Wednesday, December 16, 2009

RABUWAR AURE DA IDDAH A MUSULUNCI #2.


Gabatarwa:Bayanda a kasidar data gabata mukai takaitaccan bayani kan yadda musulunci ya tsara yadda ya kamata rabuwar aure ta kasance, da kuma yadda ya baiwa ko wanne bangare na ma'aurata 'yancinshi, da kuma yadda bayanai suka gabanata na cewa babu wani tsari da yayiwa mabiyanshi irin wannan tsarin inba musulunci ba. to ayau za muyi bayani abinda Allah Maigirma da daukaka ya sawwake mana na yadda Idda kuma zata kasance bayan anyi saki ko anrasu Allah yai mana jagora amin, asha karatu lafiya.
Kadan daga Hikimomin Idda.

Yana daga cikin hikimomin da Allah ya sanya cikin Idda kada adauki dan-wani gida akai wani gidan, domin idan mutun ya rabu da maidakinshi takan yiwu a wannan makon ansami juna-biyu, idan tai aure batare da yin iddaba bayan kwana biyu ko uku ko makamantansu da sakinta shikenan ta tauki dan-mijinta na farko ta kai gidan mijinta na biyu wanda yake wannan bakaramin zunubi bane da barna a harkokin zamantakewarmu, saboda haka musulunci ya tabbatar da cewa ba zatai aure na biyuba sai antabbatar da bata da juna biyu saboda haka aka shar'anta takaba, saidai kawai idan aka saketa kafin asadu to awannan lokacin babu wata Idda da zatayi, kamar yadda bayanai zasu zo nan gaba kadan idan Allah ya yarda. Haka kuma yana daga cikin Shar'anata Idda fatan bijin ya maida ita matar ta shi kafin ta kammala iddar idan sakin baikai ukuba, kamar yadda bayani ya gabata a makalar farko inda muka kawo fadin Allah Maigirma da daukaka " Baka saniba ana fatan Allah ya aiwatar da wani al'amari" Suratut-Talaq, aya ta 1, domin ba din da iddarba da shikenan kana sakinta yau gobe sai wani ya aura taimaka Fintinkau. Kazalika yana daga cikin manufofin yin Idda juyayin megidanta daya rasu ko dako basu taba saduwaba, kamar yadda bayani ya gabata arubummu metaken "Takaba a Musulunci". Saboda haka ko iyanan muka dakata kasan Allah Maigirma da taukaka ya sanya hikimomi masu tarin yawa cikin Idda, munsan su duka ko bamu sansu ba. Allah mungode maka.
Karkasuwar Idda a musulunci.

Idda ta kasu kashi biyu a musulunci, wato Iddar mamaci wacce muke ce mata takaba, da kuma Iddar Saki. Itadai iddar mamaci\Takaba mungudanar da bayanai akanta, saboda haka awannan karon bayanai zasu kasance ne kan "Iddar Saki"! Allah yai mana jagora amin,
Karkasuwar mata

Da farko yana dakyau mufahimci cewa mata sun kasu kashi-kashi lokacin da
zasu rabu da mazajansu, saboda haka ko dole iddarsu tasha ban-ban, anan zamu fahimci mutun zai iya rabuwa da matanshi biyu ko uku lokaci guda amma wata ta riga wata kamma Idda. Yanzu ga kasha-kashannasu :

(1) Mace me juna biyu : Alokacin da mutun ya rabu da medakinshi tana da juna biyu to ita Iddarta itace ta sauke abindake cikinta, ma'ana inda zai saketa da karfe 5:00 na yamma sai ta haihu karfe 5:20 na yammar shikenan ta kammala iddarta inta sami wanda zata aura aranar ya yi sai adaura auren da 6:00 na yammer. Yanzu ya zama dan-kallo, saidai kawai idan ya kuru Allah ya taimakeshi saki daya ne ko biyu, sai ya bogo fasta ya shiga cikin 'yan-takara wata kila ya samu ya kai labari. Allah yana cewa " Kuma wadanda suke da juna-biyu to lokacin (kammala Iddarsu shi ne ) su sauke abinda suke dauke dashi" Suratu-Talaq, aya ta :4, hakanan kuma inda zasu rabu juna biyunnata bai huce wata dayaba saidai ta haife abinda take dauke dashi, kamar yadda wannan bayanin ya gabata a ' Takaba a Musulunci' mun dan fadada bayanai a lokacin.

(2) Mace meganin Al'ada. Itakuma matar da take ganin al'adarta iddarta itace samun tsarki uku, saboda haka idan mutun ya rabu da maidakin shi, iddarta itace ta yi tsarki uku, shi kuwa tsarki uku ya sha ban-ban da wata uku, domin mace zata iya tsarki a kwanakin da suke kasa da wats uku, haka kuma zata iya iya tsarki uku a watannin da suke sama da haka, akwai matar da ashekara sau daya take yin al'ada to kaga wannan iddarta zata tasamma shekaru kenan. Allah yana cewa " Dukkani matan da aka sakesu zasu zauna da karankansu (suna jiran) tsarki uku" Suratul-Bakara, aya ta: 228 Idan kuma tana cikin lissafa al'ada sai ya bayyana tana da juna-biyu, to anan iddarta zata koma iddar mai juna biyu saitai zaman haihuwa (Allah ya sauke ta lafiya amin).

(3) Mace mara ganin al'ada. Matan da basa ganin al'ada sun kasu kashi biyu, kashi na farko: basagin al'adane saboda yarinta ma'ana batakai lokacin al'adaba gashi mijinta ya rabu da ita, sai kashi na biyu :wadanda basa ganin al'ada saboda tsufansu don sun wuce lokacin al'ada. To wadannan matan da basa ganin al'ada ko saboda karancin shekaru ko kuma saboda angirma, iddarsu itace su lissafa wata uku. Alllah Madaukakin sarki yana cewa " Kuma matayen da suka debe tsammani daga al'ada daga matanku idan abin ya rikice musu to iddarsu itace wata uku, da kuma ma wadanda basu fara ba" Suratut-Talaq, aya ta :4.

(4) Macan da ka rabuda ita kafin Tarewa. Ita matar da aka rabu da ita kafin su san junansu ita da mijin, babu wata idda da zata yi, kawai inta sami wani alokacin sai adaura aure, (sabanin rasuwa idan rasuwa mijin ya yi kafin su tare za tai takaba). Domin Allah yana cewa " Ya ku wadanda sukai Imani, idan kuka auri mata mummunai sannan kuka sake tun kafin ku sadu da su, ba ku da wata idda a kansu (matan) da za su yi" Suratul-Ahzab, aya ta :49.
Kammalawa. Ina fatan cikin wannan dan takaitaccan bayanan da suka gabata sun dan warware mana madansu al'amurran da suka shafi Idda, da kuma irin yadda musulunci ya haskaka mana rayuwarmu. Ni ina bada shawara ga dukkan wanda wadansu al'amurran addini suka shamasa kai, da kada yai kasa agwiwa ya garzaya makaranta ya yi tanbaya, masu iya maga suce 'Tambaya mabudin ilimi, amma azauna haka ko unkula gaskiya ba zai haifadda Da me ido ba, kuma wadansu hakkokinshi da damar da musulunci ya bashi ba zai sansu ba. Allah yai mana jagora kuma ya tabbar da dugadugammu kan wannan addin amin.

Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda Minna,

 jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a  08064022965

ko kuma a Imei : aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com


No comments:

Post a Comment