Friday, September 28, 2012

HUKUNCE-HUKUNCEN LAYYAH


Gabatarwa: Dasunan Allah Mai yawan rahama maiyawai jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a wannan karon za mu karkata akalar mu zuwa wani bangare da ya ke hararomu a 'yan kwanakin nan, wannanan bangaran kuwa shi ne na LAYYAH! Domin mu ga yadda musulunci ya tsara mana komai abinda ya rage kawai a garemu shi ne bi, komai angama, Allah tabbatar da duga-dugammu akan tafarkin Ma'aikin Allah.
Mecece Layyah?: "Layyah, ita ce dukkan abinda ake neman kusanci ga Allah ta sanadiyyar yankashi ko soke shi, a kwanukan yanka na abinda ya shafi dabbobin gida"( wato: Rago da tinkiya, akuya da taure, sa da saniya, rakumi da rakuma). Wannan shi ake nufi da layya, wanda anan kawai mai karatu yasan wanne yanka ne na layyah? Wannene kuma na aci nama kawai. Yanzu inda za mu bi wannan ta'arifin a hankali zamu ga cewa, da aka ce ""Layyah, ita ce dukkan abinda ake neman kusanci ga Allah ta sanadiyyar yankashi ko soke shi," wannan yana nuna cewa idan ba'a nufaci Allah da yankanba to abinda aka yanka zai amsa sunan Layyah kamar cewa 'Sabo da yara' da makamantan irin wadannan maganganu day a kamata a kauce musu. Amma da akace ' a kwanukan yanka' wannan ya nuna idan akai kafin wadannan kwanuka ko bayansu abin yankan bai zama Layyaba. Da aka ce 'na abinda ya shafi dabbobin gida' wadannane kawai dabbobin da ake layya da wadanda aka ammata a sama cikin baka biyu.
Tabbatuwar Layyah Ashara'a: Layyya ta tabbata da fadin Allah Mai girma da daukaka a Suratul-Kauthar aya ta 2. "To kai sallah don Ubangijinka, kuma ka soke abin Layyarka" wato ya yi Sallar idi, sannan kuma iyi sanka, adaya daga cikin maganganun malaman Tafsiri. Sannan kuma Layyah ta tabbata da aikin Ma'aikin tsira da a mincing Allah su tabbata agashi domin ya yanka Layyarshi da hannun mai alfarma ya yanka ruguna biyu masu kaho, kamar yadda Anas ya ruwaito, kuma malamai sunyi Ijma'I akan haka.
Hukuncin Layyah: Sunna ce maikarfi ga wanda ya sami iko mace ko namiji, ba wajibi bace saidai idan mutum ne ya dorawa kansa, kamar ya yi alwashi cewa In ya samu wannan aikin ko in ya ci jarabawannan ko in medakin shi ta sauka lafiya sai ya yi layya, to da zarar abinda ya anbata ya auku layya ta zama wajibi akanshi.
Falalar Yin Layyah: Nana Aishah Allah ya kara mata yarda ta ruwaito cewa lallai Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce " Dan'adam bai taba yin wani aiki aranar Babbar Sallah ba da yafi soyiwa a gurin Allah  kamar zubar da jinni ba. Lalle tabbas zata zo (tabbar layya) ranar kiyama da kahonta, da gashinta, kuma lallai jinin tabbas yana aukuwa ga Allah a wani wuri tun kafi ya diga a kasa, ku yi ta da dadin rai." Tirmizi ya ruwato shi hadisi na 1493.
Mace Na Layyah?: Anan mu sani duk abibda  shari'ar musulunci ta zo da shi ba banbanci mace da na miji sai abinda dalili ya banbance, saboda haka ya halatta mace ta yi layya kuma mijinta ya yi idan yana da hali hakanan 'ya'yanta, mu sani layyah ba biki bace ibadace da ake baiwa mutum lada idan ya yi kamar yadda akace ya yi kuma ya yi shi domin Allah, anan yana dakyau maza su sani iyalansu ba gasa suke da su ba, ibadace da Allah Ya shar'anta ta akan maza da mata.
Ya Halatta Aci Bashi?: E, ya hallata ga mutumin da yake da tabbas na kudi ya ci bashi domin ya sayi dabbar da zai layya da ita, mu lura munce wanda yak e da tabbas, kamar ma'aikacin da yake jiran albashi, ko dankasun da ya sayo kaya ga shi jibge ba'a yana jiran masu saya.
