a kasidar data gabata mukai takaitaccan bayani kan yadda musulunci ya tsara yadda ya kamata rabuwar aure ta kasance, da kuma yadda ya baiwa ko wanne bangare na ma'aurata 'yancinshi, da kuma yadda bayanai suka gabanata na cewa babu wani tsari da yayiwa mabiyanshi irin wannan tsarin inba musulunci ba. to ayau za muyi bayani abinda Allah Maigirma da daukaka ya sawwake mana na yadda Idda kuma zata kasance bayan anyi saki ko anrasu Allah yai mana jagora amin, asha karatu lafiya.
Kadan daga Hikimomin Idda.
Yana daga cikin hikimomin da Allah ya sanya cikin Idda kada adauki dan-wani gida akai wani gidan, domin idan mutun ya rabu da maidakinshi takan yiwu a wannan makon ansami juna-biyu, idan tai aure batare da yin iddaba bayan kwana biyu ko uku ko makamantansu da sakinta shikenan ta tauki dan-mijinta na farko ta kai gidan mijinta na biyu wanda yake wannan bakaramin zunubi bane da barna a harkokin zamantakewarmu, saboda haka musulunci ya tabbatar da cewa ba zatai aure na biyuba sai antabbatar da bata da juna biyu saboda haka aka shar'anta takaba, saidai kawai idan aka saketa kafin asadu to awannan lokacin babu wata Idda da zatayi, kamar yadda bayanai zasu zo nan gaba kadan idan Allah ya yarda. Haka kuma yana daga cikin Shar'anata Idda fatan bijin ya maida ita matar ta shi kafin ta kammala iddar idan sakin baikai ukuba, kamar yadda bayani ya gabata a makalar farko inda muka kawo fadin Allah Maigirma da daukaka " Baka saniba ana fatan Allah ya aiwatar da wani al'amari" Suratut-Talaq, aya ta 1, domin ba din da iddarba da shikenan kana sakinta yau gobe sai wani ya aura taimaka Fintinkau. Kazalika yana daga cikin manufofin yin Idda juyayin megidanta daya rasu ko dako basu taba saduwaba, kamar yadda bayani ya gabata arubummu metaken "Takaba a Musulunci". Saboda haka ko iyanan muka dakata kasan Allah Maigirma da taukaka ya sanya hikimomi masu tarin yawa cikin Idda, munsan su duka ko bamu sansu ba. Allah mungode maka.
Karkasuwar Idda a musulunci.
Idda ta kasu kashi biyu a musulunci, wato Iddar mamaci wacce muke ce mata takaba, da kuma Iddar Saki. Itadai iddar mamaci\Takaba mungudanar da bayanai akanta, saboda haka awannan karon bayanai zasu kasance ne kan "Iddar Saki"! Allah yai mana jagora amin,
Karkasuwar mata
Da farko yana dakyau mufahimci cewa mata sun kasu kashi-kashi lokacin da
zasu rabu da mazajansu, saboda haka ko dole iddarsu tasha ban-ban, anan zamu fahimci mutun zai iya rabuwa da matanshi biyu ko uku lokaci guda amma wata ta riga wata kamma Idda. Yanzu ga kasha-kashannasu :
(1) Mace me juna biyu : Alokacin da mutun ya rabu da medakinshi tana da juna biyu to ita Iddarta itace ta sauke abindake cikinta, ma'ana inda zai saketa da karfe 5:00 na yamma sai ta haihu karfe 5:20 na yammar shikenan ta kammala iddarta inta sami wanda zata aura aranar ya yi sai adaura auren da 6:00 na yammer. Yanzu ya zama dan-kallo, saidai kawai idan ya kuru Allah ya taimakeshi saki daya ne ko biyu, sai ya bogo fasta ya shiga cikin 'yan-takara wata kila ya samu ya kai labari. Allah yana cewa " Kuma wadanda suke da juna-biyu to lokacin (kammala Iddarsu shi ne ) su sauke abinda suke dauke dashi" Suratu-Talaq, aya ta :4, hakanan kuma inda zasu rabu juna biyunnata bai huce wata dayaba saidai ta haife abinda take dauke dashi, kamar yadda wannan bayanin ya gabata a ' Takaba a Musulunci' mun dan fadada bayanai a lokacin.
