بسم
الله الرحمن الرحيم
الحمد
لله رب العالمين، والصلاة والسلام على نبينا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين
Gabatarwa: Dasunan Allah mai yawam
rahama mai yawan jinkai, dukkan godiya ta tabbata a gareshi. Tsira da amincin
Allah su kara tabbata ga Annabimmu Annabi Muhammad, da iyalanshi da sahabbanshi
baki daya.
Bayan
haka hakika wannan gidauniya ta Annuriyyah ta nema daga gare ni da in kasance
cikin wadanda za su gabatarwa da Alhazai bita cikin jerin gwanon abubuwan da
yake da alaka da su inda aka fara wannar bita tun ranar lahadin da ta gabata,
matashiyar da zan gabatar da jawabi akai itace: Ziyara A Garin Madina.
Wanda nake rokon Allah da dukkanin sunayansa mafiya tsarki da siffofinsa mafiya
kamala da ya yi mini jagora, ya kuma albarkaci wannan zama namu da wannar
gidauniya ya karba mana ayyukammu, amin.
Wannan
jawabi zai tattaru ne akan:
-
Gabatarwa
-
Shinfida
-
Falalar Birnin Madina
-
Ladubban Zama A Birnin Madina
-
Falalar Sallah A Masallacin Ma'aikin Allah (Tsira
da amincin Allah su tabbata a gareshi)
-
Abubuwan Yi A Birnin Madina
-
Ibadu
-
Wuraren Ziyara Da Takaitaccen Tarihinsu.
Shinfida. Lalle madina wacce take
birnine na Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi)
inda kuma take masaukar wahayi inda Ma'ika jibrilu amintaccen Allah ya dinga
sassauka ga Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi),
birnin da yake shi ne matattarar imani, mahadar dukkanin wadanda suka yi hijira
da wadanda suka tarbesu, hedikwatar musulunci ta farko wanda yake anan ne aka
kafa tutar jihadi, daga nan ne kuma aka fita domin a fitar da mutane daga duhu
zuwa ga haske, daga nan dinne duniya ta dau haske baki daya, nan ne kuma Allah
Madaukakin sarki Ya zabawa Manzan Shi (Tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi) ya zama wurin hijirarshi, a wannan birni kuma ya rayu, kuma a nan
ya koma ga Mahaliccin shi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi),
anan kuma kabarinshi yake wanda yake babu wani mutum da zai iya tabbatar da
inda kabarin wani Abbabi yake inbanda kabarin shi (Tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi). Allah Ya kaimu wannan birni na Ma'aikin shi lafiya,
amin.
A
yanzu haka za mu bi wadancan gabobin da suka gabata daya-bayan-daya Allah Ya yi
mana jagora, amin.
Falalar Birnin Madina: Hakika wannan birni
yana da dunbun daraja da falala wanda yake Allah kadai ya san iyakarsu, ayanzu
haka ga kadan daga cikin abinda ya tabbata daga Ma'aikin Allah (Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi) na falalar wannan birni:
(1) Allah madaukakin sarki ya sanya shi Harami
amintacce kamar yadda ya sanya birinin Makkah harami amintacce, Allah
madaukakin sarki yana cewa dangane da birnin Makkah:
Ma'ana: ''Kuma sukace: Har in mukabi gaskiyar
dake tare da kai za'a fitar da mu daga kasarmu. Sai Allah yace: Yanzu shin bamu
tabbatar musu da wani Harami (na musamman) wanda yake amintacce ba, ana shigo
da dukkan nau'ukan 'ya'yan itatuwa wanda yake arzikine daka garemu?, sai dai
mafi yawansu ba su sani ba''. (Suratul-Kasas, aya ta:57) Allah madaukakin
sarki ya fadi haka a wurare da dama dan gane da Makkah.
Kuma
Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yana cewa
dangane da Madina
(( إِنَّ إِبْرَاهِيمَ حَرَّمَ مَكَّةَ،
وَإِنِّي حَرَّمْتُ اَلْمَدِينَةَ)) رَوَاهُ مُسْلِم
Ma'ana: Lalle (Annabi) Ibrahim
ya haramtar da Makkah, Kuma lalle ni na ramtar da Madina)).
