Thursday, December 24, 2009

TAKABA A MUSULUNCI

Gabatarwa:
Da sunan Allah Maiyawan rahama Mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halitar Allah Annabi Muhammad, da SahabbanSa da Iyalan gidanSa amin. Muna son a wannan lokacin muyi bayanin yadda addinin musulunci ya haskaka duhun da duniya ta dade a ciki, ayayin yin takaba lokacin da mace megidanta ya rasu, ta yadda kowacce kabila take yi yadda ta tashi ta ga haka mutananta ke yi , a irin wannan lokacinne mata suke dan-dana kudarsu, domin suna kan wani tsari da Allah Madaukakin sarki bai turo wani Annabi da wannan tsarin ba. Ayau zamuyi kokarin fayyacewa tsanin zare da abawa ne, akan yadda takaba take a musulunci, da kuma irin gatan da musulunci ya yi wa mata. Asha karatu lafiya Allah yai mana jagora amin.

Mecece Takaba?: Takabadai itace" Zaman da mace zatayi bayan rasuwar megidanta, na wadansu kwanuka sanannu, batare da ado da kwalliya ba, ba kuma da yin wani aure ba, ko yi wa wani alkawari, ko sanya dukkan abinda zai ja hankalin wani ba, na tufafi ko kayan karau." Awanna bayani daya gabata zamu tsinkayi abubuwa masu yawa, wadanda kusan za mu bisu a hankali gaba-gaba domin fayyace su.(anan Takaba ta sha babban da Iddar saki, wadda muke fatan a wani lokaci muyi bayaninta, in Allah ya yarda).

Wacece mai yin Takaba?: Matar da zata yi zaman takaba, itace dukkar matar da mijinta ya rigamu gidan gaskiya, tana matarshi, sunyi saduwar aure ko busu yi ba. Anan zamu fahimci cewa muddin akwai igiyar aure a tsakanin su, to za ta yi takaba. Misali (Allah ya kiyaye) idan aka daura auren mutun da karfe 2:30 na rana, sannan bayan minti 30 ko awa guda ya rasu, to fa takaba ta ganta, kuma zata ci gadonshi, domin matar shi ce. Kamar yadda Abdullahi Dan Mas'ud Allah ya kara masa yarda, ya bada amsa lokacin da aka tanbaye shi, akace da shi : "Mutunne ya auri mace amma bai bayyana mata sadakinta ba, kuma bai sadu da ita ba har ya rasu? Sai Dan Mas'udin ya ce" Zan bada amsa da fahimta ta, idan na yi daidai to daga Allah ne, idan kuwa ban yi daidai ba to daga Shaidan ne, Allah da Ma'aikin Shi sun barranta da wannan amsar. Tana da sadakin mata ire-irenta, ba kari ba ragi, kuma za ta yi Takaba, sannan tana da gado". Sai Ma'akil Dan Sinan wanda yake daga kabilar Ashja'a ya mike yace: "Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, ya yi irin wannan hukuncin da ka yi ga Rauh Diyar Washik –wata mace ce daga cikin mu, sai Abdullahi Dan Mas'ud yai farinciki da wannan Magana tashi" Imam Ahmad da Abu-Daud da Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah suka ruwaito wannan hadisin, kuma Tirmizi ya Inganta shi.
Hakanan kuma inda mutun zai rabu da mai dakinshi da saki daya ko biyu, sannan ya rasu kafin ta kammala iddar saki, shikenan sai ta koma takaba, matarshi ce yana da dama yado da ita a ko yaushe muddin bata kammala idda ba.

Gwargwadon kwanakin Takaba: Alokacin da mutun ya rasu, to zaibar iyalin shi a dayan halaye biyu, kodai ta zama tanada Juna biyu ko kuma bata da shi. Idan bata da juna biyu to Takabarta itace "Wata hudu da kwana goma" Kamar yadda Allah yace cikin Suratul-Bakara "Kumma dukkanin mazan dake rasuwa daga cikin ku subar matansu, to matan za su zauna wata hudu da kwana goma" aya ta :234.