Dabbobin Da Ba'a Layya Da Su: Anan yana da kyau wanda zai yi layyah ya sa ido sosai ya tabbatar da cewa dabbar da zai yanka bata sami kanta cikin wadannan dabbobin da ba'a layya dasu ba, domin mu sani shi Allah ba'a masa karbi kar ka rasa -tsarki ya tabbata a gareshi. Hadisi daga Barra'u dan Azib Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce "Ba'ayin layyah da gurguwa wacce gurguntakatta ta a fili take, hakanan da Mai ido daya wacce hakan a fili yake (ina ga makauniya baki daya?), hakanan da mara lafiya wacce rashin lafiyar tat a a fili yake, hakanan da kyamusassa wacce take bata da mai. Hakanan Aliyu bn Abi Talib Allah ya kara masa yarda, ya ce ' Ma'aikin Allah -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- ya umar ce mu da musa ido sosai akan idanu da kunnuwa, kuma kada muyi layya da mai yankakken kunne ta fuskar tsawo ko fadi na kunnen' Timizi ya ruwaito 1498, duk wannan idan ya bayyana kamar daya bisa uku, dukkanin wadannan bayanai suna nuna mana itafa layya ibada ce yadda ake so zaka yi, ba yadda kai kake so ba, balle ace kwai bage-bagen dabba.
Siffar Ragon Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata aga reshi. Wannan yana dakyau amatsayinka na wanda yake koyi da Ma'aikin Allah kasan Shi da me ya yi layyah? Anas ibnu Malik, yake cewa ''Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya yi layya da raguna biyu, farare masu ratsi baki-baki, masu kaho, ya yankasu da hannunshi, ya anbaci Allah ya yi kabbar''  Bukhari 5565, Muslim 1966, Tirmizi1494. wannan hadisi ba karamin sakwnni yake dauke da su ba, kamar yadda bayanai za su zo nan gaba. Zamu fahimci abinda ya fi shi ne duk mai layyah ya yanka layyar shi da hannun shi, kuma karatun yankan 'Bismillahi Wallahu Akbar. Ya Allah ka karbamin ni da iyalan gidana (in ya sanya iyalan na shi cikin layyar)
Ya Halatta A Hada Kudi Ayi Layyah? Tabbas wanna ba karamar tambaya bace so ake musulmi ya zama da zaran wani abu ya same shi ya san yadda zai warware al'amurra akan karantarwar Annabinshi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Bai halatta sama da mutum guda su taru akan rago ko tinkiya ko taure ko akuya ba, amma ya halatta mutane biyu zuwa bakwai su hada kudi akan sa, ko saniya, ko rakumi, ko rakuma, domin su yi layyah.
Kwanakin Layyah: Abinda aka fi so shine mutum ya yanka layyarsa a ranar sallah bayan ansakko sallah kenan, amma idan hakan bai samuba ya halatta ya yanka washegari wato ranar shadaya idan hakan bai yiwuba ya samu ya yanka wanwashegari wato ranar shibiyu duk wadannanan layyarsu ta yi ba kuma ramuwa suka yi ba.
Yadda Ake Da Naman Layyah: bayan anyanka dabbar kai da ka yi  zaka diba a ciki ka ci kuma zaka bayar da wani kason kyauta wani kuma kabayar sadaka, wato zaka kasa shi gida uku kenana, ya halatta kabayar da shi danye kamar yadda ya hallata kabayar da shi soyayye ko gasasshe, anan idan an tashi rabon bawai lalle zakaba wanda ya baka bane, babban makasudin layyah bayan neman kusanci da Allah shine  al'ummar musulmi su tashi su kasha kwalamar dake cikin wadannan kwanaki da wanda ya yi da wanda bai yiba, kenan ba maganar ka jin-jina nauyin wanda aka kawo maka domin kaima ka maida irinshi.
Kammalawa: Awannan dan-takaitaccan bayani da ya gabata munsan mecece layyah da matsayinta a musulunci, kuma munsan cewa layyah ibasace ba biki bace, sannan maza na yi kuma mata na yi, sannan ba'ace sai mai mata ba ko sai mai miji, kuma munfahimci cewa layyah wata hanyace ta takaita talauci da kwadayi a cikin al'umma, sannan munsan kadan daga cikin hukunce-hukuncenta, Allah nuna mana lokacin ya kuma karbi ibadarmu amin summa amin, ayi sallah lafiya Allah Ya maimaitana cikin koshin lafiya da imani. Naku:
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
 e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu

4 comments:

  1. Allah madaukakin sarki yasakama sheikh da gidan aljanna.

    ReplyDelete
  2. Allah ya saka wa Malam da mafificin sakamako

    ReplyDelete
  3. Allah yasaka da alkhairi,Allah ya ba musulmai ikon saukar da nauyin dake kawunarmu. Ya Allah mai kyawawan suna ya tausaya mana.

    ReplyDelete
  4. Allah ya kasance mana jagora. JazakalLahu khairan.

    ReplyDelete