Wannan Hadisi Muslim ne ya ruwaito shi.
(2) Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi) ya kira wannan birni da suna ''Taibah'' wato
daddadan abu, wato kenan birnine mai dadi, mai albarka.
(3) Imani yana tattarewa ya koma wannan birni
mai albarka, Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi)
yana cewa :
مُتَّفَقٌ عَلَيْهِ (( ((إِنَّ اَلإيـمَانَ
لَيَأْرَزُ إِلَى اَلْمَدِينَةِ كَمَا تَأْرَزُ اَلْحَيَّةُ إِلَى حُجْرِهَا
Ma'ana: "Lalle Imani
yana tattara zuwa madina kamar yadda macijiya take tattara a raminta".
Bukhari da Muslim suka
ruwaito.
(4) Birnine da yake
haxiye sauran birane. Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata
a gareshi) ya siffanta ta da cewa garine da yake cinye garuruwa, kamar
yadda yake cewa ''An umarceni –da yin hijira zuwa-wani gari da yake cinye
garuruwa, suna kiranshi da: Yasriba-wato-Madina'' Bukhari da Muslim suka
ruwaito.
Yasriba shine sunan Madina
kafin isar Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi)
da ya isa sai ya canza sunan garin, Allah madaukakin sarki yana cewa –A lokacin
da yake fada mana maganar munafuqai aranar Gwalalo. Ma'ana: Kuma a lokacin da wata
tawaga daga cikinsu (su munamukai sukace) Ya ku mutanan Yasriba baku da matsaya
ku koma….)
(5) Birnine da Allah ya
zabeshi ya zama wurin hijirar manzonshi (Tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi).
(6) Yadda ma'aikin Allah
(Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya nuna darajarta da
girman sabawa Allah a cikinta, Ma'aikin Allah yana cewa:
((اَلْمَدِينَةُ
حَرَمٌ مَا بَيْنَ عَيْرٍ إِلَى ثَوْرٍ، مَنْ أَحْدَثَ فِيهَا حَدَثًا أَوْ آوَى مُحْدِثًا
فَعَلَيْهِ لَعْنَةُ اَللهِ وَالْمَلاَئِكَةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ)) رَوَاهُ اَلْبُخَارِيُّ
وَمُسْلِم.
Ma'ana: Madina Haramce daga
(Dutsan) Air zuwa (Dutsan) Saur, duk wanda ya aikata barna a cikinta ko ya
baiwa mabarnaci mafaka Tsinuwar Allah ta tabbata a kanshi da Mala'iku da mutane
baki daya'' Bukhari
da Muslim.
(7) Addu'ar Albarka.
Yana daga cikin falalar wannan birni addu'ar albarka da ya samu daga ma'aikin
Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), ma'aikin Allah yana
cewa:
اَللَّهُمَّ
بَارِكْ لَنَا فِي ثَمَرِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مَدِينَتِنَا، وَبَارِكْ لَنَا
فِي صَاعِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مُدِّنَا)) مسلم
Ma'ana ''Ya Allah ka sanya
mana albarka a 'ya'yan itatuwammu, ka sanya mana albarka a Madinarmu, ka sanya
mana albarka a Sa'immu, ka sanya mana albarka a mudummu''
Muslinme ya ruwaito.
(8) Annoba da Julal basa
shiga madina. Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi)
yana cewa:
''Mala'ikune akan
ganuwowin madina Annoba bata shigarta haka namma Jujal'' Bukhari da Muslim.
Wannan kadan kenan dangane da birnin
madina banda abinda ya gabata tun a shinfida, sabo da lokaci.
Ladubban Zama A Madina: Lalle duk wanda Allah
ya kaddari cewa yana cikin wadanda za su zauna kwana ko awanni a cikin wannan
birni mai albarka to lalle ya sani cewa wannan ba karamar falala bace da Allah
ya yi masa, sabo da haka sai ya godewa Allah akan wannan falalar, ya kuma kula
da ladubban zama a wannan birni mai daraja kamar haka:
(1) Ka so wannan gari
sabo da falalar da yake da ita, da son da ma'aikin Allah (Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi) yake masa.