To amma idan ya rasu ya barta da juna biyu, a wannan lokacin karshen Takabarta shine ta sauke abinda take daoke da shi, koda ko ranar da ya rasu ne, Misali ya rasu 7:00 na safe ita kuma ta haihu 7:10 na safiyar, shi kenan ta kammala takabarta, idan wani ya gani ya ce yana so aka daura aure 2:30 na ranar aure ya dauru(ana karbar gaisuwa ana daurin aure) dalii kuwa shi ne. fadin Allah a cikin Suratut-Talak aya ta 4 " Kuma dukkanin mata masu juna biyu to lokacinsu shine su sauke abinda suke dauke dashi" da kuma Hadisin Subai'a Al-aslamiyyah, " Ita ta kasance tana auran Sa'ad Dan Khaulah, shi kuma ya fito ne daga gidan Amir dan Lu'ayy, yana daga cikin wadanda suka halarci gwabzawar Badar, sai ya rasu yabarta a hajin bankwana tana da juna biyu, bata ko jima ba bayan rasuwar shi saita haihu, a lokacin data kamma biki sai ta yi kwalliya, sai Abu-Sanabil Dan Ba'akk ya zo wurinta, shi kuma ya fito ne daga gidan Abduddar, sai yace da ita " Lafiya na ga kin cancara ado?, ko kina son ki yi aure ne? Na rantse da Allah lokacin auranki bai yi ba, harsai kin yi wata hudu da kwana goma.
Sai Subai'a ta ce "Yayinda ya fada min haka, maraice na yi sai na tattara kayana naje wurin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, na tambaye shi hakan, sai ya ban amsa da cewa ai na kammala Takabata tun lokacin dana haihu, ya ban dama da inyi aure a duk lokacin da naga dama". Wanna hadisin Bukhari ya ruwaito shi, hadisi na 4909 da kuma na 5318, hakanamma Muslim da Abu-Daud da Tirmizi da Nasa'I, da Ibnu Majah. Inbu Shihab yake cewa : "Bana ganin akwai wani laifi idan ta yi aure lokacin data haihu, koda tana cikin jinin biki, saidai kawai mijin ba zai kusanceta ba sai ta yi tsarki.

To haka kuma idan yarasu ya barta da juna biyu na kimanin wata daya ko ma baikai haka ba, tofa sai ta haihu ka ga wannan Takabarta na neman wata tara koma fiye kenan domin dai sai ta sauka. Zai iya yuwuwa alokacin da maigida yarasu bata samma tanada juna biyu ba, wata kila a saduwarda bai huce masa saura minti 30 aduniya ba ta sami juna biyun, to kaga wannan zata fara lissafin kwanaki ne na Takaba sai daga baya Takabarta ta koma sauraran haihuwa, Allah ya sauketa lafiya shi kuma maigida Allah yajikan shi. Wannan ya nuna mana cewa mutun zai iya rasuwa ya bar matanshi, amma wata ta riga wata kammala Takaba, domin musulunci bai yadda a dauki dan wani gida akai wani gida ba, wannanfa ko da mace mai Takaba ta samu kwanciyar ciki, domin ciki yakan kai shekara 4 ko 6 kamar yadda malamai sukai bayani, duba Tafsirin Adhwa'ul Bayan Suratur-Ra'ad aya ta :8. Abinda ake nufi data sauka shi ne, ta sauke duk abinda ke cikinta, ya zo da rai ko bai zo da rai ba, saboda haka ko bari tayi ta kammala idda ko Takaba idan aka samu shaidu akan hakan, koma ace siffar mutun ta bayyana a tare da shi barin, idan mai Takaba ta haihu sannan ingantaccen bincike yanuna cewa tana dauke da 'ya'ya biyu ne kuma gashi ta haifi daya, tofa bata kammala ba sai ta haifi na biyun, domin abinda ake bukata ta sauke duk abinda take dauke da shi.