(2) Mace meganin Al'ada. Itakuma matar da take ganin al'adarta iddarta itace samun tsarki uku, saboda haka idan mutun ya rabu da maidakin shi, iddarta itace ta yi tsarki uku, shi kuwa tsarki uku ya sha ban-ban da wata uku, domin mace zata iya tsarki a kwanakin da suke kasa da wats uku, haka kuma zata iya iya tsarki uku a watannin da suke sama da haka, akwai matar da ashekara sau daya take yin al'ada to kaga wannan iddarta zata tasamma shekaru kenan. Allah yana cewa " Dukkani matan da aka sakesu zasu zauna da karankansu (suna jiran) tsarki uku" Suratul-Bakara, aya ta: 228 Idan kuma tana cikin lissafa al'ada sai ya bayyana tana da juna-biyu, to anan iddarta zata koma iddar mai juna biyu saitai zaman haihuwa (Allah ya sauke ta lafiya amin).
(3) Mace mara ganin al'ada. Matan da basa ganin al'ada sun kasu kashi biyu, kashi na farko: basagin al'adane saboda yarinta ma'ana batakai lokacin al'adaba gashi mijinta ya rabu da ita, sai kashi na biyu :wadanda basa ganin al'ada saboda tsufansu don sun wuce lokacin al'ada. To wadannan matan da basa ganin al'ada ko saboda karancin shekaru ko kuma saboda angirma, iddarsu itace su lissafa wata uku. Alllah Madaukakin sarki yana cewa " Kuma matayen da suka debe tsammani daga al'ada daga matanku idan abin ya rikice musu to iddarsu itace wata uku, da kuma ma wadanda basu fara ba" Suratut-Talaq, aya ta :4.
(4) Macan da ka rabuda ita kafin Tarewa. Ita matar da aka rabu da ita kafin su san junansu ita da mijin, babu wata idda da zata yi, kawai inta sami wani alokacin sai adaura aure, (sabanin rasuwa idan rasuwa mijin ya yi kafin su tare za tai takaba). Domin Allah yana cewa " Ya ku wadanda sukai Imani, idan kuka auri mata mummunai sannan kuka sake tun kafin ku sadu da su, ba ku da wata idda a kansu (matan) da za su yi" Suratul-Ahzab, aya ta :49.
Kammalawa. Ina fatan cikin wannan dan takaitaccan bayanan da suka gabata sun dan warware mana madansu al'amurran da suka shafi Idda, da kuma irin yadda musulunci ya haskaka mana rayuwarmu. Ni ina bada shawara ga dukkan wanda wadansu al'amurran addini suka shamasa kai, da kada yai kasa agwiwa ya garzaya makaranta ya yi tanbaya, masu iya maga suce 'Tambaya mabudin ilimi, amma azauna haka ko unkula gaskiya ba zai haifadda Da me ido ba, kuma wadansu hakkokinshi da damar da musulunci ya bashi ba zai sansu ba. Allah yai mana jagora kuma ya tabbar da dugadugammu kan wannan addin amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda Minna,
jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a 08064022965,
ko kuma a Imei : aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI #1
Gabatarwa:Da sunan Allah Maiyawan rahama Mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halitar Allah Annabi Muhammad, da SahabbanSa da Iyalan gidanSa amin. A wannan karan zamu gudanar da bayani ne kan yadda Addinin musulunci ya tsara yadda za'a gudanar da saki, batare da ancutar da Mata ko miji ba muddindai anbi wannan tsarin. Da zaran ance saki sai gaban namiji ko mace ya fadi, ko menene dalili? Musulunci bai shara'anta sakiba don cutar da wani ban gare, asalima musulunci ya shar'anta hakanne don ceto su daga muwuyacin hali, yana daga cikin rahamar musulunci tabbatar da saki, domin yana daga cikin mizar musulunci bai yadda a cutar da kowa ba, saboda haka idan akace a zauna babu maganar cewar akwai rabuwa ga duk wanda yaga anzalince shi kuma ya yi iyakar hakurin da zai iya yi, to wannan zai ba abokin zamanshi cewar shimafa yana da gata a musulunci, da yawa akan sami na miji yana dandanawa iyalin shi azaba, to yanzu sai kace yaya?, ko kuma matar tana gasawa maigidanta aya a hannu, to ananfa dole ne asa ido domin tabbas wani na matukar cutar da dan'uwansa kuma asan wanna mataki za'a dauka, amma musulunci tuni ya dauki matakai daba-daban domin shawo kan al'amarin tun kafin yakai ga rabuwa.