Anas Ibnu Malik (Allah Ya Kara mishi yarda)
yana cewa ''Lalle ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi) ya kasance idan ya dawo daga tafiya sai ya hango gine-ginen madina
sai ya gyara abin zamansa, in kuma yana kan dabbane sai ya motsa ta, Saboda son
da yake mata (wato madina).
(2) Ka kwadaitu da
tsayuwa a kan al'amarin Allah, ka zama mai lizimtar biyayyah ga Allah da manzan
Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), kana mai tsananin
kaucewa sabon Allah da bidi'oi domin wadannan al'murra yinsu a harami ba karamin
zunubi bane.
(3) Lizimtar Sallah a cikin
masallacin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi)
kamar yadda bayani zai zo.
(4) Ka zama kyakkyawan
abin koyi, domin fa kana inda daga nanne hasken ya haskaka duniya baki daya.
(5) Ka tuna fa kana inda
nanne masaukar wahayi, kuma inda Allah ya zabawa manzanshi ya zame masa wurin
hijira, kana inda yake nanne matattarar imani, kana inda nance makarantar da
sahabban ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) su
kai karatu kada kai wani aiki da ya sabawa na makarantarsu da malaminsu (Tsira
da amincin Allah su tabbata a gareshi).
(6) Kada kaga tsuntuwa
ka dauka sai dai idan zakai cigiya.
Falalar Sallah A
Masallacin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi).
Hakika sallah a wannan masallaci da
wannan Annabi ya gina tana da matukar falala wacce bai kamata wanda ya sami
kanshi a inda wannan masallaci yake ba ya yi sakaci, hadisai tabbatattu sun yi
bayanin matsayin wannan masallaci da matsayin sallah a cikin shi. Na farko dai
wannan masallaci yana cikin masallatai uku da ake nikar gari domin ziyartar su,
kamar yadda Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi)
yake cewa a hadisin Bukhari da Muslim.
((لاَ
تُشَدُّ اَلرِّحَالُ إِلاَّ إِلَى ثَلاَثَةِ مَسَاجِدَ: اَلْمَسْجِدِ اَلْحَرَامِ،
وَمَسْجِدِي هَذَا، وَالْمَسْجِدِ اَلأَقْصَى)) متفق عليه
Ma'ana: ''Ba'a nikar
gari (don ziyara) sai masallatai uku; Masallaci mai alfarma (dake makka), da
kuma wannan masallacin nawa, (dake birnin madina) da kuma masallacin can nesa
(wandake Kudus). Bukhari da Muslim.
Abinda Ya Shafi Falalar Sallah a
wannan masallacin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi) yana cewa;
((صَلاَةٌ فِي مَسْجِدِي هَذَا أَفْضَلُ مِنْ أَلْفِ صَلاَةٍ
فِيمَا سِوَاهُ
إِلاَّ اَلْمَسْجِدَ
اَلْحَرَامَ)) متفق عليه
''Yin Sallah a cikin
masallacin nan nawa ya fi salloli dubu a (masallacin) da ba shi ba in banda
masallacin harami (Makka)'' Bukhari da Muslim.
Lalle wannan ba karamar garabasa bace da
rahamar Allah ga bayinsa, kuma yana da kyau mu fahimci abubuwa kamar haka:
a.
Wannan ninkin ladan da abinda yafi dubu ba wai
ya takaitu da farilla bane banda nafila, ko ko nafila banda farilla, a'a ya
shafi duka, raka'a biyu ta farilla acikinsa ta fi raka'oi dubu na farilla a
inda ba shiba in banda haramin makkah, raka'a biyu ta nafila sun fi raka'o'i
dubu na nafila a inda ba nan ba.
b.
Wannan ladan bawai ya takaitu a iya inda
masallacin yake a lokacin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata
a gareshi) kawai bane ya shafi har fadadashin da aka yi ne.
c.