Yaushe za'a fara lissafin Takaba?. Za'a fara lissafin maitakaba ne daga lokacin da megida ya rasu, ba wai kamar yadda akebin al'ada ba wai sai ran juma'a, ko dako ya rasu ranar asabar, sannan ai mata wankan shiga Takaba, wannan kwata-kwata ba shi da alaka da addinin musulunci, sannan ace za'aba maitakaba wuka ko sanda, in zata shiga makewayi ta rike, kuma ta tafi a hankali wai mijinta na biye da ita, a firgita baiwar Allah. Saboda haka daga ranar da mijinta ya rasu daga ranar ta fara idda, yana rasuwa ta shiga Takaba. Saboda haka Malamai sun yi maganganu biyu, idan ya rasu bata sami labarin rasuwarshi ba, sai bayan wata hudu da kwana goma, ko bayan haihuwarta sannan ta sami labarin shikenan ta kamala takabarta, adaya daga cikin maganganun, Magana ta biyu kuma shi ne zata fara lissafi daga ranar da labari ya zo mata, in kuma bayan wata biyune da rasuwar shi ta sami labarin rasuwar shi. Sannan kuma babu wani wankan fita daga Takaba a mulunci, da zaran ta kammala wata hudu da kwana goma, ko ta haihu to ta kammala Takaba, saboda haka duk abinda ya haramta a gareta lokacin tana Takaba to yanzu ya halatta ta yi domin ta kammala takaba.

To me ya haramta ga maitakaba? A dunkule abinda ya haramta ga maitakaba shine 'Ado da kwalliya, da kuma yin aure ko yi wa wani al'kawari, ko fita ba tare da wani dalili na Shara'a ba. anan yana da kyau mu banbance tsakanin Kwalliya da Tsafta ya haramta ta yi kwalliya da ado, kamar sa Tozali, Kunshi, sa hoda yin dizayin janfarce janlebe, sanya tufafi na ado sa turare –indai ba bayan ta kammala al'ada ta diga shi akyalle domin tasa agabanta saboda rage karnin jiniba- da dai dukkan wani nau'I na ado ko kwalliya, koda ko rangada kitsone. Amma ita tsafta babu wanda ya hana maitakaba yin ta, yin wanka kullun yin kitso idan bukatar hakan ta taso ba kuma ayi don kwalliyaba, suma sun san na kwalliya kuma kun san wanda za'adan kakkama alallaba, kuma ya halatta ta yi wanki domin duk suna cikin tsafta ba kulliyaba, sannan ya halatta ta share dakinta ba ta zauna kamar wata mai haukaba, sannan dukkanin wadannan abubuwa babu wata rana da aka ajeye musu don gudanar da su, kamar ace 'sai juma'a ko laraba' za ta yi aduk lokacin da bukatar hakan ta samu. Anan nake cewa lallai akwai babbanci wanda ba zai yiwu ahadaba da irin yadda musulunci ya fayyace mana al'amura dalla-dalla ya haskaka mana su, da kuma irin yadda al'adu sukai kane-kane cikin harkar Takaba, Allah ya sauwake.

Kammalawa: daga dukkanin bayanan da suka sauwaka zamu fahimci irin gatan da musulunci ya yi mana shi, irin saukin da ya nema mana, musamman idan muka kalli yadda Allah ya tsara mana kuma muka kalli yadda ake yi a al'ada lallai zamu fahimci ya zama wajibi mu dada godewa Allah akan wannan ni'ima da Ya yi mana.

Aliyu Muhammad Sadisu,Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda Minna, jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a +2348064022965,

 ko kuma a Imei : aliyusadis@gmail.com
Ko  a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-
musulunci.blogspot.com

Littafan da aka duba.
1- Alkur'ani Maigirma.
2- Tafsirin Ibnu Kasir
3-Adhwa'ul-Bayan Na Muhammad Amin As-Shankiti
4- Ahkamul-Kur'an Na Ibnul-Arabi
5- Fat'hul-Bari Na Ibnu-Hajar
6- Al-Mughni Na Ibnu Kudama
7- Taisirul-Allam Na Abdullahi Bassam.

1 comment:

  1. Assalamu Alaikum, lallai na ziyarci wannan munbari na ka, kuma na gamsu da sakonnin da ke ciki. Dangane da abinda ya shafi tsarin Mudawwanar kuma, yayi insha'Allah. Allah tabbatar da alheri, amin.

    Baban Sadiq

    ReplyDelete