Kandagarkin da musulunci ya yi.
Lalle ne musulunci ya yi kandagarki don hana rabuwar aure, ta yadda ya umarci dangin miji dana mata dasu tura wakilai guda-daga daga kowane bangare na miji da mata a lokacin da suka ga cewa lalle ka akwai sabani tsakanin wance da wane, su wadannan wakilai zasu nazarci dukkan bangarorin biyu su kuma yi kokarin daidaita al'amarin. Allah yana cewa " Idan kuka ji tsoron sabanin dake tsakanin su (miji da mata) to ku tura wani mai hukunci daga dangin sa da kuma mai hukunci daga danginta, muddin sukai nufin gyara to Allah zai daidaita tsakanisu"! Suratun-Nisa'I, aya ta :35. sanan Allah yana cewa adai cikin wannan Surar a aya ta 128 " Sulhu dai shine mafi alheri" sabo da haka a wannan bayani ya nuna mana lalle musulunci ya kula da dukkanin bangarori biyu (mata da miji), domin ganin kada rabuwa ta auku, saboda haka yana da 'yau mutun ya iya daurewa akan wani hakkinshi ya dan sassauto domin ganin ansami daidaituwa, domin daidaituwa ta fi rabuwa muddin ba akan asabawa Allah da Ma'aikinShi bane. Sauda da yawa mata sunyi hakuri da wani hakkinnasu kamar yadda mazan suma sukai hakuri da nasu domin ganin aure ya tabbata, masu iya Magana na cewa 'Tsakanin harshe da hakorima ana sabawa' wai 'zo muzauna zo musaba' saudayawa wadansu abubuwan basukai atada jijiyar wuya ba sai kaga za'a ba hammata iska, Allah ya sawwake.
Adadin Saki!
Idan Allah ya kaddari sai an rabu tofa ba makawa sai hakan ya faru, to amma ya addinin musulunci ya tsara yadda sakin zai kasance? Kafin zuwan addinin musulunci mutanan jahiliyya sun kasance suna sakin mata yadda suka dama
ba wani adadi, sannan idan mijin ya ga ta kusa kamma idda sai ya dawo da ita, wannan ba sau daya ba, ba kuma sau biyu ba, yazamana suna azabtar da mata akan wannan mummunar al'ada, sai mace ta zauna shekara-da- shekaru ita ba mai mijiba kuma ba kuma mara mijiba, domin idan ya saketa ta kusa kamala idda sai ya dawo da ita, idan aka dan kwana biyu sai ya sake sakinta, da musulunci ya zo sai yai wa tufkar hanci, domin gallazawa mata a irin wannan bai kamata ba, musulunci yace ' Sakin da zai yiwu ai komai akanshi karo biyu ne' Suratul-Bakara, aya ta :229. anan sai aka nuna mana mutun zai iya sakin medakinshi kuma ya iya yin kome karo biyu, anan wata hikima ta musulunci sai yace saki sau biyu, domin ya nuna maka cewa abin da akafi so shine kayi daya sannan kasake yin dayan domin idan kai biyun lokaci guda tofa damarka ta kome daya ce ba biyuba, sabo da haka har idan ya zama ba makawa to sai kai dayan domin wata damarkace ka ajema kanka. Idan kai kake da laifi zaka gane idan kuma ita ce zata fadaka, idan ba hakaba sai ka kara gudan wani lokaci ya zama biyu kenan, to daga nan sai kowa ya shiga taitayinshi ya kuma kula da hakkokin da musulunci ya dora akan kowannensu domin ana kara saki na uku to ba kome ba biko sai kuma wani jikon, domin sai ta kammala idda ba kuma a gidanshi ba, sannan sai ta auri wani mijin ya dan-daneta ta dan-daneshi tasu ta hadasu sun rabu ko ya rasu sannan ya fito cikin 'yan-takara, dirkashi! Domin Allah maigirma da daukaka yana cewa " To idanfa ya saketa (saki na uku) bata halatta a gareshi hassaita auri wani mijin da ban" Suratul-Bakara, aya ta : 230. Kuma bayani ya tabbata daga Ma'akin Allah cewa saisun dan-dani juna. idan kai laka'ari ai anbashi damar yabi a hankali amma yai gaggawa, zaka ga wani duka biyun yake yi lokaci guda wani ukumma kwata-kwata kenan (malam mai gaba daya) sannan ya zo yana neman wai malamai su yi mishi fatawar yiwuwar dawo da ita, dankari!. Yanzudai saki ya auku to menene abinyi?