Sai dai duk wanda yabi sallah a wajan masallaci
yana da ladan jam'i amma baida wancan ladan da aka anbata domin a waje ya yi
sallah ba a ciki ba. Anan nake cewa irin sakacin da ake na a zauna a waje aita
fira ko aje a sayo kaya niki-niki jami'ai su hana a shiga masallaci da shi
mutum ya yi sallah a waje bakaramar asara bace.
d.
A cikin masallacin akwai wani wuri wato Raudha,
Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) a hadisin
Bukhari da Muslim ya siffanta wurin da cewa Dausayine daga cikin dausayin
aljanna. Kebance wannan wuri da irin wannan siffa lalle ya nuna falalarsa doruwa
akan sauran wuraren.
Abubuwan Yi A Birnin
Madina:
Lalle ilalla a yanzu kasan takaitaccan bayani dangane da birnin madaina falalar
birnin da ladubban zama a birnin. To yanzu idan Allah ya sa ka isa wannan birni
menene abinyi kada ka manta tafiyarka ba tafiyar bude ido bace. Saboda haka
babban abinda ya kaika shine ziyarar wannan masallaci da wannan Annabi
cikamakin Annabawa farin jakada ya gina da hannayanshi masu albarka, sabo
dahaka kada hankalinka ya dauku daga barin salloli da karatun alkur'ani da
zikiri a cikin wannan masallaci, domin duk ibadar da ka gudanar a cikin wannan
masallaci ladanta ya nin-ninka wacce aka yi a wajan wannan masallaci inbanda
masallaci Ka'abah.
Sannan yanzu bari a kawo abinda ake yi a
birnin madina:
Ibadu. Idan akace ibadu to
jam'ine na ibada ita kuma ibada
''Gamamman sunane da ya tara dukkan abinda Allah yake so kuma ya yarda
da shi na ayyuka ko na Magana na zahiri ko na baxini''
Yanzu munsan mecece ibada, kuma lura
da ta'arifin ta lalle munsan tanada nau'i daban-daban, kadan daga ciki sune:
(1) Ikhlasi: Yi domin Allah, kada ka kuskura ka yi wani aiki a wannan
birni mai tarin albarka wanda yake badon Allah ba ko Allah bai saka ba, lalle
mutum zai yi asara, ba'a lissafawa Allah ayyuka ko ayi mishi gori wadannan suna
lalata ayyuka.
(2) Salloli A Kan
Lokaci:
Lalle wanda ya sami kanshi a wannan birni mai albarka kada ya kuskura ya sake
da sallah, to yanzu wanda ya yi sake da sallah a inda aka saukar da sallar to a
inane ba zai yi sake da itaba, musamman a cikin wannan masallaci maitarin
albarka.
(3) Yawaita Karatun Alkur'ani: anan ba wai sai ka
haddace ba ko ka sauka a'a iya inda ka iya ka nace da karanta shi, wannan ba karamin
alkhairi bane.
(4) Yawaita Zikiri,
Istighfari, Salatin Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi)
Zikiran safe da na yamma, kada ka manta
saboda wadannan al'amura kabar kasarka, wurin aikinka, ka rufe shagonka kada
mutum ya yi wasa da wadannan ayyuka musamman a cikin wannan masallaci da ake
nunnunka ayyuka.
(5) Taimakon Juna: Lalle kada zuciyarmu ta
yi nesa da taimakawa juna abune mai mahimmanci tabangaren guzuri shawara nasiha
ga juna, zaburar da juna, neman …''
Wuraren Ziyara Da Takaitaccan
Tarihinsu:
Yana dakyau mu tsaya mu yi karatun ta-natsu a kan abinda ya shafi ziyara a
makka ko a madina kada harkar ziyara tasa ka rasa sallah a cikin wadannan
masallatai wadanda suke sune jigo uban-tafiya. Yanzu za'a lissafo wuraren
ziyara, kamar haka:
(1) Masallacin Ma'aikin
Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi). Wannan
masallaci ma'aikin Allah Ya sayi filin wurinne da kudinsa sannan ya aza
harsashin gininshi da hannayen sa masu albarka, masallacin ya zama nanne wurin
sallah nanne kuma makaranta inda yake karantarwa kuma ananne yake alqalanci (Tsira
da amincin Allah su tabbata a gareshi), anan yake tarbar baqinshi.
Yadda Ake Ziyara a wannan masallaci
shi ne, dazarar kun isa madina ankaiku masauki kowa ya aje kayansa sai a nufi
wannan masallaci maialbarka idan akaje sai afara gabatar da kafar dama lokacin
shiga, sai kai addu'a kace:
بِسْمِ اَللهِ،
وَالصَّلاَةُ وَالسَّلاَمُ عَلَى رَسُولِ اَللهِ، اَللَّهُمَّ اَفْتَحْ لِي
أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ
Sannan sai ka yi sallah
raka'a biyu, idan ka tarar ana farilla sai kabi ta wadatar maka, idan kuma ka
isa an idar da sallah sai ka yi
farillar.
(2) Kabarin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah
su tabbata a gareshi)
Da manyan sahabbanshi biyu: wadannan kabarurruka suna cikin dakin sayyida
Aisha ne –Allah ya kara mata yarda- kamar yadda kowa ya sani ne masallacin
ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) daban yake dakunan
iyalanshi ma daban suke wato gini ya rabasu, bayan da Allah ya karbi yaruwar
wannan Annabi mai daraja a dakin Sayyida Aisha sai aka yi masa kabari a dakin,
haka kuma wadannan manyan sahabbai nashi guda biyu wadanda zaka ji yana cewa na
kasance ni da Abubakar da Umar na yi
kaza ni da Abubakar da Umar, Allah ya kara musu daukaka da karamci da
kuma yarda, amin.
Yadda Ake Ziyara anan mutum zaizo
ta gaba sai ya fuskanci qabarin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi) sai yace:
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ يَا رَسُولَ
اَللهِ وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكَاتُهُ صَلَّى اَللهُ وَسَلَّمَ وَبَارَكَ
عَلَيْكَ، وَجَزَاكَ أَفْضَلَ مَا جَزَى نَبِيَّا عَنْ أُمَّتِهِ.
Ma'ana: Amincin Allah ya
tabbata a gareka ya ma'aikin Allah da rahamarsa da albarkarsa, Allah ya kara
maka salati da aminci da kuma albarka, ya sakanka maka da mafificin abinda ya
sakankawa wani Annabi dangane da al'ummarsa.
Mutum zai yi hakane ba
tare da daga murya ba, domin ba'a daga wa ma'aikin Allah (Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi) murya yana da rai ko bayan ya rasu, ka duba
Suratil-Hujrat aya ta (2-3).
Sannan sai ya dan yi
dama kadan sai yace:
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ
يَا أَبَا بَكْرِ اَلصِّدِّيقَ
Ma'ana: Amincin Allah
ya tabbata a gareka ya Abubakar maigaskiya.
sannan sai ya danyi dama
kadan, sai yace:
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ
يَا أَبَا حَفْصٍ عُمَرَ اَلْفَارُوقَ
Ma'ana: Amincin Allah
ya tabbata a gareka ya wannan gwarzo Umar.
Sai mutum ya yi musu
adda'a domin sun yiwa wannan addini hidima da duk abinda za su iya, Allah ya kara
musu daukaka.
(3) Makabartar Baki'a: ita wannan kushewa bata
da nisa da masallacin ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi) bai wuce taku kadan ba, itace babbar kushewar madina nan aka binne
su Nana Aisha da Nana Fafima da Sayyina Usman da manya-manyan sahabban ma'aikin
Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), nan kuma aka binne
su Imamu Malik, Allah ya kara musu yarda, amin.
Idan mutum yaje wannan makabarta zaicene :
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكُمْ
دَارَ قَوْمٍ مُؤْمِنِينَ وَإِنَّا إِنْ شَاءَ اَللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، يَغْفِرُ
اَللهُ لَنَا وَلَكُمْ
Ma'ana: Amincin Allah ya
tabbata a gareku ya mutanan wannan gida da suke muminai, muma in Allah ya yarda
munanan zamu tarar da ku, Allah ya gafartama ya gafarta muku.