Idda
Idan sakin da akai bai wuce daya ko biyuba to matar zatai iddar ta ne a dakinta, bai halatta miji ya fitar da ita daga dakin, balle har ya watso mata kayan ta waje ko ya dakko mota akwashe mata kayanta, ko kuma ita tace ai tana da gidan ubanta bari ta tafi da dai sauran irin wadannan kazaman maganganu da musulunci bai amince da su ba, Allah Yana cewa " Kada ku fitar da su daga dakunan su, su kuma kada su fita sai dai idan sunzo da wata alfasha bayyananniya, dukkan wadannan dokokin Allah ne kada ku ketare su, dukkan wanda ya ketare dokokin Allah tofa hakika ya zalinci kanshi" Suratut-Talaq, aya ta :1, to anan zakaga lalle irin yadda ake gudanar da rabuwar aure hakika abin yana bukatar gyara sosai wannan fa gamu musulmai da muka yadda da dokokin da Allah ya dora mana, ya Allah ka yafe mana, kuma ya Allah kada ka kamamu da abinda wawayencikimmu suka aikata, amin. Me cece hikimar yin hakan mace tai idda a cikin dakinta?
Hikimar Idda a dakin aure.
Lalle ne dukkan abinda Allah madaukakin Sarki ya tsara mana akwai hikimomi da alherai masu yawa agaremu munsani ko bamu sani ba, kuma ba'a dora mana cewa dole sai munsan hikimar hakan kafin mu ai watar da abida aka umarce mu. Tabbas mutuminda ya rabu da medakinshi ta hanyar saki yada ko biyu, matar shi ce fa , domin inka lura ai ba zaka bar wani ya zo zawarciba, inkuma ka rasu a wannan lokacin kafin ta kamma idda zata gajeka, kuma zatai maka takaba (kamar yadda ya gaba a makalarmu metaken Takaba a musulunci) to anan tunda tana Idda a gidanka zaka dawo da ita aduk lokacin da kaso ba tare da ansake daura aureba domin bata kamala Iddaba, kuma ba saika ta tuttura masu bikoba, wannan shi ne ma'anar fadin Allah daya ke cewa "Baka sani ba ana fatan Allah ya kawo wani sabon al'amari" Suratut-Talaq, aya ta :1, to amma sai wannan damar da Maigirma da daukaka ya bamu itama ana wasa da ita, bayan da mutun ya sabawa Mahaliccin shi sannan matar tana nema ta gagareshi, galibi kuma alokacin ba wacce yake so inba itaba, dabara kaga tana neman ta karewa kada. Saidai kamar yadda ishara ta gabata a baya matar da zatai idda a dakinta itace matar da saki daya ko biyu ya rabasu amma matar da saki ukune nan ba magar yin idda a dakinta, saigida!. Saidai akwai abin tanbaya anan shin akowanne lokaci ya halatta mutun ya rabu da medakin shi?.
Lokotan Saki da musulunci ya amince da su.
Anan nake ceawa lalle yana daga cikin irin gatan da musulunci ya nuna mana cewa ba'a sakin mace lokacin da take cikin al'ada. Kuma idan mutun ya aiwatar da sakin ta saku kuma dole ya mayar da ita cikin matanshi, inyaki kuma alkali ya hukunta shi, sabo da Sayyidina Umar Allah ya kara masa yarda ya tambayi Ma'aikin Allah Tsirada amincin Allah su tabbata agareshi, cewa danshi Abdullahi ya saki matar tana ckin al'ada. Sai Ma'aikin Allah ya umarci Sayyidina Umar daya umarci dannashi Abdullahi ya dawo da ita, sannan tana karkashinshi hassai ta kammala wannan al'adar ta sakeyin wata ta kammala sannan in yaga yiwuwar ya saketa sai ya saketadin, kuma aka lissafa wannan sakin cikin sakinna shi, Bukhari ya ruwaito wannan hadisin kuma shine hadisi na : 4908, 5252 ,5253 da Muslim. To idan mutun ya saki matarshi shikenen ba dai za'a raba kirki da itaba, ma'ana bata cikin matan da za'ai karba-karban girki da su, to haka za'a kyaleta? A'a za'a bata :
Kwabo kashewa.