(4) Shuhada'u Uhud: Kushewar shahidan Uhudu
kushewace dake dab da dutsan Uhudu, anan ne aka yiwa sahabban ma'aikin Allah wadanda
suka yi shahada a wannan yaki mai cike da darussa janaza, wanna a cikinsu akwai
Sayyidina Hamza wanda Allah yaba da labarinsa a cikin suratul Ali-Imrana.
Siffar yadda ake ziyara anan itace irin yadda
aka yi a baki'a, wato idan kaje makabartar sai kace:
اَلسَّلاَمُ عَلَيْكُمْ
دَارَ قَوْمٍ مُؤْمِنِينَ وَإِنَّا إِنْ شَاءَ اَللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، يَغْفِرُ
اَللهُ لَنَا وَلَكُمْ
Ma'ana: Amincin Allah ya
tabbata a gareku ya mutanan wannan gida da suke muminai, muma in Allah ya yarda
munanan zamu tarar da ku, Allah ya gafartama ya gafarta muku.
(5) Masallacin Kuba: Wannan shine masallacin
da ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya gina
kafin ya shiga birnin madina, domin ya yi kwanaki anan kafin ya shiga, anan ne
kuma ya yi sallar juma'a ta farko a
musulunci.
Falalar Masallacin Kuba: wannan
masallci yana da falala ta musamman da ma'aikin Allah (Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi) ya bayya, Abdullahi dan Umar (Allah ya kara
masa yarda) yace: ''Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi) ya kasance yana zuwa masallacin Kuba a duk ranar asabar wani
lokacin ya tafi a kafa wani lokacin kuma ya hau abin hawa sai ya yi sallah
raka'a biyu''
Bukhari da Muslim.
Hakanan ankarbo daga Sahal dan Hunaif (Allah
Ya kara masa yarda) yace Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi) yace:
''Duk wanda ya yi tsarki daga
gidanshi sannan ya je (masallacin) Kuba ya yi sallah a cikin shi to ya kasance
yana da ladan Umarah'' Ibnu Majah da
wasu suka ruwaito.
Wadannan sune wuraran ziyara shar'antattu su
biyar (5), biyu masallatai (Masallacin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi) da masallacin Kuba), uku makabartu.
Amma
akwai wasu wurare da mutane suke zuwa da sunan ziyara wadannan wurare sun kasu
kashi biyu:
(1)
Akwaishi A Tarihi: Kamar kiblatai, wannan
a kwai shi a tarihi sai dai masallacin da ake kira kiblataini a yau shine wanda
tarihin ya nuna ? to wannan malamai masana Sira da Tarihi sun karawa juna sani
akan haka.
(2)
Babu Shi A Tarihi: a kwai wuraren da suke
inda zaka karade littafai dakyar ka ji duriyarsu domin babu su, an same su ne a
zamanin wadansu dauloli da suka wuce.
Shawarwari:
Ni ina gabatar da nasiha ga 'yan-uwa kamar haka:
1.
Rikon abinda ya kaika.
2.
Kada ka dauki wannan tafiya a matsayin yawon bude
ido.
3.
Lizimtar Ibada a wadannan masallatai.
4.
Sanya lokacin ziyara ya kasance da safe, domin
kada ka rasa sallah a masallacin ma'aiki (Tsira da amincin Allah su tabbata
a gareshi).
5.
Kimanta lokaci.
6.
Abokantaka da wanda yake da himma.
7.
Barin shiga kasuwa sai an idar da sallar isha.
8.
Daraja wannan wuri domin Allah ya daraja shi
9.
Ba'a dawafi a madina domin a ka'aba kawai ake dawafi,
kamar yadda ya fada a Suratul-Hajj
Kira ga wannan gidauniya da ta ci gaba da gudanar da irin wannan bita,
da fatan Allah ya sanya mata albarka, ya kuma karbi ayyukammu.
وصلى الله وسلم على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu,
bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar
Neja Nijeriya.
Za'a iya
tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu
Muhammad Sadisu
www.youtube.com/Aliyu
M.Sadisu
Question about clipping nails during menses?
ReplyDeleteIs it permissible for a woman to clip her nails during menses?This is a matter concerning which many women are confused, namely the ruling on removing hair and nails and other Sunnahs of the fitrah during the menstrual period. This stems from a false belief that some of them have, that all parts of a person will come back to him on the Day of Resurrection, so if he removes them when he is in a state of major impurity due to janaabah, menses or post-partum bleeding, they will come back to him impure (naajis) and not purified (taahir) on the Day of Resurrection. This is a false notion and an illusion which is not correct at all.
AVG Internet Security key
ReplyDeletewebstorm crack Thanks for this post, I really found this very helpful. And blog about best time to post on cuber law is very useful.
ReplyDeleteutorrent pro crack Thanks for sharing such great information, I highly appreciate your hard-working skills which are quite beneficial for me.
ReplyDeletenordvpn-crack-full-version is pricing quite reasonably. Even when you're on a budget, then it is easily affordable. Certainly, NordVPN now offers the very best value available on the current marketplace, particularly if you're searching for lasting support using premium features.
ReplyDeletenew crack
Thanks for the post. Very interesting post. This is my first-time visit here. I found so many interesting stuff in your blog. Keep posting.. smartdraw-crack
ReplyDeletehttps://munbarin-musulunci.blogspot.com/2012/09/ziyara-birnin-madina.html?showComment=1538185281156#c8505397246213908888
ReplyDeleteadobe-creative-cloud-crack
ReplyDeleteThis design is wicked! You most certainly know how to keep a reader amused.
ReplyDeleteBetween your wit and your videos, I was almost moved to start my own blog (well, almost…HaHa!) Great job.
I really loved what you had to say, and more than that, how you presented it.
Too cool!
norton utilities activation code free
adguard serial key
araxis merge serial number
1click dvd copy pro free download
bitwig crack
Crack Like
Your hard work has not gone unnoticed. I and the entire senior management would like to congratulate you on doing a great job.
ReplyDeletekaspersky anti virus crack
norton internet security crack
zonealarm antivirus crack
Your website is fantastic. The colors and theme are fantastic.
ReplyDeleteAre you the one who created this website? Please respond as soon as possible because I'd like to start working on my project.
I'm starting my blog and I'm curious as to where you got this from or what theme you're using.
Thank you very much!
musicbrainz picard crack
pcdj dex crack
activatorsqlite expert personal
corelcad crack
Windows 7 Professional Crack creates more unequivocal photographs and makes games, video web based, and media altering smoother. You can likewise appreciate more clear, more excellent sound through the refreshed sound driver.
ReplyDeleteOutstanding Blog, Thanks for sharing this Amazing information. Very helpful for me. Asian Drama,
ReplyDeletepinstripe crack
jump king crack
The Settlers Crack
I guess I am the only one who came here to share my very own experience. Guess what
ReplyDeleteI am using my laptop for almost the past 2 years, but I had no idea of solving some basic issues.
I do not know how to Crackadvise Free Download But thankfully, I recently visited a website named Crackadvise.Crack
Corel VideoStudio Crack
SoftPerfect Network Scanner Crack
Aeesoft Buisrnova Crack
Nero Burning ROM Crack
VMware Fusion Pro Crack
Arclab Watermark Studio Crack
Nice article and explanation Keep continuing to write an article like this you may also check my website Crack Softwares Download We established Allywebsite in order to Create Long-Term Relationships with Our Community & Inspire Happiness and Positivity we been around since 2015 helping our people get more knowledge in building website so welcome aboard the ship.
ReplyDeletereloader-activator-crack
sparkol-videoscribe-crack
spotify-premium-crack
ReplyDeleteNice article and explanation Keep continuing to write an article like this you may also check my website Crack Softwares Download We established Allywebsite in order to Create Long-Term Relationships with Our Community & Inspire Happiness and Positivity we been around since 2015 helping our people get more knowledge in building website so welcome aboard the ship.
nova-launcher-prime-apk crack
rhinoceros-crack-license-keygen crack
sony-vegas-pro-crack