Yana daga cikin hakkin dukkar matar da mijinta ya saketa da ya bata kwabon batarwa, wannan shine malamai suke kira Mut'atuttalaq, domin zata sai sabulu omo katin waya da dai sauransu, musulunci bai kayyade gwargwadon nawa za'a bayarba saidai ya fadi a wurare da dama kowa zaiyine daidai karfinshi, sabo da haka mutumin da yake da damar yaba wacce ya saka Naira dubu 40, misali sai yabata N 10,000, wannan bai yiba sai ya cika ko ta kaishi koto, haka kuma mutumin da bashi da karfin haka baya taba halatta a tilasta mishi sai ya bayar da hakan, musulunci cewa yayi kowa daidai karfin shi, Allah yana cewa cikin Suratul-Bakara aya ta :236 "Kuma ku jiyar da su dadi, me yalwa gwargwadon karfinshi, kuma mara yalwar arzikima gwargwadonshi" ayoyi akan baiwa matar da aka saka kudin kashewa sun memetu a wannan surar aya ta :241 da Suratul-Ahzab,aya ta :28 data 49, duk wadannan suna daga cikin dinbin ayoyin Alkur'ani mai girma da suke ceto mata daga cikin bakin kangin da suka sami kansu a tsarin da bana musulunci ba. kasancewar al'amarin rabuwar aure ba haka yake sakakaba. Kamar yadda alokacin daurin auren saida aka sami shaidu to hakama lokacin rabuwar saida musulunci yabada umarnin.
Shaidawa Dattijai biyu
Abin sanine cewar Dattijai yana nuna mutanan kwarai mutane masu mutunci masu yawan shekaru ko masu matsakaicin shekarune muddin sunkai shekarun girma da sanin ya kamata, saboda haka musulunci yabada umarni shaidawa akalla Dittijai biyu domin tabbatar da saki nawa akai kuma nawa ya rage, amma inba hakaba sai aita gardaddami akan nawa ya auku kuma nawa ya ragedin, Allah Maigirama da daukaka yana cewa " Kuma ku shaidawa Adilai biyu daga cikinku, ku tsayar da shaidar domin Allah" Suratut-Talaq, aya ta:2. to kan lalle akwai kulawar musulunci cikin dukkanin motsi da juyi da Dan-adam yake yi, ya Allah ka tabbatar damu akan wannan addini naka amin.
Kome \ Biko.
Kome kamar yadda bayanai suka gabata yana kasancewa ne lokacin da mutum ya rabu da medakinshi ta sanadiyyar saki daya ko biyu, anan mutun ke kokawar yaga ya mayar da matarshi, amma idan ya kasance sakin saki ukune to kan ai ba maganar biko balle kome. Shi wannan al'amari na kome yana faruwane kafin matar ta kammala Idda, amma idan ta kammala Idda tofa saidai da sabon aure tunda sakin baikai ukuba, amma indai ya kai uku to sai ta yi sabon aure, saboda haka tunda saki dayane ko biyu kuma ta kammala idda bai dawo da itaba to yanzu sai ya fito cikin 'yan-takara, idan Allah ya sa ya kai labari to idan kuma ya sha kaye sai hakuri. Amma idan bata kammala Iddaba to mijin shi ke da damar ya mayar da ita ba tare da wani ya yi kaka gida cikin lamarinba muddindai sunyi nufin gyara(wato miji da mata) Allah Maigirma da daukaka yana cewa "Kuma mazajansu sune mafi cancantar su mayar da su (matansu) matukar sunyi nufin gyara" Suratul-Bakara, aya ta : 228, wannan shike nuna cewa duk lokacin da miji ya mayar da matar muddin akwai nufin gyara babu wani ta koma kawai.
KammalawaDaga dukkanin bayanan da suka gabata bayanai sun bayyana karara na gata da jinkai da musulunci ya yi mana, domin babu wani tsari a duniya da yake da irin wannan al'amari filla-filla ya fayyace tsakanin zare-da-abawa, musammamama mata, domin zakaga duk wani tsari da ba musulunci ba to bautar dasu yake kai tsaye ko a fakaice, amma lalle musulunci ya yi mata gata saidai idan ta jahilceshi wannako babbar cuta ce, Allah ya tsaremu amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a 08064022965,
ko kuma a E-mail: aliyusadis@gmail.com

Subscribe to:
Posts (Atom)